𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalam alaikum malam barka da warhaka Malam ni budurwa ce amma ina da yawan sha'awa har ya kai sai na matse ƙafafuwana nake jin daɗi. kuma inyita tunani game da yadda ake saduwa ko kuma yadda zanji in da ni ake yi, haka dai naketa aiyana abubuwa a cikin raina. kuma gashi sai nan da shekara guda ne aurena. to malam dan Allah akwai wata hanyar da zan
bi in rage jin sha'awar ba tareda na cutar da lafiyata ba? kuma shekarata sha bakwai.Na gode Allah shi ƙara ilimi ina jiran
amsa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa alaikumus salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Ita sha'awa wata
siffa ce wacce Allah mahalicci ya sanyata a jikin Ɗan Adam har dabbobi.
Kuma kamar yadda Ɗan Adam a mafiya yawan lokuta ba ya iya hana jikinsa jin
yunwa ko kishirwa, to haka itama sha'awa take gine a cikin halittar jikinsa.
Allahn da ya sanya
wannan siffar a jikin Ɗan Adam, kuma ya sanyata ne amatsayin jarrabawa gareshi.
Idan ya tsoraci Allah ya tsare idanunsa da hannayensa da sauran gabobin jikinsa
daga bin haramtattun hanyoyin Ƙosar da wannan sha'awar to shi ke nan
ya ci jarrabawar.
Amma idan Ɗan Adam ya kasa tsare
idanuwansa na fili, da idanuwan zuciyarsa daga kallon abin da zai motsa
sha'awar, har ya kaiga bayar da jikinsa domin Ƙosar da wannan
sha'awar, to hakika ya kama mummunar hanyar da za ta kaishi ga hallaka. (Allah
shi kiyayemu baki da6ya).
Allah Maɗaukakin Sarki ya gaya
wa Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam) cewa:
وَقُلْ
لِلْمُؤْمِنَاتِ يَغْضُضْنَ مِنْ أَبْصَارِهِنَّ وَيَحْفَظْنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا
يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنْهَا ۖ وَلْيَضْرِبْنَ بِخُمُرِهِنَّ
عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّ ۖ وَلَا يُبْدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوْ
آبَائِهِنَّ...
"KUMA KA GAYA WA
MUMINAI MATA SU RUNTSE IDANUWANSU (DAGA KALLO KO TUNANIN DA ZAI MOTSA MUSU
SHA'AWA) KUMA SU KIYAYE FARJOJINSU (DAGA ZINA DA MADIGO DA SAURANSU) YIN HAKA
(WATO KIYAYEWAR) KUMA KADA SU BAYYANAR DA ADONSU SAI GA MAZAJENSU KO UBANNINSU...."
[suratul Al-Nur aya 31]
Sannan Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya faɗi wata muhimmiyar shawara ga marassa aure
daga cikin al'ummarsa. Yace: "Yaku taron samari!! Wanda keda ikon rike
iyali, to yaje ya yi aure. Domin hakika (yin haka) shi zaifi rintsewa ga
idanuwa da kuma kiyayewa ga al'aura. Wanda kuma bashi da iko, to na umurceshi
da yin azumi, domin hakika shi (azumi) mai yanke sha'awa ne. (wato yana kulle
kofofin sha'awar). (Jama'ar maruwaitan hadisi ne suka riwaitoshi).
Don haka nake baki
shawarar cewa kiji tsoron Allah, ki kiyaye mutuncinki, kada ki bar wani saurayi
ya taɓa sassan jikinki
(koda wanda za ki aura ɗin ne) kar ki bashi
wannan damar ya lalata rayuwarki.
Kiji tsoron Allah ki
kiyaye idanuwanki daga kallon hotuna ko finafinan batsa, ko yin chatting na
batsa, ko karanta labarai na batsa, ko yin Ƙawance da miyagun Ƙawaye masu Ƙazaman dabi'u. Ki
tuna cewar Allah yana tare da ke ko yaushe kuma yana ganin dukkan abin da kike
tunani har wanda kike aikatawa, kuma akwai ranar da zai miki hisabi.
Sannan ki yawaita
azumin nafila, da karatun Alƙur'ani da yawan tunanin mutuwa,
kwanciyar Ƙabari, duhun Ƙabari, da kuma
hisabi. In sha Allahu wannan shi ne babban magani.
Daga cikin magungunan
Musulunci waɗanda ake amfani da su
wajen dakile sha'awa akwai:
1. SHAJARATU MARYAM:
Bishiya ce wacce ake amfani da ita don magance matsalolin Mata. Kuma Idan
namiji yasha, tana cire masa sha'awa sosai daga jikinsa da zuciyarsa.
2. Ki Yawaita shan
Lemon tsami (Idan baki da Olsa). Ko kuma Jar kanwa ('Yar Ƙalilan).
3. Ki samo kuzbara
busassa wanda akayi garinta kwatankwacin karamin cokali sai azuba aruwan mai
sanyi da yamma har zuwa asuba sai asanya sukari asha, In shã Allah yana saukaka
tsananin sha'awa ga namiji ko mace.
4. Ki samo wani haki da
ake cemasa ARRAJLA sai arika tafasawa anashan sa shi ma yana saukaka tsananin
sha'awa ga maza ko mata, za ki iya samun sa amma sai dai a Kano.
5. Ki samo Zait
Kafuur sai ki rika diga ɗan kaɗan a cikin kofin
shayi, idan ana shan wannan yana kashe tsananin wutar sha'awa.
6. Ki samo yansun da
kako sai ki rika tafasawa kina sha, shi ma yana saukaka tsananin sha'awa.
7. Ki samo kwayoyin
salak Irin wanda masu lambu suke shukawa ya fito sannan su dasa shi yagirma
yazama salak, to wannan kwayoyin da ake yafawa su za ki samo sai ki rika
tafasawa kinasha, wannan hanya yana yanke tsananin sha'awa gaba ɗaya.
Ubangiji Allah yabamu
dacewa, masu yawan yimana tambaya akan yadda za su rage tsananin sha'awa ga
hanya. Lallai ga wanda yake da tsananin sha'awa ko bashida da mata. ko ba ta da
miji, kuma babu halin yin Aure to amaimakon yin Istiminai (musterbution) to
kwara bin ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin domin
asami sauki!!! Allah ta'ala yasa mudace.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.