Ticker

6/recent/ticker-posts

Iddar Mace Mai Shayarwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan aka saki Mace tana Shayarwa yaya hukuncin Iddarta zai kasance idan Jinin-Al'ada ya dena zuwa mata saboda Shayarwar da take yi??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wannan tambayar dama nataɓa bada amsa akanta kimanin Shekaru biyu da suka wuce, wato kamar yadda yake sanennen abu awajen Mutane cewa akwai Nau'ikan-Mata da yawa waɗanda Jinin-Al'ada yake tsaya musu alokacin da suke Shayar da Jariransu, wasu bazasu sake ganin Jiniba har sai sun yaye ''Ɗan'' da suke Shayarwa, Saidai wasu Matan jinin yakan dawō musune bayan Shekara ɗaya, wasu Matan kuma bayan watanni Shidda(6) ko wani abu makamancin haka sai suga Jinin-Al'adarsu yazo, yayin da wasu Matan kuma dama kwata kwata su Jinin-Al'ada baya tsaya musu sakamakon Shayarwar da sukeyi, kawai da Jinin-Bīƙi yaɗauke musu sai kuma Jinin-Haila yabiyo bayansa idan lokacin zuwansa yayi.

Idan ya kasance Mace batayin Jinin-Al'adane sakamakon Shayar da Jariri da take yi, Malamai sukace irin wannan Matar idan aka Saketa to zatayi ta jirane har sai tayi Jini-3 koda kuwa hakan zai kaita zuwaga lokacin da zata yaye Jaririn da take Shayarwar wato Shekaru biyu kenan, to dōlene har sai tagama waɗannan Jinane-Guda-3 sannan iddarta zata ƙare, danhaka kenan idan Sakine irin na "Kōmē" to Mijin yana da damar yace yadawō da Matarsa koda kuwa bayan Shekara biyune da yin Sakin matuƙar dai batayi Jini-3 atsakaniba, wannan maganar kuma dukkan Malamai-Fuƙaha'u sunyi Ijma'i akan haka, Hujjarsu kuwa ita ce faɗin Aʟʟaн( ) dake cikin wannan aya:

وَالْمُطَلَّقَاتُ يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ ثَلَاثَةَ قُرُوءٍ ۚ

MA'ANA:

(Matan da) aka Sakesu zasu zaunane harsuyi Jini-3 (tsarki-3) (Suratul Baƙara Aya ta 228)

Danhaka kenan idan Mace tana so Jinin yazo mata da wuri to saita bayar da Jarīrin nata wata Matar ta Shayar dashi, kokuma tayi amfani da wani magani wanda zai janyo mata al'adarta alokacin datake Shayarwar amma da Sharaɗin ya kasance ba Saki bane irin na "Kōmē" domin idan Sakine irin na "Kōmē" to bai halatta tayi amfani da magani dan ta janyo al'adarta ba, domin kuwa Mijinta yana da haƙƙi akanta na ya mayar da ita kokuma yarabu da'ita, amma idan Sakine irin wanda ba Sakin-Kōmēba to ya halatta tasha maganin da zai janyo mata jinin da wuri, amma shima da Sharaɗin ya kasance anada tabbas kokuma zato mafi rinjane akan cewa maganin yadace da Jikinta bazai cūtar da'itaba.

To amma idan ya kasance Al'adar-Mace taɗaukene sakamakon wani Sababi kamar irin na Shayarwa kokuma rashin lafiya, daga baya kuma sai wannan Sababin yagushe, Misali ace tawarke daga rashin lafiyar, ko ta yaye ''Ɗan'' da take Shayarwa, amma duk dahaka jinin bai zomata ba, to anan sai mafi yawa daga cikin Malamai sukace Iddar irin wannan Matar zata zaunane har tsawon Shekara guda cur, wato watanni-9 amatsayin mafi galibin tsawon lokacin da mai ciki take yi kafin ta haihu, Saikuma watanni-3 amatsayin Idda, idan anhaɗa yazama watanni-12 kenan.

Danhaka idan yakasance Mace zatayi Iddane na tsawon Shekara ɗaya, Misali ace tayi watanni-11, kwatsam kawai sai taga Jinin-Al'ada yazo mata, to yanzufa lissafincan da tayi na watanni-11 yariga yarūshe, danhaka yanzu dolene sai ta sake jiran zuwan Jini na-2 da na-3 idan bai zoba har ta sakeyin wata Shekarar guda cur, to shikenan tagama idda, amma idan taga Jini na-2 yazo koda kuwa ta sake yin wasu watanni-11 da zuwan na farko, to anan ma lissafinta yasake rūshewa, danhaka dole sai ta sake jiran wani Jini na-3 yazo sannan tagama idda, idan kuma jini na-3 bai zoba har ta sake yin wata Shekarar shikenan tagama Iddarta.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'α'αʟαм

AMSAWA

Mυѕтαρнα Uѕмαn

08032531505

Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:

'' ﻣﻮﺍﻫﺐ ﺍﻟﺠﻠﻴﻞ " ‏( 3/404 (

" ﺍﻟﺘﺎﺝ ﻭﺍﻹﻛﻠﻴﻞ " ‏( 4/143 (

" ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ ﻹﺑﻦ ﻗﺪﺍﻣﺔ " ‏( 8/87 (

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments