Ticker

6/recent/ticker-posts

Son Zuciya

Rufaida Umar (2023). Son Zuciya. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communcation Company LTD

SON ZUCIYA...

Na

Rufaida Umar

Wadatacciyar iskar da ke karakaina a farfajiyar ofishin ba ta taka rawar ku zo ku gani ba dangane da tururin da ke ambaliya daga ilahirin sassan jikina. Likitan dai ya duƙufa ga nazarin takardun sakamakon gwajin da aka yi min da ke gabansa.

Bayan wani lokaci da ya zame min tamkar shekaru ya dago kai ya dube ni da kyau. Ya cigaba da rubuce-rubucensa a fayil ɗina. Na sunkuyar da kai ina share hawayena, ko bai faɗa ba, na san silar matsalata wanda a yanzu nake cike da nadama. Na soma lissafin waɗanda ke bina bashi a duniya don ina da tabbacin abin da zai fito daga bakin likita daidai yake da albishir na kusantowar ajalina.

“Maimunatu Sa’ad, kina tuammali da miyagun ƙwayoyi ne? Na ɗaga kai da sauri muka haɗa ido. Kafin na maida numfashi ya ci gaba da cewa, “Ina nufin shaye-shaye ba bisa ƙa’ida ba.”

Tsabar kunya ban san ya akai gumi ya lulluɓe ni ba tamkar mai jegon da ta sha tururin ruwan zafi, sannu-sannu ba ta hana zuwa, yau ga ranar ƙin dillanci. Da ƙyar na iya motsa leɓɓana wanda suka yi min nauyi.

“Eh to... Ina shan magungunan rage damuwa...” Ni kaina ban yarda da muryar da ta furta hakan a cewar ni ce mamallakinta ba.

Ya girgiza kai cikin alhini, fuskarsa na kalla sau ɗaya ban ƙara kallo ba, yanayin kallon da yake yi min tamkar na malamin da ya ga karuwa. Ban iya fayyace kallon na ƙyama ne ko na tausayi ba. Na tsinci kaina mai tausayin gurɓatacciyar rayuwar da na tsunduma ciki.

“Ko kin san cewa yawan ɓarin da ki ke yi yana da nasaba da waɗannan shaye-shayen? Har ila yau kuma kina da hatsarin kamuwa da cututtukan da suka shafi ciwon hanta da ƙoda da ƙwaƙwalwa da kuma bugun zuciya.”

Gabana ya yanke ya faɗi. Idan mijina ya ji wannan labarin wane irin mataki zai ɗauka game da ni? Ni kam na ga ta kaina! Wani kuka ya kubce min mai ƙarfi, wannan shi ne ihu bayan hari, me ya sa a baya ban yi ƙoƙarin yaƙar zuciyata ba? Da ƙyar na tsaida kukana ganin yadda likita ya dage yana rarrashina da ban baki.

“Mahaifiyata ce ta koyamin shaye-shaye.” Na furta hakan ba tare da na yarda na haɗa ido da likita ba. Na lura da yadda likitan ya kalle ni hankali tashe, na bi shi da murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo.

“Kika ce me?”

“A zamanin da uba yake haiƙe wa ɗiyar cikinsa, uwa take kyautar da yaranta mata ga ‘yan ta’adda don kwaɗayi da burin abin duniya, uwa ke neman ‘yarta da baɗala, har akwai abin da za ka ji ya ba ka mamaki?”

Sai a sannan ya numfasa gami da zare farin gilashin da ke maƙale a idanunsa.

“Ba mamaki nake ba, a tsarin aiki irin namu, jin ire-iren waɗannan labarun da ma waɗanda suka zarta hakan, ba wani sabon abu ba ne. Mun kasance kullum akwai shafin ƙaddara iri-iri da muke karantawa waɗanda da yawansu son zuciya ke haddasawa.

Na gyaɗa kai cike da gamsuwa da maganganunsa. Kaina a ƙasa, kamar yadda bai nemi na sanar da shi ta yadda aka haihu a ragaya ba, haka ni ma ban yi gigin warware masa zare da abawa ba har ya kammala rubuce-rubucensa ya miƙo min.

Godiya kawai na yi masa na miƙe, har na kama ƙofa da zummar fita ya dakatar da ni ta hanyar kiran sunana. Na juyo na dawo da baya, na ƙara bin umarninsa na nemi wuri na zauna.

“Ba zan maki magana ta hujjar cewa ni likita ne a wurinki ba kadai, zan maki nasiha ne ganin cewa da ni da ke duka musulmai ne, ‘yan uwan juna. Mutane da dama sun ɗauki shaye-shaye hanya ta gusar musu da dukkan matsalolin rayuwa, ta sanya musu nishaɗi. Sai dai sun manta ba a nan gizo ke saƙar ba, a matsayinmu na musulmai, Allah Ubangiji bai halasta mana cutar da kanmu ba balle ‘yan uwanmu. To akan wane dalili za mu ɗauki turbar da ba shi ba har a garin neman gira mu rasa ido? Ina imaninki da Allah ne mai yaye dukkan matsala da damuwa ya tafi? Ina ki ka bar azumi, sallah da addu’a? Ko kuwa kin shagala da jin daɗin duniya ta turbar da kike ganin za ta haifar maki da ɗa mai ido har kika mance hasken da Allah ya saukar mana ta hanyar Annabinsa (S.A.W)? Wato alkur’ani mai girma. Ina kika bar Suratul Fatiha, surar da ta kasance mai kawo warakar zuciya da gangar jiki?”

Kuka mai ƙarfi ya ƙwace min, kamar yadda ban fasa ba, haka shi ma bai dakatar da ni ba har dai na yi mai isa ta na share hawayena. A karon kaina na ji na muzanta, wata irin kunya ta lulluɓe ni wadda na ji kamar ƙasa ta tsage na shige cikinta. A karon kaina na sani, ba zan jeranta halin da na shiga ba a layin ƙaddara, wannan son zuciyata ne, son zuciya kuwa ɓacinta. Na share hawayena, hakanan na ji na sami nutsuwa da Likita, na ji zan iya zayyane mishi damuwata kai tsaye. Don haka na gyara zama da niyyar zayyane masa yadda uwa mahaifiya wacce ta kasance abar alfaharin kowane ɗa, ta zama silar rushewar tawa tarbiyyar, ko da dai ba ita kaɗai ba, shi ma mahaifin nawa, ban cire shi a lissafina ba. Kusan shi ne ummul aba’isin komai, idan na ce komai, ina nufin komai.

“Tarbiyyar ‘ya’ya a kan imani da ibada; da ɗabi’u da mu’amala; da kula da lafiyar jiki da hankali da tunani; da tsarin zamantakewa, wajibi ne da Allah Ya ɗora a kan iyaye da dangi, da malamai, da shugabanni, da sauran jama’a gaba ɗaya. Iyaye su ke da alhakin farko na ginin tarbiyya, idan har ba su ɗora mu akan turbar da ta dace ba tun da fari, to fa shakka babu akwai tarin kaico a rayuwarmu. Wannan gatan na rasa tun farko, na buɗi ido ni ɗaya tilo a hannun iyayena, ance ina da yaya wanda ya rasu kafin na wanzu a doron ƙasa sakamakon bugun da Babana ya kai wa Mama shi kuma yana jariri ta goya shi, aikuwa daga wannan bugun ta faɗi rigingine hakan ya yi sanadiyyar ajalinsa.

Ba abin mamaki ba ne idan na shaida maka cewar iyayen nawa sun haɗu ne a uwa duniya sakamakon yawon uwa ba kwaɓa da kowanensu yake yi. Na kan yi shiru cikin ƙoƙarin gano inda hankalina ya fi amincewa tsakanin mai tsananin ƙaddarar rashin tsayayyun iyaye ko kuwa mafi rashin gata.

Babana kusan ɗan a bi yarima a sha kiɗa ne a fannin siyasa. Shi dai ba shi da alƙibla ɗaya tsayayya, yau idan ka gan shi da wancan honarabul din, gobe za ka gan shi cikin ‘yan adawa. Shi dai duk inda zai faɗi ya ji lema, to kuwa nan ne makwancinsa. Abu biyu zuwa uku da suka kasance babbar matsala ga rayuwarsa su ne, rashin sallah bisa ƙa’ida, dukan mace da kuma shaye-shayen abubuwan gusar da hankali. Da wannan munanan ɗabi’un ya yi suna ya shahara har ya goga wa kansa da ma gidanmu baƙin fentin da har yau ba a bar kallonmu da shi ba, mun dai rasa rigar mutunci. Ba na jin tun da na yi wayo a gidan nan, daga fitowar rana har zuwa faɗuwarta, ban ga ranar da Babana bai kai hannu ya daki Mama ba. Duka ba irin wanda hankali zai ɗauka, duka ne da kulki wanda koyaushe yana nan ajiye a bayan kujera. Sau da dama na sha jin wani irin angizo na ƙoƙarin ƙwatar wa Mama ‘yancinta, sai dai tun wani mangari da ya yi min ban sake karambanin shiga huruminsa ba, sai dai na yi zuru ina kallon abin da ya fi wuta zafi.

“Shegiya! Tsinanniya ‘yar bariki!” Kai da ma sauran wasu kalolin ashariyar da sun girmi ɗaukar kwakwalwa, su ke fita daga bakinsa a kullum. Wannan ya haifarmin da tsananin tsoro da fargabar ganinsa. Ko gyaran murya ya yi, zan shiga taitayina, numfashina kuwa da kyar nake fitar da shi tamkar mai cutar asma.

A gidanmu nasan idan mace ta yi dariya mai ƙarfi laifi ne, ko kuma idan ta yi girkin da ta ke ra’ayin ci, shi ma laifi ne, daidai da fita unguwa yakan zama laifi a wurin Baba balle a kai ga zuwa asibiti don duba lafiya. Daidai da rediyo idan ta kunna cikin rashin sa’a aka sanya waƙar abokin hamayyarsa a siyasa, to kuwa ranar babu zaman lafiya. Mama ba ta da damar yin baƙi ta dafa ta ba su su ci, ranar ihunta sai ya cika maƙwafta har sai sun fahimci abin da ke faruwa.

Babu mai zuwa kawo mata ɗauki, sun yi har sun gaji da kalar zagi na cin mutunci da su ke fuskanta daga Babana, toh abin mamakin ma da ban haushin, ita kanta Mama ba ta goyon bayan su shiga sabgarta har su kawo mata ɗauki. Ban taɓa ganin makauniyar soyayya ba sai akan Mama, son da take yiwa Baba da yawa ma sun ja wa kansu alhaki da tunanin asiri ya yi mata. Da dama kuma suna ganin rashin tabbatacciyar makoma ne ya sa ta liƙe masa. Shi ma kuma ba shi da wata tsayayyiya sai ita ɗin domin kuwa na tuna wani lokaci da ya ambata sakinta, shi da kansa ya yi ta rusa kuka yana marin kansa yana tumami kamar ƙaramin yaro. Ka san fa duk wanda ƙwaya ta yi wa karo, yawancin abubuwan da yake aikatawa ba irin na daidaitattun mutane ba ne.

Yau da gobe mai sa uwa ta zama ƙawa, sannu a hankali Mama ke sanar da ni faɗi tashin da ta sha a baya da irin ƙaddarar da ta jawo ta auri mahaifina. Ta kan ce da ni, “asalina wanda nake so aka tilasta min rabuwa da shi. Aka aurar da ni ga wani tsoho wanda ya girmi mahaifina. Ina jin ma zai yi sa’an kakana. An ce min wai dalilin da ya sa ya nace akan aurena, wai saboda wani tsiminsa zai tashi idan ya auri budurwa mai siffa irin tawa. Yana da mata uku kuma dukkansu suna da ‘ya’ya da dama, ƙaramar cikinsu ma ta girme ni. Ke daga ji kin san wannan haɗi ba mai yiwuwa ba ne. Don haka na yi ta bori da guje-guje na ƙi yarda da zama da shi. Bayan ɗaurin aure da tariyata, washegari zakara ya bani sa’a na shiga mai faɗin.”

Idan tana ba ni irin wannan labarin nakan yi ƙoƙarin tuna irin azabar ko tsananin da ya tilasta mata gwammacewa zama ƙadangaruwar duniya akan zama na halaliya ƙarƙashin ikon majiɓintanta. Sai dai ba ni da kaifin hankali ko ilimin da zan iya gano dalili ballantana mafita.

Ta ɓangaren mahaifina kuwa, wanda ya zame mana tamkar zaki a tsakiyar garken awaki, koyaushe na yi ido huɗu da shi sai na ji hantar cikina na kaɗawa. Sanin ɗacin ransa da mugun nufinsa wajen duka ba ji ba gani ba iyakancewa ya sa ko gaisuwa sai na yi da gaske nake iya buɗe baki na yi masa. Shi kuwa amsawa ma bata zama wajibi ba. Baya shakkar aiwatar da dukkan ƙudurinsa gabanmu, don haka nake iya tabbatar da cewa yanzu dai ya bar harkar neman mata, babban abin da ya sa gaba shi ne safara da kuma shan miyagun ƙwayoyi.

Na yi haddar sunayen abubuwan gusar da hankali tun ma ban san takamaiman ma’anar su ba har zuwa sadda na mallaki hankali na fahimci komai, kamar dai irin su slow motion, ƙurunƙus, ‘yar hutu. Waɗannan da ma sauran su haka zan ji Babana yana waya, yana tambayar adadin da ake da buƙata. Ko naji yana kiran ai babu kaya sun ƙare sai an kawo.

Ranar da na fara ganin abin da ya kusan sumar da ni, shi ne sadda aka wayi gari wata laraba na shiga ɗakin Mama na tarar ta ɗaga kwalbar maganin da take ba ni na mura ta shanye tas ta kuma jawo wani kwalin ta buɗe shima ta kai baki ta zuƙe. Duka-duka lokacin ban fi shekaru goma sha uku zuwa huɗu ba. Koda na ƙarasa na dafa kafaɗarta a tsorace, ta jawo ni jikinta ba a hayyaci ba ta zaunar da ni gefenta ta shafa kaina.

“Mene ne kike kallona? Mura fa nake yi, kuma wannan maganin duk sadda aka sha kwalba biyu uku hudu, yana haifar da nutsuwa, yana warkar da ciwon zuciya da ma damuwa. Kin ji? Kar ki faɗawa kowa.” Na ɗaga kai na kalle ta cikin rashin fahimta. Na lura dai idanunta sun juye zuwa wata irin siffa abin tsoro, to amma kwarjinin firgicin bai kai na irin gizon da mahaifina ke mini ba. Na ji muryarta ta ƙara kumbura tana furuci da ƙyar kamar mai koyon magana.

“Mama me yasa muryarki ta canja?” Na tambaye ta ba tare da tabbacin samun amsa ba. Ta miƙe daga wajena ba tare da ta bani amsa ba.

A hankali kuma sai na dinga lura da wani abu, duk sadda Babana ya dawo, Mama na shiga ɗaki ta afa wasu ƙwayoyi a bakinta, koda na tambayeta na mene ne? Sai cemin ta yi ai maganin ƙarfi ne, yakan saka jarumta ta yadda ko da ace da rodi Baba zai buge ta, ba za ta ji ko ɗarr ba. Aikuwa haka na gani, don dukan duniya idan Baba zai yi a wannan rana, to fa ko a jikinta, ihu dai take zubawa da a ƙarshe na fahimci duk na bogi ne don yana gama dukan za ta shigo ɗakin tana dariya har ta dinga faɗin ko a jikinta.

Abin kan yimin ciwo, sam ba na ganin laifin Mama, na fi tsanar Baba sama da ita don shi ba ya ta rayuwata, ji yake tamkar su biyu ne kaɗai ke rayuwa a gidan. Ita kuwa Mama, ta mayar da ni ƙanwa kuma ƙawarta domin dai Mama ba ta da wani wanda ke raɓar ta, a farko lamarin na damuna yadda ake gudun haɗa duk wata alaƙa da gidanmu, a ƙarshe kuma ganin ban rasa duk wani gata a wurin Mama ba sai na watsar. Idan har zan furta na ce mata ina son abu kaza, to ko babu za ta nema ta yi min.

“Sata babu kyau amma dole ce ke haifar da ita a rayuwata Maryam, kar kiga ina ɗauka daga asusun Babanki, idan muka biye mishi ba za mu mori rayuwa ba. Shegen maƙon tsiya ba zai bari ya amfana mana da komai ba. Gwara mu ci duniyarmu da tsinke.”

Wannan maganar Mama ta furta min sa’ilin da na kama ta dumu-dumu tana lalube aljihun wandon Baba. Ba a kaina kawai kuɗin suke tafiya ba, ta fi siyan abubuwan bugar da hankali, na lura duk ranar da aka wuni ba ta samu kuɗi ba, to fa a ranar wuni za ta yi ɓacin rai da faɗace-faɗace. Haka za ta sanya ni dakatawa a ƙofar zauren gida na yi mata gadin Baba, da zarar na ga tahowarsa da mashin zan ruga a guje cikin gidan na sanar mata, ita kuwa za ta yi sauri ta mayar da kayayyakinsa da ta fiddo don kawai neman inda ya adana abubuwan mayen da yake siyarwa a ɓoye.

Duk sadda ta ci nasarar samu, babu tunanin komai haka za ta kwasa ta ɓoye cikin kayana ta dinga sha, sai ta wuni tana jan munshari abin ta, ta bar ni da alhakin gyara gida da ɗora irin dahuwar da na ƙware wajen yi. Baba kuwa, idan ya laluba ya ga an wawushe masa kayan sana’a, to a ranar mai kwatar Mama sai Allah. Ita ma idan a sama take, yana yi tana yi, duk ranar da hakan ta kasance ƙulle kaina nake a ɗaki na ci kuka, wannan ne kaɗai na kasa sabawa da shi. Duk radda kowannensu ya hau su na zage-zage ji nake kamar na shiga duniya. Wataran sai na ji kodai idan sun fara, na bankaɗa kayana na ɗauki ajiyar Mama na afa? Sai kuma tsoro ya hana ni duk kuwa da cewar na san muhimmancin shan su daga wurin Mama, ko a tunani ban taɓa kawo musu wani amfani ko rashinsa ba sama da yadda ta faɗamin. Gani nake abin da ta faɗi babu ƙari babu ragi, hakan ne, su ke maganin damuwa.

Hausawa suka ce rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya, jami’an hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙasa (NDLEA) su ka yi wa gidanmu dirar mikiya a cikin wani dare suka tasa ƙeyar Baba suka ta fi da shi bayan sun bincike ɗakinsa tsaf sun gano miyagun ƙwayoyin da yake siye da siyarwa. Tashin hankali gobarar gemu! a wannan ranar haka matasa suka dinga jefo mana duwatsu a gida ga tsinuwa da aka dinga jifanmu da shi, ni da Mama ban da kuka da ihu ba abin da muke yi, da taimakon dattawan unguwa aka samu komai ya lafa, kowa ya koma muhallinsa.

A daren Mama ta haɗa kayanmu a gurguje muka bar unguwar nan gaba ɗaya sai gidan wata tsohuwar ƙawarta. Ta karɓe mu a wulaƙance don a cewarta, ba ta mance zagi na uwa da uba da Mama da Baba suka yi mata ba, akan ta shigar wa Mama faɗa. Ta watsa mata ƙasa a ido.

Satinmu biyu a gidanta muka tattara zuwa gidan iyayen Mama, da kyar suka karɓe mu sai da Mama ta dinga neman gafararsu da alƙawarin ba za ta sake ba ta yi nadama kafin su karɓe mu.

Bayan shekaru uku, abubuwa da dama sun faru ciki har da gushewar Mama daga doron ƙasa a sanadiyyar bugawar zuciya farar ɗaya wanda a tunanin mu damuwar rashin Baba ta haifar mata, na samu tsayayyen miji nayi aure. A lokacin ne kuma Babana ya samu fitowa daga hannun hukuma. Na yi mamakin sauyin da na gani tattare da shi, abin da ya fi ƙayatar da ni bai wuce ɗaukarmin alƙawarin cewa zai nemi sana’ar hannu mai kyau koda kuwa bai ci moriyar digirinsa ba a fannin aikin jarida, ba zai ƙara bari ya zama tamkar waina ba a kaskon ‘yan siyasa, su juya shi son ransu.

Ba iyaka alƙawarin ne ya burge ni ba sai da a zahiri na ga ya cika domin kuwa da ɗan abin da ya rage masa na dukiyarsa ya kafa ƙaramin shago yake siye da siyarwa a ciki. Bai tsaya a nan ba sai da ya kyautata mu’amalarsa da iyaye da ‘yan uwansa. Kana naka Allah na tasa, Baba ya yi nufin sake fasalin rayuwarsa da inganta hanyoyin samunsa.

Ba zato ba tsammani ya kwanta wani irin ciwo mai kama da mura. Da farko ana zaton ko mashaƙo amma da aka je asibiti sai likitoci suka buƙaci tilasta a killace shi inda ba zai yaɗawa kowa ba. Suka tabbatar mana cewar Baba na ɗauke da cutar Korona mai sarƙe numfashi. Babu jimawa ya ce ga garinku nan. Duk da ba mu cika jituwa da shi ba, mutuwarsa ta sa na ji na zama tamkar tsuntsun da ke yawo a samaniya ba tare da sanin inda zai kwana ba. Babu abin da ya rage mini martaba da madogara sai gidan mijina, ɗakin aurena.

Rayuwar aurena rayuwa ce mai tarin ƙalubale da dama, na yi sa’ar samun miji irin wanda nake so, wato mai tarin dukiya da kuma kyawun halitta sai dai abin takaicin da dana sani shi ne ba mazauni ba ne. Babban ɗan kasuwa ne mai yawan tafiye tafiye saro kaya. Ta dalilin haka ne na shiga ƙunci da damuwa, ga dai gida har gida nan amma babu wani abu mai ɗebe kewa. Wannan ya tunasar da ni huɗubar Mama, na kuma yi amfani da ita don magance tawa matsalar, sosai idanuna suka rufe, ban tuna komai ba sai kawai abin da zuciyata ta ƙissima min. Na tsunduma harkar shaye-shaye. Mijina yana sakar min kuɗi sosai, har mota ya siyamin.

Da wannan damar da kuma ƙawata na ci nasarar gane wuri mafi sirri na siyan kayan maye. Sau ɗaya da na je ban ƙara ba, ƙawata ita ke siya take kawo mini har gida na sha. Nan da nan walwalata ta dawo, na daina zaman ƙunci, idan ya dawo nakan yi duk dabarar da zan yi kada ya fahimci halin da nake ciki, sai dai Allah ya jarabceni da mugun son ‘ya’ya watakila kuma don ni kaɗai na rayu gaban iyayena, sai wannan matsalolin suka biyo baya. Wannan shi ne silar komai, mafarin dukkan wasu musibu na rayuwata.”

Ina kaiwa ƙarshe wani sabon kuka ya tahomin, wannan karon likitan shi kansa na lura ba shi da ƙwanjin dakatar da ni balle ya ban baki, a karo na biyu ya bar ni na yi mai yawa kafin ya yi gyaran murya ya soma magana.

“Ba zan hana ki kuka ba Maryam, tabbas kin aikata laifi wanda musabbabinsa iyayenki ne. Sai dai koda ki ka ambaci mahaifiyarki kaɗai na yi mamaki domin labarin da ki ka ban ya nuna cewa da sanya hannun mahaifinki dumu-dumu a ciki. Ba don uzzura rayuwar Mama da ya yi ba, da duk hakan ba ta faru ba. Bai yi amfani da damar da Allah ya ba shi na lafiya da baiwar hankali ya kyautata rayuwarsa da iyalinsa ba.

Iyaye su ne tushen duk wata tarbiyya kafin a gangaro kan ‘yan uwa, malamai, al’ummar gari da ma gwamnati. Shi icce tun ya na ɗanye ake tanƙwara shi. Ke uwa ce, koda ba yanzu ba, ina maki fatan haka, ya kamata ki sani cewa, shi fa yaro duk abin da ya gani iyayensa na aikatawa shi a wurinsa kawai wannan abu mai kyau ne. Kinsan babbar matsalar da yawanmu, ba mu damu da sanin su wa yaranmu ke hulɗa da su ba, ko kuma a’a, waye mijin da ɗiyarmu za ta aura, alhalin ko a musulunci, ya halarta a yi bincike kafin aure.

Iyaye idan sun gyara, dole ne makwafta da ma al’ummar gari su taya su, ba a nunawa masu shaye-shaye ko dai wani muggan ɗabi’un tsana, kokari ake wurin jan su a jiki tamkar marayun da suka rasa iyaye, a hankali yau da gobe ana nuna musu illolin wannan abu da suke aikatawa sai ki ga an samu maslaha.

Hakanan su ma Malamai su ci gaba da ƙoƙarin zaburar da su don ganin sun kaucewa faɗawa halaka. Idan aka yi haka sannan aka haɗa da addu’a kaso saba’in cikin ɗari za’a samu mafita. Kin ji nace addu’a, saboda ita ce takobin mumini, ba zamu iya ba sai an haɗa da ita. Sa’annan kinga akwai tallafin gwamnati, su ne masu muryar da za a ji kuma a yi aiki da shi. Wato dai su ke da alhakin nemawa matasanmu sana’a’oi, wadanda ba su da kwalin digiri a nemi sana’o’i na kafa kai a koya musu, a basu jari. Kin ga an kashe zaman banza wanda daga shi ne komai yake faruwa. Shaye-shaye, daba, sata, bangar siyasa da ma sauransu.”

Yana kaiwa nan ya ja numfashi, nima da nayi shiru ina sauraronsa ina gyaɗa kai cikin gaskatawa na gyara zama. Ya kara jawo takarda ya yi rubutu sannan ya miƙomin.

“Ga wannan ki haɗa cikin magungunan da na rubuta maki, sannan abu na karshe da zan ce maki kafin muyi sallama shi ne, sai kin rabu da mugayen ƙawayenki matuƙar kina so da gaske ki rabu da wannan ɗabi’ar. Ki maida alƙur’ani abokin hirarki, ki kuma zauna da mijinki ku yi magana sosai akan matsalarki, idan har kuma abin ya fi karfinki, ki samu iyayensa ki kai kokenki garesu. Wannan shi ne shawarar karshe da zan ba ki a yau, ina roƙon Allah ya baki ikon cimma manufarki ta alheri.”

Tun zamana a ofishin sai yanzu nayi murmushi domin ba ƙaramin ƙwarin gwuiwa na samu da zantukansa ba. Na yi mishi godiya sosai sannan na fice ina ji na tamkar a sabuwar duniya. Na so na cuci kaina, dama Hausawa na cewa son zuciya...ɓacinta.

Cikin ƙwarin gwiwa na tafi gida da zummar sake sabuwar rayuwa bisa yaƙinin cewa sannu a hankali kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Na ƙudiri aniyar ƙauracewa shaye-shaye har abada sannan na shirya yadda zan rabu da miyagun abokai tare da shimfiɗa sabuwar rayuwa.

Ɗaukar Jinka

Post a Comment

0 Comments