ZAMANI SARKI NE,
DOLE A BI SHI!
(Sauyi a Hanyoyin Karatu
Da Nazari)
Daga
Abu-Ubaida SANI,
Ph.D.
Department of
Languages and Cultures,
Federal University
Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
25 May 2026
Ga waɗanda za su karanta ɗan wannan rubutu har zuwa ƙarshe, za su iya yarda da ni cewa mafi yawan matasa za su so a ce a cikin bidiyo yake. Hakan zai sa su saurara kawai ba tare da sun wahalar da idanuwansu wajen karantawa layi-layi ba.
Wannan 'yar shawara ce ga
'yan'uwana ɗalibai. Mu
tuna cewa, tun lokacin da aka halicci duniya abubuwa suke sauyawa. Waɗannan sauye-sauye sun shafi
kusan dukkanin ɓangarorin
rayuwa, tun daga kan tsari da surar halitta kanta, har zuwa sutura da abinci da
al'adu da sauran kayan amfanin rayuwa. Allah bai halicci duniya domin ta zauna
yadda take ba tare da sauyi ba.
Wani babban abin lura shi ne, a
kullum ɗan'adam yana
nemo hanyoyin da za su sauƙaƙe masa gudanar da rayuwa ne. Tun yana yanka dabbobi da duwatsu
masu kaifi, har ya fara amfani da wuƙaƙe, har ya koma kan na'urori masu sarrafa
nama da kansu - tun yana amfani da tsarin ba ni gishiri in ba ka manda, har ya
koma amfani da wuri (shells), zuwa tsakiya (beads) zuwa sulallan albakatun ƙasa,
zuwa kuɗin fatun
dabbobi (leather money), zuwa sulalla (coins), aka wuce ga takarda (notes), har
kuma aka kai yanzu kuɗaɗen suna cikin asusun
bankuna.
Za a iya tuna nason sauƙaƙawa da
take cikin sauye-sauye da zamani yake kawowa a cikin waƙar "Keke:"
Muna shukura ga Rabbal Alamina,
Da alherin da yai mana ba kaɗan ba.
Muna murna da mulkin Ingilishi,
Zuwan da sukai ƙasarmu
ba tai tsiya ba.
Zama zamaninsu ne aka zo da faifa,
Kuɗi
ba masu nauyaya aljihu ba.
Daɗa
zarafinsu ne aka zo da jirgi,
Ka je Maka ba da tashin hankali ba.
Da yake wannan rubutu taƙaitaccen
ne, ba zan mayar da hankali kan faɗaɗa bayanai game da waɗannan ba. A maimakon haka,
bari mu tafi kai tsaye kan zuciyar batun.
Wannan ɗan rubutu ya shafi muhawara da ake kan yi game
da cewa a yanzu Hausawa manazarta sun auri kasala. Ba sa son zuwa ɗakunan karatu domin
bincike. Ba sa son takardu sai dai ɗanyen
kwafe a cikin na'urori... Lallai zamani ne ya kawo hakan - lokacin abin ya zo,
kuma ba za a iya sauya shi ba.
Ba Hausawa ba ne kaɗai suke a haka. Hasali ma,
al'ummomi da dama tuni sun yi nisa a wannan fannin (duk da ƙalubale
da ake fuskanta). Za a fahimci haka tun daga kan jami'o'i da sauran makarantu
da ake da su a kan intanet. A manyan kasuwannin littattafai kuwa, yanzu an ma
wuce maganar takarda da ɗanyen
kwafe. An shiga babin "sauti" (audio) inda ake mayar da littattafai
zuwa sautukan magana. 'Yan zamanin yau ba su da lokacin da za su karanta ɗanyen kwafen ma, sai dai su
saurari sautin kawai.
Tafiya ta ƙara nisa inda mutane ba
su da lokacin sauraron sautin ma. An samu manhajojin ƙirƙirarriyar basira (AI) waɗanda suke taƙaita
littattafai domin karanta wa mai buƙata iyaka wuraren da yake buƙatar
ji kawai.
A duba sabon tsari (feature) da aka
fitar a Chrome, wato "Playback feature". Wannan tsari ne da yake ba
da dama ga wanda yake burawuzin da ya saurari taƙaitaccen bayani (summary) na shafin da ya
buɗe. Wato dai, idan
mutum ya buɗe shafin
intanet da yake ɗauke
da rubutu, akan ya sha wahalar karanta rubutun, zai danna wannan tsari. Tsarin
zai takaita (summarize) duk bayanan da suke kan shafin sannan ya karanta masa
cikin lokacin da bai haura minti ɗaya
(1) ba. Da taimakon haka, bayanan da mutum zai ɓata
mintuna ashirin (20) yana nema, zai iya fahimtar su cikin ƙasa da
minti ɗaya. Idan yana
buƙatar
ci gaba da karanta shafin, sai ya yi, idan ba buƙata, sai ya wuce zuwa gaba.
Yayin da duniya har ta kai wannan
mataki na sauƙaƙa harkokin karatu (ban da ma ɗimbin
waɗanda ba mu ambata
ba), bai kyautu ba a da'irar nazarin Hausawa mu ci gaba da muhawarar lallai
dole sai an ci gaba da bin tsohuwar hanyar koyo da koyarwa da nazari, wato ta
takarda (print copies).
An yi rubutu a kan fatun dabbobi
An yi rubutu ta amfani da allo da
tawada
An yi rubutu ta amfani da tafireta
(typewriter)
An yi yayin rubutu a kwamfuta
...
A yanzu, rubutun ma mutane sun sama
wa kansu sauƙin
yadda zai kasance. A maimakon a rubuta da kwamfuta, sai dai a ba wa kwamfutar
umarni, ita kuma ta rubuta da kanta. Kada a wannan zamani manazarta Hausa su yi
yunƙurin
mayar da hannun agogo baya cewa dole a dauwama a kan tsarin da ake.
Matsalar ita ce, idan aka kashe wa
'yan yau guiwa kan amfani da hanyoyin nazari na zamani, to fa sai dai a yi biyu
babu. Dalili shi ne, ba su zo da ruwan halitta na wancan zamani ba - ko dai su
ci gajiyar zamaninsu, ko kuma a yi hasara baki ɗaya.
Abin da ya dace shi ne a ƙarfafa musu guiwa, a tallafa musu ta yadda za su yi ƙoƙari a
wannan bagire, sannan su amfana da shi.
Rayuwar yau kanta irin ta 'yan yau
ce. Mu tuna yadda aka ce a ƙarshen zamani shekara za ta koma kamar wata, wata kamar mako,
mako kamar kwana, kwana kamar awa, awa kamar daƙiƙa... Yadda rayuwa take gudu, dole ne ɗan'adam ya yi gudu daidai
da ita. Idan ba haka ba kuwa, za ta yi masa nisa.
Duk waɗannan ba sa nufin bin hanyoyin da zai tagayyara ingancin karatu ko ya saɓa wa addini ko datacciyar al'ada. Abin nufi kawai shi ne, dole a bi datattun hanyoyin sauƙaƙa wa rayuwa da zamani ya zo da su. Dalili kuwa shi ne, shi zamani sarki ne, dole a bi shi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.