Fatima Bello Bala (2023). Sara Suka. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communcation Company LTD
SARA
SUKA
Na
Fatima
Bello Bala
Gumi
ke sartu a fuskata da goshina kamar ana gasa masara a tsakiyar garwashi a cikin
rana, akai akai nake sharce gumi ina daɗa riƙon tayar keken da nake yiwa faci.
Rediyon da ke kusa da ni ta sauya salon sautinta daga waƙe zuwa taken labarai, bayan gushewar
taken muryar zabiyar dake gabatar da shirin labarai ta fara aikinta cike da ƙwarewa da zilaƙar harshe.
"Rundunar
jami'an tsaro ta jihar nan, ta cika hannunta da wani matashin saurayi mai suna
Auwalu Damfo. Matashin dai an kama shi ne da laifin aika Mahaifinsa lahira ta
hanyar daddaɓa masa wuƙa a
ciki.
Jami'i
mai magana da yawun 'yan sanda Bamai Dabuwa, shi ya bayyana wannan al'amari a
zantawarsu da manema labarai a wurin da al'amarin ya faru. Jami'in ya shaida wa
manema labarai cewa Matashi Auwalu Damfo ya aikata wannan ta'asa ta wulla
mahaifinsa ƙiyama ne bayan ya yi
mankas da kayan maye..." Maganar ma'aikaciyar gidan radiyon ta ratsa dodon
kunnuwana, wanda nake jin saukar
maganar kamar an doka min guduma a ƙahon
zuciyata ne.
"Ka
ji ko?" Cewar wani Dattijo wanda ya kawo facin kekensa wajena, ina iya
hango fuskarsa ƙunshe
da takaicin abin da aka faɗa a rediyon, bai huta ba ya
ci gaba da cewa.
"Ni
dai na san hannu banza ba ya ɗaukar wuta, sai dai da
magani ko sharifta. A irin ƙima
da matsayi ko soyayyar ɗa ga iyaye, babu yadda za a
yi mutum ya kashe mahaifinsa a cikin hayyacinsa, ashe dai wannan abin nasu na
jaraba ya je ya sha ya fita a hayyacinsa ƙwaƙwalwarsa ta faɗa
masa ƙarya ya ƙare
a kan ubansa." Ya yi shiru yana kallon wani saurayi wanda shi ma facin ya
kawo min, ina ganin saurayin ya buɗi
baki ya fara magana.
"Gaskiya
wannan ɗa
dai ba ɗan
halak ba ne..." Tuni gabana ya sake dokawa da ƙarfin gaske, ina jin bugun zuciyata na
ninkuwa fiye da kima, wanda da za su lura da yanayina da sun fahimci na rasa
nutsuwata tun farkon fara jin rahoton kisan kan da matashin ya yiwa mahaifinsa,
na yi firgigit na kalli saurayin da ke wannan furucin, na goge gumin bazatan da
ya fara karyo min fiye da na bayan da nake yi, a can cikin raina ina tuna ranar
da nima aka jefe ni da irin waɗannan kalamai, ƙwaƙwalwata
tana so ta yi min tariyar wani shuɗaɗɗen
al'amari a cikin rayuwata ta baya, amma kwata-kwata ruɗanin
rahoton kisan ya hana ni kataɓus.
"In
banda ɗan
haram, ya rasa wanda zai kashe ma sai mahaifinsa? Shi ya sa fa ba abin mamaki
ba ne yanzu don an ce maka an aikata komai na laifi a ƙasar nan, don indai har mutum zai iya
kashe wanda ya kawo shi duniya to babu abin da ba zai iya aikatawa ba..."
Matashin ya sake faɗa da sautinsa mai amo, da
nake jin kamar yana kwara min ruwan dalma a ƙahon
zuci.
"Yo
da ma mana!" Dattijon ya katse shi da hanzari.
"Ai
illar shan kayan mayen nan da kake gani ta wuce duk yadda muke zato, shi ya sa
Ubangiji ya la'anci mutum takwas da suka shafi sha'anin giya. Tun daga kan masu
yin ta, da masu dakon ta har zuwa kan masu shan ta da dai sauransu. To kuma ba
ita kaɗai
ba, duk wani kayan maye ma Malamai suna ganin hukuncin ɗaya
ne, bisa dogaro da wani hadisi na Ma'aiki Sallallahu alaihi wa sallam da yake
cewa 'Dukkan abin maye giya ce... Giya kuma haramun ce.' " Ya ɗan
tsagaita bayan gyaran murya ya ci gaba.
"Saboda
shi shan kayan maye mutum ya fita a hayyacinsa shi yake jawo harkar daba, da
sara suka tunda masu shan ba sa kunya ko shakkar kowa suke yin abin da suka ga
dama..."
Tuni
ƙwaƙwalwar
da ke adana saƙo a kwanyata ta yi
caraf, cike da zafin nama ta cafko min wata kalma a cikin kalaman Dattijon...
'Sara suka' ina maimaita kalmar ina tuna yadda 'yan sara sukan suka kewaye ni a
wata shuɗaɗɗiyar
rayuwata. Kamar a lokacin komai yake faruwa, kawai sai gani na yi majiyin ƙarfi cikin 'yan daban ya ɗaga
zafgegiyar addarsa ya zafga mini sara a hannu, irin yadda ake girbe karan dawa
ko na maiwa haka na ga matashin ya tsinke mini hannuna guda ɗaya.
.....Na
sake yin firgigit na dawo daga duniyar tunani da kiɗimar
da na shiga, zuwa duniyar zahiri, hannuna mai kyan yana dafe da dungulmin
hannun da aka sare mini a waccan lokacin, wanda nake ji kamar a lokacin aka
datse shi. Ba na fatan ko a mafarki na sake ganin irin wannan baƙar rayuwa, ba ni ba ma, ina Addu'ar duk
wani mai ƙaunata kada Allah ya
jarrabe shi da shaye-shaye, don kuwa ba ƙaramin
nakasu ba ne, ga rayuwar duk wani matashi mai yin shi.
"Subhanallahi!
Malam Abba kukan me kake yi kuma?" Ban san cewa na bar kukan zuci na koma
na zahiri ba, sai da na tsinkayi muryar Dattijon nan yana tambayana, a sannan
ne na ji ɗumin ruwan hawayen da suke wasan tsere a
kumatuna. Sai da na saka
hannun rigata na share hawayen, sannan na nisa na fara magana da cewa.
"Ko
ka san cewa Auwal Damfo shi ne ya sare mini hannu ɗayan
nan nawa?" Da Dattijon, da matashin gaba ɗaya
sai suka bi ni da kallo, irin na kaɗuwa
da mamaki, ba su samu damar magana ba na ci gaba.
"Hatta
mahaifinsa da kuka ji an ce ya kashe yanzu ba kowa ba ne face mahaifinmu."
Sai a lokacin Dattijon ya fahimci dalilin da ya sa tunda aka fara wannan
rahoton kisan hankalina ya tashi, kamar wanda yake zaune a kan zuga-zigin wuta.
"Amma
dai wannan Auwal! Wannan Auwal! An yi asarar haihuwarsa." Furucin da
Dattijon ya iya yi kenan yana yi kamar zai yi kuka. Jin hakan ne yasa na yi
saurin katse dattijon na ce.
"Duk
abin da ka ga Allah ya yi akwai hikima a ciki Baba, kuma yawancin rayuwar nan
muna yin ta ne a kan doron karin maganar Bahaushe da yake cewa, ‘’abin da ka
shuka shi za ka girba’’. Don haka ina tabbatar maka hatta shaye-shayen yawancinmu ke yi, iyayenmu ne suke shuka irinmu a haka, idan mun
tsiro kuma wajen girbar mu yadda suka shuka mu sai mu zame musu damuwa."
Cike da alamun rashin fahimta Dattijon da matashin suke kallona, haka ne ya
sake sani jan numfashi da furzar da iska mai ɗumi
a bakina na ce.
"Da
yawan Hausawa sun jahilci wani hadisi na Ma'aik (S.A.W) da yake bayyana cewa a
yi aure a hayayyafa don ya yi alfahari da yawanmu ranar alƙiyama. Shi ya sa za ka samu mutum ɗaya
da mata uku ko huɗu, alhalin kwata-kwata ba ya
samun abin da zai iya ɗaukar ɗawainiyarsu.
Mahaifinmu
sana'ar gadi yake yi, kwata-kwata albashinsa bai wuce dubu goma sha biyar ba a
wata. Amma kuma haka muka taso muka gan shi da mata uku, mu 'ya'yansa mun doshi
arba'in a halin yanzu, sannan hatta gidan da muke ciki gidan haya ne mai ɗaki
uku kacal.
Haka
iyayenmu ke cunkusuwa a ɗaki ɗaya
da ƙannenmu mata da ƙananun maza, sai dai wacce yake a
kwananta ranar ta raba wa sauran matan 'ya'yanta kafin ita ma nata lokacin ya
zagayo.
Mu
kuwa 'ya'yansa maza tun muna shekara goma muke daina kwanan gidan, sai dai ya
kaɗa mu
waje mu je mu yi ta gararamba a masallatai da shagunan abokai. Ba kuma ya taɓa
damuwa da a ina muka kwana, ko kuma ya binciki halin waɗanda
muke kwana a wurinsu. Bahaushe ya ce, ' Kowa ya sayi rariya, ya san za ta zubar
da ruwa', to kamar haka ne kowa ya san idan aka yi wa yaro irin wannan
tarbiyyar tamu babu wani abin mamaki don an gan shi tsamo-tsamo a cikin tekun
shaye-shaye yana nunƙaya.
A
gidanmu hatta abincin da kowanne yaro da mahaifiyarsa za su ci sai dai su nema
da kansu, tun da ba sai an faɗa ba, a bayyane yake
albashin Mahaifinmu na dubu sha biyar, ko kuɗin
hayar gidanmu a tsittsinke yake iya biyan masu gidan balle ya ci da mu. Shi ya
sa duk wani aikin ƙarfi
ko wankau na unguwar uwayenmu ke yi su samu na rufa wa kai asiri.
Mu
ma 'ya'yansa tun muna shekara sha biyar muke ƙwarewa
wajen neman kuɗi maimakon karatu, saboda ba a rayuwa
sai da abinci, kuma ba abincin a gidan sai wanda muka nemo. Neman kuɗin
kuwa ta hanyar halal ko haram, duk wanda ya zo karɓa
kawai muke yi mu aika wa uwar hanji.
Auwal
Damfo shi ne babban ɗan Mahaifinmu, a wajen neman
abin da zai ci shi da mahaifiyarsa cikin tasha ya haɗu da
abokanan da suka ɗora shi a layin zuƙe-zuƙe.
Wanne tudu wanne gangare kawai sai gani muka yi ya koma ɗan
sara-suka. Su ke tare mutane su ƙwaci
wayarsu a unguwa, su ne farke shagunan mutane da daddare su ɗebi
kuɗi da
kaya, abubuwan ta'addanci dai iri-iri.
Tsautsayin
tauna, in ji maye da ya cinye jariri. Wata rana Auwal ya jefar da kuɗinsa
dubu biyu na tsinta, abinka da mai tsananin buƙata
babu wata cigiya na je na fara kashe su. Ina tsaka da cin abincin da na saya
Auwal ya zo kaina shi da abokanansa, ashe wai yaron da na tsinci kuɗin a
gabansa ne ya sanar da su suna hannuna. Shi ne fa suka yi mini dira irin ta
mikiya.
Bayan
na gama sanar da su cewa na fara kashe kuɗin
ne suke ta masifa, ashe wai wani ɗan
siyasa ne ya bayar su raba suka faɗi.
To a nan ne fa kayan mayen da suka sha ya fara yi musu tafsiri. Wata Shehiya a
cikin ƙwayoyin da suka kora ustazancinta ya
motsa, ta ba su fatawar cewa 'ai da ma an ce duk ɓarawon
da aka kama ya yi sata a sare masa hannun satar, don haka ne ni ma wai a cikin
mayen suka yanke hukuncin yi mini haddi su datse mini hannu tunda na yi musu
satar kuɗinsu.
Kamar
wasa haka nake ganin abin, ban taɓa
zaton za su aikata ba sai da na ga hannuna ɗaya
a ƙasa. Tun daga sannan kuma ban sake sanin
a inda nake ba sai farkawa na yi na gan ni a asibiti an nannaɗe
mini dungulmin hannun da bandeji. Su kuma wai tunda suka san sun yi ta'asar sai
suka shuri takalmansu zuwa Legas cunkus ɗakin
tsumma don gujewa hukunci.
"Kun
san Depression ai?" Na tambaye su, ganin kamar suna buƙatar ƙarin
bayani ne ya sa na ci gaba da magana.
"Ni
ma da farko ban san ma'anarsa ba sai da na tsince ni tsumu-tsumu a cikinsa,
wanda shi ne silar afkawa shaye-shayena.
Depression
wani irin hali ne da mutum yake tsintar kansa na tsananin ƙunci da damuwa, irin damuwar da zai ji
gaba ɗaya
duniyar ta yi masa zafi kamar ya kashe kansa. Yana daga cikin murtuƙa-murtuƙan
igiyoyin da suke yi wa da yawan matasa zarge mugun ƙulli su turke su a tirken shaye-shayen
kayan maye babu ji babu gani ba tare da sun farga ba.
Yawanci
wani abu na ƙunci ko damuwa ne
yake kawo Depression, don haka ni dai yanayin baƙin
ciki da ɓacin
ran da nake shiga idan na ƙyalla
ido na gan ni na koma mai hannu ɗaya
ne masomar komai, ƙari
a kan hakan kuma kawai sai Mahaifinmu ya saki Mahaifiyata a daidai lokacin da
take jigilar yin jinyata ita da 'yan'uwanta, kuma kawai ya sake ta ne babu wani
laifi na zaune ko na tsaye, sai don ya gano wata yana so ya aura.
Da
farko ko barci ba na iya yi saboda baƙin
ciki, da damuwa da kuma koke-koke da nake yawan yi, don haka likita ne ya fara
rubuta mini magunguna da allurar da zan dinga amfani da su na yi barci, kafin
daga baya kuma da ƙwayar
ta zame mini tamkar sanyin idanuna, ta zame mini tamkar ƙarfen-ƙafa
ta yadda indai ina son zaman lafiya da kwanciyar hankali to dolena sai na kora
ta, ko kuma a yi mini allurar.
Akwai
ƙalubale biyu da na fara fuskanta da waɗannan
magungunan da nake amfani da su, na farko shi ne tsadarsu wajen saye, na biyu
kuma dole sai da rubutun likita ake sayar da irin su. Sannan kuma shi asalin
likitan da ya fara rubuta mini ita ya ce wai na kai matakin da bai kamata na ci
gaba da shan ta ba don gudun irin matsalar da yawan sha ba bisa ƙa'ida ba zai haifar mini. Ga shi ni kuma
idan ban sha ba ɗin babu lafiya, don haka ne
na fara neman mafita ta kowanne hali.
Dungulmin
hannun da baƙin cikin ganin shi a
haka ya sa na faɗa shaye-shaye, da shi na yi
amfani nake fakewa ina zaga gari inda ba a san ni ba, na nuna cewa ni musaki ne
a ba ni sadaka, da haka nake tara kuɗin
sayan ƙwaya da allurar.
Wajen
sayowar kuwa kwanaki na ɗiba ina nazarin tsohon
rubutun da likitan ya yi mini ina koya wa kaina yadda zan rubuta ba tare da an
gane ba, da yake ina da basira daidai gwargwado kuwa a haka nake zuwa na sayo
babu wanda zai gane cewa ba likita ba ne ya rubuta mini. Sai dai kawai na dinga
canza kwanan watan ranar da na je sayayyar.
Don
haka kafin na farga na zama gawurtaccen ɗan ƙwaya. Saɓanin
kowanne magidanci da yake fafutuka don nema wa kansa da iyalansa abin da zai
ci, sai ya zamana ni fafutukata kawai ta yadda za a yi na sayo rocket (wato ƙwayar) da za ta harba ni zuwa gajimare
ko duniyar wata ne, ko da kuwa hakan na nufin sai na yi sata. Sai ya zamana
gaba ɗaya
nemana ina yin shi ne don na naɗa wa kaina rawanin tangaɗi ko
barci kamar mushe.
Sai
dai an ce mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi, shi ya sa yau da gobe har mai
kemis ɗin
ya ramfo ni. Don haka ne a wata rana da na je ya yi mini magana.
"Amma
ranka ya daɗe, na ga kamar kana yawan zuwa nan kana
sayan maganin nan."
Da
murmushi na ce masa "Eh."
"Waye
zai yi amfani da su?" Ya tambaye ni da wani irin kallo kamar na tuhuma.
Cikin ƙoƙarin
yi masa basaja na amsa masa.
"Ɗana ne, sikila ne." Na zaci da ya
ji na faɗi
haka kawai zai ɗauko mini na tafi, amma
kamar wani ɗan jarida sai ya ci gaba da kwararo mini
tambaya.
"Amma
har na tsawon wanne lokaci yake amfani da su? Domin na ga ka daɗe
kana zuwa nema, kuma har zuwa yaushe zai daina amfani da su? Saboda gaskiya waɗannan
magani da allurar suna da matsala na saurin sabo da dogaro. Idan har mutum yana
amfani da su akai-akai toh zai zamto jikinsa ya zo ya saba da su, daga nan kuma
sai jikin ya zo ya dogara kacokan akan amfani da su, ta yadda idan har bai yi
amfani da su ba, toh gani yake kamar mutuwa kawai zai yi. Wannan ya sa ake kula
wajen bayar da su."
Na ɗan
shafi busasshen leɓena da harshe, sannan na ce.
"To shi likitan ne dai yake rubuta mana ita. Kuma yaron nan kuka yake yi
indai ba wannan allurar aka yi masa ba ko barci ba ya iya yi balle mu ma ya
bari mu yi."
Mai
kemis ya sake yin murmushi sannan ya ce, "Duk ba jayayya nake yi maka ba,
amma abin da nake so ka sani shi ne, yi wa ɗan
naka wannan allurar zai samar masa da sauƙin
raɗaɗin
da yake ciki a yanzu ne kaɗai, amma kuma zai iya jaza
masa wata matsalar da za ta iya tarwatsa rayuwarsa gaba ɗaya.
Saboda yanzu kuna yi masa ita, jikinsa kuma yana ƙara
sabawa da ita har ya zamana ya dogara da ita, sannan kuma allurar tana da nata
illolin kamar sauran magunguna, daga ƙarshe
illolin wannan allura kaɗai sun isa su hallaka shi, ƙari akan cutar amosarin jini da yake
fama da ita.
Daga
cikin illolin shan waɗannan magungunan ba bisa ƙa'ida ba akwai hawan jini, faɗuwar
farat-ɗaya,
cushewar ciki, bushewar baki, barci fiye da ƙima,
zaucewa, rikicewa da sauran su.
Ka
ga kenan, dawwama ana yi masa wannan allura kamar nakasa shi kuke yi, wataƙila ba da sanin ku ba. Don haka ina ba
da shawara ku yi magana da likitan domin samun mafita, ko dai a canza masa
magani ko kuma a fara rage yawan ba shi magani da allurar."
Kalamansa
sun firgita ni matuƙa da
gaske, har ma na ji a raina ya kamata na daina. Sai dai tun ba a je ko ina ba
na fahimci cewa tuban nawa irin tuban muzuru ne, yana riƙe da kaza a baki yana cewa ya tuba.
Domin kuwa ko a daren ranar kasa barci na yi sai da na ji ni ɗif!
Na yi madiri.
Tun
daga sannan kuma sai na fara tunanin daina shan wannan magani da allurar, sai
na fara tunanin na nemi wata mafitar daban, wato dai kamar na ƙi cin biri kenan na sha romo. Sila kenan
da na fara shan tabar wiwi da sholisho. Wani lokacin ma har kwata da take da
matuƙar ɗoyi
nake zubawa a kwalba na yi ta shaƙa da
hanci.
A
haka na yi ta rayuwa cikin gararamba, har zuwa lokacin da rana a tsaka na ga na
fara yin wani irin fitsari mai ɗauke da wani abu kamar
kumfa, jikina musamman hannaye da ƙafafuwa
duk suka ɗan fara kumbura kamar fulawar da aka
saka wa yis. Da farko kamar da wasa abin ya fara, ganin yana neman ta'azzara ne
na yanke shawarar zuwa kemis ɗin mutumina.
Na
yi sa'a kuwa shi na tarar, don haka ne bayan mun gaisa na fara faɗa
masa damuwata. Ya yi mini tambayoyi da dama, amma tambaya ta ƙarshe da ya yi mini ita ce 'ko ina yin
shaye-shaye.' To a nan ne na yanke shawarar faɗa
masa gaskiya, na ce.
"Don
Allah ka yi haƙuri, kwanaki na yi
maka ƙarya. Gaskiya wannan takardar maganin
ina samun ta ne ta ɓarauniyar hanya. Kuma ni ne
nake amfani da duka abubuwan da nake zuwa saya, ina yin amfani da su ba ta
hanyar da ta dace ba."
"Kana
nufin maganin da allurar duka kake amfani da su lokaci guda?" Yanayin
yadda ya mini tambayar ya nuna mini akwai matsala, don haka ne ko iya amsa masa
ban yi ba sai dai gyaɗa kai da na yi kamar ƙadangare.
Ya
ce, "Bayan su babu abin da kake sha?" Jin haka na faɗa
masa duka abin da nake sha.
"Ai kuwa ina mai baƙin cikin sanar da kai cewa amfani da su
da kake yi ba bisa ƙa'ida
ba ya jawo wataƙil ƙodarka ta taɓu.
Abin da na guje maka kenan kamar yadda na faɗa
maka tun watannin baya." Ya ƙarasa
zancen yana kallona.
Cike
da tashin hankali na fara sambatu, "Na yi ta so na daina amfani da su tun
lokacin da ka ba ni shawara wallahi amma na kasa. Kuma da ni ina ganin kamar
illar ba ta kai haka ba..."
"Kaico!
Gaskiya ka yi gajeren tunani. Shi ya sa na ce ka je ka nemi shawarar likitanka,
saboda barin shaye-shaye ga wanda ya zame masa jiki ba abu ne mai sauƙi ba, dole akwai matakan da ake bi.
Akwai
abin da ake kira da (withdrawal syndrome). Shi ne yanayin da mai shan wasu
rukuni na magunguna yake shiga idan aka ce ya bar shan su lokaci guda. Kowa da
irin tasa matsalar da take biyo baya, wasu suna shiga tashin hankali, wasu
sambatu, wasu gumi, wasu zazzaɓi, kaɗawar
ido zuwa ja, da sauransu." Ya ɗan
yi shiru, ya shaƙi
numfashi ya ɗora.
"Dangane
da illar magunguna kuwa, shan su ba bisa ƙa'ida
ba na tsawon lokaci yana haifar da illoli da dama amma muhimmai a cikin su
akwai:"
Ya fara ƙirge
da yatsa na farko,
"•Matsalar
numfashi: Ƙwayar da mutane ke
sha ta hanyar haɗiya ko shaƙa da hanci. Ko kuma hayaƙi irin na taba sigari da tabar Ibilis,
suna haifar da matsala a sassan jiki da ke da alhakin samar da numfashi. Hakan
na jawo mutum ya kasa numfashi sai da abin numfasawa (oxygen tank)"
Ya
sake taɓa
yatsa na biyu,
"•Ciwon
ƙoda: Magunguna masu ɗauke
da sinadaran, (heroin, ketamine, da synthetic cannabinoids) suna toshe matatar ƙoda su haifar da lalacewarta ko gazawa
wajen aiki."
Ya
taɓa
yatsa na uku,
"•Cushewar
Mafitsara: Saboda aikin rukunin magani na (Opiod) a tantanin da ke rufe
mafitsara wato (Urinary sphincter), alamar hakan shi ne jin tsananin zafi a
lokacin fitsari.
•Cushewar
Ciki: Wannan ma yana samuwa ne sakamakon aikin waɗannan
magunguna a tantanin da ke kulle ƙofar
tumbi, sai ya rage motsin tantanin (gastric sphincter tone) da ma na ciki gaba ɗaya.
•Ciwon
Hanta: Yawan shan ƙwaya
ko giya yana lalata hanta.
•Kashe
ƙwayoyin haihuwa (infertility)
•Tsananin
raguwar gudun jini (hypotension).
•Hawan
jini: Wasu daga cikin waɗannan magunguna kamar barasa
(Alcohol) na saka jini ya hau.
•Yawan
yin ɓari
ga mace mai ciki, da haihuwar yaron dake da illa a yanayin halittarsa."
Tun
da ya fara bayanin nake kwarara gumi kamar wanda ake yi wa surace, sai a lokacin na fahimci irin girman
hatsarin da na jefa kaina. A ƙarshe
ma ban san lokacin da na fara kuka ba, gani nake yi kawai kamar mutuwa zan yi.
Ganin
yadda na tashi hankalina ne ya shiga yi wa zuciyata tausa, "Ka kwantar da
hankalinka, sannan ka gode wa Allah da ya sa ka farga da wuri. Kamar yadda na
faɗa
maka akwai alamun cutar ƙoda
a tare da kai, don haka kana buƙatar
daina shan duk wani kayan maye da kake sha cikin gaggawa. Hakan kuma ba za ta
yiwu da sauƙi ba dole sai dai ka
kai kanka gidan gyaran hali (rehabilitation center).Domin a can ne za su ba ka
dukkan wata gudumawa, kama daga kan shawarwari, magunguna, da kuma dabarun da
za su raba ka da wannan ɗabi'ar a sauƙaƙe."
Na
tsaya na ja numfashi daga basu labarin da nake, na mayar da kallona ga Dattijon
mutumin da yake kallona kamar majigin da ake haskawa, haka shima matashin
saurayin ko ƙwaƙƙwaran motsi ya gagara yi,
kai na girgiza kana na ci gaba.
"Na
yaba da tsarin gidan gyaran hali sosai, tabbas sunan nasa ya dace da shi,
musamman bisa tasirinsa na sauya mummunar ɗabi'a
zuwa kyakkyawa.
Irin
yadda ake wankin babban bargo, haka suke wanke zukatan masu shaye-shaye ta
hanyar ba su magungunan da suke maye gurbin waccan mai illar, wanda illar su
bata kai ga waccan ba. Misali, amfani da cingam mai ɗauke
da sinadarin (nicotine) a madadin shan taba sigari tare da rage adadin da ake
amfani dasu a hankali har mutum ya saba.
Haka
nan suna ba da magungunan da suke toshe aikin waɗancan
magungunan da aka riga da aka dogara akan su. Misali, amfani da sinadarin
(naltrexone) domin toshe aikin da (opioids) suke yi da kuma amfani da sinadarin
(Flumazenil) domin toshe aikin (benzodiazepines) kamar su (diazepam) kenan.
Bayan
wannan kuma akwai sashe na koyon sana'a, wanda a can ni ma na koyo wannan facin
da nake yi. Ga shi yanzu ni da shaye-shaye sai tarihi, domin dai ko sigari ba
na sha, kuma ina zaune ƙalau
cikin farin ciki.
Na
so matuƙa a ce an kai yayanmu Auwal Damfo wannan
gidan shi ma ko zai daina. Sai dai shi kwata-kwata ba na ganin alamun saduda a
tare da shi. Ina zargin hatta kashe mahaifinmun nan da ya yi yana da nasaba da
sakin mahaifiyarsa da Abban namu ya yi ya auro wata bazawara, wataƙila hakan ne bai yi masa daɗi
ba, ya sha faɗa masa sai ya kashe shi.
Shi
ya sa a kullum na yi salla sai na nemi tsari da shaye-shaye da sharrorinsa.
Sa'annan har na koma ga mahaliccina ba zan manta da 'Yan Sara suka ba, don su
ne silar komai" Na ƙarasa
zancena ina kallon dungulumin hannuna, daidai lokacin da na gama haɗa
kayana na rufe shagon domin tafiya jana'izar mahaifinmu. Ina kuma iya jiyo
sautin muryar dattijon na ratsa kunnuwana da cewa
"Ka fahimci kamar mutuwar mahaifin nasu
ba ta wani girgiza shi ba ko? Wataƙila
hakan yana da nasaba da irin tarbiyyar da mahaifin nasu ya yi musu, ya watsar
da su bai ja su a jiki ba ballantana ya nuna musu so har suka afka shaye-shaye.
Lallai
wannan kukan kurciya ne ga mai hankali. Tabbas Abba ba zai taɓa
mantawa da 'yan sara suka ba, saboda sun yi masa tabo mai wahalar goguwa."
Alhamdulillah!
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.