Ticker

6/recent/ticker-posts

Ceton Kananan Yara Ga Iyayensu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Mallam Shin da gaske ne yara kanana da suka rasu za su yi ceton iyayensu?

CETON ƘANANAN YARA GA IYAYENSU

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Eh, tabbas akwai hujjoji daga Sahihancin Hadisan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ke nuni da cewa lallai akwai ladaddaki da darajoji masu yawa da muminai suke samu, yayin da kananan yaransu suka rasu a lokacin kuruciya kuma suka yi haƙuri suka jure. Yaran da suka rasu suna da matsayi babba a wurin Allah, kuma za su zama masu ceton iyayensu a ranar kiyama matukar iyayensu sun yi hakuri da rashinsu. Wannan alama ce ta rahamar Allah da kuma falalar sa ga iyaye masu hakuri da juriya a kan rashin jariransu.

Imamu Muslim sun ruwaito ta hanyar Sayyiduna Abu sa'eed Alkhudriy (radhiyal-Lahu anhu) wanda ya ce Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya gaya ma wasu mata cewa : "duk matar da 'ya'yanta uku suka rasu, to zasu zama kariya gareta daga shiga wuta". Sai wata mata ta ce :"Ya Rasulallahi guda biyu fa". Sai ya ce "koda guda biyun ne".

Imamut Tirmidhy ya ruwaito ta hanyar Abu Sinan daga Sayyiduna Abu Musal Ash'ariy (radhiyal-Lahu anhu) shi kuma daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) wanda a cikin hadisin ya ce Allah zai umurci Mala'iku su gina wa mutum wani gida na musamman a cikin Aljannah, saboda hakurinsa bisa rasuwar 'dansa ko 'yarsa.

A cikin wani hadisin kuma wanda Imamu Muslim ya riwaito, (hadisi mai lamba 2,635) wani mutum ya zo wajen Sayyiduna Abu Hurairah (radhiyal-Lahu anhu) ya ce masa "Ya Aba Hurairah, hakika 'ya'yana guda biyu sun rasu. Ina so ka gaya mun wani hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) wanda zai hakurkurtar damu". Sai Abu Hurairah ya ce masa "Ai Kananan yaransu, sune Ƙananan yaran gidan Aljannah. Idan dayan cikinsu ya haɗu da mahaifinsa ko mahaifansa (afilin Alƙiyamah) zai rike hannunsa ne kamar yadda nake rike da hannunka ɗin nan, bazai sakeshi ba har sai Allah ya shigar dashi da mahaifin nasa gidan aljannah.".

Sannan Imam Ibnu Ƙayyimil Jauziyyah a cikin littafinsa Tuhfatul Maudud akan shafi na 69 yana magana game da fa'idodin da ke cikin yi wa yaro yankan suna (AƘIƘAH), akan lamba ta biyu, ya ce : "Ita Aƙiƙah fansa ce ga yaron da aka haifa. 'Aƙiƙarsa za ta fanshe shi a ranar Alƙiyama, domin ya je ya yi ceto ga mahaifansa'."

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Na rantse da wanda rai na yake hannun sa, Lallai jaririn da ya zube (cikin da ya zube), zai jawo uwar sa da igiyar cibiyar sa zuwa Aljanna idan ta yi hakuri saboda shi (Allah)" (صحيح إبن ماجه 1316).

Yaran za su tsaya a kofar Aljanna su ki shiga. Za'a ce Yaran su shiga Aljanna, sai su ce ba za su shiga ba sai iyayensu sun shiga tare da su. Za su rika jan iyayensu da tufafinsu ko hannayensu har sai Allah ya shigar da su Aljanna saboda falalar hakurin da iyayensu suka yi.

Dole iyayen su nuna hakuri da juriya tare da fadin "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" lokacin da rashin ya faru. Suyi tawakkali Su yarda cewa Allah ne ya ba su kuma shi ya karbi abinsa a lokacin da ya so.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments