Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallah Da Takalmi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam Khamis. Allah Ya saka maka da alkhairi. Gaskiya muna jin daɗin wannan channel, muna ƙaruwa sosai. Tambayata ita ce: Mene ne hukuncin Sallah da takalmi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu.

Sallah da takalmi ya halatta, idan takalmin yana da tsarki (babu najasa a jikinsa), kuma ba zai cutar da masallaci ko sauran masu ibada ba. Dalili kuwa shine a lokacin Annabi (SAW) da Sahabbansa suna sanya huffi su yi sallah da su a ƙafafunsu.

HUJJAR DAGA SUNNAR MANZON ALLAH (SAW): Ya halatta mutum yayi sallah da takalma domin Manzon Allah (SAW) yayi kuma yayi umurni da ayi. Manzon Allah (SAW) ya ce: "Ku yi sallah da takalmanku, (ku sãɓawa Yahudawa) domin lalle Yahudawa ba sa sallah da takalmansu." . An rawaito daga Abi Maslama Sa'id bin Yazid Al-Azdi, ya ce: Na tambayi Anas bin Malik ko Manzon Allah (SAW) ya yi sallah da takalmi, sai ya ce "Kwarai kuwa." . Har ila yau, Amru ɗan Huraith ya ce: "Na ga Manzon Allah (SAW) yana yin sallah yana sanye da takalma da aka ɗinka." .

SHARUƊƊA DA KA'IDODI: Sallah da takalmi Sunnah ce ta Annabi (SAW), idan takalmin suna da tsarki (babu najasa a jikinsu). Amma a yau, idan kana cikin masallaci mai tsafta, ya fi dacewa ka cire takalminka. Musulunci addini ne na sauƙi, yana koyar da tsafta da sassauci a ibada. Saboda haka, kada kayi sallah da takalma a duk inda zaka janyo tarzoma – idan ka sami jama'ar da ke kula da masallaci basu aminta da ayi masu sallah da takalma ba, to kada kayi. Ko idan takalminka zai kazamta masallaci, duk da haka kada kayi. Idan kayi ka cutar da jama'a, zaka iya samun zunubi. Sallah da takalmi ta fi dacewa idan mutum yana yin sallah a fili, a kan titi, a gona, ko a wuraren da babu shimfida.

A taƙaice, sallah da takalmi halal ne kuma Sunnah ce idan takalmin suna da tsarki, amma a masallatai masu tsafta, cire su ya fi dacewa don kiyaye tsafta da kuma guje wa cutar da wasu. Allah ne Mafi sani.

Allah ne Mafi sani.

Amsa ta ƙare. Alhamdu lillah.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments