Ticker

6/recent/ticker-posts

Marigayi Alhaji Abdullahi Bello Ka'oje

"Ɗan Sarki fa Sarki ne,

Kai ko bai yi Sarki ba,

Ɗan Sarki fa Sarki ne

Magana tai ta Sarki ce,

Son jama'a kamab Bello,

Wasa da dariya kamab Bello,

 Ga milki kamab Bello,

Ga kyauta kamab Bello,

Kuma ga ilimi kamab Bello ".

Haka☝️Makaɗa Alh. Garba Super Gwarzo, Kano yake cewa a cikin waƙar da ya yi wa Marigayi Alhaji Abdullahi Bello Ka'oje mai amshi "Toron Giwa mai ban tsoro, Abdullahi Ka'oje ".

Wane ne wannan bawan Allah?

Marigayi Alhaji Abdullahi Bello Ka'oje ɗan Sarkin Bargun Ka'oje na 9 ne wato Sarkin Bargu Bello, shi kuma Sarkin Bargu Bello ɗan Sarkin Bargu na 6 ne wato Sarkin Bargu Aliyu, shi kuma Sarkin Bargu Aliyu ɗan Sarkin Bargu na 4 ne wato Sarkin Bargu Buhari, shi kuma Sarkin Bargu Buhari ɗan Sarkin Bargu na 2 ne wato Sarkin Bargu Muhammadu Zangi, shi kuma Sarkin Bargu Muhammadu Zangi ɗan Sarkin Bargu na farko ne wato Sarkin Bargu Yakuba wanda yayi mulki daga shekarar 1823 zuwa wafatinsa a cikin shekarun 1850s, shi kuma Sarkin Bargu Yakuba ɗan Malam Sakita ne da ya kafa sarautar Fulani a masarautar Ka'oje dake Jihar Kebbin Nijeriya ta yau a farko farkon ƙarni na 19.

An haifi Marigayi Alhaji Abdullahi Bello Ka'oje a garin Ka'oje dake Ƙaramar Hukumar Mulkin Bagudo, Jihar Kebbi, Nijeriya a cikin shekarar 1931.

Ya yi karatun addini ya kuma shiga Makarantar boko ta garin Ka'oje a shekarar 1938. Ya halarci Makarantun Sakandare na Lardi a Sakkwato da Kano(Provincial Secondary School) da Cibiyar Koyar da Dabarun mulki ta Kongo, Zaria (Institute of Administration, ABU Zaria).

Ya soma aiki a Majalisar Dokokin Lardin Arewa a Kaduna inda bayan juyin mulkin soji da aka yi na farko a Nijeriya ya koma da aiki a Ma'aikatar lamurran cikin gida ta Tarayyar Nijeriya.

Ya yi aiki a Lardin Zazzau da kuma Lardin Jos. Alh. Abdullahi Ka'oje ya yi aiki a Cibiyar horas da Jami'an Gwamnati(Staff Training Center) a Bida da Kano da Kamfanin buga Jaridar New Nigeria da Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna inda ya taɓa gabatar da wani shiri mai suna "Kunun Kanwa" ya kuma rubuta wani littafin ƙagaggen labari mai suna "Dare Ɗaya Allah Kanyi Bature" ya kuma taɓa aiki a Sashen Hausa na Gidan Rediyon BBC London. Haka zalika yayi aiki a Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa(Nigerian Ports Authority, NPA).

Ya shiga aikin Kwastan a matsayin Sufiritandan inda ya zauna a Sapele da Idi-Iroko da kuma Sakkwato.

Allah SWT ya yi masa rasuwa a shekarar 1979 a lokacin da yake jagorancin ofishin Kwastan na Sakkwato a mashigin ruwan Kogin Neja na Tuga, Ka'oje sanadiyar hatsarin /haɗarin jirgin ruwan dake ɗauke dashi.

Ya bar matan aure guda biyu, Hajiya Asma'u (Ladidi) da Hajiya Rabi da ya'ya guda 5, biyu maza da mata 3. Daga cikin ya'yan akwai Buhari Abdullahi wanda Jami'in Yan Sanda ne a Kano da kuma Hajiya Hadiza dake aiki da Hukumar Kwastan a Abuja.

Ƙasar Ka'oje wasu jinsin mutane ne da ake kira Bargawa waɗanda a halin yanzu ana samun su a wasu sassa na Jihar Neja ta Nijeriya kamar Bussa da kuma wani sashe na Jamhuriyar Benin ne suka ƙirƙire ta shekaru da dama da suka wuce.

Wasu Fulani da suka fito daga Futa Toro dake Kasar Senegal ta yau sun shigo yankin Kasar Hausa daga ɓangaren yamma. Suka jiɓinci lamarin Jihadin jaddada Addinin Musulunci na Daular Usmaniyya da Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo Tagammadahullah Birahamatihi ya jagoranta a ƙarni na 19.

Bayan kammala jihadi aka damƙa su ga jagoran yankin Daular na yamma mai hedikwata a Gwandu wato Malam Abdullahi Ɗanfodiyo, suka zauna a wani gari kusa da Gwandu da ake kira Gulumbe.

Bayan wafatin Malam Abdullahi Ɗanfodiyo sai masu jagoranci na Gwandu suka nemi waɗannan Fulani a ƙarƙashin shugabanci Malam Sakita da su kafa mazauni na Ribaɗi wajajen Kogin Neja domin kariya daga hare-haren al'ummomin dake zaune a wannan wuri.

A lokacin da Malam Sakita da Jama'arsa suka riski Ka'oje sun tarad da Bargawan nan da ba addinin Musulunci suke biya ba a lokacin a ƙarƙashin mulki wasu mutane guda biyu, Doka da Galadima suka yaƙe su har sai da suka samu galaba a kan su. Wannan ne dalilin samar da sarautar Fulani a Ka'oje ya zuwa yau, inda Yakuba ɗan Malam Sakita ya zama Sarki na farko daga zuriyar waɗannan Fulani da laƙabin "Sarkin Bargu" a shekarar 1823.

Daga wancan lokaci ya zuwa yau an yi sarakuna 13 kamar haka :-

1. Yakuba ɗan Malam Sakita.

2. Muhammadu Zangi ɗan Yakuba

3. Ibrahim Zangi ɗan Yakuba

4. Buhari ɗan Muhammadu Zangi

5. Muhammadu ɗan Buhari

6. Aliyu ɗan Buhari

7. Abdullahi ɗan Aliyu Buhari

8. Umaru Kigo ɗan Aliyu Buhari

9. Bello ɗan Aliyu Buhari

10. Amadu ɗan Aliyu Buhari

11. Shehu ɗan Aliyu Buhari

12. Usman Adamu

13. Mustapha Usman

 Adamu.

A cikin wannan waƙa da ta bijiro da wannan sharhi Makaɗa Alh. Garba Super ya taskace wasu muhimman batutuwa kamar gadon sarauta na wanda ya yiwa waƙar inda yake cewa "Ɗan Sarki fa Sarki ne kai ko bai yi Sarki ba", da muka bibiyi salsalar Marigayi Alhaji Abdullahi Bello Ka'oje mun gano cewa mahaifinsa da kakansa duka sun yi sarauta.

Ya ambata masa ilimi, mun lura har littafi ya rubuta, ya ambaci matarsa Ladidi (Asma'u) da ya'yansa Hadiza(Hadizatul Kubura) da Buhari da sauran batutuwa masu yawa.

Haƙiƙa wannan waƙa tana ɗauke da lamurran da ake iya nazarta a duniyar Adabin Hausa.

A wannan hoto Marigayi Alhaji Abdullahi Bello Ka'oje ne.

Allah SWT ya jiƙan Marigayi Alhaji Abdullahi Bello Ka'oje da dukan sauran magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.

Daga Taskar:

Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) Jihar Zamfara, Nijeriya.

03/07/2026.

Marigayi Alhaji Abdullahi Bello Ka'oje


Post a Comment

0 Comments