Ticker

6/recent/ticker-posts

Fassarar Wasu Kalmomin Fannu a Littafin Damfara a Duniyar Intanet

Ga jerin fassarar wasu kalmomin fannu da aka yi amfani da su a wannan littafi.

Admin - Adimin

Artificial Intelligence (AI) - Ƙirƙirarriyar Basira

Automation – Na’urantarwa

Black Market – Kasuwar Bayan Fage

Block - Toshe

Blockchain – Bulokcen

Blocking - Toshewa

Crypto – Kirifto

Cryptocurrency – Kuɗin Intanet

Domain Name - Sunan Kafar Intanet

Downloading - Saukewa

Gas Fee – Kuɗin Kasuwanci A Kan Bulokcen

Hacking - Kutse

Holding – Riƙewa

Install App - Girke Manhaja

Launching – Ƙaddamarwa

Liquidity – Uwar Kuɗi

Login Details - Bayanan Shiga Akawun

Mining – Haƙo/Haƙa

Minting - Rajista/Daidaituwa

Mission[1] - Jinga

P2P (Peer-to-Peer) – Mutum Zuwa Mutum

Password - Kalmar Sirri

Personal Information - Keɓantattun Bayanan Mutum /Bayanan Kai

Phishing - Tatsar Bayanai

Phishing Scams - Damfarar Tatsar Bayanai

Pre-Market – Kasuwar Somin-Taɓi

Rating - Sa Ƙima

Redirect - Sauya Akalar Nema

Referral - Gayyata

Robot - Saƙago

Search Engine - Injin Nema

Second Step Verification (2nd Step Verification) - Matakin Tantancewa Na Biyu

Task - Jinga

Two-Step Verification - Matakan Tantancewa Biyu

Username - Sunan Mai Akawun/Yuzanem

Virus – Bairos/Bairas

Website/Blog Cloning - Basajar Kafar Intanet



[1] Wani aiki da kamfani yake bai wa ɗan kasuwa ko mai hadahadar kuɗin intanet wanda idan ya kammala zai samu ladan aikin, ko dai ta hanyar biyan kuɗi ko maki ko kuma kadarar intanet.

 An ciro daga littafin:

Damfara a Duniyar Intanet

Na
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Damfara a Duniyar Intanet

Post a Comment

0 Comments