Ticker

6/recent/ticker-posts

Mukaddimar Littafin Sunayen Hausawa

Muƙaddima

Turƙashi! Lallai, Sunayen Hausawa! Tabbas wannan katafaren littafi ne, “sabulun salo amfaninka dubu” wanda ya zo a lokacin da ake buƙatar irinsa. Haka kuma, wanda aka rubuta shi tare da ɗora shi bisa ingantaccen bincike da nazarce-nazarcen wasu bayanai, waɗanda wasu manyan masana magabata suka samar aka adana, waɗanda kuma suka shafi rayuwa da sunayen Hausawa baki ɗaya, har ma da wasu maƙwaftan Hausawa. Waɗannan maƙwafta sun haɗa da Al’ummar Fulani, da Kanuri ko Barebare. Dalili kuwa shi ne, kusan ana iya cewa marubutan sun tattaro sunaye na shekaranjiya, da jiya, da na yau. Ma’ana dai, sun tattaro na zamanin da kafin zuwan addinin Musulunci, da kuma na zamanin yanzu, bayan Musulunci ya bayyana a ƙasar Hausa.

Haka kuma, sun kawo ire-iren sunaye, da dalilan Sanya su, tare kuma da hasko wasu sauye-sauye waɗanda zamanin ya kawo. Babu shakka littafin ya fito da wasu abubuwa tare da ƙara haske dangane da abin da ya shafi sunayen Hausawa. Marubutan sun yi bayanai da suka shafi sunayen Hausawa maza da mata da na haɗaka manya da ƙanana waɗanda ake Sanya su a da, wasu ma Bahaushe ya manta da su, a yanzu bai kula da su, ko bai ba su mahimmanci ba, saboda samun baƙin sunaye. Akwai inda suka ƙawata littafin ta hanyar kawo ma’anar suna da matsayinsa, da rabe-rabensa, da matakan sanya suna.

Bayan haka, marubutan sun binciko wasu abubuwa masu nuna alaƙa ko dangantaka da ke tsakakanin suna da rayuwar Hausawa. Haka kuma, waɗannan marubuta sun fito da wasu abubuwa waɗanda rayuwa ba ta yiwuwa sai da su, kamar yanayi na shekara, da lokuta, da yanayi na rayuwar yau da kullum, sannan a ka samu jirwayensu a cikin sunaye. Babu shakka wannan littafi zai tallafa wa masu ruwa da tsaki a fagen ilmi. Zai kuma taimaka wa ɗalibai na kowane mataki daga sakandare, da kwalejojin ilmi zuwa jami’o’i, da malamai da sauran manazarta gaba ɗaya.

Ina godiya tare da jinjina wa marubutan da fatan Allah ya ƙaro mana irinsu saboda ana ƙishin ruwan irinsu. Amin.

Dr. Mu’azu Sa’adu Muhammad
Associate Professor
Department of Nigerian Languages
Faculty of Humanities
Sule Lamido University Kafin Hausa
Jigawa State, Nigeria

Sunayen Hausawa

Manazarta

Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2024). Sunayen Hausawa (Bunƙasar Sunayen Hausawa da Maƙwabtansu). WT Press. ISBN: 978-978-782-932-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19512083

Post a Comment

0 Comments