𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aassalamu alaikum Allah ya kara lafiya da nisan kwana. Malam tambaya na shi ne ni Ina aikin gwamnati mijina Kuma ba yayi Kuma kasuwanci mijina ba me karfi ba ne sai ya zamana duk wani bukatu da kamata ya mana ni da yarsa bayayi sai dai ni na yi, to malam yanzu har yake idan Yana da shi bayayi sai dai ya ce min bashi da kudi ko da kuwa Yana dashi, to malam tambaya a nan shi ne idan nasiya Abu na ci ko na tufatarwa na ci ko na dafa acikin gidansa ba tare da nabashi bah na ci nikadai bawani hakkin akai na bassalamu alaikum?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
A shari'ar Musulunci,
ciyarwa da shayarwa da tufatarwa da bayar da makwanci da ilmantarwa, mutuntawa,
da kiyaye mutuncin iyali wadannan kusan sune hakkokin da suka rataya akan
kowanne namiji alokacin da aka daura masa aure da mace.
Ba wajibi ba ne a kan
mace ta ciyar da mijinta ko ta ɗauki nauyin gidansa, ko da kuwa tana da kuɗi. Nauyin ciyarwa, tufatarwa,
da kuma kula da iyali yana kan miji ne shi kaɗai. Idan mace ta yi amfani da
dukiyarta ta ciyar da mijinta ko iyalinta saboda tausayi da taimako, tana samun
babban lada a wurin Allah (SWT). Amma hakan ba wajibi ba ne a kanta, aikin
sadaka ne ko taimako. Mace ba ta da laifi idan ta ki ciyar da mijinta, domin ba
a ɗora mata nauyin ba.
Ainihin nauyin ciyarwa da dawainiyar gida yana rataya ne a wuyan miji bisa
shari'a.
Idan miji ya gaza
saboda rashin lafiya ko talauci na gaske, za a yi hakuri tare da shi gwargwadon
yadda hali ya yi. Idan kuma ya ki yin aikin ciyarwa alhali yana da ikon yi ba
tare da wani uzuri ba, babban laifi ne kuma ya saɓawa umarnin Allah da ManzonSa.
Allah Yana cewa:
لِيُنۡفِقۡ ذُوۡ سَعَةٍ مِّنۡ سَعَتِهٖؕ وَمَنۡ قُدِرَ عَلَيۡهِ
رِزۡقُهٗ فَلۡيُنۡفِقۡ مِمَّاۤ اٰتٰٮهُ اللّٰهُؕ لَا يُكَلِّفُ اللّٰهُ نَفۡسًا
اِلَّا مَاۤ اٰتٰٮهَاؕ سَيَجۡعَلُ اللّٰهُ بَعۡدَ عُسۡرٍ يُّسۡرًا
"Sai mawadaci ya
ciyar daga wadatarsa kuma wanda aka ƙuntata masa arzikinsa,
to, sai ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi. Allah ba
Ya kallafa wa wani rai face abin da Ya ba shi. Allah zai sanya
sauƙi
a bayan tsanani. (Surah: At-Talaaƙ, Ayat: 7).
اَلرِّجَالُ قَوَّامُوۡنَ عَلَى النِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ
اللّٰهُ بَعۡضَهُمۡ عَلٰى بَعۡضٍ وَّبِمَاۤ اَنۡفَقُوۡا مِنۡ اَمۡوَالِهِمۡ...
Maza masu tsayuwa ne
a kan mata, saboda abin da Allah Ya fifita sashensu da shi a kan sashe kuma saboda
abin da suka ciyar daga dũkiyoyinsu... (Surah: An-Nisaa, Ayat: 34).
Wani Sahabi mai suna
Saya yiiduna Mu'awiyatul Kushairi (radhiyal-Lahu anhu) ya tambayi Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) dangane da hakkokin da matan aure suke dashi akan
mazajensu. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce masa : "Ka
ciyar da ita idan kaima kaci, Kuma ka tufatar da ita idan ka rufatar da kanka.
(Idan kuna fada da ita) Kada ka mari fuskarta, kada kayi mata wulakanci. Idan
har za ka kaurace nata, to kada ka aikata hakan sai a dakinta (wato kada ka
kaurace wa matarka sai acikin dakinta). (Abu Maajah da Abu Dawud ne suka
riwaitoshi).
Saboda haka idan kin
sayi abinci ko kaya da kuɗinki kika cinye ko
kika sa ba tare da kin ba mijinki ba ko kin nemi izininsa ba, babu laifi a
kanki kuma ba ki da wani zunubi, tunda ke ce da kuɗinki. Kuɗi ko dukiyar da kika
samu da gumin ki naki ne. Ba ki da wani laifi idan kin kashe shi a kan
abincinki ko suturarki.
WALLAHU A'ALAMU
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.