Ticker

6/recent/ticker-posts

Annabawan Da Allah Ya Ambaci Sunayensu Da Kuma Zuwansu Duniya Tun Kafin A Haife Su

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam khamis. Gaskiya muna jin dadin wannan group naka mai tarin albarka. malam khamis Allah ya biya ka da gidan Aljanna Allah ya tsareka a duk inda kake Allah yasaka maka da mafificin alkhairi. Tambaya ta a nan shi ne; wanne Annabawa ne waɗanda Allah Ya ambaci sunayensu da kuma zuwansu duniya tun kafin a haife su? Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

A cikin Alƙur'ani Mai girma akwai Annabawa waɗanda Allah Ya ambaci sunayensu da kuma zuwansu duniya tun kafin a haife su. Sune:

1. Annabi Yahaya (A S).

2. Annabi Isma'il (A S).

3. Annabi Ishaƙ (A S).

4. Annabi Yakub (A S).

5. Annabi Isah (A S).

6. Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam)

1. Allah Ya ambaci sunan ANNABI YAHAYA tun kafin a haife shi acikin Alƙur'ani:

يَا زَكَرِيَّا إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلَامٍ اسْمُهُ يَحْيَىٰ لَمْ نَجْعَلْ لَهُ مِنْ قَبْلُ سَمِيًّا

"Yã zakariyya! Lalle ne Mũ, Munã yi maka bushãra da wani yãro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabãni. " (Suratu Maryam aya ta 7).

2. Allah Ya ambaci sunan ANNABI ISMA'IL tun kafin a haife shi. Bayan tsawon lokaci da Annabi Ibrahim (A. S) bai samu haihuwa ba kuma ya tsufa, sai ya roƙi Allah Ya ba shi ɗa na gari. Addu'ar ta zo a cikin Suratul Saffat (aya ta 100):

رَبِّ هَبْ لِي مِنَ الصَّالِحِينَ

"Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne. "

Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi addu'arsa, Ya kuma yi masa albishir da haihuwar ɗa mai haƙuri (ANNABI ISMA'IL A. S) tun kafin haihuwarsa, kamar yadda aya ta 101 a cikin Suratul Saffat ta tabbatar:

فَبَشَّرْنَاهُ بِغُلَامٍ حَلِيمٍ

Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri.

Wannan ɗa da aka haifa (wato ANNABI ISMA'IL) daga matarsa Hajara. Allah Ya siffanta shi da kasancewa mai haƙuri tun kafin a haife shi. shi ne kuma Allah Ya jarrabi Annabi Ibrahim da umurnin yanka shi, suka yi biyayya tare, wanda hakan ya zama babban jarrabawa da kuma tushen babban tarihin gina Ɗakin Ka'aba tare.

3. Allah Ya ambaci sunan ANNABI ISHAƘ tun kafin a haife shi acikin Alkur'ani. Bayan haihuwar Annabi Isma'il (A. S) ne kuma daga bisani Allah Ya sake yi wa Annabi Ibrahim (A. S) bushara da haihuwar ANNABI ISHAƘ (A. S) a lokacin da ya tsufa. An yi masa albishir tare da bayyana sunansa ga mahaifiyarsa (Sayyida Sarah) da mahaifinsa (Annabi Ibrahim) ta bakin Mala'iku. inda Allah Ya ce:

وَامْرَأَتُهُ قَائِمَةٌ فَضَحِكَتْ فَبَشَّرْنَاهَا بِإِسْحَاقَ وَمِنْ وَرَاءِ إِسْحَاقَ يَعْقُوبَ

"Kuma matar tasa tana tsaye, sai ta yi dariya, sai Muka yi mata bushara (albishir) da haihuwar ISHAƘ, kuma a bayan ISHAƘ (Muka yi mata albishir) da haihuwar YAƘŪB. " (suratu Hud, aya ta 71).

Wannan bushara ce da Allah Ya yi a lokacin tana zaune, kafin a haifi Annabi ISHAƘA, wanda shi ne mahaifin Annabi YAƘUB.

وَبَشَّرْنَاهُ بِإِسْحَاقَ نَبِيًّا مِنَ الصَّالِحِينَ

Kuma Muka yi masa bushãra Da IS'HÃƘA ya zama Annabi daga sãlihan mutãne. (Surah: As-Saaffaat, Ayat: 112)

Bayan wannan lokacin da aka ambaci sunansa a matsayin wanda za a haifa, Allah Ya sake jaddada matsayinsa da albarkar da ke tattare da shi a wasu ayoyin:

الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي وَهَبَ لِي عَلَى الْكِبَرِ إِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ ۚ إِنَّ رَبِّي لَسَمِيعُ الدُّعَاءِ

"Gõdiyã ta tabbata ga Allah wanda Yake Ya bãni inã a cikin tsufa ISMÃ'ILA da IS'HÃƘA. Lalle ne Ubangijina, haƙĩƙa, Mai jin addu'a ne. " (Suratu Ibrahim Aya ta 39:')

4. Haka kuma Allah Ya ambaci ANNABI ISA (Almasihu) kafin a haife shi a cikin alkur'ani ta bakin Mala'iku inda aka ce:

إِذْ قَالَتِ الْمَلَائِكَةُ يَا مَرْيَمُ إِنَّ اللَّهَ يُبَشِّرُكِ بِكَلِمَةٍ مِنْهُ اسْمُهُ الْمَسِيحُ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ وَجِيهًا فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ وَمِنَ الْمُقَرَّبِينَ

A lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya da Lãhira kuma daga Makusanta. (Suratu Ali 'Imran Aya ta 45).

5. Allah Ya ambaci sunan ANNABI MUHAMMAD (Sallallahu Alaihi Wasallam) tun kafin a haife shi acikin Alkur'ani. Allah Maɗaukakin Sarki ya bayyana cewa Annabi Isa (A. S) ya yi wa jinsin Bani Isra'ila bishara da zuwan Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) kafin ma a haife shi, inda ya ambace shi da sunansa na sananniya wato "AHMAD" inda Allah Ya ce wa:

وَإِذْ قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ يَا بَنِي إِسْرَائِيلَ إِنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ مُصَدِّقًا لِمَا بَيْنَ يَدَيَّ مِنَ التَّوْرَاةِ وَمُبَشِّرًا بِرَسُولٍ يَأْتِي مِنْ بَعْدِي اسْمُهُ أَحْمَدُ ۖ فَلَمَّا جَاءَهُمْ بِالْبَيِّنَاتِ قَالُوا هَٰذَا سِحْرٌ مُبِينٌ

Kuma a lõkacin da Ĩsã ɗan Maryayama ya ce: "Yã BanĩIsrã'ĩla! Lalle nĩ Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bãyar da bushãra da wani Manzo da ke zuwa a bãyãna, Sunansa Ahmad (Mashãyabo). " To, a lõkacin da ya j musu da hujjõji, suka ce: "Wannan sihiri ne, bayyananne. " (Suratus-Saff Aya ta 6).

A cikin wannan ayar, sunansa ya zo da suna "AHMAD", wanda yana daya daga cikin manyan sunayen Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) da ke nufin "wanda ya fi kowa cancantar yabo".

Sunan nan AHMAD da MUHAMMAD duka sun fito ne daga tushe guda a yaren Larabci wanda ke nufin "Wanda ake yabo" ko "Mai yawan godiya". Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da kansa ya tabbatar a cikin Hadisi cewa yana da sunaye da dama, ciki har da MUHAMMAD da AHMAD.

Alƙur'ani ya bayyana cewa wannan bishara ba a baki kawai Annabi Isa ya faɗeta ba; an kuma rubuta ta a cikin littattafan dā (Attaura da Linjila) kamar yadda aka ambata a Suratun Al-A'raf.

الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ الرَّسُولَ النَّبِيَّ الْأُمِّيَّ الَّذِي يَجِدُونَهُ مَكْتُوبًا عِنْدَهُمْ فِي التَّوْرَاةِ وَالْإِنْجِيلِ

"Waɗanda suke sunã bin Manzo, Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla. (Surah: Al-A'raaf, Aya ta157)

Wannan aya shaida ce mai ƙarfi da ke nuna cewa zuwan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) shiri ne na Allah tun can fil azal, kuma dukkan manyan annabawa sun san da zuwansa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa. . .

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments