Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma'anar Sunan Hurem Da Samreen

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum ina wuni y ƙoƙari Allah Ubangiji ya biya ku da mafificin alkhairi. Dan Allah, ina son in San ma'anar suna Hurem

Da ma'anar suna Samreen

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Sunan HUREM ko HÜRREM suna ne na mace mai kyau da daɗi, wanda ya samo asali daga kalmar Farisanci (Persian) wato Khorram (خرم). Babban ma'anar sunan tana nufin "mace mai fara'a, mai faranta rai, ko wacce take yawan murmushi". Wacce fuskarta ke cike da annuri da walwala. A wata ma'anar ta harshen Farisanci, yana nufin abu mai sabo, kore, ko mai raye-raye kamar tsiro.

Wannan suna ya yi fice ne a duniya saboda HÜRREM Sultan (Roxelana), matar fitaccen Sarkin Daular Usmaniyya (Ottoman Empire), wato Sultan Suleiman the Magnificent. Asalinta baiwar da aka kamo ce daga yankin da yanzu yake Ukraine. Saboda wayo, hazaka, da kuma fara'arta, Sultan Suleiman ya canza mata suna zuwa HUREM (mai fara'a), sannan ya 'yanta ta kuma ya aure ta a matsayin halatacciyar matarsa. Ta kasance daya daga cikin mata mafi iko da tasiri a tarihin Musulunci da na duniya.

A takaice, sanya wa yarinya sunan HUREM yana nuni da fatan ta kasance mai faranta rai, mai farin jini, da kuma jaruma mai hazaka a rayuwa.

Sunan SAMREEN ko SAMREENA ko SAMRIN ko SAMARINE ko SAMRENE suna ne na 'ya'ya mata mai asalin Larabci da kuma Farisanci, wanda ya shahara a al'adun Musulunci.

A fannin fassarar sunaye, SAMREEN yana nufin "mai albarka, " "mai 'ya'ya, " ko "wadda ke da kyawawan halaye da tausasawa".

Ma'anar SAMREEN da Larabci: Ana amfani da shi wajen nuna alamar "mai 'ya'ya da yalwa" (Fruitful). A asalin Larabci, an danganta shi da kalmar "SAMAR, " wanda ke nufin tattaunawa ko hira a lokacin dare. Wannan na nuni da mutum mai son jama'a, kwanciyar hankali, da kuma jan hankali wajen hira.

Ma'anar SAMREEN Farisanci da Urdu: A ƙasashen Asiya (kamar India da Pakistan da Bangladesh), sunan yana nufin 'ya'yan ita ce mai daɗi (Fruitful), ko fure / fure mai ƙamshi. Yana nuna alamar kyau, furewa, da kuma amfani ga al'umma. Yana nufin "kyakkyawar yarinya mai tausasawa" (A lovely and graceful girl).

A addinin Musulunci, malamai sun yarda da sunan SAMREEN saboda yana da ma'anoni masu kyau wadanda suka dace da koyarwar musulunci, kuma babu wani tarihi da ya sabawa shari'a a cikinsa. Ana son a rika zaban sunaye masu ma'anoni na gari kamar wadannan don bayar da kyakkyawar ma'ana ga rayuwar yaro.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments