𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Mallam. Dan Allah tambaya ne gareni, Dan Allah idan ina jin yunwa Zan iya barin sallah na bari sai na ci abinci?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
A’a, ba daidai ba ne
mutum ya bar sallah saboda yunwa. Idan lokacin sallah ya yi, dole ne a yi ta a
kan lokaci, domin Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa:
ۚ اِنَّ
الصَّلٰوةَ كَانَتۡ عَلَى الۡمُؤۡمِنِيۡنَ كِتٰبًا مَّوۡقُوۡتًا
“Lalle ne sallah tana
kan muminai farilla a cikin lokuta ƙayyadaddu.”
(Suratun Nisa Aya ta 103).
Amma idan yunwa ta yi
tsanani sosai har ba za ka iya yin sallah da nutsuwa ba, sai ka ci abinci kaɗan don rage yunwa,
sannan ka yi sallah cikin nutsuwa, ana so mutum ya yi sallah cikin natsuwa ba
tare da hankalinsa ya rabu biyu ba.
Wannan uzuri ne na
barin sallar jam'i a masallaci ko jinkirta sallah zuwa wani dan lokaci. Amma ba
ya halatta ka cigaba da cin abinci har lokacin sallah gaba ɗaya ya fita.
Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Idan an kawo abinci, to ku fara cin abinci
kafin ku yi sallah, kuma kada ku yi sallah kuna jin yunwa.” (Bukhari da
Muslim).
Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ce: "Idan aka halartar da abincin dare, kuma aka
kaddamar da sallah, to ku fara da abincin dare." (Bukhari da Muslim).
Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ce: "Babu sallah a lokacin da abinci ya halarta (aka
ajiye shi), kuma babu sallah ga wanda yake tura abubuwa guda biyu masu kazanta
(fitsari ko bayan gida)." (Muslim).
Wannan yana nufin cewa
idan abinci yana gabanka kuma yunwa ta yi tsanani, za ka iya cin kaɗan domin samun
nutsuwa a cikin sallah. Amma ba wai ana barin sallah gaba ɗaya saboda yunwa ba
tare da dalili ba.
Sallah ita ce
ginshikin addini, kuma dole ne a yi ta a kowane hali. Ko da mutum yana cikin
tsananin rashin lafiya, matuƙar yana cikin hayyacinsa, dole ne ya
yi sallah, koda a zaune ne ko kwance.
Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ka yi sallah tsaye, idan ba za ka iya ba,
sai ka yi a zaune, idan ba za ka iya a zaune ba, sai ka yi kwance.” (Bukhari)
Haka nan, ko da ana
cikin yaƙi mai tsanani, dole ne a yi sallah. Allah (S.W.T) Ya
shar’anta yadda za a yi sallah a irin wannan yana yi, kamar yadda Ya ce:
فَاِنۡ
خِفۡتُمۡ فَرِجَالًا اَوۡ رُكۡبَانًا ۚ فَاِذَآ اَمِنۡتُمۡ فَاذۡکُرُوا اللّٰهَ
کَمَا عَلَّمَکُمۡ مَّا لَمۡ تَكُوۡنُوۡا تَعۡلَمُوۡنَ
“Idan kun kasance a
cikin tsoro (a fagen yaƙi), to ku yi sallah a ƙafa (cikin tafiya) ko
a kan doki. Amma idan kun sami lafiya, sai ku tuna Allah kamar yadda Ya koya
muku abin da ba ku sani ba.” (Suratun Baƙara Aya ta 239).
Idan ana iya yin
sallah a cikin yaƙi da tsananin rashin lafiya, to babu wani dalili da zai
sa mutum ya jinkirta sallah saboda yunwa.
Daga Karshe: Ko da
mutum yana cikin tsananin rashin lafiya, dole ne ya yi sallah a duk yadda zai
iya yi. Ko da ana cikin yaƙi ko wata matsananciyar rayuwa, dole
ayi sallah ko ta yaya ne. Ba a jinkirta sallah saboda yunwa, sai dai idan
yunwar ta yi tsanani har tana hana mutum nutsuwa, zai iya cin kaɗan kafin sallah.
Wajabcin sallah yana da ƙarfi fiye da buƙatar ciyarwa. Wannan
yana nuna cewa babu wani uzuri mai ƙarfi da zai hana
mutum yin sallah a kan lokaci, sai idan mutum ba ya cikin hayyacinsa
kwata-kwata.
Allah Ya bamu ikon
tsare sallolinmu a kan lokaci.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Zaku iya samun shafinmu ta wannan hanyar...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.