Ɗanladi Haruna (2020). Tushen Farin Ciki. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.
TUSHEN FARIN CIKI
Na
Ɗanladi Haruna
Yanayin garin ba yabo ba fallasa, to amma duk da kasancewar akwai lullumin
gajimare, zufa na bajekolinta. Cikin ma’aikatar ilmi kuwa, a ofishin su
Sammani, sanyin Iyakwandisha ne ke karakaina gwanin daɗi.
Ibrahim Shehu na ta waɗari cikin kwamfuta. Sammani kuma na zaƙulo takardu a
fayiloli yana miƙa masa. Ni'imar ofishin bata sa fuskar Sammani ta sauya daga
ta shanu ba, lokaci zuwa lokaci sai ya girgiza kansa ya yi ajiyar zuciya.
Ibrahim ya lura da yanayin da Sammani ke ciki. Bai ce masa komai ba, har sai da
suka kammala aikin tukunna.
“Yau da alamun baka cikin walwala. Allah ya sa dai ba Madam ce ta jawo ba.”
Ibrahim ya ce da Sammani cikin zolaya. Sammani ya yi ajiyar zuciya
ya ce, “kai dai ayi sha'ani yallaɓai. Yau da nahisa na tashi. Gidana da kwanaki
katangar ta rushe sakamakon ruwan sama, yau kuma ɓarawo ya shiga ya sace min
ragon sunan da na yi tanadi. Ga haihuwa ko yau ko gobe.”
Cikin tausaya wa Ibrahim ya ce, “assha! Abu bai yi daɗi ba, Allah ya
maida alheri.”
“Amin yallaɓai. Na gode.” Sammani ya faɗa. Daidai lokacin wayarsa ta yi
ƙara. Ya duba ya ga matarsa ce ke kira. Ya ɗauka. Ya ji muryarta a raunane tana
magana kamar mai raɗa cikin alamun ciwo.
“Ba ni da lafiya. Ka ceci raina!”
A ɗarare ya ce, “gani nan zuwa mu je asibiti.” Ya dubi Ibrahim watau
maigidansa na ofis ya ce, “yallaɓai, zan koma gida. Wataƙila haihuwar ce ta zo.
Tana kwance ba lafiya.”
Ibrahim ya ce, “Allah ya raba lafiya. Ka hanzarta kai ta asibiti. Kar a
zauna gida tsammanin wa rabbuka.”
Tuni Sammani ya yi fita bai ji ƙarshen maganar maigidansa ba. Ya buga
babur ɗinsa da hanzari ya fita daga ma'aikatar tasu ya nufi gida. Lokacin kuwa
gari ya soma canja kamanni, yanayin samaniya ya zama murtuk. Curarrun gajimare
sun dunƙule sun lulluɓe hasken rana, cikin hanzari kuma suka rikiɗe zuwa
baƙiƙƙirin. Babu jimawa iska ta soma kaɗawa tana awon gaba da tarkace da sauran
abubuwa marasa nauyi.
Ƙura na bubbule fuskar
Sammani ya yin da yake shara gudu, amma bai kula ba. Burinsa ya isa gida ya
taimakawa matarsa. Ya san wannan watan ne zata haihu, don haka ya shiga tanadin
kayan haihuwa amma ga ɓarawo ya yi
masa ƙafar ungulu.
Bai yi nisa sosai ba ruwa
ya tsuge kamar da bakin ƙwarya. Shi kuwa kamar kaza yake, idan ruwan sama ya taɓa
shi sai ya kwanta zazzaɓi. Don haka ya zaɓi hanyar lafiya a bi ta da shekara.
Ya samu waje ya fake.
Yana fakewa sai wayarsa
ta shiga ƙara, alamar kira ya shigo. Ya duba mai kiran. Matarsa ce. Nan take ya ji hankalinsa ya tashi. Ga bikin
zuwa amma babu zanin ɗaurawa. Sammani na tsananin ƙaunar matarsa. 'Yarsu ɗaya,
yanzu ne haihuwa ta biyu. A baya a gidansu ta haihu.
Unguwar Zurmawa inda gidan Sammani yake, galibi 'yan 'Rabbana-Ka-wadata mu’
ne ke zama irin na 'yan marina. Kowa da inda ya sa gaba. Duk da sababbin
gine-gine ne amma kowanne gini da inda ya karkata. Gwamutsin gine-ginen ya jawo
cunkoson lunguna da kwataman da ruwan da ba ya gudana. Kana dosar unguwar za ka
wani iri ɗoyi gami da samami na tashi. Ga wani irin zafi mai ratsa jiki na
bugun fuska. Mata da yaran unguwar sau tari su kan kamu da wasu irin ƙuraje da
tari mara kan gado.
Gidan Sammani wanda a baya yake a sarari, yanzu ya koma cikin lungu
sakamakon ginin da aka yi wanda ya toshe babbar hanyar shiga unguwar.
Duk wani ƙoƙarin hanya da mutanen unguwar suka yi domin daƙile ginin ya
tashi a tutar babu. Wannan ginin ya toshe babban layin unguwar, har ya zamana
babu inda mota za ta shiga, sannan magudanan ruwa duk sun toshe. Shi kuwa ruwa
ba a yi masa shamaki, da aka toshe masa hanya, sai ya koma gidajen da ke kusa
ya mamaye, masu rarraunan gini suka yi ta zubewa ciki har da katangar gidan
Sammani. Da buhu ya kange gidansa yadda ba za a hangi ciki ba.
Ya kara wayar a kunnensa
yana mai cewa, “ina tafe. Ruwa
ne ya hana ni isowa.”
Cikin rarraunar murya ta ce, “ga maƙota sun zo za mu tafi asibiti.”
Ya ce, “to a samu abin hawa kafin na zo.”
Daga ɗaya ɓarin sai ya ji maganar wata mata na faɗin, “bani wayar na yi
masa magana.” Ya ji muryar maƙociyarsu na cewa, “ba za ta iya tafiya ba fa.
Dole sai ka zo an tallafa mata. Mu nan duk mata ne, muna buƙatar taimakon
namiji. Ka yi wa Allah ka zo yanzu.”
Ya kashe wayar cikin
tashin hankali da tunani iri-iri. Ya haƙiƙance dai babu abin hawar da zai iya
shiga lungun da gidansa yake. Shekararsa biyu a ciki amma har yanzu bai san
yadda za ya
yi wa maziyarta kwatancen gidansa ba, domin duk alamar da yake bayarwa, kafin wani lokaci sai ta ɓace.
Wata zuciyar na yi masa
gargaɗi cewar, 'ka yi gaggawa ga ceton matarka. Idan ka kuskura ta rasa ranta,
to alhakin na wuyanka, kuma 'ya'yanta ba za su taɓa yafe maka ba!' Ya yi
firgigit kamar wanda ya farka daga barci. A lokacin ya lura a tare da shi akwai
wasu jama'ar da ke fake ruwa har da ma su haya da babur mai rumfa.
Ba tare da jinkiri ba ya
yi wa ɗaya daga cikinsu bayanin halin da yake ciki. Ya ƙara da cewa, “ka taimaka min mu je a ɗauke ta zuwa
asibiti.” Mai babur ya amince suka tafi.
Lokacin da suka isa ruwa ya tsagaita sai yayyafi. Aka yi dabara aka taitayo
Sadiya aka saka cikin babur zuwa asibiti.
Suna hanyar zuwa asibiti Sammani na ta karatun wasiƙun jaki cike da
takaicin yadda unguwar Zurmawa ta zarme, kullum sai ƙara matsewa take da
gine-ginen rashin kan gado ba tare da la'akari da abin da ka je ya zo ba. Wata
zuciyar kuma ta ƙara ingiza shi bisa tsanar Alhaji Gambo wanda ya jawo musu
tarin matsaloli birjik a unguwa. Sun sha tattauna wannan maganar da maƙwabtansa
amma babu yadda suka iya. Mai ƙumba shi ke susa, shi kuwa kuturu sai dai shafa.
Suna ji suna gani ginin Alhaji Gambo ya zame musu ƙurjin gwiwa mai wuyar
fasawa.
****
Malam Mamman wanda aka fi sani da Dogo, shi ne maƙocin Sammani na kusa.
Ƙaramin ma'aikaci ne a wani kamfanin gina hanyoyi. Gidansa kamar na sauran
ya-ku-bayi, bai wuce a kira shi kango ba. Da ƙyar ya ƙuƙuta ya yi rufi ya shiga
ba tare da ko ƙasar ciko ba.
Rannan ya nemi alfarma a wajen aiki aka ba shi ƙasar ciko mota guda. Sai
dai ba hawan ba saukar inji madugun kutare. Motar da ake wa laƙabi da
gingimari ba za ta iya kutsawa lungun nan ba. Dogo kuma ba shi da kuɗin da za ya iya
biya a kwaso daga titi zuwa gidansa.
Sai ya yi wata dubara, ya shaidawa direban ya bi ta wata siriryar hanya da
motar za ta kurɗa ta shiga. Mota ta shiga lungu tana bi ta tsakanin kwatoci da
ramukan ‘soakway’. Cikin rashin sa'a ta taka wani ramin 'soakaway'
da aka gina a ƙofar wani gida. Nan fa ƙafa ɗaya ta rufta ciki. Nauyin kaya da
nauyin motar suka tararwa katangar gidan ita ma ta rubza.
Juyin duniya motar ta kasa fita. Mutane suka taru, aka ga cewar ba za a iya
cire motar ba sai an juye ƙasar da ta ɗebo a wajen. To amma daga juyewa, sai ƙasar ta toshe ƙofar shiga gidan. Nan fa aka yi haihuwar guzuma, layin ya
zamana ba shiga ba fita, ƙofar
gidan ta toshe, ga mata da yara a ciki suna koke-koke.
Jama'a suka samo tsani aka fitar da su.
Jidali tun safe har gefin magariba ana fama, aikin hula ya kai ga dare. Sammani na cikin
waɗanda suka tafi kamfanin su
Dogo
suka sanar da su abin da
ke wakana. Bayan hawa da sauka tsakanin mutanen Zurmawa da kamfanin, aka da
aiko da katafila domin cire
motar.
Assha, ashe dai gyaran
gangar auzinawa aka yi. Katafila
ta shiga lungun a kaikaice. Ta miƙa hannunta mai ruguje gini ta tura motar daga
inda ta maƙale. Garin direban ya dawo da hannun daidai ya
daki falwaya. Nan take kuwa ta faɗi, wayoyin jiki duka suka tsinke. Ita kuma
motar da aka yi nasarar cirewa daga ramin bayan gida ta daki wani garu, nan
take shi ma ya zube.
Dogo ya gigice, ya ransa
inda zai sa kansa. Ya tabbatar asarar da ya
janyowa kamfaninsu da
masu gidajen unguwarsu,
ko an sayar da gidansa ba zai biya ba. Ya ji kamar ya zura a guje ya bar garin.
To amma ya saduda, domin
gudun da babu
tsira kwanciya ta fi shi.
Gwano baya jin warin jikinsa.
Mutanen unguwar gaba ɗaya ba su
dubi cewar rashin tsarinsu ne ya jawo wannan matsala ba, sai suka ɗauki laifin
gaba ɗaya suka ɗorawa Alhaji Gambo wanda ya gine babban layin da motoci suke
iya shiga unguwar salum alum.
Labarin tsautsayin nan ya
watsu cikin unguwa, hankalin kowa ya karkata kan tilas a samo mafita. Cikin
daren nan jama'a suka taru ana tattauna yadda za a ɓullowa lamarin. Dogo ya
zama kamar wani taɓaɓɓe ba shi da kataɓus.
A wajen taron wani dattijo ya ce, “tun
farko dai wannan unguwar ba a gina ta bisa tsari ba. Masu gonaki ne suka cuce
mu. Kowa ya yanka feginsa yadda yake so mu kuwa muka saya saboda tsira da
mutuncinmu.” Wani mutum ya yi
farat ya ce, “son zuciyarmu ne ya jawo. Kowa aka nuna masa fili, ba zai yi wani
tunani ba sai kurum ya hau gini. Ni ban taɓa ganin unguwa
mara kan gadon wannan ba. Ga ƙazanta, ga shi ta zama mafakar ɓarayi ga ba wani
abu da gwamnati ke iya yi mana. Babu ruwa, babu makaranta, babu komai sai
azaba.”
Wani kuma ya ce, “duk mu
bar wannan zance, da a ce ba mu
zuba ido har aka gine mana babban layin da ababen hawa ke bi ba. Da bamu tsinci
kanmu a wannan hali ba. Ku tuna fa jama'a, kyakkyawan muhalli, shi ne tushen
farin cikin kowacce al'umma.”
Sammani wanda ke cikin
taron jama'ar ya ji an taɓo masa inda ke masa ƙaiƙayi. Don haka ya miƙe ya ce, “wallahi duk
sakacinmu ne, mun mayar da muhallinmu kamar garken awaki, kowa ya zo da kuɗinsa
sai ya yi gini yadda yake so ba tare da la'akari
da haƙƙin waɗanda ke kewaye da shi ba.”
Mutane suka maida hankali
ga saurarensa ya yin da yake zayyana musu irin ta'asar da ginin Alhaji Gambo ya
jawowa mutanen da ke kusa da shi.
“Ya zubar min da katanga, Dogo ɗin nan saura kaɗan tasa ta zube. Rashin katanga ya sa aka shiga gidana aka sace min ragon
da na jima ina kiwo. Malam Iliya kuwa, ɗakunansa biyu duk sun zube. Ko jiya
matata da ƙyar muka kai ta asibiti za ta haihu. Saboda ba hanyar
shigowar abin hawa. Bayan haka, ga sace - sace da ayyukan masha'a da ake
tafkawa cikin wannan gini. Jama'a indai muna son kanmu da arziki ya zama wajibi
mu kawo ƙarshen wannan ginin da aka yi mana ƙarfa-ƙarfa.”
Mutane suka ji an yi musu ƙaimi, kowa ya yi ta faɗin
albarkacin bakinsa. Tsohuwar gabar
da ke tsakanin mai akwai da babu ta motsa. Cikin daren nan zuciyar mai
tsumma kamar ta yage.
****
Tashin hankali wanda ba a sa maka rana. Wannan azancin ya tabbata ga
mutanen unguwar Zurmawa waɗanda suka gamu da gamonsu sabili da ɗaukar doka a
hannunsu.
Sun yi haka ne kuwa domin ganin duk koken da suka sha kai wa ga mahukunta
a baya bai samu nasara ba. Alhaji Gambo ya tsaya kai da fata cewar gininsa na
kan daidai kamar yadda aka tsaga gona aka sayar masa. Don haka ya cigaba da
gininsa da taimakon ƙarti madaka kare. Yanzu dai tura ta kai bango, mutanen
Zurmawa sun zurma kansu rami mai zurfi.
Sammani na sahun gaba riƙe da dundurusu. Biye da shi matasa ne kowanne riƙe
da marushi irin su dagi da masaba da kuma gatari. Suna
ihu suna cewa, “sai an rushe, sai an rushe! Hanya muke so. Bama son gini!!”
Sammani ne ya soma dukan
katangar iyakacin ƙarfinsa sannan
ya waiwaya ga matasan ya ce, “ku rushe ginin nan ku samarwa kanku hanya!”
Akuyar ɗaure ta samu saki! Matasa masu jiran kaɗan suka yi kukan kura
suka yanyame katangar nan kamar ƙuda akan nama. Baka jin komai sai ƙarar gatura
da masabai suna kirɓar katanga tare da ihun samari. Kafin a yi haka, tuni sun
yi gagarumar ɓarna.
Ana tsaka da wannan ta'annati sai aka ji wata irin ƙara mai kama da rugugin
aradu. Sai ga wani curarren hayaƙi ya yi sama sannan ya baje ya sulmiyo
ƙasa. Duk wanda ya shaƙi iskar sai ya kama tari ba ƙaƙƙautawa. Kafin ƙiftawar ido jami'an tsaro sun
bayyana. Nan take suka shiga aikin nasu.
Jama'a suka ce 'ƙafa mai na ci ban baki ba?' Tabbas in ka
ga ƙi-gudu lallai sa-gudu ne bai zo ba. Cikin ƙanƙanin lokaci
waje ya zama ba kowa sai masu tsautsayin da ruɗewa ta sa suka kasa
gudu. Wasu kuma, garin aka tunkuɗe su ƙasa,
suka kasa tafiya.
Al’amarin ya zama 'in ba ka yi ba ni wuri'. Unguwar gaba ɗaya
ta turnuƙe, babu abin da
kake ji sai tari da iface-ifacen neman agaji da ƙarar fashewar barkonon tsohuwa.
Jami'an ba su saurara ba, sai bugu da kulki suke suna kama mutane
suna cusawa cikin shiga-ba-biya.
Duk da kasancewar rana
tsaka ne, amma unguwar Zurmawa ta yi
baƙiƙirin sakamakon ƙura da ke
tashi saboda titirniyar da ake sha tsakanin jami'an tsaro da gungun matasan da
suka sha alwashin rushe ginin nan ko ana ha maza ha mata. Ƙwanjin da hukuma ta
nuna ya tilasta su watsar da
aniyarsu, kowa ya shiga gudun neman tsira.
Sammani na cikin waɗanda yaji ya gigita. Ya zura
gidansa a guje. Ya
shiga wawaken neman ruwa. Babu ruwa inda ya yi
tsammani in ban da
na shansu wanda ke cikin randa. Cikin
gigicewa da ɗimautar yaji da ke shiga ta ido da hanci da kunne, Sammani ya cusa
kansa cikin randar. Nan take randar ta fashe.
Bayan kwana bakwai
Faffaɗan falo ne mai ɗauke
da kayan alatu daidai gwargwado. Akwai babbar talabijin maƙale a bango ana
gudanar da labaran duniya. Hankalin Ibrahim Shehu baya kan labaran da ake nunawa, ya maida hankalinsa ga Sammani
wanda ke durƙushe gabansa kamar mai neman gafara yana zayyana masa irin
balahirar da ya shiga kwanaki bakwai da suka wuce.
Tun bayan kwana guda da kama su ‘yansanda suka miƙa su kotu da laifin haɗa baki da ɓarnata
dukiya da kuma ɗaukar doka a hannu. Alhaji Gambo yana da'awar a biya shi asarar
da aka jaza masa sannan kuma
yana neman maƙudan kuɗaɗe na ladan gaɓe.
A zama na biyu alƙali ya
ba da belin mutanen da aka kama sannan aka ɗaga shari'ar
zuwa lokaci na gaba. Dangin
Sammani da matarsa mai
ɗanyen jego suka yi ta zarya har ya
samu kansa.
“Har gida suka bi ni suka kama. Yaji ne ya gigita ni ban san lokacin da na
cusa kaina cikin randa ba.” In ji Sammani yana ba wa Ibrahim labarin.
“Yaya ka yi da iyalinka sabon jego?”
“Da aka sallame su daga asibiti
gidansu ta wuce. Yanzu haka tana can.”
Ibrahim ya ce, “Allah dai ya kiyaye
gaba, amma ka riƙa lura sosai. Ba kowacce rigima ake shiga a fita lafiya ba. Ka
auna arziki ma da bata shafi aikinka ba.”
Sammani ya ce, “wannan ma tsautsayi ne wallahi. Irin
rashin mutuncin da ake mana a unguwar tamu ya wuce ƙima. Ga shi muna jin raɗe-raɗin wai gwamnati za ta yi mana rusau saboda gine-ginen
da ake yi a unguwar ba bisa ƙa'ida ba. Wai za a
rushe unguwar gaba ɗaya a sake tsaga filaye awon gwamnati.”
“Ta yiwu su yi hakan. Ko makamancin haka.”
Sammani ya yi ajiyar zuciya ya ce, “Ni dai fatana Allah ya ba ni iko na sake muhalli
zuwa wuri mai yalwa. Me za a yi da gini a irin wannan unguwar
tamu? Kana gidanka amma baka da walwala? Kullum cikin fargaba. Ga ba tsaro, ga
cututtuka, ga ..... Yallaɓai ku dai kun haye tudun mun tsira. Ba ruwanku da
wannan ja'iba.”
Ibrahim ya ce, “Kai ma ɗin
da ka so da tuni ka mallaki gida mai yalwa, sai ka nuna wayon rashin wayo.”
“Yallaɓai kamar yaya?” Sammani ya ce cikin rashin fahimta. Cikin nutsuwa
Ibrahim ya ce, “in ka tuna, shekaru biyu da suka wuce na baka wani fom ka cike.
Na
shaida maka na bankin lamunin ginin gidaje ne watau Federal Mortagage Bank of
Nigeria (FMBN). Na ce da kai duk ɗan ƙasa yana iya nema a ba shi amma a
matsayinka na ma'aikaci ka fi kowa damar cin moriyar shirin. Tun ranar da na baka fom ɗin baka
ƙara yi min maganarsa ba, sai kwatsam ka sanar da ni tarewarka a unguwar
Zurmawa.”
Sammani ya ji wani irin
sanyi a jikinsa kamar an kwara masa ruwan ƙanƙara, ya ji jikinsa na ƙyarma
kamar ana kaɗa masa kurya gangar yaƙi. Sai dai ba irin tsimar jarumai yake yi ba, tsima ce ta jin tsoro da
firgici.
Nan take ya tuna da fom ɗin
da Ibrahim ya taɓa ba shi domin
samun tagomashin daga bankin lamunin muhalli. Ya yi ajiyar zuciya mai cike da
nadama. Babu shakka a lokacin da ya ba
shi fom ɗin ya cike bai ɗauki batun da wani muhimmanci ba.
Ya dubi maigidansa ya
ce,”lallai kam na tafka kuskure ga shi wankin hula ya kai ni dare. Ban gama
ginin ba, ga ba kwanciyar hankali.” Ya sauke numfashi irin na ƙaƙa-ni-kayi.
Ibrahim ya ce, “baka makara
ba har yanzu. Ka ci arzikin ana yankar maka 2.5% a albashinka duk wata. Wannan
zai zamar maka kandagarki. Sannan kana da shekaru da yawa nan gaba kafin ka bar
aiki. Sauran dabara ya ragewa mai shiga rijiya.”
Sammani ya ce, “yallaɓai
wanne irin lamuni suke bayarwa ga jama'a?” Ibrahim ya ce, “da farko dai suna
iya ba ka kuɗi ka gyara gidanka, ko kuwa idan kana da fili ka gina kayanka.
Idan baka da waɗannan duka, za su iya ba ka gida sukutum ka zauna ciki kana
biya sannu a hankali. Abin da za a riƙa cirewa daga albashinka bai taka kara ya karya
ba. Ana iya rarraba kuɗin har tsawon shekara 30 yadda ba za ka jigata ba.”
Sammani ya yi
zumbur ya miƙe tsaye yana cewa, “yallaɓai bari na je ofis na dubo fom ɗin nan
na cike yanzun nan.” Ibrahim ya bi shi da kallo yana murmushi ya ce, “ɗokin
mazallaƙo ka manta ne an tashi daga aiki? Sannan kuma ai fom ba wahala yake ba,
kana iya sauko da shi ta intanet daga shafin yanar gizo na FMBN, ko kuma ka je
ofishin su baka shawara da sauran bayanai.”
Sammani ya koma ya zauna
yana mai cewar, “Allah ya kai mu.”
*****
Dare mahutar bawa, amma wannan dare ga Sammani ya zama maƙirƙirar tunani.
Tun da ya kwanta bai iya runtsawa ba, sai ya ƙulla ya kwance. Gani yake kamar
gari ba zai waye ba balle ya je bankin FMBN ya karɓi fom.
Duk tsananin son da yake wa matarsa, amma ta haihu rikicin da ya same shi
ya hana masa zarafin gudanar da hidimar suna kamar yadda ya tsara. Yana
ji yana gani ko rago bai samu ya yanka ba. Zuciyarsa ta shiga zarginsa bisa
yadda ma aka yi ya yi gini a unguwar Zurmawa.
“Tsautsayi ba ya wuce
ranarsa, in ban da
tsautsayi da ƙaddara me zai sa mutum ya yi gini a inda rayuwarsa za ta ƙuntata.
Ga cututtuka ga ɓacin rai ga gulmace-gulmace....” Zuciyarsa ta yi ta ƙissima
masa abubuwa barkatai har zuwa lokacin da gamzaki ya bayyana.
****
Asubancin Sammani zuwa bankin FMBN ya yi rana, domin kuwa shi ne na farkon
da wani jami'i ya saurara a bankin.
“Za mu iya baka kuɗi har naira miliyan ɗaya domin ka gyara gidanka.” In
ji jami'in banki. “Wannan shi ake kira 'Renovation Loan.’ Sannan muna da wanda ake kira 'Construction Loan',
shi kuma zai ba ka dama ka gina gida a filin da ka mallaka muddin ka cika sharuɗɗan
da aka gindaya. Za a iya ba ka har naira miliyan 15 gwargwadon yadda albashinka
zai iya ɗauka domin ba za a iya yankar abinda ya wuce sulusin albashinka ba
kuma biyan kada ya zarce shekaru talatin.”
Sammani ya ce, “ka ƙaddara ban mallaki fili ko taki ɗaya ba ballantana kuma
gida. Wanne irin lamuni za a bani? Wanne agaji za ayi min?”
Jami'i ya ce, “muna da tsarin ɗan haya ya mallaki gida watau 'Rent to
Own'. Za mu iya baka gida ginanne kana biyan aunaka har ka ida biya. Kuma
muna da tsarin da ake kira 'Mortgage Loan'. Shi ma za a mallaka maka
gida kana biya sannu a hankali amma sai ka bi ta ƙarƙashin wasu yardaddun
kamfanoni da ake kira 'Mortgage Loan Orginator (MLO).' Ta hannunsu za ka
samu gidan mu kuma za mu zama tamkar alƙalai tsakaninku.”
“Ranka ya daɗe, wanda ruwa ya ci ko takobi ka miƙa masa riƙewa yake. Duba
min wanda ya fi dacewa da ni cikin tsarin 'Rent to Own' ko 'Mortgage
Loan' ɗin nan.”
Jami'i ya yi nazarin takardun aikin Sammani da
sauran bayanai sannan ya ba shi fom ya yi masa bayanin yadda za ya cike tare da takardun da ake buƙata.
“Ka haɗo da takardunka na
ɗaukar aiki da na tabbatarwa
da katin shaida da kuma bayanin asusun ajiyarka na banki da kuma lambar BVN.
Har ila yau za ka je ma'aikatarku
a ba ka takardar garantin za su riƙa yankar kuɗin aunaka daga albashinka
suna aiko mana. Haka kuma za ka samu wasu ma'aikatan da za su tsaya maka.”
Sammani ya ji kamar ya daka tsalle don murna. Ya tafi ofis ya nunawa
Ibrahim tare da duk abubuwan da ake buƙata.
“Ina fata idan al'amarin
nan ya tabbata don Allah Sammani
ka
kula da gidanka da kyau. Duk wani gyara da ya taso ka daure ka yi. Ka tuna fa,
muhalli shi ne tushen farin ciki. Haƙiƙa ma dai, muhalli shi ne tushen rayuwa,
domin daga nan ne ake samar da iyali lafiyayyu da za su haifar wanzuwar zuriya
ta gaba. Shi ya sa ma a Hadisi aka ambaci muhalli a matsayin ɗaya daga tubalan
arziki.” Ibrahim ne ke yi wa Sammani nasiha bayan ya kammala duba takardun.
Sammani ya rusuna ya ce,
“yallaɓai da yardar Allah zan kula sosai da dukkan iyawa ta.” Ya gyara zama ya ce, “ya zama wajibi
gare ni na kula da muhallina, domin kuwa na ga illar gini a waje mara fasali.
Ina ji ina gani aka yi min haihuwa amma ban iya zama na yi bikin suna cikin
iyalina da 'yan uwa
da abokaina ba. Ba domin taimakonku ba ma yallaɓai da yanzu labari ya sha
bamban. Ai ni kam an sha ni
na warke, ni da gini awon mai gona haihata - haihata.”
Ibrahim ya sauke numfashi ya ce, “Allah dai ya rufa asiri. Sai ka je ka yi
himma ka harhaɗa abubuwan da ake buƙata domin ka samu da wuri.”
****
Unguwar Zurmawa ta amsa sunanta, domin kuwa ƙarfi da yaji gidajen sun zurma
cikin lunguna. Babu wani layi wanda jama'a ke iya walwala cikinsa ballantana
ababen hawa su samu matsuguni.
Rikicin mutanen unguwar da Alhaji Gambo ya sa gwamnati ta farka daga barcin da
take yi dangane da fasalin unguwar. Jami'ai suka tafi gudanar da bincike kan
yadda za a inganta muhallin domin unguwar ta
samu ababen more rayuwa. Jami'an suka bayar da shawarar a rushe wasu gidaje domin
samar da hanyoyin da za su iya ratsa unguwar domin inganta lafiya da tsaro.
Mutanen Zurmawa suka yi ta gudanar da tarurruka domin neman mafita. Cikin
kowa ya ɗuri ruwa domin tsoron kada rusau ɗin ya faɗa gidansa. Sammani bai taɓa
halartar ko taro sau ɗaya ba duk da kasancewarsa ɗaya daga jagororin mazauna
unguwar. Ya maida hankalinsa kacokam wajen neman tabbatuwar samun mallakin gida
daga bankin FMBN. Duk inda ya tsuguna zancen yake yi,
kullum ya kwanta mafarkin da yake yi kenan. Lallai ruwa ya daki babban zakara.
Wata ranar Alhamis yana ofis yana ta fama da aiki sai ga saƙo ya shigo
wayarsa. Bai tsaya dubawa ba sai da ya kammala abinda yake yi. Saƙon yana ɗauke
da sunan FMBN. Cikin fafarniya ya duba. Saƙon na cewa, “muna taya ka murna.
Ka samu lamunin gida mai ɗaki biyu a unguwa awon gwamnati.
Maza ziyarci ofishinmu domin ƙarin bayani. Danna *219# daga wayarka domin sanin
matsayin lamunin da aka baka.”
Sammani ya yi ihu kamar wani taɓaɓɓe. Ya ji kamar an yi masa ƙaimi, ya kasa
zaune ya kasa tsaye. Ya yi ta zagayawa tsakanin 'yanuwa da abokan arziki yana shaida
musu abin da ya same shi na farin ciki. Wasu kuma ya buga musu waya ya sanar da
su. Nan take ya ji duk wani ƙunci da ke tauye masa walwala ya kau.
Danginsa da sauran 'yanuwa da abokan arziki aka yi ta zuwa ana taya shi
murna. Maƙwabtansa na Zurmawa suka taya shi murna tare da fatan su ma kurtun sa'a ya fashe
akansu yadda za su samu ikon barin unguwar nan mai kama da ƙuncin kurkuku.
Bayan wata uku - Ranar Litinin
'Mande tushen aiki ko nasara na tsoronki.’ Wannan
ne kirarin da ake yi wa ranar Litinin domin ita ce rana ta farkon zuwa wuraren
aikin gwamnati bayan an shafe ranakun Asabar da Lahadi ana hutun
ƙarshen mako. Ga Sammani kuwa wannan Litinin ɗin ta zama ta farkon komawa ofis tun bayan
da ya tare a sabon gidansa.
Bayan an danƙa masa mukullan gida bai yi wata-wata ya haɗa nasa ya nasa
daga Unguwar Zurmawa ya koma sabon gidansa. An yi dace kuma, lokacin ya zo
daidai da zai soma gudanar da hutun shekara. Wannan ya ba shi dama ya sakata ya wala.
Gidan dai fasalin ginin da ake kira 'bungalow’ ne, ya ƙunshi ɗakunan kwana biyu da babban falo da kuma
kicin da banɗakuna biyu. Akwai wadatacciyar haraba da aka kewaye da ƙaramar
katanga inda aka dasa bishiyoyi gajejjeru masu bada iska yalwatacciya da ke
bugawa cikin gidan. Duk wanda ya je ganin gidan sai ya yi marmarin mallakar irinsa.
Arziki kamar jiran Sammani yake a sabon gida. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake babur ɗinsa
da ya tsufa, kuma ya sayo ƙaton rago biyan bashin sunan ɗansa wanda
ya ci sunan mahaifinsa watau Bashir. Ana kiransa Abbaji.
Ya yin da yake kan hanyarsa ta
zuwa
ofis, sai ya ji shi kamar sabon ango. Tafiya yake cikin nishaɗi
da annashuwa. Gani yake duk duniya babu wanda ya kai shi sakewa da jin daɗi.
Duk unguwar da ya wuce sai ya tsaya ya yi nazarin
layukansu da irin fasalin da suka yi wajen gini. Cikin zuciyarsa yakan yanke
hukuncin irin jin daɗin da mazaunan ke yi. Zuciyarsa na
shaida masa cewar, duk wanda bai
mallaki muhalli a wuri mai kyakkyawan fasali ba yana da sauran aiki gabansa.
Ya yin da ya isa ofis, tun
daga nesa maigadi ya hango shi. Ya taso da hanzari yana yi
masa gaisuwar yaushe gamo yana cewa, “ni na fara ganinka. Lallai Sammani ka
samu duniya a daidai. Hutun nan ya yi
maka kyau. Fes da kai. Ga
sabon gida, ga sabon babur ga kuma sabuwar duniya. Allah ya ba mu i-taku.”
Sammani cikin jin daɗi ya sa hannu ya fito da kuɗi ya danƙa masa ya ce,
“riƙi wannan ka sha ruwa.” Maigadi ya hau godiya yana cewa, “na gode ƙwarai
yalllaɓai. Allah ya sa ka fi haka. Duk wanda ya raina arzikinka, ya Allah ka yi
masa mutuwa irin ta shaddar talaka.” Sammani ya fashe da dariya ya wuce zuwa
ofishinsa.
Da yamma, ya koma gida kenan, sai aka aiko ana sallama da shi.
Ya yin da ya fita sai ya ga ashe mutanen unguwar Zurmawa ne, ciki har da Liman da Dogo wanda ya samu kansa da ƙyar daga kamfaninsu.
Bayan an yi raha da gaisuwa irin ta yaushe-gamo sai Liman ya soma
cewa, “Malam Sammani, mu wakilai ne aka aiko musamman domin neman alfarmarka.”
Sammani ya gyara zama ya ce, “ina sauraro.” Liman ya cigaba da cewa, “kana
sane da dukkan balahirar da ta auku a unguwarmu ta Zurmawa. To
yanzu haka dai gwamnati ta aiwatar da shawarwarin rahoton kwamitin nan na
kwanaki. An rushe gidaje da dama hatta shi kansa ginin nan na Alhaji Gambo bai
tsira ba, an rushe fiye da rabinsa domin samar da hanya mai inganci da kuma
tsaron unguwar.
“Don haka sai mu duka
mazauna unguwar muka tattauna tsakaninmu sannan muka miƙa ƙoƙon bara ga
gwamnati kan ta yi mana agajin ginin asibiti. Gwamnatin ta bamu damar mu lalubo
duk wurin da muke so a yi mana wannan aiki. Da taimakon jami'an safiyo muka zaɓi
rukunin gidaje shida da za a haɗe a samar da asibitin.
Kwamitin ya tuntuɓi
mutane biyar ɗin har da Dogo maƙwabcinka ga shi a zaune. Kuma duk sun amince za su sayar da gidajen nasu. Kai ne
kaɗai ka rage ba a tuntuɓa ba da yake yanzu baka unguwar. Shi
ya sa aka wakilto mu domin neman alfarmar ka sayar wa mutanen unguwa gidanka da
za a mayar asibiti.”
Sammani ya nutsu yana
sauraren Liman
har ya ƙare jawabinsa sannan ya ce, “kasancewa ta mutumin da ya zauna a Zurmawa
kuma na yi gwagwarmaya domin cigaban ta, to duk abin da ya taso na bunƙasar
unguwar zan yi maraba da shi. Don haka, ni Sammani Bashir, na mallakawa mutanen
unguwar Zurmawa gidana da ke turba,
domin samar da asibiti. “
Yana rufe baki wakilai
suka hau sowa da kabbara suna gode masa bisa wannan namijin tagomashin da ya yi musu. Sammani na wangale baki cikin
fara'a ya yin da suke sa
masa albarka shi kuma yana cewa, “ba ni za ku godewa ba, ku godewa Allah da
bankin FMBN da suka mutunta
ni suka
maida ni ɗan adam bayan na maida kaina tamkar muzuru.”
Liman ya ce, “haka fa, to
su ma bankin Allah ya ƙarfafe su bisa aniyarsu ta alheri da taimakon da suke yiwa talakawa samun ingantaccen muhalli.”
Wakilai gaba ɗaya suka amsa da “amin, amin.”
Ƙarshe
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.