Ticker

6/recent/ticker-posts

Sanin Hanya

Aliyu Rabe Aliyu (2020). Sanin Hanya. Muhalli, Sutura (Labaran Da Suka Samu Nasara a Gasar Gajerun Labarai a Kan Muhalli Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2020). Darma Digital Prints.

SANIN HANYA

Na

Aliyu Rabe Aliyu

A zamuna da yawa da suka wuce, da yawa ba a da masaniya a kan yadda al’amurra suke tafiya, wannan bai rasa nasaba da yadda ake rufa-rufa a kan ayyukan gwamnati musamman a ma’aikatu da sassansu, wannan ya sa da yawa daga cikin Mutane ko ma’aikata suke yin fargar jaji a duk sanda suka zo gabar ajiye aiki musamman rashin samun muhalli da zasu mike kafafuwansu a duk sanda suka kammala aiki..Sai dai sarki goma zamani goma; juyi-juyin siya sa da kuma sanya ƙwararru akan hukumomi da sassansu ya kawo wata sabuwar rayuwa in da ƙananan ma’aikata ma suke rabauta da ayyukan gwamnati tun a matakin farko ta hanyar bayar da dama ga dukkan wanda yake da buƙata ya amfana ba tare da banbancin siya sa ko aiki ba; wannan kuma bai rasa nasaba da yadda ake tafiyar da abubuwa a buɗe da kuma gangamin wayar da kan al’umma a kan shirye-shirye da ayyuka na gwamnati mai ci a yanzu abin da masana da ƙwararru suke da yakini cewa wannan itace babbar hanyar da zata magance cin hanci da rashawa da kuma gina al’umma ta hanyar da ya dace.

FARKO

A duk sanda aka ce safiyar litinin ce, zaka samu babban titin Ahmadu Bello da ke Abuja motoci ne ke zirga zirga , wannan bai rasa nasaba da yadda yake ɗauke da manyan ma’aikatu na gwamnati, ciki har da ma’aikatar ilimi wadda take da gurbi a cibiyar ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Zubairu Ɗanmalam ya fito daga cikin motarsa Toyoto Lexus wadda kuɗinta ya kai naira miliyan sha-takwas, rike da yar jika ya hau sama zuwa ofishinsa da ke hawa na biyar.

Matsayin Zubairu shi ne mataimakin darektan ilimi, a yanzu shekara ɗaya ta rage masa ya yi ritaya, kuma wannan ce shekara ta biyu da dawowarsa Abuja bayan yi masa sauyin wurin aiki daga kwalejin gwamnatin tarayya da ke Zaria. In da ya baro can a matsayin shugaban makarantar watau principal.

Kusan rayuwar Malam Zubairu ya yi ta ne a ire iren waɗannan makarantu na gwamnatin tarayya tun daga matsayin malamin makaranta har zuwa yau da yake a cibiya inda yake ƙoƙarin yin ritaya a matsayin mataimakin darektan ilimi.

To sai dai wani hanzari ba gudu ba idan akwai abin da yake tada wa Zubairu hankali a rayuwarsa ita ce yadda ya kwashe shekaru 34 yana aiki amma har yanzu bashi da gida mallakar kansa, wannan bai rasa nasaba da dalilai guda biyu;

Na farko duk tsawon rayuwarsa a wuraren da ya yi aiki a kusan jihohi guda takwas yana zama ne a cikin gidajen malaman makaranta da shi da iyalinsa;

Na biyu kuma bai taɓa yin wani tanadi na aje isassun kuɗaɗe domin mallakar muhalli akalla koda fili ne a garinsu na asali watau Gashua ko kuma a garuruwan da ya yi zaman aiki, wannan shi ma ba ya rasa nasaba da irin salon rayuwarsa ta son kawa da burge mutane da sharholiya da kuma rashin sanin ya kamata.

Ko a yanzu zaman da yake yi a Abuja dankareren gida ne ya sa aka kama masa ya biya naira miliyan shida domin yin wa’adin shekara biyu a ciki, kaga kenan naira miliyan uku kenan duk shekara.

Ga mota mai tsada, ga gidan haya mai tsada, ga kuma lokacin ritaya ya matso. Sai yanzu ne Zubairu ya fara tunanin yadda rayuwar shi za ta kasance idan har ya yi ritaya, na farko ma bai san inda zai koma ba, saboda a garinsu na asali baya da gida, sannan matan shi guda biyu da yara guda shida, rayuwar birni suka saba da ita; kuma dukkansu a gida suke zaune in banda babban dansa Mutari wanda yake ya yi digiri kuma har ya samu aiki a hukumar kamfanin dillancin labarai na najeriya watu NAN.

Lokacin da yake a FGC Kano ya taɓa cin bashin banki da niyar ya sayi gida, daga baya kuma sai ya fasa inda ya kara aure kuma ya sayi sabuwar mota marsandi ya ci gaba da fantamawarsa.

A Zaria ne ya samu makudan kuɗaɗe sakamakon kasancewarsa shugaban makarantar kuma a wancan lokacin aljihun gwamnati a bude yake duk wata almundahana ba wanda ya damu da sa ido a kanta, wannan ya sa Zubairu ya yi tsayin daka wajen azurta kanshi ba tare da ya yi la’akari da mallakar gida ko muhalli a can ba, sai kawai ya yi kundunbala ya sayi mota Toyota Lexus abin da ya janyo masa hayaniya da sa ido wanda shi ne sanadiyar dawo da shi Abuja cibiyar ilimi ta ƙasa don kamala aikinsa anan.

A daidai wannan lokacin ne kuma ɗansa Mutari yake cika shekara uku da fara aikin gwamnatin tarayya kuma ya rage wata uku kenan za a ɗaura masa aure da wata yarinya a Minna ta jihar Niger inda a can ne yake aikin aiko da labarai ga kamfanin dillancin labarai na najeriya watau NAN.

Bayan zaman sa a ofis Zubairu ya ɗauki waya ya tuntubi ɗansa Mutari akan ko ina aka kwana akan maganar bukinsa, da kuma inda zai zauna da matarsa bayan ɗaurin aure.

Sai dai sabanin Zubairu, ɗansa Mutari yana da taka tsantsan da kuma lura da yadda rayuwa ta canja, sannan yana jin ciwo a duk sanda suka je Gashua sallah da Babansa da yan gidansu sai suyi ta raɓe- raɓe na wurin da za su zauna, wani lokaci a gidan kakanninsu suke kwana, wani lokaci a gidan kawunsu, wannan ya sa a kodayaushe yake jan hankalin Babansa cewa ya kamata ya yi kokari ya mallaki muhalli a kalla koda na fita kunya ne a garinsu don kaucewa shiga matsala a rayuwa musamman ma idan aka ce yau ya yi ritaya.

Wannan ne ya sa daga lokacin da Mutari ya fara aiki da NAN a shekarar 2016, ya fara tsimi da tanadi akan yadda zai mallaki muhalli nashi.

A wani lokaci ya je ɗaukar rahoto a kan wata yarjejeniya da aka kulla da bankin bayar da lamunin gidaje na ƙasa da kuma kungiyar Ƙwadago ta Jihar Niger, akan wani shirin samar da gidaje ga ma’aikatan jihar, wannan ya ba Mutari damar yin bincike da kuma tuntuɓar jami’ai na bankin inda suka bashi isassun bayanai da hanyoyin da zai bi wajen cin gajiyar shirin bankin akan samar da gidajen ma’aikata.

Tun daga wancan lokacin yake kwanci tashi har sai da ya cika sharuɗɗa na mallakar muhalli wanda yake cikin rukunin gidaje da bankin ya gina a shiyar da zummar tallafama al’umma mallakar muhalli cikin sauki da kuma rangwame.

A daidai lokacin da Mutari yake yi wa mahaifinsa bayani cewa ya mallaki gida ba ƙaramin kaduwa uban ya yi ba yana nazari ta yaya a wannan karon yaron zamani ya fi dattijo kyakkyawan tunani irin haka? Ta yaya haka ta kasance? Yanzu kuma mine ne makomarsa nan gaba idan ya yi ritaya da mata biyu da yara guda shida? Ina zai sa gaba? Wane irin barcin kwalwa ne ya yi a tsawon shekara 34 yana aiki bai tsinana komai ba??? Tunaninsa ya katse a daidai lokacin yaji ɗansa yace ”Baba kai ma baka Makara ba zan bincika maka yadda zaka mallaki gida a ko’ina ne a Najeriya” TA WACE HANYA CE MUTARI ??? Uban Ya Tambaya cikin ɗoki a lokaci ɗaya kuma yana tunanin kamar abin ba zai taba yiwa ba.

“Ka kwantar da hankalin Baba akwai gidaje da bankin bayar da lamunin gidaje na kasa da ya gina ta hanyar haɗaka da wasu masu harkar gine gine a wasu jihohin kasar nan kuma tabbas gidajen nan an kamala su har ma an fara amfani da su a wasu jihohin ƙasar nan don haka zan bincika maka don ganin cewa kaima ka mallaki gida a yan kwanakin ka na kamala aiki, kuma zan tabbatar da cewa gurin ka ya cika na shiga sabuwar rayuwa da ƙafar dama” cewar Mutari.

* * *

Babban ɗakin taro ne mai ɗaukar mutane aƙalla ɗari biyu, kowanne mutum daga cikin mahalarta taron ya yi ƙasake yana sauraron mukalar da Farfesa Yakmut Bahago yake gabatarwa akan yadda rayuwa zata kasance ga waɗanda suke gab da yin ritaya kuma ake musu bita akan yadda za su wanye lafiya a rayuwarsu bayan kammala aikin gwamnati.

Duk da cewa abin da Farfesa Yakmut yake faɗa a muƙalarsa a matsayinsa na masanin tattalin arziki da zamantakewa abu ne da yake zurfafa bincike kafin ya gabatar da ita a duk wani taro da aka gayyace shi, yakan yi kokari ya fitar da wasu mas’aloli waɗanda galibi ba kowanne masani yake da irin wannan gwaninitar ba, a don haka a duk sanda yake gabatar da bita zaka samu kowa ya nutsu yana sauararon ilimi mai cike da basira da kuma ratsa zukatan masu sauraro.

A wannan karon bitarsa ta ta’alaƙƙa ne akan tsallen baɗake da ma’aikata suke yi a duk sanda suka fuskanci lokacin ritaya ta hanyar yaki haram-yaki- halak.

“ bincike na baya-bayanan ya nuna cewa kashi sittin cikin ɗari na waɗanda ke yin almundahana da babakere da ruf da ciki na kuɗaɗen ma’aikatu zaka samu masu shirin yin ritaya ne waɗanda galibi suka yi baccin ƙwalwa tun farkon fara aikin su ba su yi kokarin mallakar muhalli ba, sai a dadai lokacin da ritaya ta riske su sannan za su yi abin da ake cewa fargar-jaji”

Zubairu wanda yake cikin waɗannan mutane yaji gaban shi ya faɗi ba shakka wannan kamar wani shagube ne Farfesa yake yi a cikin wannan taro domin yana ɗaya daga cikin wanda ya tsinci kansa a wannan rukunin mutane masu fafutakar muhalli a ƙurarren lokaci.................... maganar Farfesa ce ta katse tunanin da yake yi.

“ rashin mallakar muhalli ga mutumin da yake gaɓar ritaya yana da ƙalubale mai yawa ga al’umma, kamar yadda na faɗa muku shi ne ummul aba’isin cin hanci da rashawa a ma’aikatu, sannan yana kawo durƙushewar ayyukan gwamnati, sannan kuma yana haddasa ruɗani ga iyalan mutum, baya ga haka kuma akwai rashin tabbas ga rayuwar yaranka nan gaba saboda ba su da wata sahihiyar makoma”

Tabɗi! Zubairu ya faɗa tare da gyara zama

Farfesa Yakmut ya ci gaba da cewa “ abin takaici a nan shi ne zaka samu mutum ya yi ritaya a matsayin darakta ko mataimakin darekta ko wani babban jami’i na gwamnati amma wata ɗaya da yin ritaya sai ka samu ya fara lalacewa yana ramewa sai yawan zuwa asibiti, hawan jini, cututtuka na zahiri da na ɓoye, sai ƙorafe-ƙorafe shin kun san babban dalilin wannan ciwo? Rashin samun muhalli ne da kuma yankewar kuɗaɗen cuwa-cuwa da ya saba samu, ga kuma batun kuɗaɗen haya, dana ɗawainiyar iyali ga kuma rashin sanin makoma ta yaya mutum ba zai kasance ba a cikin larurar da bata da magani har tsawon rayuwarshi? kai in takaice muku wani lokaci idan kun ga mutum farat ɗaya ya yanke jiki ya faɗi sumammme ko matacce duk bai rasa nasaba da abin da muke magana a kai na rashin muhalli”

“Wannan ya sa a yanzu na yi nazari akan samar muku da mafita ta yadda waɗannan ƙalubale za su zo muku da sauki amma kafin nan zamu je hutun ɗan takaitaccen lokaci”

Raf-raf-raf-raf-raf............. sai tafi abin da yaba Farfesa Yakmut dariya saboda sai a yanzu ne aka yi masa tafi don sun ji cewa zai kawo musu mafita a rayuwar da suke taraddadin shigarta.

 * * * *

Kusan kowa daga cikin mahalarta taron bitar masu ritaya a shekarar nan ya yi kasake yana sauraron Farfesa yakmut akan yadda za su gama aiki lafiya, kowa da abin rubutu ya yin da wasu kuma suka kunna wayoyinsu domin ɗaukar bayanan da ake don adanawa, ga mamakinsu sai suka ji Farfesa ya furta wata magana ta hanyar tambaya; Shin ko kun san cewa sabbin Ma’aikata da aka ɗauka daga shekarar 2015 zuwa yanzu za su fi ku jin daɗin rayuwa a nan gaba? Shin ko kun san cewa a yanzu an sami gagarumin ci gaba wajen baiwa al’umma damar amfana da shirye shirye ko ayyuka na gwamnati? Shin kuna da labarin cewa ƙananan ma’aikata yan shekara uku da fara aiki sun fara mallakar muhalli ya yin da wasun ku a yanzu shekaru 35 da fara aiki amma basu da ko fili mallakarsu?..........; saurara yallaɓai….. “gaskiya ba mu ce ba haka ne ba; amma zai yi wuya ma’aikaci a mataki na takwas ko tara ya mallaki gida; mun san yadda aikin gwamnati yake kwarai, kuma duk salon tsarin aiki da zasu bi mun bi amma ga halin da zamu kare aiki” malam Bala Jogana kenan ya katse hanzarin Farfesa wanda yake ta warwarar bayani akan yadda ma’aikata na wannan zamani suka fara samun ribar aiki a kuruciyarsu.

“ Farfesa duk tsarin da ya kamata mubi na samun muhalli mun shiga, kuma tun 1983 aka fara cire mana kuɗaɗen mallakar gidaje (NHF), sannan tsawon lokaci babu wata amsa dangane da kuɗaɗenmu da aka rika cirewa a baya tun lokacin ana yi da hannu, aka zo sabon tsari a 2010 sannan ne ma muka fara sanin inda kuɗaɗenmu suke shiga ta hanyar komawa manhajar zamani ta bankin gidaje, kuma daga nan babu wata dama ko gina gidaje ko bashi ko tallafi, sai dai jefi-jefi, yanzu ne muka fara ganin cewa al’amurra sun fara canjawa dangane da batun mallakar muhalli a ƙasar nan …………” “dakata malam, duk na fahimce ka” Farfesa Yakmut ya katse hanzarin Bala Jogana fitaccen malamin makaranta kuma ɗan gwagwarmaya mai akida.

“ ai abin da na faɗa ne ɗazu cewa ma’aikatan yanzu za su fi ku rayuwa ingattacciya saboda sun riski zamani da ake yin komai a buɗe, a cikin ƙa’ida da kuma sanin yakamata, na gaya muku cewa daga 2015-2020 an samu ci gaba sosai a wannan ɓangare na kyautatatawa ma’aikata da ba su haƙƙoƙinsu ta hanyar ba kowacce hukuma cin gashin kanta. Wannan ya sa ma’aikata a yanzu kai tsaye suke amfana da ayyuka ko manufofin gwamnati, kuma hakan ya faru ne dalilin ba kowa da kowa damar amfana da abubuwan da ake samarwa ga al’umma”.

Farfesa Yakmut ya ci gaba da cewa; “dalili na biyu kuma shi ne akwai gangamin wayar da kan al’umma da ma’aikatan wannan lokaci suka samu ta fuskoki da dama wannan ya hada da yawaitar kafofin yada labarai, da hanyoyin sadarwa na zamani, kana kuma wadannan hukumomi kamar bankin bayar da lamunin gidaje, da ma’aikatar ayyuka da gidaje da makamantansu kaitsaye suke ɗora ayyukansu da shirye-shiryensu akan dandalin shafinsu na yanar gizo”

“ haka kuma akwai fahimtar juna a tsakaninsu da sauran hukumomi takwaransu da ƙungiyoyin ƙwadago da kuma ɗai-ɗaikun mutane da yan kasuwa masu zaman kansu, uwa uba kuma batun yaƙi da cin hanci da gwamnati mai ci yanzu take yi na ba sani ba sabo ga dukkan wanda yaci amanar kasa wannan ya sa ma’aikatu da hukumominsu suke taka tsan-tsan wajen yin abin da ya dace”.

Idan kowa a cikin wannan ɗakin taro bai yarda da mukalar da Farfesa Yakmut yake gabatarwa ba, to ban da Zubairu Ɗanmalam, mataimakin darektan ilimi mai gab da yin ritaya wanda a zuciyarsa ya gasgata dukkan abin da Farfesa ya faɗa domin shekara 34 ya yi yana aiki amma bai tanadi komai ba dangane da muhalli kuma wannan ba matsalar kowa bace, laifinsa ne domin ya sami dama iri-iri a rayuwarshi amma ya yi sakaci da ita ƙarshe kuma yanzu yake ta fafutukar yadda zai kasance a cikin muhalli bayan ya yi ritaya. A nan ne kuma ya tuno da yadda ɗansa Muntari ya mallaki gida shekaru uku da fara aikin sa a kamfanin dillancin labarai na Nijeriya.

 * * * *

Wata huɗu kenan da yin ritayar Zubairu Danmalam, kuma yana zaune ne a ɗaya daga cikin sabbin gidajen da bankin bayar da lamunin gidaje ya gina a gundumar Tamburawa dake birnin Kano,

Ya zabi birnin Kano ne domin yaci gaba da tafiyar da sabuwar rayuwa bayan ajje aiki a watan maris da ya gabata.

Saboda a duk wuraren da ya yi aiki ya fi sabawa da Kano, sannan yana son ya fara kasuwanci, kana kuma ba za ya ji daɗin zama a Gashuwa ba mahaifarsa, saboda ba kasafai yake zuwa can ba tun ma a lokacin da yake aiki, don haka Kano nan ne wurin da ya ga ya dace ya ci gaba da rayuwarshi domin kasuwanci da kuma sanya yaransa a makarantun gaba da sikandire.

Zubairu bai taɓa tsammanin zai mallaki gida ba, amma sai ga shi yanzu ya mallaki gida cikin ƙanƙanen lokaci, kuma nagartaccen gida, ginin zamani a cikin rukunin unguwa sabuwar ya yi da ke Tamburawa.

Kasancewar Mutari ɗa ne mai hazaƙa, mai bibiyar ayyukan bankin bayar da lamunin mallakar gidaje, wannan ya bashi damar sanin aikace-aikacen bankin wanda hakan ne ya sa shima ya rabauta da mallakar gida a tsarin ayyukan bankin, sai dai duk da haka ya yi ta faɗaɗawa wajen bincike da samun ƙarin bayanai a kan yadda ya kamata ace wanda ba ma’aikacin gwamnati ba, da ɗan-kasuwa da masu zaman kansu sun amfana da ayyukan bankin.

A ƙoƙarin wannan bincike da yake yi ne kuma bukatar mahaifinsa ta taso na ganin ya mallaki gida a kan gabar ritaya. Duk binciken da Mutari ya gudanar bai ga wata kafa da bankin ya yi tanadi ga masu ritaya ko yan fansho ba, amma a duk sanda suka yi ritaya ana maida musu kuɗinsu ne na ajiya a yi sallama dasu. Don haka, a nazari da tunanin Mutari ya san ko ba komai Babansa yana da kuɗi na asusun gidaje (NHF) a bankin bayar da lamunin muhalli na ƙasa, sannan kuma akwai kuɗaɗensa dake asusun ajiyar fansho, baya ga wannan kuma akwai yan kuɗaɗe kusan miliyan huɗu a bankin da yake ajje kuɗi, kuma ga motar alfarma ta miliyan sha takwas yana hawa, don haka duk yadda za’a yi a wannan da’irar ne ya kamata a ce kuɗin muhalli sun fito don ganin cewa mahaifinsa ya shiga gida mallakar kansa.

Da farko ya tuntuɓi mahaifinsa da shawarar sayar da motar alfarma ta Toyota Lexus, sannan kuma ya bukace shi inda yake so ya zauna bayan ya yi ritaya, da kuma salon rayuwar da za ya yi nan gaba, wannan tunani na Mutari ya yi mawafaƙa da shawarwari da Farfesa Yakmut ya bayar a watan Junairun da ya gabata inda yake shaida musu cewa a “ a duk sanda kiɗa ya canja rawa ma canjawa take” inda ya basu shawarwari akan gudanar da rayuwa mafi sauki bayan ritaya, tare da dakatar da duk wasu batutuwa da suke kawo kashe kudi da yawa, kamar amfani da motocin alatu, tafiye tafiye da kuma yin rayuwa ta ƙarya ko kuma ta wuce gona da iri, sannan kuma da kaucewa biyan kuɗin haya mai yawa tare da neman wuri ko gari da suke da sauƙin rayuwa yana mai shaida musu cewa “kada ku manta a wannan matakin babu albashi, babu alawus da yawa, babu damar handama da kuma samun wani tallafi ko agaji daga ma’aikata ko wani abokin hulda, kuma kada ku manta a wannan karon iyalinku ba su da tunanin cewa duk wannan damar ta kuɓuce muku; tunaninsu shi ne kawai jiya ita ce yau”

A lokacin da Mutari ya zo wa da mahaifinsa da waɗannan shawarwari bai yi wata ja-in-ja ba ya bashi dama ya yi duk abin da ya dace saboda ya san cewa yaronsa yana da hankali sannan kuma ya goge a cikin ƙoƙarin samar da mafita a dukkan wani sha’ani na rayuwa ta yau da kullum.

Da farko motar Toyota lexus ya kai wani kamfanin sayar da motoci a Gwarimpa, inda aka yi kakara ya amshi karamar mota Toyota camry 2010 a naira miliyan biyu suka bashi cikon naira miliyan sha biyu a hannunasa ya je ya saka su asusun ajiyar bankin mahaifinsu kuma kuɗin dake ciki a ajiye dama Naira miliyan huɗu ne, gaba ɗaya suka kama naira miliyan sha shida da yankai.

Daga nan ya bincika a asusun kuɗaɗen da ake cirewa na fansho dake IBTC a nan ma kuɗaɗen da ake dasu sun kai miliyan sha takwas, duk da cewa akwai sauran hanyoyi da ya kamata abi kafin a sami damar fito dasu. Sannan yaje ya duba asusun ajiyar kuɗin mallakar gida nan ma naira miliyan biyu ne da yan kai.

A lokacin ne Mutari ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na bankin lamunin gidaje na ƙasa akan ko suna da muhallai na saidawa a jihar Kano? Domin nan ce jihar da mahaifinsu ya zaba domin ci gaba da gudanar da rayuwarsa. A nan take jami’in hulɗa da jama’a na bankin bayar da lamunin gidaje ya tabbatar masa da cewa akwai kuma an tallata su a shafin yanar gizo na bankin domin ba kowa da kowa damar sayen gidan.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga shafin yanar gizo na bankin bayar da lamunin gidaje inda ya ga gidaje da dama da aka tallata a shafin ciki kuwa har da jihar kano, kuma kowanne fasalinsa da farashinsa.

Ba tare da ɓata lokaci ba ya yi nazarin bayanan da aka rubuta dangane da gidajen da bankin ya gina a jihar kano a gundumar tamburawa tare da hadin gwiwa da wani kamfanin gina gidaje na Almukab wanda suka gina da zummar samar da nagartaccen muhalli da bunkasa walwalar birni bayan cunkoso da ƙwaryar kano take fama da shi, sannan kuma su samar da wani tsari ta yadda zai karfafawa masu son gina sabbin unguwanni ƙwarin gwiwa domin ganin cewa sun tashi daga aƙidar awon igiya ya zuwa tsararrun unguwanni na faɗa a gani.

A lokacin da Mutari yake gudanar da bincike ya yi mamaki cewa guda hamsin ne aka gina a kano sai dai mutane da dama musamman yan asalin birnin Kano ba su mallaki gidajen ba kuma duk da farashi da rangwame da gidan yake da akwai da kuma hawa hawa ne daga mai ɗaki hudu zuwa uku , zuwa ɗaki biyu, amma a binciken Mutari ya gano cewa dama can ɗabi’ar wasu daga cikin mutanen yankin ba kasafai suke son barin cikin birnin Kano ba har ma ya gano cewa, yawanci sabbin unguwannin gefen Kano baƙi ne suka fara gina su kamar rijiyar zaki , janbulo, kwandila da ire-irensu.

Amma kasancewar akwai ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka fara sayen waɗannan gidaje daga ciki har da ma’aikatan jinya daga asibitin malam Aminu Kano, da kuma wasu daidaiku daga sauran ma’aikatu na gwamnatin tarayya.

Mutari Wanda ya yi la’akari da yawan iyalin mahaifinsa, da kuma gidan da ya dace da shi inda ya zabi gida mai ɗaki huɗu wanda kuɗinsa ya kama naira miliyan sha biyar. Duk da cewa akwai masu ɗakuna uku na naira miliyan sha biyu da kuma masu ɗaki biyu na naira miliyan tara, amma kasancewar zubairu Danmalam yana da mata biyu da yara gida mai ɗaki huɗu ne ya yi daidai da tsarin iyalinsa, kuma haka aka yi ya tare a gidansa da iyalinsa da kuma motarsa ƙirar Toyota camry.

A cikin sauran kuɗin da ya rage masa ne ya yi ƙoƙarin mallakar gona a ƙaramar hukumar Kura kasancewar gundumar Tamburawa tana kusa da kura wurin da ya shahara da noman shinkafa da kayan lambu, duk fa wannan ci gaba da Zubairu Ɗanmalam ya samu a ƙanƙanen lokaci ya faru ne ta sanadiyar ɗansa Mutari wanda yake bibiyar abubuwan da suke faruwa a kodayaushe kuma yakan yi tsayin daka ya ga cewa ya amfana kuma wani nashi ma ya amfana.

A yanzu abin da ya sa a gaba shi ne yadda zai shiga ya fita wajen ganin ya taimaka wa mahaifinsa ya samu kuɗinsa na ritaya tare da shigar da shi a kan tsarin masu amsar fansho a kan kari.

A wani lokaci ne za su tafi Abuja tare da mahaifinsa domin zuwa wajen tantance waɗanda suka yi ritaya a farkon shekara , mahaifinsa yace su biya ta Zaria domin gaisawa da wani tsohon abokinsa wanda ya yi ritaya a shekarar 2018 a matsayin baban jami’in mulki da walwalar ma’aikata a hukumar ƙidiya ta ƙasa.

Da farko dai Mutari ya yi zaton zai ga abokin mahaifinsa a wani katafaren gida na alfarma, sai dai ga mamakinsa sai gashi a wata unguwa wadda an ɗauki minti talatin ana ta waya a tsakanin juna kafin akai ga gano unguwar wadda take cikin wani lungu mai sassarƙiya. Kusan tazarar mita 800 suka aje motarsu sannan suka ƙarasa gidan a ƙasa.

Zubairu Danmalam tare da ɗansa Mutari sun yi mammaki yadda abokin mahaifinsu ya kasance a cikin wannan wuri dama irin muhallin da yake ciki na tsohon ginin tubali kuma duk an yi masa yar kwaskwarima da siminti sannan kuma ga ƙunci a wurin daɗin daɗawa kuma a haka har kiwon dabbobi ake a wurin abin da ya hadu ya zama wata kwamacala a wurin.

Bayan sun zauna ne an gama gaisawa Zubairu yake shaidawa abokin nasa Magaji Maiburki cewa shi ma ya yi ritaya a yanzu haka ma akan hanyar zuwa tantancewa suke a birnin tarayya Abuja.

Ba tare da ɓata lokaci ba Magaji maiburki ya yi maraba da zuwansu ”da farko ina taya ka murnar kammala aiki lami lafiya, sai dai wani hanzari ba gudu ba, ina jin tausayinka akan halin da zaka shiga a yanzu na rayuwa bayan ritaya, bata da daɗi ko kaɗan, yanzu ne nike nadamar yadda aka yi na shiga aikin gwamnati ba tare da na tsinkayi yadda rayuwa zata kasance a gaba ba, na farko nan inda ka ganni gidan gado ne na amshi bangarena na gyara, na biyu ina da fili a wajen gari amma har yau na kasa kewaye shi, sannan na uku larurori da hayaniyar iyali da yan unguwa ta hana ni sakat, kusan kullum cikin masifa muke ta ambaliyar ruwa, cakwali, kwalara da zazzazabin cizon sauro da makamantansu, kuma babbar matsalar da nike fuskanta a yanzu ita ce yadda jama’a suke yin yadda suka ga dama wajen zubar da shara a kan magudanar ruwa da kofar gida in nayi magana sai a ce sanda nike da dama wace tsiya na yi wa al’ummar unguwar don haka sai na kame baki na na yi shiru”

Malam Zubairu Ɗanmalam ya tausaya abokinnsa kan labarinsa da ya ji, a don haka shi ma cikin ɗan ƙanƙanen lokaci ya sanar da abokin nasa yadda ɗansa Mutari ya ceci rayuwarsa a daidai gaɓar da yake ritaya, kuma duk abubuwan da ya mallaka ya mallake su ne a ƙanƙanin lokaci.

Magaji Maiburki ya yi wata ajiyar zuciya kana ya ce wa abokinsa Zubairu “ka yi sa’a da ka sami yaro mai hankali mai tunani, kuma wannan bai rasa nasaba da yadda suka zo a wani zamani da ake yin abubuwa a buɗe, sannan kuma bahaushe ya yi gaskiya da yake cewa “sanin hanya ya fi sabko” domin ka ga su son zo a zamanin da ake wayar da kan mutane a kan muhimmancin tsimi da tanadi, sannan dukkan wani romon rayuwar duniya yana farawa ne daga Muhalli, mun yi sakaci da ba mu maida hankali ba a farkon rayuwarmu wajen tanadi da kuma mayar da hankali a kan abubuwan da ya kamata, kaga yanzu sai tunane tunane da yin da na sani, amma kai kayi sa’a da ka farga a daidai lokacin da mu kuma muka yi fargar jaji”

 * * * * *

Karshe

Mutanen biyu suka taho zuwa wurin da su Mutari suka aje motarsu suna hira irin ta tsaffin abokai duk da cewa kowannensu yana da yanayi na rayuwa da ya sa a gaba, amma idan ka kalli nutsuwa da kuma salon tafiyar mutnen guda biyu zaka samu akwai banbanci domin Zubairu Ɗanmalam fuskar shi tana annuri yana ta murmushi ya yin da Magaji Maiburki zaka fahimci cewa a cikin taraddadi yake da tunzuri da kuma halin neman taimako a kodayaushe.

 A daidai lokacin da suke ƙoƙarin fitowa daga lungun ne wani yaro ya taho da taya yana garawa kwatsam ta subuce masa sai cikin kwata, a daidai lokacin da Magaji da Zubairu suna ƙoƙarin ƙetarawa kawai sai ganin cabin kwata suka yi a rigunansu musamman ma Zubairu Danmalam wanda ya sha farar babbar riga. Magaji Maiburki abin bai yi masa daɗi ba, yana ƙoƙarin ya yi wa yaron tsawa sai Zubairu ya ce masa ai ba komai akwai ruwa a mota zamu wanke kuma kada ka cewa yaron komai, domin a cikinsu kake da zama don ka da shi da iyayensa su riƙa zautar da kai a irin wannan lokaci da kake buƙatar samun nutsuwa.

Za su yi sallama ne a bakin mota zubairu Ɗanmalam ya ɗauko naira dubu goma yaba Magaji Maiburki tare da cewa” ga wannan ka sayi omo ka wanke wurin da Yaron nan ya ɓata ka da kwata” Magaji ya yi tsaye Turus kamar wanda ruwa yaji, ya shiga wani dogon tunani na daban....

Alhamdulillah

Muhalli, Sutura

Post a Comment

0 Comments