𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Ina da tambaya, tambayata gata kamar haka Allah gafarta malam ina cikin tafiya a matsayina na namiji sai na tarar da mata a hanya toh ko zan iya yimasu sallama?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam
warahmatullahi Wabarkatuh
Da farko dai Allah ya
umarcemu da yaɗa sallama a tsakaninmu ya kuma wajabta
mana mayarda sallama ga daukacin musulmai. Ya sanya sallama ta zama wani abu
dake yaɗa
soyayya a tsakanin muminai. Allah yace:
وَإِذَا
حُيِّيتُمْ بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوا بِأَحْسَنَ مِنْهَا أَوْ رُدُّوهَا ۗ إِنَّ
اللَّهَ كَانَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ حَسِيبًا
Kuma idan an gaisheku da
wata gaisuwa, to, kuyi gaisuwa da abinda yake mafi kyau daga gareta, ko kuma Ku
mayar da ita, kuma Allah ya kasance akan dukkan komai mai lissafi. [Suratul
Nisa'i aya ta 86]
An ruwaito Abu Hurairah
Yace; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Yace: baza ku shiga aljannah
ba har sai kunyi imani, baza kuyi imani ba har sai kunso junanku. Shin bazan
gaya muku wani abu ba wanda idan kunyi shi za kuso junanku?, Ku yaɗa
sallama a tsakaninku, za ku so junanku" (Muslim ne ya ruwaito shi a hadisi
mai lamba 54).
Umarnin yaɗa
sallama umarni ne ga kowa (maza da mata) kuma ya shafi dukkan musulmai. Ya haɗa da
maza suyiwa maza sallama, mata suyiwa mata sallama, da sallama tsakanin
muharraman juna. Anan an shar'anta sallama a tsakanin wannan sashe yayi sallama
ga ɗayan
sashen da ya aka wajabta ma mayar da sallama.
Amma akwai hukuncin da ya
hana namiji yin sallama ga macen da ba muharramarsa ba idan yaji tsoron aukuwar
fitina a dalilin wannan sallama.
Babu laifi ga namiji yayiwa
mace sallama batareda yin musabaha da ita ba, idan ita tsohuwa ce. Amma bazai
yiwa wacce ba tsohuwa ba sallama idan baida tabbacin rashin aukuwar fitina.
Wannan shine sharhin malamai Allah yayi musu rahama.
An tambayi Imam Malik shin za
a iya yiwa mace sallama? sai yace: "Idan tsohuwa ce banga karhanci a
sallamar ba, amma idan ba tsohuwa bace bana son haka"
Al-Zarƙaani yayi bayanin dalilin da yasa imam
malik yace baya son haka, a ```sharhinsa na Al-Muwatta```: Saboda yana tsoron
fitina idan yaji muryarta idan zata mayar da sallama.
Acikin _*(Al-Adaab
al-Shar'iyyah 1/370)*_ ance:
Ibn Muflih ya kawo cewa Ibn
Mansoor ya tambayi Imam Ahmad akan yiwa mata sallama sai yace: Idan matar
tsohuwa ce babu laifi.
Saalih (Dan Imam Ahmad) Yace
na tambayi babana akan yiwa mata sallama sai yace: sallamar da ta shafi
tsofaffin mata babu laifi, amma waɗanda
ba tsofaffi ba baza a sa suyi magana ba wajen mayar da sallama.
Al-Nawawi yace acikin
littafinsa mai suna _*Al-Adhkaar a shafi na 407)*_ cewa: Sallamar mata ga mata
yan uwansu kamar sallamar maza ne ga maza. Idan macen kuma matarsa ce ko
baiwarsa ko muharramarsa, to kamar shi ne yake yin magana da wani namiji.
Saboda haka zasu yiwa juna sallama haka mayarwa.
Amma idan wata mace ce daban
kuma tanada kyau, kuma yana jin tsoron zata fitineshi, to shi bazai yi mata
sallama ba, idan kuma yayi mata sallama, to bai halatta ta amsa masa ba.
Hakanan itama bazata yimasa sallama ba, idan tayi masa bazai amsa mata ba, idan
ya amsa to yayi makaruhi.
Idan akwai taron mata,
namiji zai iya yi musu sallama. Haka idan taron maza ne zasu iya yiwa mace
sallama matukar akwai yaƙinin
cewa dasu da ita babu Wanda zai fitinu.
An ruwaito daga Asma bintu
Yazeed (radiyallahu anhaa) tace; Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) ya
wuce ta wajenmu (Mata) sai yayi mana sallama. (Abu Dawood, 5204). Albani ya
ingantashi a Saheeh Abi Dawuda.
Al-Haafiz yace acikin
Al-Fath: Akan halaccin sallama tsakanin mata da maza: Abinda ake nufi da ya
halatta shine idan babu tsoron fitina.
Al-Haleemi yana cewa Saboda
Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) Ma'asumi ne kuma an kiyaye shi daga
fitina. Duk wanda keda yaƙinin
ya tsira daga fitina, to zai iya yiwa mata sallama. Idan kuma akasin hakan ne,
to ya tsare kansa yayi shiru.
An ruwaito Al-Muhallab yana
cewa: Ya halatta maza suyiwa mata sallama haka mata suyiwa maza sallama idan
babu fitina.
Domin Neman karin bayani
duba: _*(Ahkaam Al-Awrah wa'l-Nazar na Musaa'id ibn Ƙaasim al-Faalih.*_
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.