Ticker

6/recent/ticker-posts

Mukaddima: Aure a kunshiyar Karin Magana

MUƘADDIMA: AURE A ƘUNSHIYAR KARIN MAGANA

Na

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Da sunan Allah, mai rahama, mai jinƙai, wanda bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Salati da sallam su tabbata ga farin jakada, cikamakon Annabawa, Shugaban Manzanni, Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da iyalansa da sahabbansa da duk waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Alal haƙiƙa, na yi matuƙar farin ciki da samun damar yi wa wannan littafi mai suna Aure a Ƙunshiyar Karin Magana na Malama Shafa’atu Salihu Labbo da Dakta Abu-Ubaida Sani muƙaddima, duk da cewa ba ni na fi cancanta in yi ba, amma ba ni wannan damar babban abin jin daɗi ne a gare ni.

Masu hikimar magana suna cewa, ba don aure ba da iri ya ƙare. Tabbas! Wannan batu haka yake, domin aure muhimmin abu ne a cikin rayuwar Hausawa, kasancewarsa hanya ɗaya tilo da yake samar da tsarkakakkiyar zuri'a wanda kan sanya mutum ya yi alfahari da dangantakarsa.

Wannan muhimmancin da aure yake da shi a cikin rayuwa ne ya sanya bayanansa da kusan dukkan wasu al'amura da suka shafe shi suka riƙa bayyana a cikin ƙushiyar adabin Hausa, musamman ma karin maganar Hausawa.

Karin magana wata falsafa ce ta Hausawa da take dunƙule zance mai faffaɗar magana, wadda ke buƙatar zurafafa tunani, da faɗaɗa bayani kafin jama'a su fahimci ƙunshiyarta.

Alal haƙiƙa, marubuta wannnan littafi sun yi zuzzurfar nazari, duba da yadda suka kawo bayanai daki-daki, kan abin da ya shafi aure da karin magana tun daga kan maanar karin magana da kuma yadda suke ƙunshe da falsafar zamantakewar aure a cikinsu. Kasancewar na karanta littafin tun daga farkonsa har ƙarshe, wannan ya sa na fahimci lungu da saƙonsa kuma na yi bitarsa ta hanyar bayyana fahimtata dangane littafin kamar haka:

Littafin shi ne irinsa na farko da ya tattaro karin magana masu ɗimbin yawa da suke da dangantaka da aure, ya kuma yi bayanin ƙunshiyarsu filla-filla tare da fito da falsafar da ke cikinsu. Kamar yadda mai karatu zai gani, wannan litattafi na musamman ne domin ya bambanta da sauran litattafai, domin kuwa ya tattauna muhimman abubuwa da suka shafi aure a matsayin ginshiƙi na samar da tsaftatacciyar alumma.

Marubutan wannan littafin sun yi hoɓɓasa wajen kawo rabe-raben aure tare da bayyana yadda Hausawa suke aiwatar da su. Hakazalika, marubuta littafin sun yi amfani sassauƙan salo wajen tattauna batutuwan da littafin ya ƙunsa, ta hanyar kawo bayanan tirya-tiryan da kuma bayyana komai dalla-dalla don a fahimci yadda karin maganar Hausa suke ƙunshe da alamuran da suka shafi aure da zamantakewar iyali a Bahaushiyar alada. Bugu da ƙari, littafin ya kawo karin maganganu da Hausawa suke da su waɗanda suka shafi tun daga neman aure da wadda ya kamata a nema a aura da bukin aure da zamantakewar ango da amarya da dai sauran abubuwa muhimmai waɗanda ake samun su a dalilin zamantakewar aure.

Gaskiya ban san wani littafi da aka rubuta da Hausa wanda ya kawo bayani filla-fillah a kan auren Hausawa a cikin ƙunshiyar karin magana ba kamar wannan. An dubi falsafar da ke cikin karin maganganun da aka kawo a cikin littafin aka warware tare da tsettsefe bayanansu domin a fahimce su da kyau.

Wannan littafin zai taimaka wa ɗalibai har ma da malamai da masu nazari a matakai daban-daban na ilimi, wajen bunƙasa adabi da al'adun Hausawa, ta hanyar bayyana muhimman abubuwan da suka shafi aure. Tun daga neman auren da zamantakewar auren da ma abubuwan da auren kan haifar.

Bugu da ƙari, littafin zai taimaka matuƙa gaya wajen samar wa ɗalibai musamman masu nazarin adabi da al’adun Hausawa abin karatu, musamman a jami’o’in Nijeriya da ma na ƙasashen waje. Domin marubutan wannan littafi sun cika sharuɗɗan rubutu na ilimi wajen kawo duk wani tushen bayani da madogara da suka yi amfani da ita wajen kalato bayanan da suka haɗu suka tayar da littafin.

Don haka, ina sanar da al’umma cewa wannan littafi ya cancanci yabo da jinjina kuma ya tsere wa tsara. Kuma ina shelanta fitowarsa, domin amfanin ɗalibai da malamai da manazarta da sauran al’umma. Ina kira ga malamai da ɗalibai da duk masu ruwa da tsaki a kan nazarin Hausa da su tabbatar sun mallaki wannan littafi, domin za su amfana ƙwarai daga ɗimbin ilimin da ke ƙunshe a cikinsa.

A ƙarshe, ina adduar Allah ya saka wa marubutan wannan littafi da mafificin sakamako, ya kuma ƙara masu dubun sani da faɗin ƙirji.

Dr. Jibril Yusuf
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe
Jami’ar Jihar Kaduna.
26 ga watan Oktoba, 2025

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments