Ticker

6/recent/ticker-posts

Sallar Mara Lafiya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam dan Allah a taimaka a yi min karin bayani yadda zan dinga sallah a zaune saboda ina fama da ciwo a kafana. Sannan kuma ina baran addu'a daga gareka da sauran 'yan uwa Musulmai Allah ya yayemin lalurar da nake fama da ita. Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Game da sallar mara lafiya a zaune ya tabbata cikin hadisi Imrana dan Hussain (R.A) ya ce cutar basir ta kasance agareni, sai na tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam sai ya ce kayi sallah a tsaye, kuma idan baka samu iko ba, to kayi a zaune, kuma dai idan baka samu iko ba toh kayi a gefan jikinka (addini dan sauki ke nan).

Haka dai shi Imrana R.A ya kara cewa na tambayi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam game da sallar mutum Alhali yana zaune, sai yace: Wanda ya yi sallah a tsaye toh shi ya fi falala, kuma wanda ya yi sallah a zaune toh yana da rabin ladan wanda ya yi ta a tsaye, kuma dai wanda ya yi a kwance (awata ruwayar a kishingide) toh yana da rabin ladan wanda ya yi ta a zaune (Abin nufi da shi wannan

hadisin) mara lafiya, saboda hadisin Anas R.A: ya ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya fito wata rana ya tarar da wasu mutane alhali su suna sallah a zaune saboda rashin lafiya, sai yace: lalle sallar na zaune tana a bisa rabin sallar na tsaye.

Dole ne akan maras lafiya ya yi sallah daidai iyawarsa, idan zai iya yin ta kamar yadda mai lafiya zai iya to ya zama wajibi a kansa ya yi, in kuwa ba zai iya ba, to sai ya yi yadda zai iya.

Wajibi ne akan maras lafiya ya yi sallah a tsaye in zai iya tsayuwa, idan ba zai iya tsayawa ba, to ya yi sallah a zaune, idan ba zai iya zama ba, to ya yi sallah a kwance akan gefensa, fuskarsa tana fuskantar alƙibla, idan ba zai iya kwance akan gefe ba, to ya yi a rigingine, ƙafafunsa suna fuskantar alƙibla in zai iya, in kuwa ba zai iya ba, to ya yi a gwargwadon halinsa.

Dalili kuwa shi ne abin ya gabata na faɗin Allah:

فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ

 “Ku ji tsoron Allah iya iyawarku” (Attagabun: 16).

WASU DAGA HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR MARAS LAFIYA:

1. Idan maras lafiya yana Sallah a zaune, amma zai iya yin sujjada, to sujjada ta wajaba a kansa.

2. Idan kuwa yana sallah a zaune, amma ya kasa yin sujjada, to ya yi nuni da jikinsa a ruku’u da sujjada, sujjadarsa tafi ruku’unsa ƙasa-ƙasa, idan nuni da jikinsa zai masa wahala, to sai ya yi da kansa, haka ma zai yi idan ya yi Sallah a rigingine, zai yi nuni da kansa.

3. Idan yin alwala a kowace sallah zai yi wa maras lafiya wahala, ko kuma yin salloli a kan lokacinsu zai masa wahala, to yana iya haɗa sallar azzahar da la’asar, magariba da isha, a lokacin ɗaya daga cikinsu, ko dai a lokacin ta farkon ko ta biyun, gwargwadon yadda ya fi masa sauƙi.

4. Sallah ba ta saraya daga kan maras lafiya matuƙar yana cikin hankalinsa, saboda haka bai dace ga maras lafiya ya yi sakaci da sallah ba, don da’awar bashi da lafiya, don haka ya yi iyakar ƙoƙarinsa wajen yin sallah.

5. Idan maras lafiya yana suma tsawon wasu kwanaki sannan ya farfaɗo, to zai yi sallah ne a lokacin da ya farfaɗo gwargwadon yadda zai iya, kuma ba zai rama sallolin da suka wuce shi ba a lokacin sumansa, amma idan suman kaɗan ne, na yini ɗaya ne ko kwana biyu, to wajibi ne a kansa ya rama sallolin da suka wuce shi, a duk lokacin da hakan ya sauwaƙa a gare shi.

Wallahi yan'uwa mugodewa Allah swt kuma mu yi amfani da lafiyar da Allah yabamu mu bauta masa yadda ya kamata..Allah kabamu ikon bauta maka yadda kakeso. kuma dan ALLAH aringa share domin wasu su amfana.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments