Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Auren Macen Da Ta Taba Yin Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alekum waramatullahi wbrkth mlan tambayata auren wacce ta taba zina har ta samu ɗan?

HUKUNCIN AUREN MACEN DA TA TAƁA YIN ZINA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Hukuncin auren macen da ta taɓa yin zina har ta sami ɗa ya halatta a Shari'ar Musulunci, matukar ta tuba, tuba na gaske da kuma tabbatar da rashin juna biyu (Istibra'i).

Aure a Musulunci ibada ne mai tsarki, kuma Shari'a ta tanadi hanyoyin da mutum zai iya gyara rayuwarsa bayan ya aikata kuskure. Zina babban zunubi ne amma baya haramta aure. Idan mace ta yi zina ta tuba, tuban tsakani da Allah, to aurenta ya halatta kamar kowace mace.

Duk girman laifin mutum in dai ta tuba da gaske, to Allah zai karbi tubanta ya gafarta mata kamar yadda ya umurci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya gaya mana:

 قُلۡ یَـٰعِبَادِیَ ٱلَّذِینَ أَسۡرَفُوا۟ عَلَىٰۤ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُوا۟ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ یَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِیعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِیمُ

"KACE YAKU BAYINA WAƊANDA SUKA AIKATA ƁARNA BISA KANSU!! KAR KU FIDDA TSAMMANI DAGA (SAMUN) RAHAMAR ALLAH. HAKIKA ALLAH YANA YAFE DUKKAN ZUNUBAI BAKI ƊAYA, HAKIKA SHI NE MAI GAFARA MAI JIN ƘAI" (Surah Az-Zumar: 53)

Malamai sun yi bayanin cewa idan mace ta tuba, ba wajibi bane ta gaya wa wanda za ta aura cewa ta taɓa yin zina a baya.

Dole ne macen da shi kansa namijin idan wanda suka yi zinar ne zai aure ta su fuskanci Allah cikin kaskantar da kai, su yi nadama, kuma su kuduri aniyar rashin komawa ga wannan zunubi. Shari'a ba ta halatta auri mazinaciya mai ci gaba da zinar ba. Dole ne mace ta nuna tsantsar nadama ta gaske kuma ta tuba zuwa ga Allah (S. W. T) kafin a ɗaura auren. Ba za a ɗaura aure ba har sai an tabbatar da cewa mahaifarta ba ta ɗauke da wani cikin na daban.

Mazhabar Malikiyya: Sun tafi akan cewa haramun ne a ɗaura aure idan mace tana da juna biyu na zina, sai bayan ta haihu. Idan kuma aka ɗaura auren tana da ciki, auren ya ɓaci kuma dole ne a raba auren.

Mazhabar Hanafiyya da Shafi'iyya: Suna ganin za a iya ɗaura aure ko da akwai cikin zina (musamman idan wanda ya yi cikin ne zai aure ta). Sai dai sun yi gadi da cewa miji ba zai sadu da ita ba har sai ta haihu domin kare tsarkakar shayarwa. Wannan ya dace da fadin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa: "Kada mutum ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa". Idan wanda zai aure ta shi ne ya yi zinar da ya haifar da cikin, Malamai sun fi karkata zuwa ga cewa zai fi kyau ta haihu tukunna sannan a ɗaura auren don kiyaye shari'ar ko kuma a ɗaura din amma a kiyaye saduwa.

A karkashin Addinin Musulunci bai halatta a Ɗaura ma mace aure da wani sabon Miji ba, har sai ta tabbatar da cewar babu komai a cikin mahaifarta. a Bisa wannan dalilin shi ya sa Mata suke yin iddah bayan sun fita daga hannun Mijin su kafin su sake aurar wani Mijin daban. Hakanan duk Matar da ta yi Zina, ko budurwa ce ko bazawara, toh bai halatta a Ɗaura Mata aure ba har sai ta yi Istibra'i. Wato ta yi Jini uku, ko kuma a Ƙalla jini guda (a fa'dar wasu Maluman).

Duk Matar da ta zamanto ita Mazinaciya ce, toh bai halatta a Ɗaura mata aure da cikakken Mumini wanda ba ya Zina ba. Sai dai idan sun tuba Sahihin tuba irin tubar da ba za'a sake koma Ruwa ba, Ita Mazinaciyar sai ta yi istibra'i. Sannan zai halatta Mumini ya aure ta. Allah ne ya fada a cikin ayah ta Uku a cikin Suratun Nuur.

الزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ

Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai. (Suratul Nur Ayata 3).

Al Imam Ahmad bn Hanbal ya ruwaito hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru bn Al-Aas (R. A) yace, "Wani Mutum Mumini ya nemi izinin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) akan yana so zai auri wata Mata mai suna UMMU MAHZOUL wacce ta kasance kowa ya san tana yin Zina. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya karanto masa wannan ayar 3 ta cikin Suratun Nuur (A duba Hadisi na 11359 a cikin Sunanul Kubrah ta Imamun Nisa'iy).

Hakanan akwai wani Sahabi mai Suna MARTHAD IBNU ABI MARTHAD (ra) ya taɓa neman izini awajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa yana so zai auri wata Mata mai suna 'UNAAƘ" ta kasance Mazinaciya ce agarin Makkah. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi shuru bai bashi amsa ba, har sai da wannan ayar ta 3 cikin Suratun Nuur ta sauka. Aduba Sunanu Abi Dawud hadisi na 2051. Da kuma Sunanun Nisa'iy juzu'i na 6 shafi na 66 acikin kitabun Nikahi.

Bisa waɗannan hujjojin ne Malamai irin su Imamu Ahmad suka dogara. Sun ce bai halatta a auri duk Matar da ta yi zina ba, har sai bayan ta tuba.

Duk wacce ta tuba daga zunubi kuma ta yi nadama sannan ta nisanci wannan laifin, to Allah zai gafarta mata wannan laifin koda kuwa ta yi shekaru masu yawa tana aikatawa. Allah ya faɗa acikin Alƙur'ani cewa:

إِلَّا ٱلَّذِینَ تَابُوا۟ مِنۢ بَعۡدِ ذَ ٰلِكَ وَأَصۡلَحُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ

"SAI DAI WAƊANDA SUKA TUBA BAYAN NAN (WATO BAYAN SUN AIKATA LAIFIN) KUMA SUKA KYAUTATA AIKI, TO HAKIKA ALLAH MAI GAFARA NE MAI JIN ƘAI GARESU". (Surah An-Nuur: 5)

Ɗan da aka haifa ta hanyar zina ba ya bin uban da ya yi zinar ta fannin nasaba na shari'a, sai dai yana bin mahaifiyarsa. Wannan ɗa zai gaji mahaifiyarsa da danginta, amma ba zai gaji uban da ya yi zinar ba, kuma shi ma uban ba zai gaje shi ba.

Haifuwarsa ta hanyar zina ba ta rage masa daraja ko haƙƙoƙi na ɗan Adam a gaban Allah ba, muddin ya tashi da tsoron Allah da aikata nagarta.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments