Maryam Umar (2023). Gadar Zare. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD
GADAR
ZARE
Na
Maryam Umar
Zaren rayuwata ya fara tsinkewa ne tun daga ranar da nayi
wa Bangis dukan kawo wuƙa sanadiyar asirina da ya tona a
wurin Magaji da ce war ni na dauki kayan sana’arsa da suka fi komai da kowa
daraja a faɗin duniyarsa.
Hakan
ya sanya Magaji hukuntani da hukunci mafi tsanani da cutarwa a rayuwata.
Tsananin
damuwa da tashin hankalin da na samu kaina a ciki su suka daskarar da gudun
lokaci a wurina. Ban san lokacin da na ƙara
duba agogo a karo na barkatai ba ina mai lissafin sa’o’in da suka rage gari ya
waye, Ina mai ƙoƙarin fahimtar ko ni kaɗai
ce duniya kan rub’anya wa tsawon lokaci a wannan yanayi.
Na
miƙe daga kan shimfiɗata
ina mai riƙe b’aren kaina da ke barazanar
tsagewa. A lissafe ina cikin awa ta talatin da tara rabon da in runtsa da sunan
barci, wanda ba shakka yana ɗaya daga cikin abin da ya ƙara jefa ni cikin ƙuncin rayuwar da nake ji.
Na
matsa kusa da makunnin fanka na ƙara
gudunta, ganin yadda suturar jikina take jikewa daga tsananin gumin da ke fita
a jikina.
Kamar almara cikina ya shiga murɗawa, kan a fara
kiraye-kirayen subahi na yi laga-laga tamkar tabarmar tsohuwa, ina jin alamun
motsawar mutanen gidan na rarrafa bakin ƙofa na fasa kuka da
neman agaji.
Sai
da gari ya yi yanyar sannan ya sanya ɗan
mukulli ya buɗe ɗakin.
Yana sanyo ƙafarsa na fara kelaya
amai. Bai ce uffan ba har sai da na gama na rarrafa a gabansa ina tsananta
raunina.
“Magaji
na rantse da Allah ban ɗauki kayanka ba.”
Ya
ture ni da ƙafarsa, cikin
tsananin takaici ya ce.
“Sai
yaushe za ki daina karya? To bari in faɗa
miki Halima, dole za ki fito da kayan nan kuma daga yau ba ke ba shan kwaya,
sai dai ki mutu a cikin gidan nan.”
Ya
juya zai fita, na ruga a guje na sha gabansa ina mai cewa.
“Na
yarda Magaji, ba zan ƙara
shan komai ba, amma dan Allah kar ka rufe ni a dakin nan, wallahi mutuwa zan
yi.”
Ya
ture ni ya fice bayan ya mayar da kofar ya rufe.
Ina ji Mama a tsakar gida tana zuba ruwan bala’i da Allah
wadai da irin halin ɗauke-ɗauken da na kan jefa kaina har lokacin da na kara jin
shigowar Magaji tare da abokin harƙallarsa, Dakta
Yusuf, ya ranƙwafo ta inda nake kwance ya tab’a
wutsiyar hannuna wanda hakan ya sanya ni tashi zaune na jingina a kan bango.
“Halima,”
ya kira ni cikin sanyin murya da lallashi.
“Me
yake damunki?”
Na
buɗe
bakina da kyar na ce.
“Komai damuna yake yi, ba ni da lafiya, amai da zawo,
kaina ciwo ba na iya barci, mutuwa nake ji.”
“Yanzu
me kike so a ba ki?”
Sai na ji tamkar gatse ya yi min, ya sanya hannunsa a
aljihu ya fito da kwalbar da nake jin ƙoƙon raina a cikinta, nan take wani ƙarin tashin hankali ya ziyarci ni na kamo hannunsa na ce.
“Wallahi
na rantse idan ka ba ni wannan ba zan ƙara ɗaukar
kayan Magaji ba. Kai! ba ma zan kara shan komai ba.”
“Ki
faɗa
min inda kika ajiye kayan da kika ɗauka
a ɗakin
Sani, zan ba ki wannan kuma zan sa ya bar ki ki fita.”
Da
sauri na girgiza kai ina rantse rantsen ban ɗauka
ba.
“Halima Fentanil kika ɗauka fa, kwayoyi da
alluran da kika ɗauka suna da matuƙar haɗarin da sun zarce
heroyin da kika sani sau da yawa ta kuma fi mofin hadari.
Ba kowa zai sha fenta ya zauna lafiya ba duk kilogiram
daya nata zai iya kashe mutum dubu dari biyar, saboda idan mutum ya hadiye
wanda ya fi karfinsa, numfashinsa zai tsaya ya daina isa ga kwalwarsa, hakan
zai iya sanadiyar dogon suma ko ma mutuwa nan take.
Ba
ma wannan ba Halima, kayan da kika dauka ba na yara bane, dan Allah ki rufa
mana asiri ki fito da kayan mutane.”
Sai
na ji nan take na faɗa soyayyar Fenta, na ƙara jin wani irin zumuɗin
ganin na ɗanɗani
abin da ke cikinta.
Dakta
ya yi lallashi ya gaji na kafe kan ban ɗauka
ba, sai ya mike ya bar ɗakin. Daga bakin ƙofa na ji sa yana cewa.
“Sani
zan rubuta mata Metadon da zai taimaka mata daga ciwon sabon da ta faɗa,
kafin ka samu kuɗin tura ta asibitin Kano,
idan ba haka ba wannan yarinyar haukacewa za ta yi. Duk wannan soshe-soshen da
take yi da ta koma ruwa zata miƙe.”
“Asibitin
Kano?”Na furta a daburce, domin kuwa a yanzu na gwammace zuwa lahira da
asibitin Kanon.
Na
shiga bayi na sake fitowa cikin rudewa, cikin mamaki sai na ga kofar dakina a
bude.
Nan
take na mike har ina jin yadda karfin jikina ke dawowa na fice daga gidan ina
adu’ar kada Allah ya sa Mama ta gan ni.
Da
fita na tari abin hawa ya kai ni ɗakin
Salo da ke cikin kwatas dinsu. Ina zuwa na tarar da Bangis da Jami’u duk a
cikin dabar, ganin Bangis a wurin ya sanya ni jin ɗadi,
da alama yau zan ƙara
koya masa hankali ta yadda zai daina kawo gib’i a jindaɗina.
Kai tsaye na shige ɗakin Salo na balle katakon
gadonsa na fito da baƙar
ledar da na yi b’oyon dukiyata a ciki. Ina fitowa suka shiga ihu da neman sanin
me na ƙunso a ciki, na zauna gefen saurayina
Salo na fito da kwayar fenta wadda ta kasance kalar bula an rubuta mata lamba
talatin.
“Mtss! Ke kullum ba kya ci gaba, yanzu kuma kwaya za ki
koma sha?”
Jami’u ya faɗa yana busa hayaƙin wiwi da ya zamo
masa jaraba.
“Gwara ni, komai zafin kwaya kaina zai dauka, kai da
Dizefam kawai ka sha ka tashi mutuwa fa.”
Sai
ya kwashe da dariya, sannan ya ce.
“Da
alama wanda kike yin domin shi baya jinki.”
Ya
mayar da kallonsa a kan Bangis wanda tuni lemun kwalbar da ya sirka ya fara
gigita tunaninsa wanda hakan ya sanya ransa b’aci nan take, ni kuwa wani irin
farin ciki nake ji wanda a irin wannan lokacin ne kawai rahama kan sauka a
fuskata.
Nan
take sai Bangis ya hasala ya kwace ledar kwayoyin da ke hannuna ya zuba guda
goma a hannunsa ya ce.
“In sha goma ki sha goma, Jami’u ka yi mana bidiyo duk
wanda ta b’arar ba zai ƙara shiga harkar ɗaya ba.”
Ya
faɗa
cike da izza wanda hakan ya sanya jama’ar da ke wajen fashewa da ihu ana
jinjina masa.
Na
miƙe tsaye na zazzage kwaya goma da allura
biyu a hannuna na ce.
“Ni
na yarda har da allurar ma.
Amma
ka sani, wannan kwayar mutuwa ce dan haka dani da kai duk wanda ya rayu shine
gwarzo kuma ba zan ƙara
zuwa gidanku na kai ƙara
ba.”
Wuri
ya ƙara karaɗewa
da ihu, nan take Bangis ya jefa kwayoyin a bakinsa, ya kora da ruwa.
Tuni n san zai sha domin kuwa kamar yadda ya addabe ni
haka nima na gallabi rayuwarsa wurin tona asirin shaye-shayensa kasancewar
shine mafi zama ƙarami a cikinmu.
Da
shanyewarsa sai na zauna ina dariya, na ce.
“Na
yarda na faɗi, ba zan ƙara
tona maka asiri ba.”
Sai
aka shiga tsokanata da yi min dariyar kasawa wasu kuwa sun gano logona da gayya
na ƙular da shi.
Kamar
daga sama Bangis ya fara kakari yana rike maƙoshi
tamkar mai yin dambe da nufashinsa.
Nan
take ya fadi yana fitar da kumfa a bakinsa, da kuma ƙoƙarin
jan numafshi, sai kuma ya daina kokawar, jikinsa ya saki tamkar sabuwar gawa.
Nan
take hankula suka tashi aka fara ihun neman agaji.
“Halima
ki bar nan, Bangis ya mutu kuma ke kika kashe shi.” Salo ya raɗa
min a kunne lokacin da muke ƙoƙarin tallabo Bangis, sai a lokacin
tunanina ya dawo, na fahimci al’amarin da ke faruwa duk da irin tsanar Bangis
da alƙawarin halaka rayuwarsa da na sha yin iƙirari ba hakan na nufin ina neman
hukunta shi da mutuwa ba, a’a so nake ya shiga mawuyacin halin da iyayensa zasu
ɗauki
tsattsauran matakin da zai yi sanadiyar ficewarsa daga dabarmu.
Sayyada
na tako har unguwarmu domin tuni lissafin ƙwaƙwalwata ya rikice. Ina isa na tarar da
Magaji yana surfa wa Mama bala’i Kan fitar da na yi ba tare da saninsa ba.
Da shigata sai ya yo kaina da duka wanda hakan ya sanya
ni rugawa ɗaki na fara haɗa kayana na ƙulle su a leda na
fito tsakar gida ina mai cewa.
“Mama ki ce ya kai ni Kano amma ba asibiti ba, wurin Kawu
zan je, dan Allah mu tafi yanzu-yanzu.”
Mama
ta shaƙo wuyana ta ce.
“Barnar
me kika aikata kuma? Daga ganin wannan rawar jikin ba ki da gaskiya, ga ki nan
tsinkau, tsiyau kamar kazar matsiyata, bala’i ne kawai tattare da ke, ke ba
sata ba ke ba dabanci ba.”
Na
kwace kaina da kyar, sai kuma kunnuwana suka fara jiyo min jiniyar motar ƴan sanda.
Nan
take na yi watsi da ledar hannuna na ruga a guje na bar gidan yayin da Magaji
ya biyo ni, tuni na yi masa nisa.
Tsananin
tsoro da tausayin halin da na sanya Bangis sun taru sun yi mini rubgudu, ina
son sanin halin da yake ciki sai dai ba zan ƙaunaci
me zai je ya dawo ba.
Ina
ganin an fara shigewa masallaci domin sallar magariba na ƙoƙarta
na fito daga kwalbatin da na shige, na yanke shawarar komawa gida domin ban san
ina zan tunkara ba.
Tarin
mutane a ƙofar gidanmu na
hango, yayin da ihu da kukan Mama ya cika sararin unguwar, ganin haka sai na
fara ja da baya, ina mai neman komawa inda na fito. Kwatsam, na ji an tokare ni
ta baya. Sai na ɗaga hannayena cike da
saranda, ina ce wa.
“Kar
ku harbe ni. Wallahi ba ni na kashe shi ba.”
Na
haɗiye
yawu da ƙyar lokacin da na ji an sauke hannayena,
ba tare da an ce komai ba kuma sai aka ja ni har cikin mota.
Sai
a lokacin na ɗaga kai na kalle shi, na san shi, ba
abokin Magaji ba ne amma nakan kai masa kaya a bayan layinmu duk da kullum
cikin takunkumi nake ganinsa.
Kai
tsaye ya cire takunkuminsa, ya yi murmushi, nan take na ji rabin tashin
hankalina ya b’ace.
“Sahibi,
Sahibi sunana.”
Ya
furta yana mai kawar da kai daga kallona, sai ya tada motar sannan ya ci gaba
da ce wa.
“Bangis
bai mutu ba, amma ya faɗa doguwar suma. Me ya sa ki
ka ba shi kwayar Fenta bayan kin san yana fama da cutar Arritamia?”
Na
ware ido domin neman ƙarin
bayani.
“Matsalar bugun zuciya nake nufi, fentaniyil fa kwaya ce
da ake bai wa masu ciwon kansa ko wanda aka yi wa tiyata domin rage raɗaɗi.”
Sai
a lokacin na samu damar fashewa da kuka.
“Ni
ban san bai zai iya sha ba. Yanzu me za ayi min?”
Cikin
mamaki sai ya yi dariya daidai lokacin da yake karya kwana, sannan ya ce.
“Ƴansanda sun tafi da Magajinki, sai sun
kamo ki sannan za su sake shi.”
Sai
na dafe gabana cikin tashin hankali na ce.
“Dan
Allah kada ka kai ni, wallahi ba zan sake shan komai ba, kai ni na tuba Allah
ya yafe mun.”
Na ƙara
sautin kukana, har ga Allah nadama ta sauka gare ni sai dai ba ni da tabbacin
taubatun nasuha nake yi.
Sai
ya fashe da dariya sannan ya ce. “Ga tsoro ga ban tsoro.
Gobe
zan je in taho da Magajinki, yanzu za ki zauna a nan ne har komai ya dawo
daidai.”
Daga wannan lokacin sai na faɗa kogin soyayyarsa,
mussaman da ya tarbe ni da kwalaben kodin da suka sanya ni manta alƙawarin tubana.
Na kwashe mako biyu a gidan Sahibi, yaro ne ga kyau ga
kudi ga iya sanya nutsuwa a zuciya, ni kuma dama a rayuwa ba abin da nake so
tamkar jin daɗi.
Shi
ya je ya taimaka wa Mama da kuɗi, duk shige da ficen da aka
yi har aka sako Magaji maganar Bangis ta mutu.
Sai
a lokacin su Mama suka san inda nake, suka kuma san tuni mun nutse a son juna.
Nan
take ya samar wa Magaji sabbin kwastomomi, sai dai al’amarin da ya fi ba ni
mamaki ko sigari Sahibi baya sha. Da na tambaye shi me yake yi da kwayoyin da
yake saya a wurin Magaji sai ce wa ya yi.
“Bana
shan komai, ina son rayuwata me yasa
zan wofintar da ƙuruciyata
wurin shaye-shaye?”
Maganar
bata yi min ɗadi ba duk da cewa ina sane da gaskiya
yake faɗa.
Haka
Sahibi yake tamkar zuma; ga zaƙi ga
harbi.
Mama
burinta ya gama cika domin kuwa tuni Sahibi ya sanya maƙudan kuɗaɗe
aka gyara gidanmu, Bello da Fatima suka koma makaranta sai ta dawo kushe sana’ar
Magaji ganin cewa yana harkar kuɗi
amma ba sa ma shi amfani, ranar a gabana har cewa ta yi.
“Ni kam Sani, da ƙulle-ƙullen tabar nan da kake sayarwa da ma dan POS din nan ka
buɗe ya fi maka wannan tambaɗar da kullum cikin
daru kake da mutanen banza, ɗan auren nan da kannenka ke yi kai ka kasa riƙe matar ma. In ban da sanya kan ka a
hatsari, ba abin da ta amfane ka.”
Sai
kuwa ya yi cikinta da bala’i wanda dole ta dawo ba shi hakuri.
A yanzu dai ni ce ‘yar gwal, duk da ba ta yi min son da
uwa ke yi wa ‘ya, ni ina ƙaunarta
kwatankwacin yadda zan so wadda ta haife ni duk da ban tab’a sanya ta a ido ba
sanadiyar ko bude ido ban yi ba ta koma ga Allah, Mama ta raine ni bayan
mahaifina ya auro ta bayan mutuwar aurenta da mahaifin Magaji.
Sannu a hankali idan na sirka maganina a lemun kwalba ba
ya sanya ni nishaɗi, koyaushe neman ƙari nake yi wanda
hakan ya sanya Sahibi ba ni shawarar gwada allurar hiroyin tare da busa tabar
wiwi wanda ada can bana yi.
Haka ko aka yi na sanar da Mama zan raka Sahibi wurin
biki, to dama ba damuwa da inda zan sanya ƙafa take yi ba muddin za a dawo mata da abin hannu, bale
ma Sahibi da take jin sa tamkar ɗanta.
Ko kaɗan ban samu fargabar miƙa hannuna Sahibi ya juye min ruwan hiroyin a jijiya ba,
bayan wasu mintuna sai na ji an lullube ni da wani irin bargo mai tsananin
laushi da sanyi, nan take sai na ga taurari sun yi wa ɗakin kwalliya yayin
da fuskar Sahibi ta daɗa haske wurin, sai na yi mumushi mai sauti ina jin wani
irin farin ciki da tsumayin yanayin da na samu kaina. Sai
kuma nan take ɗakin ya cika da ruwa har ina batun
nutsewa.
“Num...fa..shi...naaaa” na furta da kyar, sai kuma na ji
ni tsumdum a cikinsu sanyinsu yana ratsa ni yayin da Sahibi ke ƙoƙarin faɗa mini wasu kalaman
da na yi tunanin an ɗauki shekaru kafin labbansa su haɗa kalma daya.
“Fa...rin...cikiiiiii.”
Daga nan kuma sai farkawa na yi safiya ta waye.
Daga lokacin sai na faɗa tarkon hiroyin da
hayaƙin wiwi, ba na iya kwana ba tare da na samu ɗaya daga ciki ba.
Jin daɗina ya fara ƙarewa ne tun daga
ranar da Magaji ya yi faɗa da wasu mutane, bayan na je kai musu saƙonsu a bayan layi kamar yadda aka saba, sai suka yi ƙoƙarin yin lalata da ni. Cikin rashin
sa’a Magaji ya biyo ni bayan wayar da Sahibi ya yi masa, wanda hakan ya sanya
shi ƙoƙarin faɗa da su, nan take
suka harbe shi a ƙafa da gadon baya, a asibiti aka zo
ana neman sama da milyan hudu domin a yi masa aiki.
Hankalinmu bai gama tashi ba sai da muka nemi Sahibi sama
da ƙasa babu shi, sai daga baya ya zo min da sabuwar fuska ko
kuma in ce fuskarsa ta ainihi da ya jima yana ɓoyonta. Ya
zo min da yarjejeniyar da zai biyani miliyan biyar idan aka yi nasara.
“Yanzu
ya za a yi na ɗauki hodar ibilis daga nan har Dubai ba
tare da an kama ni ba?” Na fada cikin gumjin kuka ina mai Allah wadai da irin
gadar zaren da na saka wa kaina.
“Kar
ki damu, za a sanya ta a leda sannan a daure ta da salatif a saka a balo daidai
yadda za ki iya hadiye ta.”
Ya ƙara tabbatar min da ba za a samu matsala
ba har sai da nutsuwa ta zo min, musamman da ya tabbatar min Mama za ta raka ni
har Dubai yadda zargi zai ragu.
Muka nufi filin jirgin da ke birnin Abuja cikin tashin
hankali da tsoro, mussaman gargaɗin da aka yi min na idan kwaya ɗaya ta fashe ko
minti biyu ba zan ƙara yi a duniya ba.
Na fara raba ido ina neman kamannin da aka ba ni tare da
umurnin kwaikwayon duk abin da ya aikata ba tare da magana ta haɗa mu ba, wanda
hakan ne zai ba mu sauƙin kai wa ga mazauninmu na jirgi ba
tare da wahalar tambaya ba, sai ga shi ya bayyana gabana cikin farar shadda da
farin gilashi kazalika ya ɗaura shuɗin ƙyalle a wutsiyar
hannunsa maimakon agogo tamkar yadda Sahibi ya misalta mini.
“Mama
mu je.”
Na
ja hannunta kasancewar tuni an yi gaba da jakunkunanmu.
Wani
layi ya nufa wanda nan take na gane ‘yan imigireshon ne. Aka ba mu wani fom
domin cike bayanan inda muka fito, da kuma inda muka dosa.
Na cike nawa, na cike na Umma kamar yadda na ga ya yi,
sannan suka karɓi fasfo da kuma shaidarmu ta shige da fice domin duba
sahihancinsu.
Ci gaba muka yi da bin sahun mai farar shadda har zuwa
gaban ‘yan kostom da yake ba mu mallaki dukiyar da ta wuce doka ba, dan haka ba
mu sha wahalar cike-cike ba, muka sa kai muka fice.
Gabana ya yi mummunar faɗuwa ganin dogon
layin da muka shiga na binciken ƙwaƙwaf, cikina ya murɗa duk da cewar ƙwaya uku na sha na filajin domin ɗaurewar ciki.
Mama
ta kama hannuna ganin yadda ƙafafuwana
ke neman butulce mini a daidai lokacin da na fi buƙatar tsayuwarsu.
Jikina ya fara rawa ganin baƙaƙen karnukan da ke zagaye mu tamkar
mafarauta, ina jin yadda ƙulle-ƙullen da na haɗiye a cikina suke gugar hanjina wanda hakan yake haddasa
mini murɗewar ciki na wucin-gadi.
Na ɗauki jakar hannuna na koma gefe ina jiran Mama wadda
daidai lokacin da take takowa zuwa wurina kamar daga sama jami’an hulɗa da miyagun ƙwayoyi suka zagaye ni.
“Me
na yi? Ina za ku kai ni?”
“Za
mu shiga dake ɗakin bincike ne.”
“Mama!
Mama!! Mama!!!”
Cikin
mamaki sai na ga ta ƙi
kallo na kazalika na duba gabas da yamma ban ga mai farar shadda ba.
Daga
shigarmu sai aka bani wani ruwa na sha wanda ban mayar da minti ashirin ba na
yo kashin duk najasar da ke cikina.
Aka tabbatar da laifina kan ƙoƙarin safarar Hodar ibilis mai nauyin
giram goma zuwa wata ƙasar, garin neman ceton kaina aka ƙara tabbatar da laifin mutuwar Bangis mai shekaru goma
sha bakwai a kaina wanda iyayensa da ‘Yansanda suke neman haƙƙinsa.
Sai da na share watanni shida a asibitin rehabilitashin
domin yin yaƙi da sabon da na yi da kayan maye,
wanda tuni yawan allurar jijiyar da na sha ya jefa ni a tarkon dauɗar huhu da toshewar
jijiya, zunubin bai tsaya nan ba har sai da ya taɓa lafiyar hantata.
A watanin da nayi a gidan gyara hali kafin a yanke min
hukunci sai na yi sha’awar aikata aiki ɗaya da zai sa a tuna da ni bayan
mutuwa, ban bar ɗa ko jika ba amma zan bar labarina dan ya zama izna ga
masu son jin daɗi duniya kamar ni.
Na ajiye alƙalamina ina mai jimamin
yadda matakai uku na rayuwar Ɗan Adam suke cike da
haɗari, ba shigowa duniyar ba; a’a, yadda duniyar takan ja linzamin
ƙaddarorin kane abin fargaba, duk da kasancewar ita Ƙaddara rubutacciyace, sai dai tuni linzamin tawa ƙaddarar ya kubce mini har ta rikiɗe zuwa zaɓaɓɓiyar ƙaddara mai sa Ɗan Adam ga mummunan
siraɗin da yake da hauhawa uku: Farkonsa ƙare rayuwa ba ’yanci.
Tsakiyarsa mutuwa ba more zunubi. Ƙarshensa kuma shiga aljannar duniya,
sai na saƙa nawa siradin da zare wanda ya tsinke
mani a tsakiyar tekun jahannamar duniya.
Ziyarar ƙarshe da Salo ya
kawo min yake sanar da ni dama hakan ce sana’ar Sahibi, ya fara soyayya da
yarinya sai ya san ya ta yi masa safara, daga nan zai biya ta kuma ba za ta
sake jinsa ba.
Bai
tsaya a nan ba, hatta mutanen da suka harbi Magaji
duk a cikin gadar zarensa ce wanda hakan ya tilasta
muna neman kuɗi a wurinsa.
Nan
ya shaida min a Dubai aka kama Sahibi wanda tuni an zartar masa da hukuncin
kisa, sai kuma ya ba ni mummunan labarin mutuwar Magaji, ta yadda sai da ya yi ɗoyi
makwabta suka ji, na za ta mutuwar Magaji za ta sanyaya min, amma sai na ji
tausayinsa ya kama ni, duk da shi ne sanadiyar salwantar rayuwata, hakan bai
hana sa ɗaukar
alhakin hakan ba wurin ceto ni da sadaukar da dukiyarsa domin neman ilimina da
na yi fatali da su tun ina kan ganiyata.
Mama
kuwa ba labarinta, duk da ana saka ran ta koma ƙauyensu.
Jami’u
ma ya haɗu da
ciwon mantau tun fatin ƙwaya
da suka yi na murnar haihuwarsa.
Sai
tausayin su ya kama ni na fashe da kuka
ina mai tir da abin da rayuwa ta ba ni da irin munin abin da na girba.
Tun
da safe na yi wanka na sanya fararen tufafi da turare mai sanyi domin karb’ar
hukuncin da shari’a ta tanadar min. Shaihin Malamin da ya yi min jagora ya fara
yi min nasiha da neman yarda da ƙaddara
mai kyau ko akasin hakan.
“Ba
sauri kika yi ba, mu da ba mu tafi ba, ba
jinkiri muka yi ba. Shi Ubangiji mai gafara ne muddin ba ka haɗa
shi da waninsa ba.”
Ni
kuma sai na ci gaba da rubutuna ina mai shaida wa Ɗan Adam ya amfani lafiyarsa kafin tsufansa, rayuwarsa gabanin mutuwarsa.
Ina
ji aka rufe idona, sai na fara karɓar
kalmar shahada gabanin na miƙa wa
Shaihi littafin gadar zaren da na saƙa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.