Article Citation: Abdullahi Lawal Dikko (2021). Fa’idar Harshe Ga Rayuwar Al’umma. DEGEL: The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, Vol. 19, No. 1. ISSN 0794-9316
FA’IDAR HARSHE GA RAYUWAR AL’UMMA
Na
Abdullahi Lawal Dikko
Tsakure
Maƙasudin wannan maƙala ita ce bayyanar da fa’idar harshe cikin rayuwar al’umma ta yau da kulum. Nazarin ya yi ƙoƙarin tabbatar da fa’idojin harshe a wajen zamantakewar al’umma da kasuwanci da al’adu da ilimi da karatu tare da yin sharhi a kan kowane da zayyana madogarar da za su iya samun gindin zama. A ƙarshe an ankarar da cewa lallai harshe na da matuƙar fa’ida ga jama’a kasancewarsa sinadari mai muhimmanci da Hausawa ke amfani da shi wajen gudanar da hulɗoɗi a tsakaninsu da juna, tare da sauran al’ummomi baki ɗaya a cikin zamantakewar yau da gobe.
Gabatarwa
Harshe abu ne da kowane al’umma ke tunƙaho da shi, babu tababa cikin wannan magana. Ana hasashen cewa duk wata al’umma dake rayuwa a cikin doron ƙasar nan tana alfahari da harshenta. Idan muka yi la’akari da halin zamantakewar ɗan Adam babu abun da zai iya gudana in babu taimakon harshe. Cuɗanya da musayar ra’ayi da harshe ake gudanar da su a cikin gida, da cikin unguwanni, da cikin gari dama ƙasa baki ɗaya. In kuwa haka ne zamantakewar al’umma na gudana ne tare da taimakon harshe. Hulɗa tsakanin ƙasa da ƙasa, harshe ne ginshiƙin samunsa nasararta.
Muhimman bayanai da ake amfani da su wajen gane fa’idar harshe su ne ta hanyar maganganun da al’umma ke yi da kuma irin fa’idar da suke amfana da ita. Don haka, kusan a ce fa’idar harshe abu ne mai yawa da matuƙar kima. Zai yi kyau a haskaka domin al’umma su ƙyallara idonsu a kai, ta yadda za su ɗauki harshensu da muhimmanci, tare da martaba shi da karramashi da kare shi ta kowane hali. Saboda haka, in ana son kwaliya ta biya kuɗin sabulu. Akwai fahimtar cewa lallai in aka kalli waɗannan jigogi da idon basira, wato zamantakewa da kasuwanci da al’adu da karatu da ilimi na addini ko zamani aka taskace su yadda ya dace. Muna sa ran za a cimma nasarar burin da ake nufi a cikin wannan maƙala.
Ayyukan Da suka Gabata
Lallai, masana da manazarta sun yi tsokaci mai yawa kan abin da ya shafi harshe kuma sun yi bayyana da dama a kai. Alal-misali Yakasai (2004:100) ya ce: “Amfani da harshe ya wuce dogaro ga sanin harshe har na mai magana, wato ya ƙunshi har da bayanin mai magana da suka haɗa da yadda za ta sarrafa harshe cikin dangantaka.” Amma a ra’ayin Shehu (2012:46) yana ganin cewa: “Harshe tamkar takobi ne mai kaifi biyu, ko kuma tamkar birgimar hankaka ne, kowa ya ga farinsa zai ga baƙinsa. Da harshe ake gini haka ma rusawa”. Bugu da ƙari, a ganin Ɗantumbishi (2005:70) zamananci na da alaƙa da magana, kuma muhimmancin harshe a jama’a ya ƙunshi:
1. Sadarwa
2. Musayar ra’ayoyi
3. Bunƙasa al’adu da tattalin arziki.
4. Tabbacin kariya ga harshen ta fuskar amfani da shi domin hana
mutuwa.
5. Cewa ba zamu iya magana ba sai da shi.
Bugu da ƙari, Yakasai (2005), ya tattauna a kan matsayin harsunan ‘yan tsiraru ga abin da yake cewa: “Za a iya inganta ko haɓaka ɗorewar harsuna ‘yan tsirarru ta waɗannan hanyoyi, musamman ma idan aka yi la’akari da cewe “kyakkyawan aikin fasalta harsuna hanya ce, mafi dacewa ta tabbatar da ɗorewar rayuwa”.
Harshe
Wannan fage ne da ya ƙunshi yadda ake zaɓen kalmomi a lallasa su ta yadda za a sami ingantaccen zance mai ɗauke da ma’ana. Saboda haka, ana amfani da harshe ne domin cimma duk wata nasarar magana mai ma’ana. Sakamon haka ana iya ɗaukan harshe a matsayin hanyar sadarwa a cikin al’umma. Babban abin la’akari shi ne kowace al’umma ta duniya tana da harshenta na musamman da take amfani da shi domin gudanar da harkokinta a tsakaninta da jama’a, wannan kuwa ya haɗa da kasuwanci da karatu da rubutu da al’amuran da suka shafi mulki da sauransu. Dangane da amfani da harshe a wajen muhallin magana ga abin da Yakasai (2010:78) ke cewa:
Saboda haka, duk lokacin da mutum zai zai yi zance ko hira, magana ko taɗi, ko kuma yake bayar da umurni to akwai abubuwa guda uku da sukan zo cikin zuciyarsa:
1. Darajar mai saurare a idanunsa (wato a idanun mai bayar da
labarin).
2. Abin da ake magana/hirar/taɗin ko zancen a kansa.
3. Wurin da ake gudanar da hulɗoɗin (duba Gadanya ).
Sauran maganar ita ce ta ƙara tabbacin cewa kowane taɗi yana da zubi da tsari wato ba haka nan yake kara zube ba. Hasali ma, su waɗannan taɗin (ko hirar) ya shafe su suna da hanya ta gabatarwa (farawa/buɗewa) ɗorewa da kuma kammala taɗin ko hirar.
Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da harshe. Wannan ya sa aka ga ya dace a bayyana ra’ayoyinsu domin kwaliya ta biya kuɗin sabulu. Daga ciki akwai (Yakasai 2004) da kuma Muhammad (2006) da kuma Amfani (2012). Yakasai (2004:9), Ya kalli ala’ada ta fuska biyu ne a rayuwar al’umma, musamman ya yi la’akari da Bahaushe ta fuskar amfani da harshe. Ya ce: “da yake al’adun mutum na gargajiya sukan bayyana wani abu game da shi in da zai magana da kuma yadda zai yi maganar), to bahaushe ya ɗauki duniyarsa ya kasa zuwa gida biyu dangabe da rayuwa, wato namiji da mace saboda haka, ga rayuwar bahaushe, duk yadda yake ganin rayuwar duniya to haka nan furucinsu yake. A taƙaice dai, manɗiƙin harshe da al’adarsa su ne ke zama jigon da za a yi amfani da shi wajen samun kalmomin magana. Muhammad (2006:2), ya nazarin harshe ta fuskar tunani a rayuwar ɗan Adam. ya bayyana cewa: “Harshe shi ne maƙunshin tunanin ɗan Adam, ke nan hulɗa ba za ta kammalu ba tsakanin mutane sai da amfani da harshe. Hasali ma dai, harshe shi ne babbar hanyar ilimantarwa da sanarwa, ba tsakanin mutum da mutum ɗan uwansa kawai ba; har ma tsakanin ubangiji mahallacin kowa da kome da mu bayinsa. Matsayin harshe a fagen ilmantarwa a fili yake in mun yi la’akari da yadda Allah (S.W.T) ya ce (a aya ta 33 -33 ta surar baƙara), cewa shi (Ubangiji) Ya sanar da Adam sunayen (abubuwa) dukkansu, sannan ya bijirar da su abubuwan ga mala’iku, ya ce su faɗi masa sunayen abubuwan amma suka kasa… ”. Shi kuwa Amfani (2012:9), ya jawo hankali kan tabbatar da ci gaban ɗaurewar harshe. ya ce: “Don tabbatar da cigaban harshe Hausa, tilas ne Hausawa su matsa ƙwarai wajen nazarin harshen da kuma amfani da shi. A halin da ake ciki yanzu Hausa ta na gurɓata a hankali, zuwa gaba, ba mamaki gurɓacewar ta wuce gona da iri. Ana nazari Hausa a ƙanana da manyan makarantu amma yawar almajiran da ake yayewa a manyan makarantu bai kai kallo ba.”
Zamantakewa
Babban abin lura a wannan ɓangare shi ne hulɗa ko mu’amala da ‘yan uwa na kusa ko nesa da abokanin sana’a da makwaɓta, ba su inganta sai an sami fa’idantuwa da harshe. Abin tambayar a nan ita ce ta yaya ne za a iya fa’idantuwa? Manufa sai al’umma sun kasance masu la’akari ko yin amfani da harshe yadda ya dace.
Harshe na da alaƙa ta ƙud-da ƙud da rukunin jama’a ko ƙungiyoyin al’umma, sanin kowa ne babu yadda za a yi a zauna wuri guda ba tare da an gudanar da hulɗoɗi ba tun da Allah (SWT) ya bai wa ɗan Adam baki, ya sanya masa harshe wanda da taimakonsa ne ake jujjuya shi a yi magana, maganar kuma ta zama mai amfani a cikin al’umma. Sakamakon haka, za a iya tantance ɗa da uba da mata da ‘ya ko ɗa. A duk inda aka sani a zamantakewar jama’a, ana iya cewa wane shi ne shugaba ko jagora, amma inda al’amura ke tafiya yadda ya kamata. Sa’annan har wa yau ana iya tantance mai unguwa ko hakimi, sarki da shugaban karanmar hukuma, har zuwa shugaban ƙasa. Lallai duk waɗannan al’amura da taimakon harshe ne kawai aka iya babbance su, kuma a san nauyin dake bisa kan kowa.
A zahirance muna ganin wajen zamantakewar al’umma harshe na taka rawa domin sai an haɗa sauti, sa’ananan a sami kalmomi har ya zuwa jumloli idan ana son isar da saƙo yadda ya kamata. Da wannan ne ma Ɓabura (2008:2) ke cewa: “Harshe hanyar isar da saƙo ce ta musamman ba kamar yadda dabbobi kan yi amfani da sauti idan za su isar da saƙo ba, alal-misali; kare da mage duk inda suke a duniya sautin da suke fitarwa saboda isar da wani saƙo na iri ɗaya ne.” Amma shi ɗan Adam sauti da yake fitarwa don isar da saƙo na musamman. Yakan zama ƙeɓaɓɓe daga al’umma zuwa al’umma a ko’ina a nan duniya”. Sakamakon wannan batu za mu iske cewa a cikin zamantakewar al’ummar duniya kowane mutum na da keɓaɓɓiyar hanyar isar da saƙo ga ‘yan uwansa da kuma sauran alu’mma. Wani lokaci dole a koyi wasu harsuna domin cimma nasarar hulɗoɗi.
Kasuwanci
Dangane da fa’idar harshe a wajen jama’a in ana batun kasuwanci abu ne mai muhimmanci domin babu yadda kasuwanci zai gudana in babu taimakon harshe. Sa’annan wani abin da ya kamata mu lura a nan shi ne, kasuwanci nan dole ne ya tafi da tattalin arziki, saboda kamar ɗan juma ne da ɗan jummai. Auta (2006:194) ya faɗi:
“Idan muka ɗauka Kalmar kasuwanci kuwa ana cewa “wane hamshaƙin ɗan kasuwa ne” ko kuma wane ya iya kasuwanci” ko kuma a ce yau “Kasuwa ba ta yi kyau ba” da sauransu. Duk dai ana danganta abin ne da harkar saye da sayarwa, da karɓuwar abin ko akasin haka.
Saboda haka, albarkatun ƙasa da jujjuya su yadda ya dace da zamani, da kuma harkokin kasuwanci a hannun jama’a da sarrafa shi yadda ya dace domin samun bunƙasar al’umma na buƙatar yin amfani da harshe ta yadda kowa zai fahimci abin da ake nufi. In ko ba haka ba aƙalla dole mutum ya nemi tafinta, wanda zai taimaka a cimma gaci.
Idan tattalin arzikin ƙasa ya bunƙasa to, jama’ar ƙasan za su sami aiwatar da sana’o’i masu yawa, kamfanoni kuma za su yalwatu. Sanadiyyar haka, al’ummarta za su haɗu wuri guda, wannan zai haifar da samun wani karɓaɓɓen harshe da za a rinƙa magana da shi. A nan, an sami bunƙasar harshe guda, kuma ya taimaka wajen biyan buƙatar da ake nema a kan harkokin kasuwanci da sana’o’i, wanda yana ɗaya daga cikin ginshiƙan ci gaban rayuwar al’umma.
Al’adu
Gusau (2013:358) ya bayyana cewa; “kowace al’umma a duniya tana da wasu al’adu waɗanda takan keɓanta da su, kuma take tanada wa kanta lokaci bayan lokaci. Al’adun al’umma sukan zama daɗaɗɗu ko kuma sababbi kuma irin waɗannnan al’adu ne sukan kasance alƙibla na al’umma waɗanda ake sanin ta da su, ake rarrabe ta da su, ake fahimatar ta da su, kuma ake kiyaye mutuncinta da su. Haka kuma su ne, suke zama shari’ar al’umma, a dinga kaɗa wa al’umma take da suda kuma an ganosu a nuna wa al’umma kaza ne.” Alal misali, Masar ba a fahimci akwai tsohuwa da sabuwa ba sai ta fuskancir gane al’adu daɗaɗɗu da sababbi. A tsohuwar masar aka yi Fir’aunoni da suka yi gine-gine ta yanayin dala, kuma suka zama masu ƙawata duwatsu da zane-zane masu kayan yaki na gargajiya da sauransu.
Bugu da ƙari, ta fuskar abin da ya danganci sababbin al’adu ko kuma mu ce abubuwan zamani ya haifar cigaba. Harshe kan taimaka wajen yin mu su jagora da yin saiti ta yadda za su amfanar da al’umma kuma su zama abin alfahari ga rayuwar al’umma. A nan in mun duba da kyau za mu ga cewa harshe a matsayinsa na mabaɗin al’ada kan dubi al’ada da idon basira, sannan ya zaƙulo da wasu sabbabin kalamomi da suka da ce da shi. Misali kalmomi da ‘yan siyasa kan amfani da su a wajen laccoci da sukan shirya, ko kuma kalmomi na saye wadda mata su ka fi yi. Haka kuma ‘yan jaridu kan samar da wasu kalmomi na musamman da kan jawo hankalin masu sauraro, misali shirin ‘An ce ka ce’ na rediyo Nargarta da ke Kaduna, da makamantarsu. Saboda haka, idan aka yi duba da kyau a ga suna nuni da al’adun tare da samar da ƙirƙirarun kalmomi. Sa’annan a kan sami sababbin karin magana na harsuna daban-daban.
Ga al’ada a da, maza ke zuwa neman aure, mata su kan kai kayan lefe, amma yanzu wasu al’ammurar sun canza. Wata ƙila addini ne ya kawo haka, wataƙila kuma neman sauƙi da sauyen yanayin rayuwar al’aumma. Yanzu a ƙasar Hausa kusan maza ke kai kayan lefe ba mata ba, kamar yadda aka sani. Saboda haka, harshen a da matuƙar fa’ida wajen gudanar da duk zantukan da ake yi a rayuwar yau da gobe ta fuskar al’ada.
Muhimman bayanai da ake amfani da su na fa’idar harshe shi ne ta yadda za a taskace al’adun al’umma daɗaɗɗu da sababbi wannan al’amari ne da ake fahimtarsa ta hanyar tarihi, da ta hanyar kunne ya girmi kaka, (wato da ka,) ko kuwa rubutacce. Ko ma wanne ne muka ɗauka a ciki dole ne harshe ya taka rawa domin da bazarsa ne ake tunƙaho. Duk wani abin da za a faɗi ko rubuta game da al’adu harshe ne za a yi amfani da shi.
Sa’annan wani abin lura shi ne ana iya tantance al’ummomi daban-daban da tadodinsu ta hanyar al’adunsu a da da yanzu, haka kuma, ana la’akari da gine-ginensu, da sauran alamomi da aka zayyana a duwatsu da makamantansu.
Harshen Karatu
A ɓangaren karatu, wannan bincike yana ganin ko ba ace ba, an lallai, harkar karatu abu ne mai fa’idantar da al’umma a cikin rayuwar yau da kulum, kuma ginshiƙi ne wanda ke da madogari mai albarka ga al’umma, Bunza (2013:205) ya tofa albarkacin bakinsa dangane da karatu ga kuma abin da yake faɗi:
Don me ake karatun harshe? Sanin cewa, masana sun yi wa harshe tarkakken nazarin da ɗalibi zai ratsa ya sami waraka ga bayanin harshe ko ilimin harsuna, ba ana nufin Hausa ba harshe ba ne buƙata ita ce, ƙyallaro dalilan da zai sa mai harshe, ya nazarci harshensa ko ya nazarci wani harshe a matsayin fagen karatu da neman shahara a ciki.
Saboda haka, mun fahimci cewa nazarin harshe abu ne da ya zama wajibi ga duk wani mai karatu a wannan ɓangare in an yi waiwaye a baya za mu ga cewa, Annabi Muhammad (S.A.W) farkon ayar da ubangiji Allah ta’ala ya sanar da shi ita ce Iqra’a “wato ka yi karatu.” Ashe in haka ne, karatu abu ne mai fa’ida ga al’umma, kuma wannan karatu bai taɓa gudana sai da harshen da za a yi magana da shi. Sa’annan harshe na ɗaya daga cikin sinadaran da kowace al’umma ta duniya ke buƙata yin amfan da shi wajen karantar da al’ummarsu, muhimman al’amuran da suka jiɓanci rayuwa, ta fuskar addini. Da dukkan sauran abubuwan da suka shafi kimiyya da harkokin yau da gobe da taimakon karatu da rubutu ake cimma nasararsu.
Ilimi
A wannan ɓangaren wasu za su iya tambayar bambanta karatu da ilimi? Manufar a nan, ita ce a fayyace muhimmancin karatu da fa’idarsa ga harshe. Sannan kuma a ƙyallaro abin da ya danganci ilimi shi ma a iya taskace shi. Duk da yake a wajen wasu masana suna ɗaukansu abu guda ne. Ɗantumbishi (2012:38) yana cewa:
Mai ilimi na nufin masani. Ilimi ya shafi karatu da rubutu wannan ya nuna cewa yana da alaƙa da magana ɗan Adam ne kawai yake yin magana; wadda sai an yi tunani domin ta samu tsari da ma’ana ilimi ke bambanta mutum da dabba, ya bai wa mutum ‘yanci, haka kuma shi ne ke kawo ci gaba ga kowace al’umma da ƙasa.
Ashe in ko wannan batu nasa haka ne dangane da ilimi, sai an iya karatu da rubutu sannan ilimi ya samu ga al’umma, ilimi ginshiƙi ne ga rayuwar kowace al’umma. Babu wata al’umma da za ta ci gaba in ba su da ilimi. Masu ilimi suke tafiyar da harkokin gwabnati, masu ilimi suke nuna fasaharsu da basirarsu ga duk wani al’amari da zai bunƙasa rayuwar jama’a ta fuskar masanan’atu, da kamfanoni da sauran al’amuran da suka shafi ilimin kimiyya da fasaha.
Wani abin ban sha’awa shi ne ba wai sai wanda ya iya karatu da rubutu ne kawai zai zama mai ilimi ba, wani lokaci a kan sami mutum ko wasu cikin al’umma da Allah (SWT) kan yassare masu wata hikima da basira a wani fage na musamman ya zama sun yi fice a wannnan fage, ta haka za a ce suna da ilimin abin. A nan ne sai kuma aga cewa: harshe suke amafani da shi wajen cuɗanya da al’umma ko waɗanda suke yin hulɗoɗin da su. Saboda harshe na da fa’ida sosai a wajen ilimi da aiki da shi da kuma ilimatarwa.
Kammalawa
A taƙaice ana iya bugun ƙirji a ce fa’idar harshe ga rayuwar al’umma abu ne mai matuƙar kima da daraja da kuma kwarjini. Bisa ga irin nasarorin da ake samu a rayuwar al’umma. Kasancewar harshe shi ne sinadarin inganta duk wata mu’amula a rayuwar al’umma.
A wannan maƙala an yi ƙoƙarin haskaka maganganun da suka shafi harshe daga bakin masana tare da jin ra’ayoyinsu . A cikin nazarin da aka yi an yi ƙoƙarin bayyana zamankewar al’umma ta hanyar zayyana fa’idar harshe sannan kuma an kalli kasuwanci da kuma irin rawar da harshe kan taimaka wajen gudanar da kasuwanci ga al’umma.
An kuma nazarci harshen karatu da ilimi a rayuwar al’umma da gudunmuwar hashe a kansu. A ƙarshe mun fahimci cewa harshe na da matuƙar tasiri ga rayuwar al’umma ta kowace fuska.
Manazarta
Amfani, A.H (2012) Hausa da Hausawa jiya da yau Da Gobe Champion of Hausa Cikin Hausa A Festdirift in Honour of Dalhatu Muhammad. Ahmadu Bello University, Zaria.
Auta, A. L (2006) Tattalin Arzikin Al’umma: Nazarin Sana’o’i da Kasuwacin Hausa. Algaita Journal of current Research in Hausa Studies No.4 Vol. 1 Department of Nigeria Langauge, Kano: Bayero University.
Bunza, A.M (2013) Don me ake karantun Hausa? Harsunana Nijeriya Volume XXIII 2011-2013. Special Edition Centre for the study of Nigeria Language Kano-Nigeria: Bayero University.
Ɓabura, H.S (2008) Hausa A Hausa, Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies N05, Vol. 1 Department of Nigeria Langauge, Kano: Bayero University.
Ɗantumbishi, M.A (2005) Harshe, Al’umma Da kuma Zamananci: Ɗunɗaye Journal of current Research in Hausa Vol. 1 No. 2 Department of Nigeria Language Sokoto: Usman Ɗanfodiyio.
Ɗantumbishi, M.A (2012) Tasirin Harshe Da ilimi Da Addini Da Al’ada Ga Rayuwar Al’ummar Hausawa. Champion of Hausa cikin Hausa. A Fetshirif in Honour of Ɗalhatu Muhummad Department of African Languages and Cultures. Zaria: Ahmadu Bello University.
Gusau, S.M (2013) Tsokaci kan al’adun Hausawa Harsunan Nigeria Volume XXIII special Edition. Centre for the study of Nigerian Language, Kano- Nigeria: Bayero University.
Muhammad, D. (2006) Takanin Hamada Da Hamdala Waiwayen Gudummuwar Jami’o’Da Haɓaka Harshe Hausa. Algaita Journal of current Research in Hausa Studies No.4, Vol. 1 2006. Depertment of Nigeria Language Kano: Bayero University.
Shehu I. (2012) Siyasar Harshe Da Harshen Siyasa A Nijeriy: Tsokaci kan Hausa Champion of Hausa Cikin Hausa A Festsehrit in Honour of Dalhatu Muhammad. Department of Afrucan Languages and cultures, Zaria: Ahmadu Bello University.
Yakasai: S.A (2004) Sadarwa Tsakanin Maza Da Mata: Nazarin Dangantarkar Harshe Da Daidaituwar Jinsi. Harshe Da Daidaituwar jinsi Algaita Journal of current Research in Hausa Studies No. 3 Vol. 1 Department of Nigeria Language, Kano: Bayero University.
Yakasai, A.S (2005) Matsayin Harshe ‘yan tsiraru A cikin Ɗangantakar al’umma. Ɗundaye Journal of Hausa Studies Vol 1 No.2 Department of Nigeria Language Sokoto: Usman Ɗanfofiyo University.
Yakasai S.A (2010) Ɗangatakar Harshe Da Muhallin Magana: Nazari kan matakan magana a Tsakanin Hausawa. Harsunan Nijeriya valume XXII. Centre for the study of Nigerian Languages. Kano – Nigeria: Bayero University.
The official website of the DEGEL Jounal is https://www.degeljournal.com

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.