Wannan ɓangare na littafin yana ɗauke da taƙaitaccen bayani dangane da wasu kalmomin fannu da aka yi amfani da su a cikin littafin.
Adimin:
Shugaba ko mai gudanarwa a zaurukan kafafen intanet kamar Telegram da WhatsApp/Wasaf
da sauransu.
Cin Task: Yana nufin wani aiki da ake aiwatarwa domin samun maki ko sulalla da suka
danganci wani kuɗin intanet.
COTP (Crypto OTC
Trading Platform): A duba ma’anar OTC.
Escrow:
Wani wuri ko wani mutum ko na’ura da take ajiye kuɗaɗe
cikin tsaro yayin gudanar da harƙallar
kasuwanci a kan intanet. Tsari ne wanda yake tabbatar da ba a yi damfara ba a
harƙallar kasuwancin intanet. Misali, wanda
zai sayar da kuɗin intanet, kasuwar kan intanet za ta karɓi
kuɗin ta ajiye shi a escrow. Yayin da mai saya ya tura masa kuɗi, sannan mai sayarwar ya bayar da tabbacin cewa kuɗin sun shiga, to daga nan kasuwa za ta sake kuɗin daga escrow zuwa akawun ɗin
wanda ya sayi kaya.
Gas Fee – Kuɗin
Kasuwanci a Kan Bulokcen: Kuɗi
ne da ake sakawa ko dai a sigar kuɗin intanet ko kuma kuɗin
duniyar zahiri. Ana saka shi ne a matsayin wani abu mai kama da rajistar
gudanar da kasuwanci a kan intanet da ya shafi wani nau’in kuɗin
intanet takamaimai.
Inksnation: Wani shiri ne (project) na damfara wanda ya zo da sigar kuɗin intanet da iƙirarin
yaye talauci ga ‘yan Nijeriya a cikin watanni
tara (9). Hausawa masu yawa sun faɗa wannan tarko na damfara.
Mining - Haƙo: Wannan ya
shafi haƙon kuɗin
intanet ko kadarar intanet da ake yi ta hanyar amfani da na'urori.
Minting -
Rajista/Daidaituwa: A hadahadar kuɗaɗen
intanet, minting yana nufin yin rajista da daidaituwar da mutum yake yi
game da wani kuɗin intanet bisa tsare-tsare da ƙa’idojin bulokcen.
OTC (Over
the Counter): Wata kasuwar hadahadar kuɗaɗen
intanet ta damfara da aka taɓa yi. Masu kasuwar suna iƙirarin taimaka wa ‘yan kasuwa ta hanyar ba su damar
gudanar da kasuwanci a manyan kasuwannin hadahadar kuɗaɗen
intanet (kamar Binance) ba tare da sun sha wahalar shiga manyan kasuwannin ba.
Manyan kasuwannin suna da wahalar sha’ani domin sarƙaƙiyarsu da kuma
ƙa’idojinsu.
P2P
(Peer-to-Peer): Tsarin kasuwanci na mutum zuwa mutum, wato kasuwanci kai-tsaye
tsakanin mutane biyu
PinKard: Sunan
katin cire kuɗi ne wanda masu kuɗin intanet na Inksnation suka samar.
PinKoin: Kuɗin intanet ne wanda masu Inksnation suka samar.
USDT: Kai-tsaye
yana mazaunin kuɗin intanet ne da ake kira Tether. Akan kira shi da
"ticker symbol for the Tether stablecoin cryptocurrency", wato taƙaitawa da take mazaunin alama ko take wakiltar Tether.
An ciro daga littafin:
Damfara a Duniyar Intanet
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.