Ticker

6/recent/ticker-posts

Ciyarwa a Madadin Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum! ina yiwa malam fatan alkhari allah ya Kara lafiya da nisan kwana allah ya yi wa rayuwa albarka. Allah ya jikan mahaifa Allah ya Kara maka karfi basira da hikima. Mun gode da ilimartarwa, mahaifiyata ta ce yanzu ta kai shekara goma sha daya ke nan ba ta yi azumin watan Ramadan ba, dalilin Rashin Lafiya da take Fama dashi, toh malam yanzu na ce zamu iya auna tsaba ko shimkafa mu ciyar a madadin azumi da ba ta yi ba, ko dole sai mun ciyar da mutum kullum a dadin yawar azumi da bata samu Damar yi ba... dan Allah Mala ataimaka a warware min yanda zan gani. Allah ya Kara lafiya

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Idan har rashin lafiyar tata tana daga cikin nau'in cuta wacce babu fatan warkewa (kamar tsohuwa ko mai ciwon da likitoci suka tabbatar ba zata warke ba) kuma tana da hali, to kuwa dole ne ta ciyar da matalauta a madadin kowace rana da bata samu damar yi azumin ba.

Marar lafiyan da aka ɗebe Tsammanin Warkewa, ko Tsoho da Tsohuwan da basa iya azumi, suna iya ciyarwa ko su sa yayan su, su ciyar musu, idan basuda hali.

Aya ta 184 a cikin suratul Baqara ta nuna wanda ya sha azumi saboda rashin lafiya ko tsufa kuma babu tunanin ya samu damar ramawa nan gaba zai iya ciyarwa:

أَيَّامًا مَّعْدُودَاتٍ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ فَمَن تَطَوَّعَ خَيْرًا فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ وَأَن تَصُومُوا خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ

Kwanuka ƙidãyayyu. To, wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai (ya biya) adadi daga wasu kwanuka na dabam. Kuma a kan waɗanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya ƙãra alhri to, shi ne mafi alhri a gare shi. Kuma ku yi azumi (da wahalar) ne mafi alhri a gare ku idan kun kasance kuna sani. (Suratul Bakara aya ta 184)

A bisa abin da ya gabata In har likita ya tabbatar za ta samu damar ramawa nan gaba to azumin yana nan akanta, ciyarwa ba za ta wadatar mata ba.

Ga Wanda laruri yakamashi bazai iya azumi ba, kuma azumin ya wajaba akansa, To sai ya ciyar da marar qarfi mutum ɗaya Amadadin Azumi Ɗaya. Na abinda yake ci madaidaici na gidansa, batare da Tsanantawa ba, ba kuma qaranci, Amma lalle amfison kaciyar daga irin abinda kuke ci, kaman yanda Aka tambayi Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya bada amsa, da "kada ku ciyar dasu ( marassa qarfi ) da abinda ku baku ci" kamar Yanda imam Ahmad ya futar da hadisin, haithami ya ingantashi, Ibn kathi ya kafa hujja dashi cikin Tafsrin sa, qarqashin [267 baqra].

Son samu abashi a dafe, idan babu dafaffe, abashi da kayan dafi!

A kowace rana ɗaya, ana bayar da abinci wanda ya kai mudu ɗaya na abincin gari (kamar shinkafa, gero, ko masara), wanda ya yi daidai da awo (kimanin mudu ɗaya ko kilo 0.75 zuwa kilo 1 a kowace rana).

Ba lallai sai kun nemo mutane daban-daban har guda goma sha ɗaya a rana ɗaya ba. Kuna iya tara adadin kwanakin (misali kwanaki 30 na Ramadan guda ɗaya) ku baiwa miskini ɗaya idan kuna so, ko kuma ku raba su ga mutane daban-daban.

Mafi alkhairi da sauki shi ne ku auna shinkafar, ku shirya ta kamar a cikin buhu ko kwano, ku raba wa mabukata da talakawa. Akwai kuma damar bayar da kudin daidai da kimanin abincin ga wanda zai iya sayen abincin da kansa, kodayake mafi tsantseni shi ne bayar da tsabar abincin.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

  ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments