Rahma Kabir (2023). Sakaci. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD
SAKACI
Na
Rahma Kabir
Tsaye nake ina kallon saman rufin ɗakinmu, na shiga
tunanin yadda muka kwana cikin saukar ruwan sama kasantuwar yanayi ne na
marka-marka, har zuwa gabanin sallar asubahi kafin ya tsagaita. Ruwan da ya ƙare akanmu saboda ɗakin da muke ciki kwanon ya buɓɓule, a
tsugune muka kwana wasu kuma a tsaye, a haka muka kasance har garin Allah ya
waye tangaras, sanyi ya gama ratsa duk illahirin sassan jikinmu, in da sabo mun
riga mun saba da wannan rayuwa mai cike da ruɗani, haka muka fito
daga cikin ɗakin tsamo-tsamo kowa ya kama gabansa babu wanda ya yi
yunƙurin yin sallar asubahi ko neman sauya tufafi.
Zama
na yi a kan dakalin da ke gefen ɗakinmu,
na yi tagumi hannu bibiyu. Tun ina ɗan
shekara bakwai ban san ya duniya take, ba ban san ina na dosa ba, amma da garin
Allah ya waye kullum
tunanina ta wace hanya zan samu abin karin kumallo? Anya iyayena suna ƙaunata kuwa? Tambayar da kullum nake wa kaina amma ba ni da amsa har kawo
yanzu da shekaruna ashirin da biyu a duniya.
Wasu
siraran hawaye ne su ka
sauka a kuncina, na sanya hannu na goge, na soma tunanin ta wace hanya zan samu
abin da zan sanya a bakin salati? Saboda a irin wannan lokaci ba lallai na samu
abin kalaci a gidajen mutane ba, musamman da unguwar ta kasance ta talakawa su
ma rayuwar suke hannu-baka-hannu-kwarya. Ɓangaren
unguwannin masu hannu da shuni kuwa, a irin wannan lokaci ba kasafai suke tashi
barci da wuri ba, musamman yau da ya kasance ranar hutun ƙarshen mako.
Na
fesar da iskar da ke bakina na ce a fili, “Ni Ashiru yaushe zan zama cikakken ɗa
mai ‘yanci kamar yadda sauran ‘ya’ya suke zaune a gaban Iyayensu? Iyayena suna
raye amma na zama tamkar maraya wulaƙantacce
a idon duniya, ni ke kula da tarbiyyata da abincina, ina gararamba a wata
duniyar da babu dangin iya ba na Baba, babu mai kula da lafiyata, na ci ko na
sha babu mai tambaya ta. Har zuwa yaushe Iyayena za su fahimci halin da na ke
ciki?”
Na ƙare maganar da tambayar da ba ni da
amsa. Shi kansa Malam Tanimu, mun yi masa yawa ba zai iya kulawa da tarbiyyarmu
gabaɗaya
ba, Iyayenmu sun kawo mu karatu sun yasar wa duniya ta raine mu, babu wani
tallafi da suke yi wa malam wajen ganin ba mu yi kukan yunwa ba. Na sauke
gauron numfashi, na miƙe
tsaye domin zama bai gan ni ba da hutun jaki da kaya! Na wuce don sama wa kaina
mafita. Na yi nisa a tafiya ban san ina na dosa ba, a haka har na isa wata
unguwa ta gungun talakawa, na hangi yara a bakin wani kwazazzabon rafi, da
sauri na isa gurin sai na taras da wasu matasa suna shan kayan maye, har na
juya wani daga cikinsu ya tsayar da ni da cewa, “Kai zo nan!”
Jikina yana rawa na isa gabansa domin a gaskiya ina matuƙar tsoron ‘yan shaye-shaye, sai ya ciro kuɗi naira ɗari biyu ya ba ni
ya ce na sayo masa waina ta ɗari da hamsin a sanya masa a leda, ba musu na amsa na
tafi da sauri. Ban jima ba na dawo na kawo masa.
Sai
ya ce, “Kai almajiri ne ko?”
“E.”
Na faɗa cikin sauri.
“Ai
daga ganin ka an ga yaron malam, je ka sayo mini ruwa ka dawo.”
Na tafi na je na dawo, a lokacin ya ci wainar ya rage
mini guda biyu, ya ba ni na amsa jiki na rawa na tsuguna daga gefensu na soma
ci, bayan na gama na miƙe ina masa godiya, har zan wuce,
wani daga cikinsu ya kuma kira na ya aike ni. A takaice dai haka
suka dinga aike na ina zuwa sayo musu abinci su ci su rage mini, da haka na ƙoshi. Sai wani daga cikinsu ya miƙo mini sauran zoɓo a
gora na amsa ina godiya, na koma gefe na zauna dirshan a ƙasa na soma sha, kurɓa ɗaya
kawai na yi sai na ji wani abu mai yaji-yaji a maƙoshina,
na ɗaga
gorar na ƙara dubawa na
tabbatar da zoɓo ne, haka na ci gaba da sha ina jin maƙaƙi a
maƙogwarona sannan ɗanɗanonsa
ya koma tamkar maganin tari na ruwa, a haka na kammala sha, ko cikakken minti
biyar ban yi ba na ɓingire a gurin na kwanta,
nan take na ji shewarsu suna dariya wacce na tabbatar da ni suke, ban gama
sanin halin da nake ciki ba barci mai nauyi ya yi gaba da ni.
Ban farka ba sai gabanin sallar isha’i, hayaƙin tabar wiwi ne ya sa na sarƙe ina tari, wani daga cikin ‘yan shaye-shayen ya ba ni
ruwan leda yana ce mini, “Lallai ɗan malam jininka yana da ƙarfi, saboda duk wanda ya fara shan wannan ƙwayar sai ya kwana ya yini yana bacci kafin ta sake shi,
da alama kai gwarzo ne.”
Yana gama faɗar haka sai ya koma ya zauna ya ci gaba da shan kayan
mayensa, na bi su da kallo kana na dawo da kallo na kan ruwan da ya ba ni, sai
na shiga kokwanto kar a ce wani abin mayen ya kuma ba ni, sai kawai na miƙe ban ce musu komai ba, na ajiye ruwan a gurin na fara
tafiya ina jin jiri, ga wani irin ciwon kai da yake damu na da yunwa, har na
fice daga wajen babu wadda ya tsayar da ni daga cikinsu. Sai da na yi nisa da
tafiya na shiga tunanin yadda zan isa makaranta a wannan yanayin, tsoro da
tashin hankali ya cika ni saboda irin hukuncin da malam zai yanke mini akan
daren da na yi.
Da fargaba na isa makaranta na shiga ɗakinmu na kwanta
saboda har lokacin abin da na sha bai gama saki na ba, ba jimawa sai ga Ado ya
shigo wanda yake a matsayin shugaban ɗalibai mai horar da duk mai laifi. Har
an samu wanda ya kai masa labarin na dawo, da yake
ni fitaccen ɗalibi ne, shi yasa duk ranar da na yi
nisan kiwo ake ganewa. Ganin Ado a kaina ya sa na ji fitsari ya kama ni saboda
na san shi mutum ne da ba shi da tausayi. Cikin rawar jiki na miƙe tare da sunne kaina a ƙasa don ko haɗa
ido ba na so mu yi, ya daka mini wata tsawa wacce ta ƙara hautsina ni, yana cewa, “Ashiru yau
tun safe ina ka je ana ta neman ka?”
“Na
tafi bara ne a kasuwa.”
Na
tsinci kaina da yin ƙarya
saboda ba zan iya faɗa masa gaskiyar in da na je
ba, sai dai kuma muryata ta nuna ina cikin maye.
Cikin zafin nama Ado ya kama wuyan rigata ya ja ni waje
har zuwa cikin gidan malam ya gurfanar da ni a gabansa, ya ce, “Malam ga Ashiru
nan sai yanzu yake dawowa, kuma alamu sun nuna ya sha wani abu da ya sa shi
maye saboda muryarsa ta sauya.”
Cikin
ɓacin
rai malam ya ta so ya tsaya a gabana ya ce, “Haba Ashiru! Wace irin rayuwa kake
son jefa kanka a ciki? Ina iyakacin ƙoƙarina a kanku amma kana son watsa mini ƙasa a ido! Yanzu ina ka je ka yi dare?
Sannan wane abu ka sha ya saka maye?”
Jikina ne ya ɗauki rawa na kasa cewa komai, Ado ya kifa mini mari a
kuncina wanda sai da na ga walƙiya, ban gama
dawowa hayyacina ba ya dunƙule hannu ya sakar
mini ƙozo a kai, a zabure na dafe kaina na saki gigitaccen kuka
saboda raɗaɗin azabar da ya ratsa kwakwalwata.
“Wa
za ka yiwa kuka? To wallahi kafin ka ɗauko
mini magana zan yi maganinka ta yadda ba za ka sake yin tunanin zama shaiɗani
ba. Kai Ado ka je da shi ka ba shi gwale-gwale har sai ya bambance tsakanin aya
da tsakuwa.”
Malam ya faɗa a hasale sannan ya koma ya zauna, Ado ya tisa ƙeyata zuwa wani ɗaki da ke cikin gidan, ya ɗaure mini ƙafa da hannu ya ɗauko bulalar baƙar roba ya shiga duka na sai kwarma ihu nake yi da neman ɗauki, amma babu mai
ceto na, sai da ya yi mini lilis kafin ya bar ni a kwance ina fitar da numfashi
da ƙyar, a haka barcin wahala ya ɗauke ni.
Da gari ya waye, Ado ya shigo ɗakin ya kwara mini
ruwa mai sanyi a jikina, na tashi a firgice ina sauke ajiyar zuciya, sai ya
kwance ni ya tsaya a kaina yana ƙare mini kallo, ni
kuma na sunne kai ƙasa tare da tattaro natsuwata ina
sauraren abin da zai ce mini.
“Ashiru ka gyara halinka domin hanyar da ka dauko ba mai ɓullewa ba ce, zan
yi maka afuwa amma ka sani in ka ƙara ba zan raga
maka ba, don haka yanzu ka tashi ka ɗauki jarka ka fara ɗebo ruwa.”
Da
sauri na amsa da to, ina yi masa godiya, ya fita ni kuma na miƙe da kyar na fito. Na isa in da jarkar
take na ɗauka
tare da ficewa daga gidan ina jan ƙafa.
Na yi nisa kaɗan da gidan sai na samu dakali na zauna
tare da jingina bayana a bango, na saki hamma ina shafa cikina da nake jin yana
mini zafi kamar ana hura wuta, har na mance yaushe rabon da na yi salla, duk da
na yi saukar Al-qur’ani amma ban san sauran abin da ya shafi ibada ba da
hukunce-hukuncen da suka wajaba a kaina na shari’a, hatta wankan tsarki sai da
na shekara sha tara kafin na koya a wajen wani yaro da muka yi aikin wankin
mota, wanda daga bisani na sa shiririta na daina zuwa. Na kalli jarkar da zan ɗebo
ruwa, na tabbatar ba zan iya ɗaukar ta ba saboda babu ƙarfi a jikina, amma tunowa da gargaɗin
Ado ya sa na ji tsoro, sai na ja guntun tsaki na miƙe da nufin na fara neman abin da zan ci
kafin na ɗebo ruwan, sai na wuce dandalin tuƙa-tuƙar
ruwan na sanya jarkar a layi sannan na wuce zuwa bakin hanya ko zan samu
abinci.
Ina isa na hango rumfar wani mai shayi, da sauri na ƙarasa wajen na tsaya daga gefe ina kallon yadda yake
hada-hadar kunna wutar tukunyar shayin, sai da na tabbatar da hankalinsa ba ya
kusa kafin na zura hannu wajen da ya jera burodi na suri guda ɗaya sannan na ruga
a guje. Ya juyo da sauri ya bi ni da gudu yana kiran ɓarawo, nan da nan
hankalin mutane ya dawo kanmu suka soma bi na, ni kuma na ci gaba da gudu iya ƙarfina, da kyar na sha ba su samu sa’ar kama ni ba, sai
dai abin da ya ba ni tsoro, a cikin masu bi na akwai waɗanda suka gane ni
har suka ambaci sunana.
Wannan ya sa na shiga damuwa sosai saboda in maganar ta
je wajen malam ban san hukuncin da zai ɗauka ba, hakan ya sa na wuce wajen
wannan mashayar na samu babu kowa, sai kawai na samu guri na zauna na buɗe burodin na soma
ci ina haɗiya da kyar ko ruwa babu, sai da na ci rabi kafin na
tsagaita na soma hangen inda zan samu ruwa na sha, sai dai babu alamar ruwa a
gurin sai wata gora da na gani a gefen inda na zauna wacce ta yi kama da bayar
lemu ne a ciki, da sauri na isa wajen na ɗauka na kafa kai sai da na shanye
tas na jefar da gora.
Na zauna ina jin kai na yana wani hajijiya da alama an haɗa lemun da abin
maye, haka na zube a ƙasa ina surutai masara tushe da kan
gado, wanda gaba ɗaya na fice daga hayyacina. Ina cikin wannan halin sai ga
tawagar ‘yan shaye-shayen sun zo wajen, suka zauna, wani daga ciki ya hangi
wannan gorar da na shanye abin da ke ciki, ya soma dariya yana cewa, “Kai kun
ga sauran lemun jiya yaron nan ya shanye shi, da alama ya ji daɗin wanda ya sha
jiya.”
Sai
suka sanya dariya suka shiga yin zancen. Ina cikin wannan yanayi har wajen ƙarfe biyun rana kafin mayen ya soma
sakina, a lokacin na tuna da aiken ɗebo
ruwa da Ado ya sa ni, sai na miƙe da
sauri amma kuma satar da na yi ɗazun ta faɗo
mini a rai sai jikina ya yi sanyi tare da tsoron irin hukuncin da zan tarar,
domin zuwa yanzu na san labari ya isa ga malam, don haka sai na koma na zauna
ina tunanin mafita. Sai wani daga cikin ‘yan shaye-shayen ya ce min, “Ɗan malam muna yi maka barka da zuwa
tawagarmu, domin ka ɗauƙi hannu sosai yadda ya kamata, ga wannan
ka gwada sha za ka ji kanka ya washe ba ruwanka da sauran damuwa.”
“Yunwa nake ji!” Na ba shi amsa a taƙaice, sai ya ce, “Ga shi mun cinye maka sauran burodinka,
Amma bari na sa a sayo maka alale ka ci, sai ka ɗaura da wannan
wiwin za ka jika ka yi garau.”
Na gyaɗa masa kai domin ko magana ba na son yi, ya aika aka sayo
mini alale na ci na ƙoshi sannan na kora da ruwa, daga
bisani ogansu ya ba ni wiwi ya koya mini yadda zan sha, cikin ƙanƙanin lokaci na gane
komai na soma sha a hankali, tun ina jin abin babu daɗi ina ƙwarewa har kwakwalwata ta karɓi saƙon.
A cikin ƙanƙanin lokaci rayuwata ta sauya, na watsar da zancen komawa
makaranta saboda ‘yan shaye-shayen sun karɓe ni hannu bibiyu.
Ogansu mai suna Lawalli shi ne yake saya mini abinci ba na zama da yunwa kuma a
gidansu wata rana na ke kwana, sannan a duk lokacin da na sha abin maye yana
gusar mini da hankalina ya mantar da ni duk wata damuwar da nake ciki, a
hankali na goge da shan miyagun ƙwayoyin maye tare
da koyon halayyarsu ta zaman banza, sata, kwacen wayar hannu da kwana a kango,
na bar sumar kai na ta taru sosai sai dai in taje, sutura kuwa sai wacce na zaɓa nake sawa, ina
rayuwar ‘yanci babu mai takurani.
BAYAN WATA BAKWAI
A tsawon wannan lokacin da na kwashe ba na makaranta, ban
san ko iyayena sun zo gani na ba, saboda tun da na bar gidan malam babu wanda
ya taɓa zuwa nema na, kuma duk da a yanzu wasu daga cikin
almajiran makarantarmu sun sha haɗuwa da ni kuma na tabbatar labari isa ga malam. Na
cire damuwar iyayena a raina kamar yadda nake tsammanin su ma sun cire ni a
cikin rayuwarsu.
Wani taro ne ya taso na babbar ƙungiyar ‘yan shaye-shaye, ta shirya gasar shan kwayar
tiramol da hodar iblis da kuma maganin tari na ruwa duk a lokaci guda, akan duk
wanda ya tsallake zai samu kyautar babur da kuɗi masu tsoka, taron
zai gudana a wata babbar matsaya nan da kwana uku. Oganmu ya zaɓe ni a matsayin ni
ne zan shiga gasar na wakilci tawagarmu, saboda ya sha gwada ni da manyan kayan
maye ina tsallake wa saboda jinina yana da ƙarfi.
A ranar taron da wuri muka isa wajen, mun haɗu da manyan ‘yan
shaye-shaye har rukuni bakwai, kowace tawaga suka fito da wanda zai wakilce su,
ba ɓata lokaci aka ba mu ƙwayar da sauran haɗin kayan mayen, muka soma sha ana yi
mana kuwwa wanda ya sa kanmu ya ƙara caji. Bayan
minti goma mun gama shan komai, ɗaya daga cikinmu ya faɗi ƙasa ya soma shure-shure kumfa ta soma fita daga bakinsa,
nan take rai ya yi halinsa.
Wajen ya kaure da ihu wasu na murna wasu kuma na jimami,
da ma mun san gasa ce mai hatsari ko a mutu ko a yi rai ne, ganin haka ya sa
cikina ya ɗuru ruwa na shiga tashin hankali, aka ɗauki gawar aka
ajiye a gefe, bayan minti biyu wani shi ma ya faɗi nan take ya mutu
kamar yadda wancan ya yi, wani kuma ya zube a ƙasa yana murƙususu sai buga
kansa yake da hannu. A takaice dai a cikinmu bakwai huɗu
sun mutu har lahira, a lokacin ne na sare na shiga nadama tare da da na sanin
sakacin da na yi wa rayuwata na bin son zuciyata. Cikin ƙanƙanen
lokaci mu ukun da muka rage sai duk muka zube a ƙasa,
na soma jin kaina yana wani irin mugun juya mini wanda a daidai lokacin ne hukumar
yaƙi da fataucin muyagun ƙwayoyi
ta NDLEA (National Drug Law Enforcement Agency) suka farma taron, ashe sun samu
labarin yin gasar shi yasa suka zo kame, kowa ya yi ta kansa suka kama wasu
saura kuma suka gudu, ni dai ban san ya lamarin ya ƙare ba saboda gabaɗaya ƙwakwalwata
ta ɗauke
ɗif
na rasa hankalina.
Ban kuma sanin duniyar da nake ciki ba sai da na farka na
gan ni kan gadon asibiti, an ɗaura mini ruwa yana shiga ta jijiyata ga hannuna lulluɓe da bandeji, ashe
wutar lantarki na kama wacce ta sa na samu rauni a hannu, kuma shi ne ya yi
sanadin dana ƙara dawowa hayyacina. Domin na shafe
tsawon wata uku ina jinya a asibitin mahaukata, saboda tun ranar gasar nan na
samu matsala a kwakwalwata, har na soma samun sauƙi sai kuma ga shi tsautsayi ya sa na kama igiyar wutar
lantarki har hakan ya zama silar dawowar hankalina. Bayanin
da na ji likita yana koro wa waɗanda ke gurin, bayan ya gama
ya yi rubuce-rubucensa kana ya fice.
Na juyo da fuskata ina kallon mutanen da ke kaina, na ga
Malam tare da Mahaifina sai Ado, duk suna tsaye sun yi jungum-jungum, na ji
hawaye yana sauka a kuncina saboda tsantsar nadama, mahaifina ya matso jikin
gadon yana cewa, “Sannu Ashiru ya jikin?”
Na kau da kaina gefe ina nishin kuka, kwatakwata ba na
son ganin fuskarsa, sakamakon irin yadda ya kawo ni karatu amma babu wata
kulawa da ya ba ni, sai na ɓarke da kuka mai sauti ina cewa, “Baba da ma za ka zo in
da nake? Ashe zan sake ganin ka? Ka ga yadda rayuwa ta mayar da
ni.”
“Ashiru karatun nan shi ne kaɗai gatan da zan ba
ka, na yi zaton ka yi hankali ka gina kanka ashe wannan ƙazamar rayuwar ka zaɓar wa kanka. Mal.
Tanimu me yasa za ka bar shi yana wannan rayuwar kuma ba ka sanar da ni ba har
sai da abu ya zama haka?”
Cewar
Baba ya ƙare maganar ga malam cike da damuwa.
Malam ya ce, “Ai Malam Hadi lamarin ya sha ƙarfina, da matsalarsa zan ji ko da ta sauran almajirai da
ke gabana, ni tun da ya bar makaranta ban san inda yake ba, ban da Allah Ya sa ɗaya daga cikin
abokan shaye-shayensa ya kawo mini labarin abin da ya same shi to da ba za mu
sani ba.”
“Haka
Allah ya tsara duk da na san akwai sakacina a lalacewarsa, Allah ya shirye shi.”
Cewar Baba cikin sanyin jiki, su Malam suka amsa da amin.
BAYAN MAKO GUDA
Hannuna ya yi sauƙi sosai har an cire
mini bandeji, sai jami’an hukumar yaƙi da muyagun ƙwayoyi suka zo suka amsar mini sallama, suka wuce da ni
can babbar ma’aikatarsu, su Baba ma suka biyo bayanmu. Suka kai ni ofishin
shugabansu tare da gurfanar da ni a gabansa sannan suka yi masa bayanin iyayena
sun zo, sai ya ba su umarni suka shigo da su ciki kana suka wuce. Bayan
sun gaisa a tsakaninsu sai ofisan ya soma yi wa su baba bayani.
“Gaskiya kun yi sakaci da tarbiyyarsa domin matsalar
shaye-shaye abu ne mai wuyar sha’ani, saboda idan mutum ya sa kansa a
shaye-shaye haƙiƙa rayuwarsa tana lalacewa ne gabaɗaya, domin zai iya
taɓa lafiyarsa, ba zai iya sana’a ba ko aiki, sata da kwace,
sara-suka, har hankalinsa zai iya rasawa, ko mutum ya rasa ransa gabaɗaya.”
“Inna
lillahi wa inna ilaihir raji’un! Tabbas a matsayina na mahaifinsa na yi sakaci
sosai wajen kula wa da shi.” Cewar Baba cikin damuwa.
Ofisan
ya cigaba da cewa, “Yana da kyau a duk lokacin da kuka kawo yaranku karatu ku
riƙa ƙoƙarin kawo musu ziyara akai-akai kuna
ganin halin da suke ciki, tare da tallafa wa malami da abinci da kuɗi,
wanda hakan shi ne zai kawo raguwar matsalar da muke ciki a yanzu.”
“Wannan
gaskiya ne, duk da ni ma ina iya ƙoƙarina akan kula da tarbiyyarsu amma ka
san an ce in dambu ya yi yawa ba ya jin mai, sai dai kawai mu bi lamarin da
addu’a.”
Cewar malam, ofisa ya gaskata maganarsa yana girgiza kai
ya ci gaba da cewa, “Hakane, amma dole iyaye da malamai da kuma sarakuna da ƙungiyoyi, ku taya mu faɗakar da matasa akan
yaƙi da ta’ammali da miyagun kwayoyi, saboda mu da gomnati
ba zamu iya magance wannan matsalar ba mu kaɗai dole sai da haɗin guiwarku. Sannan
a yanzu haka mun kai kukanmu wajen gomnati domin ta ƙara buɗe
mana wajen da za a riƙa
kai masu shaye-shayen in mun kama su (Rehabilitation center) a turance, domin a
killace su har sai sun samu cikakkiyar lafiya.
Ashiru ma can za mu kai shi har sai ya samu lafiya
kafin za mu danƙa shi a hannunku, daga nan sai ku yi
kokarin kula da tarbiyyarsa da sanya ido sosai a kansa tare da sa shi ya koyi
sana’a wacce zai riƙe kansa ya bar zaman banza.”
Ya ƙare maganar yana kallon su, suka nuna masa sun amsa kuskurensu kuma za su gyara tare da yi masa godiya. Sai suka ƙara yi mini faɗa da nasiha sosai har sai da na yi kuka, saboda na gane in akwai sakacinsu to ni ma na bi son zuciyata, don haka na nemi yafiyarsu sannan na yi musu alƙawarin In Sha Allah ba zan sake shaye-shaye ba, suka sanya mini albarka kana suka yi sallama da ofisa sai suka tafi, ni kuma aka wuce da ni zuwa wani ɗaki suka rubuta bayanai a kaina sannan suka wuce da ni inda zan ƙarasa jinyata.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.