Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Fitsari Ko Kashin Jariri

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Godiya sosai Akaramakallahu Allah ya jikan magabata, ya sakanya da gidan aljanna🤲 Bayan haka ni ma ga tawa tambayar kamar haka:-- shin idan fitsari ko bayan gida na yaro/yarinya wacce bata fara cin abinciba ya shafi sutura yaya ingancin tsarkinta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Shi fitsarin Qananan yara ya rabu ne zuwa kashi biyu. Idan fitsarin yarinya jaririya mace ne, to daidai yake da na babban mutum. wajibi sai an wankeshi. Idan kuma fitsarin Qaramin yaro ne jariri, to yayyafa ruwa kawai ya wadatar. Amma Malaman Fiqhu sun ce wannan hukuncin ya keɓanci yaron da bai fara cin abinci bane. Idan ya riga ya fara cin abinci, to hukuncin fitsarinsa kamar na babban mutum ne. Hujjah anan ita ce hadisin da Bukhary da Muslim suka ruwaito daga Sayyidah Ummu Qays bintu Mihsaan (ra) ta kawo wani yaronta wanda bai fara cin abinci ba, ta kawoshi wajen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya karbeshi ya dorashi akan cinyarsa mai albarka, Sai yaron yayi masa fitsari. Sai Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) yasa aka kawo masa ruwa ya yayyafa a tufafinsa, bai wankeshi ba.

(aduba Sahihul Bukhary hadisi na 223, Sahihu Muslim hadisi na 287).

Akwai wani hadisin ma daga Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (ra) daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa : "KUYI YAYYAFI GA FITSARIN JARIRI QARAMI, KUMA KU WANKE FITSARIN YARINYA QARAMA". (Aduba Sunanut Tirmiziy hadisi na 610, Ibnu Maajah hadisi na 525).

Imam Qataadah yace Wannan hukuncinsu kenan kafin su fara cin abinci. amma idan har sun fara cin abinci to Wajibi ne awanke fitsarin kowannensu. Don Qarin bayani aduba Tuhfatul Maurood shafi na 190).

Matsayin kashi ko bayan gida na yaro/yarinya daban yake da na fitsari. Ko jaririn ya fara cin abinci ko yana shan nono ne kawai, idan yayi kashi, suturar ko jikinsa ta zama najasa, kuma dole ne a wanke wajen da ruwa mai tsarki har sai najasar da warinta sun tafi.

Bayan gida (Kashi) najasa ce mai tsanani (NAJASATUL MUGHALLAZAH), kuma babu wata alfarma a kanta. Dole ne a wanke suturar da ruwa sosai har sai launinta da warinta da duk wata alama ta najasar ta tafi.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments