Ticker

6/recent/ticker-posts

Gobara Daga Daji

Salim Hassan (2023). Gobara Daga Daji. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD

GOBARA DAGA DAJI

Na

Salim Hassan

Wata rana Malam Habu yana tafiya tare da ɗansa Auwalu a cikin mota zuwa garin Kan-kano daga garin Suru. Suna tafiya suna hira mai ban sha’awa tsakanin mahaifi da ɗansa, yana tambayarsa, shi kuma yana ba shi amsar iya abin da ya sani. Da yake akan garuruwan da suke wucewa yake masa tambayoyin, tunda wannan shi ne zuwan Auwal garin Kan-kano a karon farko.

A yanzu suna daidai wani gari wanda alamu suka nuna babu mutane da suke rayuwa a cikin garin a halin yanzu. Gari ne kamar an yi yaƙi ko kuma ka ce mutanen garin sun gudu sun bar shi, ka iya cewa ya zama kufai, ban da hayaƙi da yake tashi, sai wata doguwar hasumiya da ta ruguje daga ɓangare ɗaya, su kaɗai kawai ake iya hangowa. Auwalu ya ga cewa tashar motar garin ba mutane kamar yadda ya saba gani a duk tashoshin da suka wuce a baya, wannan dalili ne ya sa Auwalu ya yi wa mahaifinsa wata tambaya me cike da mamaki dangane da wannan gari “Baba wannan wane gari ne kamar an yi yaƙin duniya na uku a cikinsa!? mahaifin Auwalu ya gyaɗa kai, alamun cewa ya san cewa idan har aka zo wannan gari zai yi masa wannan tambaya. “Ka taɓa jin wani kirari da ake cewa ‘Natsika garin ‘yan maro, Natsika garin ‘yan maye, Natsika garin ‘yan mashalo, ba lafiyayye sai ɗan malam’?”

 Sai Auwalu ya yi shiru na wasu daƙiƙu, can sai ya ce “Eh baba, na taɓa jin Mati mai sai da Sigari a bakin titi yana yi wata rana mun je siyan kilin a kantinsa” Malam Habu ya yi murmushi ya ɗauke kansa daga tuƙin da yake yi, ya kalli ɗansa yana murmushi ya ce masa “To wannan shi ne garin Natsika, wanda shaye-shaye da zaman-kashe-wando ya yi musu illar da har abada babu wanda zai iya gyara wa sai mahaliccin kowa da komai” Auwalu ya gyara zama, ya yi zuru da idanu, ya ajiye wayar da take hannunsa alamar cewa ya shirya tsaf ya ji cikakken labarin wannan gari na ‘yan magaru, wanda mahaifinsa ya ce illar shaye-shaye ce ta mayar da shi tamkar an yi yaƙi a cikinsa. Ya miƙa hannu ya rage sautin radiyon da yake tashi don dai ya ƙara samu nutsuwa wajen sanin abin da ya faru da Natsika garin ‘yan mashalo.

Garin Natsika babban gari ne wanda akwai babbar masarauta a cikinsa, garin ne mai yawan jama’a wanda suka haɗar da malaman addini da ‘yan boko da alƙalai da ‘yan siyasa, suna da ƙwararrun likitoci da malaman makaranta da ‘yan kasuwa, ga shi kuma sun yi sa’a gwamnati tana kula da makarantunsu da asibitocinsu da duk inda ya kamata ta ba shi kulawa.

Masarautar mai girma ce a cikin ma su girma, mai daraja a cikin ma su daraja, ga ɗaukakar da ta samu a cikin masarautun ƙasar Hausa, idan aka ce ka lissafo manyan masarautun ma su faɗa-a-ji a ƙasar Hausa to ko ba ka saka ta a ta farko ba to za ta zo a ta biyu. Duk Sarkin da ya zo yana ƙoƙari wajen yin adalci a tsakanin al’umma, a wani lokacin ma Sarkin har aikin da yake alhakin gwamnati ne amma shi yake ɗaukar wannan nauyi, kuma cikin hukunci na mai duka sai Allah ya ba shi ikon sauke wannan nauyi. Yana daga cikin kirarin da ake yi masa: “Ka yi aikinka ka yi na iyayen talakawa, ka yi na gwamnati ka yi na malamai”.

Kwatsam! Kana naka Allah yana na shi, watarana sai Mai Martaba ya kwanta jinya, bai jima yana jinya ba ya koma ga mahaliccinsa. Marigayi Sarkin Natsika ya bar ‘ya’ya maza uku manya waɗanda ake tunanin a cikinsu ɗaya zai zama magajinsa.

Alhaji Abdurrahman shi ne ɗa na biyu a wajen Mai Martaba, malami ne, duk gari ba wanda bai yarda da nagartarsa ba. Bai nuna kwaɗayinsa na sarautar garin Natsika ba, amma kuma a zuciyarsa ya san cewa shi ya fi cancanta da wannan kujera. An ayyana ranar da za a naɗa sabon sarki na garin Natsika.

Dr. Abdulkarim shi ne babban ɗa a gidan sarautar Natsika, ya yi karatunsa a ƙasar Amuruka, ya kai matsayin Dakta a ƙasar Amuruka tun bayan da ya nuna rashin sha’awarsa ta rayuwa a ƙasar haihuwarsa ta Nijeriya. Marigayi Mai Martaba yana son Dakta Abdulkarim kamar yadda uwa take son ɗanta, a lokacin da yake tsananin rashin lafiya, wannan dalili ya sa duk abin da Dakta ya nema, to Mai Martaba sai ya cika masa burinsa.

Tun Dakta yana matakin sakandire halayensa gabaɗaya suka canza, suka koma tamkar na Turawa. Wani lokacin har mantawa yake shi baƙar fata ne kuma Musulmi, duk wata holewa da shagala za ka same shi kan gaba, ba a barinsa a baya.

Shekara huɗu ke nan bai ziyarci gida ba, kwatsam sai jin labarin mutuwar mahaifinsa ya yi. Ya shiga damuwa matuƙa, saboda ya rasa wani babban bango a rayuwarsa, amma yayin da ya tuno cewa shi ne wanda zai gaji wannan babbar masarauta sai damuwarsa ta yaye cikin ƙanƙanin lokaci kamar yadda ake cire sartse a cikin ɗan yatsa. Ya kasance yana zargin masu madafun iko da cewa ba sa bawa mutanen gari ‘yanci su yi abin da suke so, amma tunda yanzu ya samu dama, idan har aka naɗa shi sarki to kowa zai ji daɗi.

Alhaji Abdulwahab ya samu labarin cewa har da sunansa a hannun gwamnan da zai yi naɗin sabon Sarki ranar Juma’a mai zuwa. A safiyar Talata ya rubuta takarda zuwa ga gwamna kan cewa a cire sunansa daga jerin wanda za su gaji Mai Martaba, a bar na yayyensa biyu Dakta da Sheikh Abdurrahman, duk da a zuciyarsa ya san cewa Abdurrahman shi ya fi cancanta da wannan sarauta, amma sai bai bayyana ba gudun fitinar da ka iya biyo baya. Gobe bayan sallar Juma’a za a bayyana sabon sarkin garin Natsika a gidan gwamnatin jihar Natsika.

Dakta Abdulkarim ya dawo Natsika tun bayan shekara huɗu ba tare da ya ziyarci gida ba. Sheikh Abdurrahman da ƙaninsa Alhaji Abdulwahab duka suna cikin wannan gari. An zauna a gidan sarauta bayan sawu ya ɗauke, tun bayan sallar Isha’i har rabin dare, tattaunawa ta gudana akan wanda ya kamata ya gaji wannan babbar masarauta wadda kowa yake girmamata har a ƙasashen masu jan-kunne. Tun daga kan iyaye mata da duk wani mai rawani a wannan lokaci kowa ya nuna goyon bayansa ga Dakta Abdulkarim a matsayin sabon Sarki. An samu haɗin kai da fahimtar juna ba tare da wani hargitsi ko tashin hankali ba, a wannan dare na Alhamis. An kammala zama kowa yana yi wa Dakta Abdulkarim addu’a da kyakkyawan zato. Tabbas sun nuna tarbiyyar da marigayi Mai Martaba ya yi musu ta girmama junansu.

An yi naɗin sabon Sarki cikin nutsuwa da ban sha’awa da jin daɗi. Gwamna ya yi kyakkyawan yabo ga iyalan marigayi Sarkin Natsika, ta yadda suka bi komai a sannu wajen naɗin sabon Sarki.

Auwalu ya yi tsam! yana sauraron labari kai ka ce ruwa ya cinye shi. “To baba me ya faru bayan Dakta ya zama sabon Sarki, ko kana nufin shi ya lalata wannan gari har ya zama kamar kufai?” Malam Habu ya ce, “Ba za ka fahimci labarin ba har sai ka ji rawar da ‘yan siyasa da ‘yan boko da masu faɗa-a-ji suka taka a wannan gari” Amsar da ta sa Auwalu ya shiga tunanin yadda sauran labarin zai kasance. Yana tsakiyar tunani bai yi aune ba sai ya ga babansa ya saka sigina alamar cewa zai tsaya. Cikin gidan mai suka shiga domin sallar La’asar, suka kammala suka shiga shagon siyar da abinci, ba tare da ɓata lokaci ba suka sake hawa hanya.

Auwalu yana jiran babansa ya ci gaba da ba shi wananna labari mai ban al’ajabi,”Wannan labari da littafi ne, da duk inda yake sai na nemo shi na karanta shi a lokaci guda” Auwal ne yake maganar zuci. Sai ya ji babansa ya ce “Ka ga almuru ya fara yi, bari na mai da hankalina kan hanya, idan Allah ya sa mun isa lafiya sai ka ji cikakken labarin”

“To baba ai matasa aka sani da shaye-shaye, amma ya akai lalacewarsu ta zama shi ne dalilin rugujewa da lalacewar wannan gari mai babbar masarauta da gwamnati mai kula da al’amuran mutanen gari” Auwalu ya sake yiwa mahaifinsa tambaya. Malam Habu ya sake juyowa ya ɗora hannu ya shafa kan ɗansa cikin murmushi har ya bayyanar da haƙoransa ya ce “ Ka yi haƙuri mu karasa Kan-kano” Auwalu ya gyaɗa kansa alamar cewa “To baba, Allah ya kai mu lafiya”. Malam Habu ya ce “Amin. Allah Ya yi maka albarka” Auwalu ya ɗauko iyafis ya saka a kunne, shi kuma malam Habu ya ci gaba da tuƙi.

Ƙarfe shida na yamma suka shiga garin Kan-kano, ba su tsaya ko’ina ba sai a babban masallacin garin, nan suka yi sallar magariba, daga nan suka nufi masaukinsu. malam Isa aminin malam Habu ne tun lokacin yarinta, shi ne ya sauke su a gidansa, ya ba su abinci da duk abin da suke buƙata, bayan nan suka gaisa. “Su Auwalu yau an shigo birni ke nan” In ji Malam Isah. Cikin murmushi Auwal ya amsa masa da cewa “Baba ai daga birnin London sai birnin Kan-kano duk duniya.” Sai mahaifinsa ya ce “su London manya! ina ka baro birnin Manzo”. Cikin murmushi ya kai hannu ya shafa ƙeyarsa, alamar jin kunya.

Malam Habu ya cewa ɗansa “Ka nutsu na ƙarasa maka labarin?” “Wane labari?” in ji malam Isa. Sai Auwal ya yi caraf ya ce, “Labarin garin ‘yan mashalo baba ya ke ba ni” Malam Habu da Malam Isa suka kalli juna suka yi murmushi.

A lokacin da Dakta ya zama sabon sarkin garin Natsika, a ƙasa da wata uku komai ya fara rincaɓewa, komai ya fara rikicewa, ya fara tuɓe wasu masu sarauta yana naɗa waɗanda yake so, waɗanda ra’ayinsu na sharholiya ya zo ɗaya.

Ya haɗa kai da manyan ‘yan kasuwa, ɓata gari, waɗanda ba sa son ci gaban garinsu da al’ummarsu, su dai kasuwancinsu shi ne a gaban su, nan dai suka fara wasu harkoki da suka saɓawa dokar ƙasa, ciki har da miyagun ƙwayoyi. Daga nan ne wasu miyagun ‘yan siyasa suka shiga harkar ka’in da na’in, kan ka ce me, harkar shaye-shaye ta yawaita a garin, ita kuma gwamnati har yanzu ta ƙi saka baki saboda zaɓe ya ƙarato, tana tsoron ta saka baki Sarki da manyan ‘yan kasuwa da suke da magoya baya su cire hannunsu daga tafiyar gwamnatin.

A haka dai gwamnati ta ci gaba da saka musu ido suna cin karensu ba babbaka. A ɓangare guda kuma alƙalai ba su da ta cewa, duk wanda aka kama shi da laifi, in dai yana daga cikin yaran Sarki ko ɗaya daga cikin manyan ‘yan kasuwar nan, to, alƙali zai sake shi ba tare da wata tara ko hukunci mai tsauri ba.

Akwai lokacin da wani ɗan-sanda da ya shahara da yaƙi da rashin tsoro da riƙo da gaskiya ya kama babban dilar miyagun ƙwayoyin garin Natsika, da yake yaron Alhaji Kabuwaya ne, wato Audu Jangwal, bayan an miƙa shi gaban kotu da laifin safarar miyagun ƙwayoyi da kuma tayar da faɗan daba a tsakanin al’ummar gari, da wannan shari’a da belinsa kwata-kwata Kwana uku ne, sai aka saki Jangwal, aka ci tararsa kuɗi naira dubu talatin da biyu kacal, a maimakon ya ƙare rayuwarsa a gidan kaso. Ƙaryar banza ke nan ‘akwati goma zani ɗaya’ In ji Kabuwaya bayan ya biya kuɗin tara.

Bayan fitowar Jangwal daga gidan kaso na kwana uku, ya ƙara ɗaura ɗam ba na siyar da ƙwaya a duk faɗin garin. Ya samu yara waɗanda zai dinga ba wa kaya kamar yadda suke faɗa, waɗannan yara su suka ci gaba da cefanar da ƙwaya a faɗin jihar.

An yi zaɓen sabon gwamna, an samu canjin gwamnati, amma abin bai yi wa malamai da dattijan garin daɗi ba, kamar abin da Hausawa suke cewa, cin nama da kanwa, saboda wanda Sarki da su Kabuwaya suka mara wa baya, shi Allah ya ɗora a matsayin gwamna.

Sabuwar gwamnati ta kwana ɗari a ofis. Duk wasu ababan more rayuwa tana samarwa jama’ar gari, sai dai sun mai da gari na mashaya, ba babba ba yaro, ba namiji ba mace, sai wanda Allah Ya tsare.

‘Yan ƙwaya ƙara yawa suke a gari, duk gidan da ka leƙa sai ka ga cewa akwai mai bushe-bushe ko mai ɗaga kwalba a gidan, sai kaɗan da Allah ya tseratar. Saboda lalacewa sai ka ga ana raba kayan maye a cikin makarantun sakandire, amma malaman shiru kake ji kamar malam ya ci shirwa, kowa yana tsoron ya yi magana ya rasa aikinsa. Wannan shi ne tasirin ma su faɗa-a-ji a garin Natsika wajen lalacewar garin a cikin ƙanƙanin lokaci.

Malamai suna ta wa’azi suna ta jan-hankali akan wannan mummunar ɗabi’a da ta addabi wannan gari. Tarbiyya ta fara ƙaranci a idon matasa, iyaye sun fara sallama ‘ya’yansu saboda rashin ladabi da tarbiyya da suke nuna musu. A bisa al’adar wannan duniya da muke ciki, duk lokacin da aka rasa taribiyya tun daga gida, to, har a waje ba wanda zai tsira. Daga nan kowa a cikin al’umma zai rasa mutuncinsa da kimarsa, duk girman mai mulki, duk malantar malami, duk shekarun dattijo, wannan ba zai sa yaro mara tarbiyya ya ƙi yi masu jafa’i ba, ko da kuwa duk duniya ana ganin girmansa. Wannan shi ne sakamakon rashin tarbiyya a tsakanin al’umma.

A kwana a tashi malamai da dattijan gari suna ta addu’a suna neman agajin Allah da ya kawo musu mafita. A bisa sunnar Allah, ba ya bari zalunci ya ɗore a ban-ƙasa, matuƙar akwai bayinsa na ƙwarai.

Rana ɗaya Gwamna ya wari gari da ƙyamar abin da yake faruwa a jiharsa. Ba ɓata lokaci ya kira kwamishinoninsa da ya aminta da su mitin ɗin gaggawa. Aka shiga mitin tun bayan sallar magariba har lokacin sallar isha’i ya yi ba su tashi sun yi salla ba, har kwamishinan addinai honorabil Salisu Musa ya ba su fatawar cewa, ‘In dai musulmi suka haɗu suna wata tattaunawa akan maslahar al’umma, to ko da lokacin salla ya yi, za su bar sallar idan har tashin nasu zai kawo tsaiko ga wannan zama nasu, musamman ma idan sallar isha’i ce da lokacinta yake da tsayi’ suka yi kabbara saboda jin wannnan fatawa, aka ci gaba ta tattaunawa.

Da yake masana boko sun fi rinjaye a cikinsu, sai shawara ta karkata kan cewa abin da suka yanke, shi za a bi wajen magance shaye-shaye da zaman banza. Suka ce: Na farko, za mu yaƙi duk wanda yake da hannu wajen safarar miyagun ƙwayoyi da masu siyarwa ba bisa ƙa’ida ba. Na biyu, za mu baza jami’anmu masu hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi su tsaurara bincike kan duk wasu shaguna da duk wani loko da saƙo da ake tu’ammuli da ƙwaya. Na uku kuma, za mu haɗa kai da ‘yan sanda wajen kama duk wani dilan ƙwaya da duk wanda aka kama da ita. Na huɗu; gurfanar da mai laifin a gaban kotu, mu tsaya tsayin daka mu tabbatar an yi masa hukunci.

Shi dai kwamishinan addinai da wasu mutum uku wannan hukunci da aka yanke bai yi musu dadi ba, “Tunda an fi mu rinjaye ba yadda za mu yi” Salisu Musa yake faɗa a cikin zuciyarsa.

Aka rufe taro da addu’a bayan tsawon awa shida ana neman mafita.

Shekara guda cif! ana bin wannan salo da gwamnati ta ƙirƙiro don kawo ƙarshen shaye-shaye da zaman-kashe-wando, amma kai ka ce fetir ake ƙara wa wutar, eh mana, to ai miyagun ƙwayoyin sai suka zama tamkar wani gwal, saboda daraja da abin ya ƙara samu. Duk abin da ya yi ƙaranci a cikin al’umma, to darajarsa sai ta ƙara ɗagawa. Ya zamana an koma yin komai a ɓoye, su kuma manya a cikin harkar dukiyarsu sai ƙara haɓaka take. Sannan kuma duk lokacin da aka kama masu yaro, to ƙarshe dai a ce tara za su biya, su kuma biya ko ta kai miliyan ɗari.

Sai kuma zalunci ya shiga cikin lamarin, saboda su jami’an tsaro an ba su maƙudan kuɗi da kayan aiki akan cewa lallai su kamo masu laifi ko ana ha-maza-ha-mata, daga nan ne suka fara kame waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba, haka kawai matasa suna zaune a majalisa ko a gidan kallo ba su yi aune ba, sai su ga ma’aikata sun yi sumame sun caccafke su.

A ɗaya ɓangaren malamai suna ta Allah wadai da wannan tsari da gwamnati ta ɗauka. Akwai wani malami a garin wanda ake masa laƙabi da Malma Babba, malamin ya shahara da ilimi da karantar da al’umma. malami shi ne kan gaba wajen adawa da tsarin da gwamnati take ɗauka wajen magance shaye-shaye da zaman banza.

Da labari ya je wa shugaban jam’iyya akan abin da wannan malami ya ke faɗa akan gwamnatinsu, sai ya haɗa yaransa ‘yan daba, suka je masallacin Babban Malam yana tsaka da ba da darasi, bai ankara ba sai shi da ɗalibansa suka ga an yi musu ƙawanya, kai ka ce faɗan arna da musulmai ne, jifa suka fara ji rugugugu, duk wanda ya fito ko dai a sare shi ko kuma a dake shi da gora. Ba su duba darajar masallaci ba, haka suka ta yin rashin mutunci.

Shi dai Babbam Malam bai fito ba, suna daf da bankawa masallacin wuta bayan sun ruguje wani ɓangare daga jikinsa, sai ga jami’an tsaro, suna zuwa, suka harba barkonon-tsohuwa, cikin ƙanƙanin lokaci suka gudu.

A daren wannan mummunan labarin ya je kunnen Gwamna. Tabbas Gwamna bai ji daɗin wannan aika-aika da aka yi ba, take ya kira mataimakinsa da kwamishinan addinai Salisu Musa. Gwamna ya yi Allah wadai da abin da aka yi wa wannan malami da ɗalibansa, kuma ya yi alwashin ɗaukar mataki ga duk wanda yake da hannu wajen aikata wannan ta’addancin. Ya nemi shawararsu akan yadda za su ɓullowa al’amarin. Nan dai kowa ya faɗi albarkacin bakinsa, a ƙarshe dai shawarar Salisu Musa ce matsayar su. Wannan shawara ita ce, a kira wannan malami a zauna da shi, a ji hanzarinsa da hangensa akan wannan annoba da ta addabe mu. Gwamna ya amince da shawarar, take ya aika da gayyata ga Babban Malam.

Goron gayyata ya zo wa Babban Malam, da yake malami ne mai son gyaran al’umma, ba ɓata lokaci ba ya amsa wannan gayyata. A safiyar Juma’a ya tafi domin su gana da Gwamna da ‘yan fadarsa.

Bayan an tarbi Babban Malam, da yake duk sun san abin da ya haɗa su, ba su yi doguwar shimfiɗa ba, sai wannan malami ya fara bayani kamar haka;

Babban abin da yake sa wa a yi shaye-shaye shi ne; lalacewar zuciya da taɓarɓarewar tunani. To idan ana son kawar da shaye-shaye to sai an magance tunanin ɗan’adam, a gyara masa ɗabi’unsa da halayensa, ya zama ɗan’adam nagari mai kyakkyawar manufa.

Akwai wata babbar ƙasa wadda tana jin ita ce super power a duniya tun a shekarun baya, ita ma da ta shiga irin wannan matsala da muke ciki, da ta tunkari matsalar giya don magance ta a shekarar 1919, suka yi dokar hana sha da siyarwa, sun kashe maƙudan kuɗi wanda kimaninsu ya kai Dala miliyan sittin, bayan rubuce-rubuce da suka yi, sama da shekara goma sha huɗu amma abu ya ci tura, sai ga shi komai ƙara haɓaka yake, wai ɗan daudu da raino, kamar dai yadda kuka ɗauko gyara a wannan gari namu mai girma Gwamna. Ƙarshe dai majalisar ƙasar ta janye dokar, suka halatta cinikinta tare da karɓar haraji mai yawa.

Amma mai girma Gwamna idan ka duba yadda Musulunci ya hana musulmi shan barasa a wancan lokacin da musulunci bai gama yin ƙarfi a zukatan muminai ba, kuma ka san yadda zuciyar Balarabe take ɗamfare da barasa a wannan lokaci. Ba abin da Balarabe yake sha ya yi alfahari da shi kamar barasa, ta zamar musu ruwan sha; a sha da safe, a sha da rana, a sha da maraice, idan za a kwanta ma a sha, idan ka auna ba wani lokaci da ba a cikin giya yake ba. Kai! har saka ta suka yi cikin waƙensu na Larabci, za ka samu mawaƙi ya waƙe barasa.

Musulunci bai fuskanci magance shan barasa da wata doka ko ɗauri ko cin tara ba, sai dai ya fuskance su ta hanyar jan hankali da tarbiyya. Wannan shi ne abin da tun farkon gwamnati ya kamata ta yi.

Amirul Mu’uminana Umar ɗan Khaɗɗab sahabin Manzon Allah S.A.W, yana daga cikin waɗanda suke ƙyamar wanann al’ada ta shan barasa, kullum addu’a yake akan Allah ya saukar masu da bayani mai warkarwa game da barasa. Allah buwayi gagara misali, da ya so magance masu damuwar da suke ciki, sai ya fara saukar da ayar cikin suratul Baƙara, in da Allah S.W ya ce, “Suna tambayar ka game da giya da cãcã. Ka ce: “A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu”.

Sayyadina Umar Allah Ya ƙara yadda a gareshi ya sake yin addu’a, Allah Ya saukar da aya ta biyu wadda take cikin suratun Nisa’i, Allah S.W ya ce, “Ya ku waɗanda suka yi imani! ka da ku kusanci salla alhãli kuwa kuna mãsu mãye, sai kun san abin da kuke faɗa”

Sayyadina Umar ɗan Kaɗɗabi ya yi addu’a a karo na uku, sai Allah Mai amsa addu’ar bayinsa ya saukar da ayar da ta haramta musu ta’ammuli da barasa kwata-kwata, wannan aya tana cikin suratul Ma’ida; “Abin sani kawai Shaiɗan yana nufin ya aukar da adawa da ƙeta a tsakaninku, a cikin giya da caca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah, kuma daga sallah. To, shin, ku masu hanuwa ne? Tana sa Shaiɗan ya saka su ƙiyayya da gaba, tana hana su neman ilimi, tana hana ambaton Allah, tana hana su sallah, daga daina sallah kuma sai lalacewar zuciya.

Bayan waɗannan ayoyi sun gama sauka a cikin garin Madina, sai kowa ya dinga futo da barasa yana kwararar da ita a tsakar gari tana bin ruwa tana tafiya, duk soyayyarsu da ita haka suka haƙura, tarbiyya da imani sun yi tasiri a zuciyarsu.

Mai Girma Gwamna dole sai mun inganta makarantun addinanmu, ko dai a daidaita su da na boko, ko kuma a ba su kulawar da ake ba wa makarantun boko.

Iyaye su yi haƙurin bawa ‘ya’yansu ingantaccen ilimi da tarbiyya tun daga gida, su kame hannunsu ga faɗawa halaka.

A ɗauki nauyin malamai suna shiga lungu da saƙo suna wa’azi, a kafofin sadarwa. Sannan su sanar da matasa sanin girman iyaye da duk wani mai mutunci a cikin al’umma. Da yardar Allah Mai Girma Gwamna idan aka ɗauki waɗannan matakai, to za mu samu ɗauki daga ubangijin talikai.

Bayan wannan malami ya gama bayanansa a fadar gwamnati, sai Gwamna ya ka da baki ya ce: “Duk wanda Allah ya ba shi sanin addini, to ya ba shi ni’ima dawwamammiya mara yankewa. Za mu yi duk abin da ka zayyano, da yardar Allah kuma mun san in sha Allah za mu samu mafita”. Babban Malam ya sake jaddada maganarsa da wata karin magana da ta sanya His excellency murmushi “amma fa mai girma Gwamna sai an yi kamar ana yi ‘tusa da minshari’

“To yanzu ke nan baba an samu sauƙi a hakan, a yadda muka wuce garin na ga ba mutane da yawa?” In ji Auwalu, bayan ya fahimci cewa labari ya zo ƙarshe. Sai Malam Isa ya ba shi amsa da cewa Ai ɗana shekara biyu da dawowar garin Natsika hayyacinsa daga doguwar suma da ya yi, yanzu komai an samu sauƙinsa. Wata uku ke nan da suka wuce, haifaffen garin ne ya yi nasarar zuwa na ɗaya a musabaƙar karatun Alƙur’ani da aka yi ta ƙasa Malam Habu ya ce, Wannan shi ne tasirin samuwar malaman addini da ma su ƙarfafarsu a ban ƙasa”. Tabbas! yau na ƙara tabbatar da wannan karin maganar da Hausawa suke cewa, Gobara daga daji, kashe ta sai Lillahi”. Auwalu ya faɗa ya na mai nuna farin cikinsa da jin yadda Allah ya kawo wa wannan gari agaji da ɗauki.

Alhamdulillah.

Ɗaukar Jinka 

Post a Comment

0 Comments