Ticker

6/recent/ticker-posts

Alhaki Kwkuyo

Rabiatu Sani Katibu Mashi (2023). Alhaki Kwkuyo.... Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD

ALHAKI KWIKUYO...

Na

Rabiatu Sani Katibu Mashi

Ƙi!!!!” Ya tsayar da motar da sauri, matar da take baya ta buɗe ƙofar ta fito tun kafin motar ta ƙarasa tsayawa.

“Malam Adamu fito ka taya ni korar yarannan.”

Ta fara kutsawa cikin dandazon yaran da suke tafe sun zagaye matashin mahaukacin cikin nishaɗi suna tafa hannu suke faɗin,

“Baban bola!Baban Bola!!”

Wasu daga cikinsu har suna ja masa riga. Malam Adamu ne ya kore su da icen da yake hannunsa duk suka watse, dattijuwar ta ja hannun matashin zuwa wani dakali da ya ke kusa da wurin.

Duk da kasancewar lokacin zafi ne, sai da matashin ya takure a wuri ɗaya jikinsa ya na ta kyarma kamar mai jin sanyi, sai zazzaro ido yake.Ta ɗago fuskarta da ta gama cika da ƙwalla cikin tausayi ta ce.

“Allah Ya saka maka Auwal, matarnan ta cucemu, sai da tayi nasarar korar ka daga gidanmu bayan ta haɗa ka da mahaifinku, inshaa Allah duk ƙullin da ta yi kan yayanta zai koma, sai na shiga, na fita, koda abinda na mallaka zai ƙare, sai na tabbatar ta wulaƙanta kamar yadda ta yi maka.

Dai dai lokacin Malam Adamu ya iso wurin riƙe da kwandon da aka jera kayan abinci a cikin, girgiza kai kawai yayi saboda ya ɗan tsinci wani abu daga maganganunta.

Ya rasa dalilin da yasa har yanzu Hajiya ta ƙi yarda da ba wani ne ya yi wa ɗanta asiri ba, ta gane laifinsu na gudummuwar da suka bayar wurin lalata rayuwar yaronsu.

“Ka yi mini tsaye a wurin, ko abincin shi ne zai ajiye kansa?”

Da sauri ya durƙusa ya ajiye bayan ya dawo daga tunanin da ya tafi.

Haɗa lafiyayyen abincin ta shiga yi, da kanta take ba wa Auwal a baki, sai da ta tabbatar ya ƙoshi, sannan ta kira Malam Adamu ya tattara kayan ta miƙe zata tafi.

“Umma!”

Karo na farko kenan da ya yi magana tun zuwansu wurinsa, dakatawa tayi ba tare da ta juya ba, jakarta ta buɗe sai da ta tabbatar ya kwashe kuɗin da ke ciki gabaɗaya sannan ta rufe jakar, ta yi haka ne saboda ikirarin da mahaifinsa ya yi na idan har ta sake bashi kuɗi, a bakin aurenta.

‘Oho dai! Wannan ai ba Ni na ba shi ba, ɗauka ya yi.’Ta faɗa a zuciyarta sannan ta yi gaba.

Sai da ta shiga mota har Malam Adamu ya tayar, sannan ta juya kallon in da yake, har ya tashi ya ci gaba da ‘yan tsince-tsincen shi.

Bayan sun ɗauki hanya, Malam Adamu ya nisa cikin nutsuwa ya fara magana.

“Hajiya ina tausayin yaronnan, ya na matuƙar buƙatar taimako

“Kana tunanin ka fini sani ne? Kana gani ai an hana mahaifinsa ya taimaka masa, nima yana nema ya hanani taimaka masa, sai a ɓoye nake zuwa wurin malamai nema masa taimako.”

“Hajiya amma sai nake ganin kamar matsalar yaronnan bata Malamai ba ce, wurin da aka tanada don masu matsala irin tasa ya kamata a kaishi, a hankali za ki ga yana samun sauƙi har ya warke ya koma kamar da.

“Matsala irin ta shaye-shaye kake nufi wai? To ka sani ni babu inda zan kai ɗana a takura rayuwarsa, bayan nasan abin da ke damunsa. Malamai sun fi bakwai suka faɗa min wannan baƙar matar ce tayi asiri yarona ya fara shaye-shaye, ana gama masa magani na san komai zai bari ya dawo kamar kowa.”

Malam Adamu ya buɗe baki zai yi magana, ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu.

“Wannan matsalar da ta shafi iyalina ce, bana son shisshigi. Ka tsaya a matsayinka, ka ci gaba da aikinka tun kafin kayi silar rasa shi.”

Tuƙin ya ci gaba da yi cikin alhini. Yana ƙara hasko yadda iyayen yaron suka ba da gudummuwa sosai wurin lalata tarbiyyar ɗansu, sannan suka gaza neman hanyar taimaka masa.

* * *

“Alhaji ka tabbata fitar da kayannan babu matsala? Kana ganin yadda jami’an tsaro ke ƙara saka ido ta ko ina a fadin jihar nan.

Ɗayan ɓangaren ne na waya aka furta hakan, wanda aka kira da Alhaji ya ƙyalƙyala dariya sannan yace.

“Shigo da kaya bai zama matsala ba sai fitar da su ne zai zama matsala? Yanzu haka nasa an fara rarrabawa abokan kasuwancin namu, ba wani abin damuwa.”

Turo ƙofar da Hajiya tayi ne ya sanyashi saurin katse wayar.

“Wai Hajiya sau nawa zan faɗa miki ki riƙa ƙwanƙwasa ƙofa kafin ki shigomini ɗaki?”

“Na yanzu dai ya wuce tunda na shigo, magana na shigo muyi akan yaronnan, don na gaji da yadda ka zuba masa ido yake yawo a gari kamar wanda bashi da gata, duk an rufe maka baki ka kasa taɓuka komai.”

Shiru yai mata saboda shi yanzu ba ta yaron yake ba, tuni ya gama haƙura da shi ya sallama, saboda ya san lallai alhakin wasu yaran ne ya sauka akan ɗan nasa har shaye-shayen irin kayan da suke fatauci ya yi sanadiyyar aikata abin da yayi har ya kore shi daga gidan.

Alhaji da kai fa nake magana.”

Wayar shi ce tayi ƙara, ganin sabuwar number sai ya ɗaga kawai saboda ƙauracewa tuhumar da Hajiya ke masa.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!” Ya furta yana miƙewa tsaye, Hajiya ta bi shi suka miƙe a tare.

Abin da ya furta kawai kenan, har aka katse wayar bai sake cewa komi ba.

“ Alhaji lafiya? Me ya faru?.”

Bai ba ta amsa ba, ya kwashi makullanshi ya yi hanyar ficewa, ta bi bayanshi tana ɗaga murya.

“ Ni fa na gaji da wulaƙancin nan da ka ke mun Alhaji, ka ƙi ka tsaya mu yi magana a kan yaron nan, ko don yanzu kana da wasu yaran ne shi ya sa wannan ka ƙyaleshi?.

Wani abu ya tokare ma shi zuciya, idan akwai abin da ya tsana bai wuce Hajiya Rabi ta yi tunanin saboda wasu yaran nashi yake ƙin kula nata ba. Shi ya sa ba ya yadda ya kula yaran Hajiya Karima a gaban Hajiya Rabi, soyayyar duniya ya ɗora akan Auwal, ya sakar ma shi dukiya yana abin da yake so, ko faɗa ba ya mashi duk don gudun ɓacin ran uwargidanshi, kasancewar Auwal ne ɗansu ɗaya tal da suka haifa mahaifarta ta samu matsala, shi ne ma dalilin da ya saka shi ƙara auren.

“ Ni dai na gaji da shirun nan da kake mun Alhaji. Idan kaima an gama da kai ba za ka iya komai a kanshi ba sai ka min bayani.”

Ba shi da lokaci da nutsuwar tattauna maganar nan da ita, cikin yanayin sauri ya shiga rarrashinta.

“Ki yi haƙuri kin ji, idan na samu lokaci sai mu tattauna.

Tun kafin ta ba shi amsa ya yi gaba kawai ba tare da ya saurare ta ba. Suna fita suka yi karo da Hajiya Karima za ta shiga ɗakin. Fasa bin Alhajin ta yi, ta tsaya tana ta aika ma Hajia Karima da maganganu.

“ An zo a yi murna saboda halin da aka saka ni da ɗana a ciki ko? Ki cigaba da murna, mune da dariya a gaba. Yadda kika shigo gidan nan kika rabani da mijina da ɗana, sai na tabbatar da na tarwatsa miki taki rayuwar.”

Ba sabon abu ba ne a wurin Hajiya Karima, ta daɗe tana tunanin hanyar da zata bi ta fita daga zargin Hajiya Rabi ta kasa, ita kanta ƙoƙarin ganin an ceci Auwal take amma abun ya ci tura. Ita ma bar mata wurin ta yi, har tayi nisa tana jiyo maganganun da take mata cikin ɗaga murya.

Ɗakin Alhajin ta koma, bayan ta rufe ta ci gaba da duba lungu da sako tana neman kuɗin da zata kai wa Malami, iyakar nema ta yi amma ba ta samu ba, hakanan ta haƙura ta fito jiki a salube ta yi ma ƙawarta waya.

“ Lami kuɗin nan fa ba su samu ba. Na yi, na yi Alhaji ya bayar ya hana, na duba a ɗakinshi babu, ban san inda zan samo kuɗin nan a kai ma Malam ba.”

“ Haba Hajiya, dole fa sai kin siyar da filin nan.”

“ Filin ne da ba nawa ba Lami, na Auwal ne, ba ƙaramin tashin hankali zan shiga da Alhaji ba idan ya gane na siyar da filin nan.”

“ Sadda zai gane ai fili ya gama mashi amfani, ba faɗan da zai maki sai sam-barka, kina ji fa Malamin nan aikin shi ba ɓata lokaci, cikin ‘yan kwanaki za ki ga ya warke sarai.”

“ Haka ne Lami, bari dai mu gani to.”

“ Ba wani abin da za mu gani, ban sanki da gardama akan neman lafiyar yaronnan ba, an jima ko gobe zan zo miki da mai sayen filin.”

“ To shi kenan.”

Kwana biyu ta gama tattara kuɗin fili a hannunta. Ƙarya ta yi wa Alhajin, da yake baya cikin natsuwa bai tsaya bincike ba ya bar ta suka tafi kawai.

Sai da ta biya wurin Auwal don ganin halin da yake ciki. Cikin sa’a yau bai riga ya sha ƙwayoyin sun ƙarasa ɗauke mishi sauran hankalin da ya rage mashi ba. Tana ganin lokacin da mai kawo mishi ƙwayar ya bar wurin.

Bayan ta gama bashi abinci, ya kalle ta yana harhaɗa magana da ƙyar,

“ Umma wai ni yaushe zan dawo gidan nan?.”

“ Ka kusa insha Allah, ka ƙara haƙuri ka ji, yanzu ma nema maka magani zan tafi, shi ya sa daga yau ma Bala ne zai rinƙa zuwa wurinka ba ni ba.

Wani abu ke son hanata tafiya ta bar shi, gani take kamar akwai abin da zai faru da shi.

Zumbur ya miƙe kaman wanda aka mintsina, a nan inda suke ya juya baya kawai ya fara fitsari. Haka ta tashi suka bar wurin tana mishi kuka sosai kamar kar ta tafi.

Ƙasar Nijer suka nufa, kwanan su biyar ana yi ma Auwal magani a cewar Malamin, sannan suka ɗauki hanyar dawowa.

Tun a hanya da suka kunna labarai ta ji Sanarwar an kama mijinta akan laifin safarar miyagun ƙwayoyi. Bata samu fara biyawa ta wurin Auwal ba, gida kawai ta wuce don ganar wa idonta.

Dandazon mutanen da ke zaryar zuwa jaje ma kaɗai ya isa ya tabbatar mata, wata Ƙanwar Alhajin ce da suka shiga tare ta taho inda suke, ko gaisuwar ta bata amsa ba take tambayarta,

“ Fatima wai me ke faruwa a gidannan?.”

“ Komai ma ya faru Hajiya kina ina? Jiyan nan jami’an hukumar NDLEA suka zo gidan nan suka kama Alhaji, suna hanya wasu da ake zargin abokan harkarsu ne suka saka su, su yi ƙoƙarin kashe Alhaji don gudun kar ya tona musu asiri, ai jiya mun ga tashin hankali Hajiya.

“ Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un, Alhaji da fataucin miyagun ƙwayoyi Fatima.

“ Mu ma dai mun kasa daina mamaki Hajiya.”

“ To, Allah ya fitar da shi idan ba shi da laifi.”

“ Ameen Ya Allah.”

Ɗakinta ta koma, batun kama Alhaji na ta damunta, ga magungunan Auwal bata san yadda zata fita ta fara mishi amfani da su ba saboda mutanen da ke ta sintirin zuwa gidan.

Bala Driver ta kira sashenta, sun gama gaisawa, ta jawo ledar da magungunan suke a ciki. “ Magungunan Auwal ne Bala, ban san yadda zan fita daga gidannan ba, zan maka bayani idan ka je sai ka ba shi.”

Sadda kanshi ya yi ƙasa, yana so ya yi mata bayani ya rasa ta inda zai fara.

“ Lafiya dai? Ko ba zaka iya kaiwa bane?.”

“ A’a Hajiya, Auwal ɗin dai ne.

Ta zabura ta miƙe a tsaye.

“Auwal ɗin dai ne kamar ya?, me ya faru da shi?.”

“ Wallahi tun ranar da kuka tafi ni ke zuwa duba shi wurare daban-daban amma Allah bai yi na gan shi ba, yanzu haka daga wurin da ya saba kwana ni ke ko alamunshi babu.”

Zumbur ta miƙe tsaye,

“kuma ka ke nan gabana zaune? Bani makullan mota.”

“Hajiya yanzu zan je in ƙara dubawa.

“ka bani makullin mota na ce.”

Ba ta tsaya jiranshi ba ta yi gaba, da ta tuna makullan motar da suka dawo na wurinta. Da ƙyar ta iya tsayawa yi wa Fatima bayani, sannan ta tafi nemanshi.

Nema sosai ta sha Babu Auwal babu alamunshi. Mutane da yawa sun tausaya mata, duk da wasu na ganin kuskurenta ne, da kuma sakacinta tare da mugun bakin da take yiwa yaran wasu.

* * *

Waiwaye...

“Umma ki ba ni kuɗin nan fa, idan ba ki ba ni ba waye zai ba ni?.”

“To Auwal ana bayar da babu ne? Wanda ni ke da su duk ka kwashe. Ka na sane da furucin mahaifinka na hana baka kuɗi tun da ya ga ka fara shiriritar nan, kai kuma ka ƙi ka nutsu ka daina abubuwan da kake yi.

“Umma ni me nake yi? Don kawai na ce a bani kuɗi?.”

“Da ma kai ba zaka san abin da kake yi ba Auwal, saboda duk abin da kake ba yin kanka bane sanya ka ake.”

Kalaman ta da ke ƙara mishi ƙarfin gwiwa kenan yana aikata duk abin da yake yi, saboda Ummanshi ba ta ganin laifinsa, kuma duk da yasan yana ɗaukar mata kuɗi bata taɓa yi mishi faɗa ba, sai shima yake ganin kaman ba laifin nashi ba ne ya ke ci gaba da aikata shaye-shayensa.

Ganin ba zai samu komai a wurinta ba, sai ya wuce ɗakin Abban nasu, cikin sa’a kuwa yau ma ya gane inda yayi ajiyar kuɗi. Masu yawa ya kwasa, sannan ya fice wurin Abokanshi.

Yaran masu kuɗi ne kamanshi, da basu da aiki sai zuwa club da yawo da yan mata.

Ranar burinshi kawai ya nuna musu shi ma fa zai iya shan ƙwaya da yawa kamansu koma ya fi su, saboda yadda kullum su ke mishi gorin ƙaramar ƙwalwa gareshi, ba zai iya ɗauka da yawa ba.

Da yawa ya sha yayi mankas, tun a wurin ya fara tayar da hayaniya, da ƙyar Abokanshi suka bar wurin da shi, ranar bai kwana gida ba.

Abun na shi yana ta ƙara yawa, ba kullum yake kwana a gida ba. Idan bai samu kuɗi ba kayan amfanin gida ya ke ɗauka ya siyar. Kullum cikin kai shi Ofishin yan sanda, idan ba laifin sata ba to na faɗa, ko kuma damfara. Tun yana abu cikin hankali, har ya fara fita hankalinshi.

Cikin zuwan da yake neman kuɗi ɗakin mahaifinshi ne, da bai samu ba ya tsananta bincike, cikin sa’a ya ci karo da irin ƙwayar da yake siyarwa, dama irinta ne yake so ya ɗauki kuɗin ya saya, bai tsaya ƙirgawa ba ya kwarara su kawai a baki. Tun daga ranar ko babu kuɗi can yake zuwa ya duba, duk wata ma’ajiyarshi ya santa.

Shawarar yiwa Auwal aure Hajiya Rabi ta kai ma Alhajin, ya kalleta sheƙeƙe,

“Aure fa kika ce Hajiya, a ɗauri kashi ko a ɓata igiya? Ina abun yake wai maye ya ga jariri, duka shekarunshi nawa da zamu mishi aure? Kuma wanne iyaye ne za su yarda su bawa Auwal auren ‘yar su? Sai dai ko wanda suka haƙura da ita.

“Haba Alhaji, kai da kanka ka ke faɗin haka akan ɗan cikinka? To idan bamu mishi auren ba ya zamu yi da shi? So kake mu zura ido muna kallo ya lalace akan idonmu.”

“Lalacewa ta nawa kuma Hajiya? Shawarar dai dana yanke zan ɗauke shi ne na kaishi rehabilitation centre, su dan riƙe shi na wani lokaci a samu ya daina abin da yake. _rehabilitation_ fa Alhaji, ina! Nima ban yarda da wannan shawarar taka ba, akan me zaa kai shi can bayan ni da kai mun sani sarai asiri aka mishi ya fara shaye-shayennan, ina ma laifin kace zaa kai shi gidan Malamai a nema mishi magani, ko ita kaje ka matsa mata ta sa a karya abin da aka mi shi.”

“Kin ga Hajiya, don Allah ki daina maganganun nan, ki ci gaba da kyautatawa abokiyar zamanki zato. Sannan ki bari a kai yaron nan inda zai samu lafiya.”

“A’ah wallahi, babu inda za’a kai mun ɗana a takura rayuwarshi.”

“Shi kenan.”

Ya ƙyaleta kawai a haka, yana ƙara maida hankalinshi akan harkokinshi na dillancin miyagun ƙwayoyi , cikin sirri suna ƙara faɗaɗa wuraren siyarwa, duk wani club da matasa ke zuwa, da wasu wuraren daban-daban.

‘Yan uwan Babansa duk sun gwada ɗaukar Auwal sukai gidan mari saboda maganar da ya ke yawon dauko musu, anma fafur Hajiya ta ƙi yarda, ko fada bata son kowa ya mishi, haka duk suka tattara suka barta da shi.

Neman magani take sosai wurin Malamai, suna cin kuɗinta kawai.

Ranan tana zaune falo ya wuceta. Kuɗi ya duba babu, babu kuma abun siyarwa, ƙwayoyinma da yake samu a ɗakin Abbansu ya daina ajiyewa. A fusace ya fito ya mata tsaye.

Yana magana muryarshi na kyarma, tsayuwar ma da ƙyar yake yin ta.

“A bani kudi.”

“Da akwai ai da ka samu Auwal, bani da su.”

Wayarta dake saman cinyarta ya fizga ya yi hanyar fita, da sauri ta tare shi.

“Ina kuma za ka kai mun wayar?.”

“Siyarwa.”

“Siyarwa kuma kamar yaya? To ni kuma in yi amfani da wacce?.”

Bangajeta ya yi zai wuce, da sauri ta sake tararshi.

A yanayin da yake ciki baya jin zai iya haƙura, burinshi kawai ya samu kuɗi ko ta yaya ne ya je ya amso ƙwaya, gaba ɗaya baya jin daɗi da bai sha ba.

Kokawa ya shiga yi da Umman tashi, ganin bata da niyyar sakinshi ya cire charger ya fara dukan ta, duk da ta sakar mishi tana ihu bai daina ba, gani yake ta ma raina shi, gani ya ke kamar wata daga cikin ‘yan matanshi ce yake duka.

Daidai Abbanshi ya dawo gidan ya jiyo ihunta, da gudu ya shiga ya tarar da Auwal ne yake dukan ta, yayi ƙoƙarin karɓarta sosai anma ya kasa, wani irin harbi Auwal ya mishi sai da ya dangana da bango, tuni jini ya fara zuba a kanshi, bai ƙara sanin meke faruwa ba sai a asibiti.

Kafin a Sallameshi daga asibiti Auwal ya shiga wani babban supermarket ya yi sata sun gudu shi da abokanshi, da ƙyar Alhajin ya iya rufe maganar, bayan ya biyasu kuɗi masu yawa. A hankali ya rinƙa neman abubuwansa masu muhimmanci babu, ga jinyar da Auwal ya bar shi da ita.

Sake ma Hajiya maganar dauke Auwal yayi, ta ƙi yadda, duk da itama halin da ya saka ta, saboda haka ya ce lallai sai Auwal ya bar gidan ko kuma su tafi tare, saboda shi yanzu tsoran sa ma yake, haka ta haƙura ya kora Auwal daga gidan da tunanin zata nema mishi magani ya dawo.

* * *

Bayan shekara ɗaya da watanni.

Babu Auwal babu labarinshi, tuni Hajiya ta rame ta fita daga hayyacinta. Ta kasa haƙura, kullum cikin fita neman Auwal take. Alhaji an wuce da shi gidan yari saboda tabbatar da laifin da ake zargin shi da shi bayan doguwar shari’ar da aka gabatar, tun a kotun ya sawwaƙe musu aurenshi da ke kansu.

Gaba ɗaya Hajiya ta kasa hakura, har ɗaki ta tarar da Hajiya Karima ta kama ɗanta Namiji ta shaƙe za ta kashe shi su duka su yi asara, da ƙyar aka ƙwace yaron, dole aka raba su zama gida ɗaya.

Tana zaune ta zuba tagumi, ta jiyo sallamar Hajiya Karima,

Zumbur! Ta mike a fusace ta fita, sai dai tana fita ta ci karo da Auwal tsaye yana murmushi cikin shiga ta kamala, da yanayin da ta manta rabon da ta ganshi a ciki.

Tsaye ta yi ta kasa ƙarasawa, tana tunanin ko gizo ne ya mata, sai da ya ƙaraso da kanshi ta ji ya yi magana,

“Umma.”

Da sauri ta ruƙunƙumeshi ta kasa saki, kuka take sosai tana godiya ga ubangiji.

Hango Hajiya Karima ne ya sa ta sassauta riƙon da ta mishi,

“Munafuka! Dama nasan ke ce zaki ɓoye min ɗana, kuma...”

“Haba Umma, ko don yanayin da kika gan ni ai ya kamata ki haƙura a miki bayani, babu laifin Mama, taimakona ne ma ta yi.”

“To ina jinka.”

“Umma mu zauna ko.”

Suka shiga ɗaki suka zazzauna, sannan Hajiya Karima ta fara bayani,

“ Tabbas Hajiya ni ce na ɗauke Auwal, amma kuma da kyakkyawar manufa, da kuma sanin Alhaji da yan uwan Alhaji saboda ganin da muka yi ke kin kasa yadda a taimake shi. Ba wai mun ga gazawar ki bane wurin ganin kin gyara rayuwarshi, kawai dai hanyar da kika bi ce muke ganin kamar kin rufe ido ne.” Ta nisa sannan ta ci gaba,

“Duk da zaman kishi ne ya haɗamu, tsakani na da Allah nake zaune dake, ban taɓa tunanin cutar da ke ko ɗan Alhaji ba. Wannan ya sanya mu ka ɗaukeshi mu ka kai shi wurin da muka san lallai can za a taimaka mi shi.”

Auwal ne ya ci gaba da magana.

“_Rehabilitation_ mai tsada aka kai ni Umma, akwai wurin kwana mai kyau, abinci mai kyau, ana yi mana duk abin da ya kamata. Babu mai dukanmu, akwai daɗin zama sosai wurin Umma kowa magana mai daɗi yake mana.”

Ɗayan hannunshi ya ɗora saman hannunta da ta riƙe shi gam.

“Ko kaɗan banga laifinki ba Umma da ki ka barni ina yawo cikin bola bana da wurin kwana ba, ni kaina a lokacin na ɗauka shi ne gatan, bana so a kaini inda za’a hanani shaye-shaye, ina ganin kamar duk sadda ban sha ba mutuwa zan yi.”

“Na yi dana sani Umma, nayi dana sanin aikata shaye-shaye sosai. Da yanzu na zama cikakken mutum kamar kowa, da yanzu nayi ilimi kamar kowa, watakila ina aikin gwamnati ko kasuwanci da zai taimaka mana. Ban yi tunani ba ko kaɗan, dana biyewa sharrin zuciya da zugar Abokai. Umma ban san ta inda zan fara rokon yafiyarki ba akan dukkan abinda na aikata muku ba, kun nuna mun soyayya sosai kun ɗora yarda a kaina, na watsa muku ƙasa a ido.

Da ƙwalla ya karasa maganar, cikin tausayi take kallon yaron nata.

“Kar ka damu Auwal, abin da aka shuka shi yake tsira, icce tun yana ɗanye ake tanƙwara shi, mu ma da namu laifin da muka kasa tsayawa mu ba ka tarbiya yadda ya kamata, burinmu kawai muyi maka abin da ka ke so komin muninsa. Hankali na ya kasa kwanciya, kullum gani nake Hajiya za ta kai ka wurin boka a raba ka da Alhaji, saboda yanda nake ji ana cewa kishiyoyi na yi, har da su kuma Malaman da suke ƙara tunzura ni, kullum cikin yi ma yaranta fatan lalacewa na ke yanda Alhaji zai guje su ya soka kai kaɗai, sai gashi ni nawa yaron ne ya lalace, ga kuma alhakin yaran wasu da rayuwarsu ta lalace saboda mahaifinku, shi Alhaki kwikuyo ne, kuma sharri ɗan aike, abin da muka yiwa wasu ne muka gani a kanka, kaima ka yafe mana saboda kasa baka tarbiyar da muka yi.”

Ta mai da dubanta ga Hajiya Karima.

“Ina jin kunyarki sosai Hajiya, ban taba sanin ke masoyiyarmu ba ce, kullum a maƙiyiyata nake kallonki. Ba ki barni da yarona ba duk abubuwan da na miki, ki ka dage ki ka ceto rayuwarshi, na gode sosai, don Allah ki yafemun.”

“Kar ki damu, komai ya wuce wallahi ban taɓa riƙonki da wani abu ba. Insha Allah wasu yaran ma sun daina shiga halin da ya shiga, saboda yanda gwamnati ta saka tsaro sosai a na ta kama masu siyar musu da kayayyakin.”

“Masha Allah, sauran namu muma iyayen mu ci gaba da saka masu ido, muna kula da irin rayuwar da su ke, da kuma mutanen da suke tare.”

“Insha Allah.”
Ɗaukar Jinka

Post a Comment

0 Comments