𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalam da fatan malam na lafiya, ya ibada da hakuri da jama'a? Ina da wasu tambayoyi da nake so a taimaka min da amsoshinsu. Ni ne na makara sallar asubah, ban tashi daga barci ba har sai 7 oclock (karfe bakwai) rana ya fito kuma naji ance alokacin ne shaiɗan yake matso da kahonsa kusa da rana, idan mutum na sallah alokacin tamkar shi Shaiɗan ɗin yake bautawa. To awani lokaci ne ya kamata mutum ya rama wannan sallan? Sannan akwai salloli da ake bina bashi na shekaru 2 Wanda nake so in fara biya. misali idan alokacin sallar magrib ne bayan na idar sai kuma nake so in biya azahar na bashin da ake bina yaya zan biya tunda sallar zuhr a asirce ne kuma ana lokacin magrib na bayyanawa ne. shin zan yi sallar a asirce ne ko yaya?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa
rahmatullah.
Abin da ya tabbata a
hadisan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) shine: Imamu Ahmad da Muslim sun
ruwaito hadisi ta hanyar Sayyiduna Amru bn 'Abisah (radhiyallahu anhu) Yace
"Nace wa Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) "Ya
Annabin Allah bani labari game da sallah". Sai yace "Ka sallaci
sallar asubah sannan ka kame daga yin sallah har sai rana ta fito, ta 'dago
domin ita tana fitowa ne ta tsakanin Qahon wani shaiɗani kuma awannan
lokacin ne kafirai suke yi mata Sujadah..."
Imamun Nawawiy yace
"Shi shaiɗanin yana kusantar da
kansa ne zuwa ga rana a irin waɗannan lokutan domin ya zamanto masu yi mata sujadah daga
cikin kafirai tamkar shi suke yiwa sujadar a zahiri".
To kaga anan Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana cewa an hana yin sallah ne a irin
waɗannan lokutan saboda
kada muyi tarayya da kafirai cikin irin abin da suke yi adaidai lokacin. To
amma wannan hanin bai shafi sallolin ramuko ba.
Mafiya yawan Maluman
Fiqhu sun tafi akan halaccin yin ramuko (Qadha'i) koda bayan sallar asubah ne
ko bayan la'asar Sun dogara da Ingantaccen hadisin da Bukhariy da Muslim suka
ruwaito Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace "Duk wanda ya manta
da wata sallah, to ya sallaceta idan ya tunota".
Don haka ita sallar
ramuko babu wani lokacin da aka hana yinta. Zaka iya yinta akowanne lokaci.
Kuma zaka yita ne bisa yanayin da ta tsere maka, kuma akan yanayin da ake
yinta.
Misali idan sallar
azahar ce ko La'asar zaka yi karatunsu a Ɓoye ne koda acikin
dare zaka ramasu. Sannan koda sallar asubah zaka rama, ko maghriba ko isha'i to
zakayi karatunsu afili ne koda da rana zaka ramasu. Hakanan sallar da ta tsere
maka alokacin kana gida, zaka yita ne cikakkiya (ba Qasaru ba) koda sanda zaka
ramasu ɗin kana wajen tafiya
ne. Haka kuma sallolin da suka tsere maka akan yanayin tafiya ko balaguro, to
zaka ramasu ne bisa yanayin sallolin tafiya (Qasaru) koda kuwa agida zaka
ramasu).
Don Qarin bayani ka
duba babin dake bayanin yadda ake ramukon sallah acikin littafin Risalatul
Qairawaniy, Muqaddamatul Iziyyah, da Matnul Ashmawiyyah, da Matnul Akhdhariy.
Anan nake so inyi
maka gargadi game da barin sallah ta wuceka da gangan, ko kuma yin sakaci wajen
ramasu. Wannan haramun ne domin kuwa yana daga cikin wasa da sallah. Kuma Allah
yace "AZABA TA TABBATA GA MASALLATA. MASU YIN SAKACI AKAN SALLARSU".
Kaji tsoron Allah ka
kiyaye dokokinsa. Sallah ita ce mafi girman dukkan ibadodi kuma ita za'a fara
dubawa aikin ayyukanka aranar Alkiyamah. Idan tayi kyau ka tsira. Idan kuma ta ɓaci (saboda rashin
yinta akan lokaci, ko rashin yinta da ilimi, ko rashin sanya tsoron Allah
cikinta) to mutum yayi asara mai girma. (Allah shi kiyayemu).
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.