𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahmatullah bayan gaisuwa irinta addinin Musulunci ina yi wa malam fatan alkhaeri! Malam tambaya na ita ce idan ran mutam yana yawan ɓaci wace addu'a ce zai yi ya ji ransa yabar ɓaci.
ADDU’AR DA ZA A YI
DOMIN SAMUN NATSUWAR ZUCIYA DA RASHIN ƁACIN RAI:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam
warahmatullahi wabarakatuhu.
Idan mutum yana yawan
jin ɓacin rai, fushi ko
damuwa, yana da kyau ya yawaita zikiri da addu'o'in da Annabi (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya koyar damu.
Ibn Mas'ud Allah ya ƙara masa yarda ya ce:
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Wata damuwa ko baƙin ciki ba sa taɓa samun mutumin da ya
karanta wannan addu'ar, face Allah ya tafiyar masa da wannan damuwa da baƙin ciki, kuma ya
canja masa da kwaranyewar damuwar:
"اللَّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ
وَابْنُ عَبْدِكَ وَابْنُ أَمَتِكَ ، نَاصِيَتِي بِيَدِكَ ، مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ
، عَدْلٌ فِيَّ قَضَاؤُكَ ، أَسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ ، سَمَّيْتَ بِهِ
نَفْسَكَ ، أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَدًا مِنْ خَلْقِكَ ، أَوْ أَنْزَلْتَهُ فِي
كِتَابِكَ ، أَوْ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ : أَنْ
تَجْعَلَ الْقُرْآنَ رَبِيعَ قَلْبِي ، وَنُورَ صَدْرِي ، وَجِلَاءَ حُزْنِي ،
وَذَهَابَ هَمِّي ؛ إِلَّا أَذْهَبَ اللَّهُ هَمَّهُ وَحُزْنَهُ ، وَأَبْدَلَهُ
مَكَانَهُ فَرَجًا".
"Ya Allah ni
bawanka ne, ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka, makwarkwaɗata (maɗigata) a hannunka
take, hukuncinka zartacce ne a kaina, kuma ƙaddararka a gare ni
mai adalci ne, ina roƙonka da dukkan sunayenka, wanda ka ambaci kanka da shi, ko
ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka sanar da shi ga wani daga cikin
halittarka, ko ka keɓance kanka da saninsa
a cikin ilimin fake (gaibu) da ke wurinka, ka sanya Alƙur'ani ya zama daɗi ga zuciyata, ya
zama haske ga ƙirjina, ya zama kwaranyewa ga baƙin cikina, ya zama
mai tafiyar da damuwata".
A ƙarshen hadisin an
ruwaito cewa Sahabbai sun tambayi Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam)
cewa; shin ba ma koyi wannan addu'ar ba? Sai ya ce: "Tabbas, ya kamata
wanda ya ji addu'ar nan ya koye ta"". Musnadu Ahmad (3712), Sahihu
Ibn Hibban (972).
An ruwaito daga Abu
Bakrah cewa Manzon Allah (tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi) ya ce
addu'ar wanda ya shiga mawuyacin hali ita ce:
ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺭَﺣْﻤَﺘَﻚَ ﺃَﺭْﺟُﻮ ، ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻜِﻠْﻨِﻲ ﺇِﻟَﻰ ﻧَﻔْﺴِﻲ ﻃَﺮْﻓَﺔَ
ﻋَﻴْﻦٍ ، ﻭَﺃَﺻْﻠِﺢْ ﻟِﻲﺷَﺄْﻧِﻲ ﻛُﻠَّﻪُ ، ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺃَﻧْﺖ
"Ya Allah!
RahamarKa nake fata, kada Ka bar ni da kaina ko da da sakan guda (da idanuwa
suka lumshe), kuma Ka gyara mini dukkan lamurana, babu abin bautawa da gaskiya
sai Kai." [Abu Dawood (5090), Ahmad (27898)].
An ruwaito daga Ɗan Abbas cewa Manzon
Allah (tsira da amincin Alllah su tabbata a garshi) ya kasance yana yin wannan
addu'ar alokacinda ya ji kansa a yana yin damuwa:
ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢُ
ﺍﻟْﺤَﻠِﻴﻢُ ، ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺭَﺏُّ ﺍﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺍﻟْﻌَﻈِﻴﻢِ ، ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻟَّﺎ
ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺭَﺏُّ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺭَﺏُّ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻭَﺭَﺏُّ ﺍﻟْﻌَﺮْﺵِ ﺍﻟْﻜَﺮِﻳﻢ
"Babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah, Mai Girma, Mai Hakuri. Babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah, Ubangijin Arshi Mai Girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah, Ubangijin sammai da Ubangijin kasa da Ubangijin Arshi mai daraja.
[ Muslim (2730) ].
Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya cewa Asma'u bntu Umais R.A: Shin bazan koya
maki ba wata addu'a da za ki karantata alokacin damuwa da bakin-ciki, ko
lokacin kuncin rayuwa?? Kice:
ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺭﺑِّﻲ ﻻَ ﺃﺷﺮِﻙُ
ﺑِﻪِ ﺷﻴﺌًﺎ
"Allah, Allah
shi ne Ubangijina, ban yin taraya yia da shi da kowane abu (ban saɓa masa ko haɗa shi da wani a
bauta)."
Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: Adduar zinnun lokacin da ya roki Allah
yana cikin kifi:
لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ
الظَّالِمِينَ
"Babu abin
bautawa da gaskiya sai Kai, tsarki ya tabbata a Gare Ka, lalle ne ni na kasance
daga cikin masu zaluntar kainu."
«اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ
الْهَمِّ وَالْحَزَنِ»
“Ya
Allah, ina neman tsarinka daga damuwa da baƙin ciki.”
Haka kuma idan fushi
ya taso, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya koyar da damu cewa mutum ya ce:
«أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ
الرَّجِيمِ»
"Ina neman
tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefarwa.”
Ya kuma dace mutum ya
yi shiru, ya canza matsayinsa idan yana tsaye ya zauna, ko ya yi alwala. Allah
Maɗaukaki Ya ce:
أَلَا بِذِكْرِ اللَّهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ
“Ku saurara! Da ambaton Allah zukata suke
samun natsuwa.” (Ar-Ra'ad: 28).
To ire-iren wadannan
addu'o'in waɗanda suka tabbata
daga Annabi (sallalahu alaihi wasallam) sune ake son Musulmi ya lazimci yinsu a
duk lokacinda ya tsinci kanshi a cikin wani mawuyacin hali, bakin ciki, masifa
ko damuwa.
Saboda haka shawaran
dazan baka shi ne ka yawaita istigfari da salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi
Wasallam), karatun Alƙur'ani da wannan addu'a, tare da yin haƙuri in sha Allahu duk
wani ɓacin rai Allah zai
cire maka shi. Allah Ya sanya maka natsuwa a zuciya, Ya kawar maka da dukkan
damuwa da baƙin ciki damu baƙi daya.🤲
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.