Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamomin Da Ake Gane Bokaye

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam an kai ni wajen wani mai magani kafin in sanar da shi matsalata sai ya ce min ya san abinda ke damuna. Sai ya cigaba da min wasu irin tambayoyi. Shi ne nake cikin damuwa ina ji a raina kamar wajen boka na je, Amma Inason a fada min alamomin bokaye Malam.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Waalaikumussalamu warahamatullah wabarakatuhu

To bayin Allah Alamomin bokaye da yan duba da Maluman muslunci sukayi bayani suna da yawa Amma Ga wasu daga cikin alamomin nasu:

1. Bayyana wa mutum wasu labarai da suka shafe shi, wanda babu wanda ya san hakan kamar dai misalin yadda kika fada cewa daga zuwanki ya fara labarta miki abinda ke damunki, mai maganin da kika ganshi da Wannan Alamar to Boka ne.

2. Furtawa mutum sunansa ko sunan iyayensa ko sunan garinsu ko sunayen Abokanansa ko makusantansa dasauransu. Lallai a Kula da mai maganin dake da Wannan siffar Domin boka ne.

3. Baiwa mutum wata takarda cewa a je a ƙonata ko a yi turare da hayaƙin. A nisanci Mai bada magani ta irin Wannan hanyar.

4. Bawa mutum wani turaren hayaƙi da nufin mallake miji ko mallake saurayi ko budurwa.

5. Bawa mutum wani turaren hayaƙi domin neman kasuwa ko daukaka dasauransu..

6. Duk Wanda Ya ce Zai yimaka Istikhara to ka guje shi ko waye domin boka ne.

7. Duk Wanda Ya ce muku ku kawo kuďi a siyi turare domin a duba matsalarku to shima ku guje shi.

8. Baka wasu abubuwa a hargitse Ya ce ka dauko masa kwaya ɗaya ka miƙo masa.

9. Za su ce daku ba'a amfani da wannan Maganin sai Karfe kaza na dare ko na Rana.

10. Umurtar ku da Samo musu sassaken wani abu ko kuma Saiwar wani abu mai wahalar samu.

11. Ya baka magani ya ce kada ka bari kowa Yaga lokacin da zakayi amfani da shi hakanan kada wani ya san cewa kana amfani da shi.

12. Umartar mutum da cewa ya nisanci mutane na tsawon wani lokaci yana zaune shi kaɗai a cikin wani daki mai duhu.

13. Umurtar mutum da cewa kar ya ta'ba ruwa har na tsawon wani lokaci.

14. Umartar mutum da dena sallah ko karatun alƙur'ani ko zikirin Allah zuwa wani lokaci.

15. Umartar mutum da zama cikin rashin tsarki na wani lokaci kamar dena tsarkin fitsari ko kashi.

16. Umartar mutum zama cikin ƙazanta kamar dena wanka na wasu kwanaki.

17. Umartar mutum zama cikin janaba, ma'ana idan janaba ta kama mutum ba zaiyi wanka ba idan kuma mace ce za su ce sai ta jera wasu kwanaki ba tare da tana tsarkin haila ba.

18. Umartar mace ta kai kayan sawarta ko kayan mijinta ko kayan mara lafiyar.

20. Umartar mace ta kai Jinin al'adarta ko kuma maniyyin mijinta ko kuma gashinta ko na mijinta dasauransu.

21. Umartar mara lafiya daya kawo dabba (Kamar baƙar kaza ko akuya dasauransu.

22. Umartar a yanka dabba batare da an ambaci sunan Allah ba, Wani lokacin sukance a shafa jinin a jikin mara lafiyar.

23. Umartar Ku da binne dabba da ranta ko bayan an yanka dabbar.

24. Sukan rubuta wasu lissafe lissafe ko taswirori da ba'a gane ma'anarsu, ko kuma su rubuta ayoyin Alƙur'ani a kife ko a hargitse.

25. Lokacin da suke duba ko neman magani za su riƙa maganganu na sirri a murya ƙasa-ƙasa waɗanda ba'a jin me suke faɗa suna kiran sunayen shugabannin aljanu dasauransu.

26. Sukan bada Kyalle ko ƙullin Ganye, ko Laya don Binnewa ko Ratayawa.

Akwai Alamomin bokaye masu yawa Amma dai in sha Allahu waɗannan alamomin za su wadatu ga duk Mai Neman sanin Alamomin bokaye a Wannan zamanin Kuma kamar yadda alamomin nan suke haka suke koda ga bokayen social media.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Za ku iya samun shafinmu ta wannan hanyar... 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments