Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ba Ya Iya Biya Min Bukata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikuma malam tambayata na ita ce misali matar auren da mijinta baya biya mata bukata bakuma basa jima'i ba biyan bukatanne batasamu dagag wajenshi toh haryakai da yahaifar mata da matsalan ciwo mara shin malam wai za a iya raba aure.?

MIJINA BA YA IYA BIYA MIN BUƘATA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam wararahmatullah

Toh, yar uwa yana daga Ilimin da ya kamata a karantar da mutane, shine Ilimin jima'i a musulunci. Amma fa ba'a makarantun boko ba, a majalissai ya kamata, ba tare da lasifika ba, sabida sai mutane suke muku mummunan zato.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yace, kada dayanku ya Afkawa matarsa, kamar yadda jaki yake Afkawa jaka, idan dayanku zai jewa iyalinsa, ya kamata ya aika ɗan aike, wato ya kamata ace kafin ya kwanta da matarsa su gabatar da duk wani wasa da zai motsa musu sha'awa, domin samun gamsuwar su kansu ma'auratan.

sannan idan mutum ya sadu matarsa, bai kamata yayi gaggawar fitar da gabansa daga gabanta ba, har sai wannan matar ta sami gamsuwa daga gareshi. sabida wata matar ba ta samun gamsuwa a daidai lokacin da shi mijin ya sami gansuwa, har sai ya jira itama matar ta sami ta ta gamsuwar.

Yana faruwa Wani ba ruwansa, da zarar ya sami gamsuwa da matarsa koda a iya wasan da sukeyi ne, tofa shi ya gama, ba ruwansa indai ya samu gamsuwa koda matar ba ta gamsu ba, shi ba abinsa yayi masa zafi.

Wata matar kuma tana da doguwar sha'awa, sabida haka, idan mijinta baiyi wasa da ita ba, sannnn bai jira ta samu gamsuwa daga gareshi ba, to maniyyin da yake jikinta bazai sakko ya haɗu da nasa ba, sai dai ya tsaya mata a mararta, daga nan kuma sai ciwon mara, sai ciwon ciki, sai Warin gaba, da dai sauransu.

Wato ya kamata mu sani cewar, wasu matan suna da kunyar da bazasu gayawa mazajensu damuwarsu ba, sai dai abin yayi ta damunsu, a haka wata sai dai kawai kaga tana ta ramewa ba tare da anyi mata komi ba. matsalar ita ce rashin samun gamsuwa daga mai gidanta.

Sannan ya kamata mu sani cewar mata kala-kala ne kamar yadda maza suke kala-kala, Akwai mai karfin sha'awa, wadda idan ba ta sami daidai ita ba, akwai damuwa, sai dai kaga auren yana Kai kawo, karshe dai sai an Rabu hankalita zai kwanta, ba yinta bane, haka Allah yayita, haka suma mazan, wani idan ya sami wata matar, da kanta zata gudu, Ayi-ayi ta dawo bazata dawo ba, Amma wata tana kokari ta sanar da yan gidansu cewar yafi karfinta.

sai dai ni a wannan Fagen ina bada shawara akan mu maza, tinda igiyar Auren a hannunmu take, idan kasan matarka tafi karfinka, gwanda ku zauna ku tattauna cikin lillimi da limana, ko dai ka nemi maganin wanda bazai cutar da lafiyarka ba, wanda zai kara maka kuzari dan ka sami damar gamsar da ita wannan matar a kowanne lokacin da take bukatarka, ko kuma ka ba ta takardarta, idan har hakanne yafi Maslaha a tsakaninku.

sabida wasu matan, suna tare da mazajen da basa biya musu bukatarsu, sai suna fita suna neman wasu mazajen a titi wanda zasuke gamsar dasu, kai kuma ba mamaki ana haifar maka diyan da ba naka ba.

sabdida haka ya kamata muke kallon abinda shine yafi zama maslaha garemu. Ko kuma mutum ya auri budurwa, domin ita ba ruwanta, sai sabon da kayi mata.

Amma idan bazawara ce, wani ya saba mata da biyan bukata a koyaushe, kai kuma bazaka iya ba, kaga dole ta barka ta koma gidan da ta fito. Sabida wallahi ana samun barazana ta wannan ɓangaren, mutane suna tayimin magana, sai ta private nake basu Amsa. yau kuma dai nace bari in fede biri har wutsiyarsa.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments