Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Macen Da Ta Yi Wa Kishiyarta Asiri

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam mene ne hukuncin macen da tayi wa kishiyarta asiri tana bunnewa, kuma ta shiga tsakanin ‘ya’yanta da mahaifinsu, duk ta hanyar asiri”?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Yi wa wani asiri ta hanyar raba shi da wani da yake kauna da juyar da shi daga halin kauna da soyayya zuwa halin gaba da kiyayya, mummunan aiki ne, kuma nau’i ne na sihiri da ake kira ‘SIHRUT TAFRIK’, ko ‘AS-SARF’, wato sihirin rabawa tsakanin ma’aura, ko masoya, ko juya hankalin wani da susuta shi da zautar masa da hankalinsa daga wani abu da zai amfane shi zuwa mai cutar da shi, ko kuma daga kaunar abin kaunarsa ko iyayensa zuwa kyamarsu da bijire musu. Akwai hanyoyi da dama da masu irin wannan mugun aiki su kan bi wurin cimma burinsu.

Hukuncinsa a musulunci ya zo kurukuru a cikin al-Qur’ani mai girma inda Allah Maɗaukaki ya ambaci cewa kafirci ne, kuma malamai sun bayyana cewa duk wanda aka kama shi da irin wannan aiki to hukuncinsa shi ne alkali ya sa a kashe shi kisan kafirci da ridda ta barin addinin musulunci.

Don haka ya wajaba wannan mata da duk wani mai mummunan aiki irin nata mai irin wannan bamagujiyar mugunta da bakar aniya, ya ji tsoron Allah ya tuba.

Lalata kishiya ta hanyar sihiri da raba ta da mijinta da shiga tsakaninta da ‘ya’yanta ba shi ne zai jawowa mai neman a yi mata sihirin alherin duniyar da take fada da kishiyar a kansa ya dawo gare ta ba. Arzikin duniya da na lahira duk a gun Allah yake, kuma babu wata hanya da za’a same shi sai da yardarsa. Yaya za a yi kuwa a ce mutum mumini ya jefa ɗan'uwansa cikin damuwa, ya hana masa kwanciyar hankali; saboda kawai yana ganin cewa shi ne ya hana shi samun wani abin duniya ko kadaituwa da kaunar miji da soyayyarsa, kuma musamman ma a ce ta hanyar kafircewa da Allah da bautawa aljanu. Gaskiya wannan ba karamar tabewa ba ce, da kekasar zuciya, da rashin tsoron Allah, da fito-na-fito da kaddararsa, da rashin yarda da lamarinsa da dogaro da shi.

Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) Ya gaya mana cewa duk wanda ya je wurin boka ko ɗan duba, kuma ya tambaye shi kan wani abu har ya gaskata shi, to ya kafirta da abin da aka saukarwa (Annabi) Muhammad (sallalllahu alaihi wa sallam).

A wata riwayar kuma ba za’a karbi sallarsa ta kwana arba’in ba. Wannan wanda ya gaskata kenan, ba tare da ya aikata sihirin ba. Kuma mafi rinjayen maganar malamai ita ce wannan tambayar da gaskatawar kafirci ne amma karami, ba mai fidda mutum daga musulunci ba. Amma mai aikata sihirin da mai ba da kuɗi da umurni a yi wa wani, kuma wanda ake ba wa umurnin ya cika sharuddan da aljanun ke nema a yi musu, to duk wannan aikinsu ɗaya ne da shi bokan, kafircinsu na fita daga addini ne.

Babban abin da ke cikin wannan ma shi ne bautawa shaidanu da aljanu da yi musu da’a cikin abin da suke so, na yanke-yanke ko neman cika wasu sharudda masu dan karen wahala, da bada umurnin a je wani wuri a yi tono a binne. Wannan duk bautawa aljanu ne, bayan dumbin dukiyar da mutum zai halakar ta wannan mummunar hanya. Allah ya tsaremu.

Nasihata ga duk wanda Allah ya jarraba da wannan mummunar ta’ada ita ce ya gaggauta tuba zuwa ga Allah, kuma ya yi watsi da wannan shirka, kuma ya dogara da Allah bisa duk abin da yake nema, sannan ya ji tsoron cewa shi ramin mugunta in an tona shi ba a fa san wanda zai fara fadawa ba.

Daga cikin manyan hadurran da wannan mummunan aiki ya kunsa akwai: Shirka da Allah da bauta wa aljanu. Kila wata ta ce ai ita wurin ‘malami’ kawai ta je ba gun aljanu ba, to ya kamata ki gane cewa shi wannan da kike kira malami ba ya iya komai da kashin kansa sai ya yi da’a ga aljanu su kuma su ba shi umurni ya cika musu. Wannan da’ar da kuma cika sharuddan yadda aljanin ya nema shi ne bakar shirka, domin bautawa wanin Allah ne da neman yardarsa, wato sanya masa kishiya ta hanyar mika wani hakkin ibada zuwa ga waninSa, kamar yanka dabba domin waninSa ko da da sunan Allah ne, ko kuma cika wasu sharuddan da ba Allah ne Ya ce a cika su ba, musamman kuma wurin bautawa wanda za a yi wannan abu dominsa. Allah kuwa ya yi kashedi ga dukkan al’umma cewa “Duk wanda ya yi tarayya da Allah to lallai Allah ya haramta masa shiga Aljanna, kuma makomarsa ita ce Wuta, kuma azzalumai ba su da mataimaka. Allah ta'ala yasa muda ce.🤲

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments