Jibrin AJir (2023). Ka Fi Dan’uwa. Ɗaukar Jinka (Labaran Da Suka Samu Nasara A Gasar Gajerun Labarai Ta Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2022). Kangiwa Multimedia and Communication Company LTD
KA FI ƊAN’UWA...
Na
Jibrin Ajir
Rana
a tsaka ƙararrawar karyewar alƙadarina ta fara bugawa ba tare da zato
ko tsammani ba... Kodayake an daɗe
ana yi mini wani azancin cewa ‘A juri
zuwa rafi, watarana tulun zai fashe.’ To amma ko kaɗan
ban gamsu da azancin ba, gani nake yi fashewar tulu na waɗanda
ba sa lissafi ne, gani nake yi fashewar tulu na waɗanda
ba sa neman sa’ar Malamai ne, gani nake yi ni tuluna na ƙarfe ne wanda ko da faɗuwa
ya yi sai dai kawai na karkaɗe kayana na sake ɗauka.
Sai
dai babu zato babu tsammani na ga jami’an hukumar hana sha da safarar miyagun ƙwayoyi wato NDLEA a gaban motarmu, wasu
riƙe da bindigu, wasu riƙe da lafiyayyun sanduna. A she wai tuni sun
samu rahoton sirri cewa ina ɗauke da wasu kayan maye masu
nauyi, don haka suka shirya yi mini tara-tara suka ritsa ni.
Tunda
da ma suna da masaniyar cewa ina cikin wannan motar, irin yadda nama yake yi wa
gungumen wuta carbi a tukubar tsire, haka su ma suka yi wa motar ƙawanya.
Shugaban
jami’an yana murmushin zakin da ya rutsa barewa, hannunsa riƙe da wata zungureriyar bindiga ya zame
daga cikin rukunin ya ƙaraso
gaban motar, ya fara zagaya ta yana ƙare
wa kowa kallo ta cikin gilashin wundunan.
A haka har ya ƙaraso inda nake muka
haɗa
ido, kawai sai ya ce wa yaron motar ya buɗe
mini ƙofa na fito.
In
da a ce ni nake tuƙa
motar, to da babu abin da zai sa na tsaya su kama ni, a maimakon haka duk ta
kansu zan bi a guje na mutsittsike su. To amma tunda ba ni ba ne direba haka
ina ji ina gani na sauko, ya ce.
“Lallai
sai yau na ƙara gamsuwa idan
farauta ta so ka kana zaune sai ka kama gada, yau Rabiyu Kacalla babban dilan ƙwaya da tabar wiwi na ƙasa-da-ƙasa
ne ya shigo komata?”
Da
kallon benen wada na bi shi, ba tare da alamun tsoro ko fargaba ba na amsa.
“Ai
ba komarka na shigo ba ofisa, don na san ba za ka iya ɗaure
kashi ba sai dai ka ɓata igiyarka...”
“Rufe
mini baki!” Jami’in ya daka mini tsawar da ta sa na haɗiye
ragowar lafuzana. Da yake a goye nake da irin jakar nan ta ‘yan makaranta, sai
ya umarce ni da cewa na ajiye jakar a ƙasa
na buɗe ta
kowa ya ga me ta ƙunsa.
Da ma ni mabiyin fatawar kurege ne wajen gina gida da ƙofofin bigi-da-ka, shi ya sa na yi wata ƙofa ta basaja wacce na tabbatar iya
bincikensu hankalinsu ba zai taɓa kaiwa kanta ba har na guje
musu ta cikinta... Take na fara zazzage kayan cikin jakar hankali kwance, tunda
na san babu wani abu na rashin gaskiya da za su samu a cikinta ko a jikina.
Yadda
kaza take zumuɗin tono a jujin da take da yaƙinin samun kalace, haka na ga jami’in da aka saka ya binciki
jakar da kayan yana zumuɗi wajen bincika dukkanin
abin da yake ciki. Tashin hankali aka ce ba a saka masa rana, kamar yadda ni ma
nawa hankalin ya yi tashin tattabarun Ma’azu bagatatan...
Yanayin
yadda na ji wasu kwaɗuna da akuyoyi suna yin ƙugi a cikina shi ya tabbatar mini da
cewa lallai girgizar tumbi ake yi a cikin nawa kwatankwacin girgizar ƙasa. Budurwata, kuma ma’ajin sirrina Farida na hango
ta fito daga cikin motar jami’an
da take fake a gefe ta tunkaro inda muke. A raina tambaya nake yi me hakan ke
nufi? Ko da ma ita ma jami’ar
hukumar NDLEA ce? Ko da ma da ita aka haɗa
baki aka san sirrikana don a kama ni? Wataƙila
ma ita ta ba su masaniyar cewa ina cikin wannan motar ɗauke
da nannauyan kayan maye...”
Bahaushe
ya ce ‘Banda tuna baya, cewar gyartai da ya ci sarauta.’ Sai dai ni nawa bayan
idan aka tunano har ma aka rubuta shi, darasi ne ga duk wanda ya nazarta.
Musamman don gudun kada shi ma ya yi tsalle ɗaya
ya faɗa
rijiya irin yadda na yi, yayin da kuma tsalle dubu ya gagare ni iya fitowa.
Sau
tari mukan buƙaci ruwa don kashe ƙishi, tsananin buƙatar ruwan yakan sa mu sha da ciyawar da
ka iya zama mana illar da ba za mu fahimta ba sai lokaci ya ƙure. Da irin wannan salon rayuwata ta
fara, ni mutum ne mai matuƙar ƙishin ruwan yin sana’a, ko kaɗan
ban taso da ɗabi’ar zaman kashe wando ba, na fi son ɓarje
gumina kawai na samu abin rufa wa kai asiri. Wajen tabbatar da hakan ne kuma na
sha ruwa da ciyawar da nake faɗa ta yi mini sartse a maƙoshi.
Da
yake aikin ƙarfi nake yi, sau
tari idan na je ƙwadago
na dawo nakan tsinci kaina a matuƙar
gajiye, watarana ma tsubirin gajiyar yana iya hana ni tsinana abin kirki idan
na fita wani aikin washegari. Sila kenan da na fara zuwa kemis ina karɓar
maganin gajiya don kaucewa wannan yawan kasalar da mutuwar jiki, wanda hakan ya
zama kamar wani ruwan dare gama duniyar al’ummata, babu rubutun likita babu
komai suke yanke hukuncin irin maganin da za su je kemis su saya su sha.
Na fara fahimtar cewa hakan matsala ce a wata rana da muka karɓi aikin huɗar gonar wani likita Dakta Sulaiman. Kodayake
da bai yi niyyar bamu aikin ba, wai ya fi ƙarfin
mu shanu zai saka su huɗe masa saboda girman gonar.
Da ƙyar muka samu wani ƙaninsa abokinmu ya lallaɓa
mana shi ya bamu.
Shi
ya sa muka yiwa aikin nasa shiri na musamman, muka haɗiɗiyi ƙwayoyin ƙara
kuzari muka dinga gana wa gonar azaba don mu ba shi mamaki.
Da
ya zo ya ga yadda muka tona mata asiri kamar gardin da ya yi tunanin zai yi wa
yaro duka aka samu akasi yaron ya buga shi da ƙasa
haka yake kallon mu, ba na buƙatar
na tambaye shi, na san ya cika da tsananin mamakin aikin da ya ga mun fafaka
ne, aikin da yake ganin kamar ya fi ƙarfin
mutane sai motoci.
“Ina
ragowar abokan aikin naku?” Na ji ya fara yi mana tambayar da ta tabbatar da
zatona cewa aikin namu ya ba shi mamaki. Audu Lauje da sauran abokan aikin namu
suka bushe da dariya, ni kuwa dama na kai kunyata ta ƙarshe kenan, don haka na matsa cikin
inuwar wata bishiya na zauna na shiga fito da kayan aiki a aljihuna zan sake ɗuri.
“Kar
dai ka ce mini ba ka da lafiya ma ka yi wannan aikin?” Ya dawo da tambayarsa
gareni ganin na fara haɗiɗiyar
maganin gaɓa-gaɓa.
“Me
ka gani?” Na mayar masa da tambayarsa bayan na sake zaro maganin ciwo-takwas.
“Gani
na yi kana shan magani.” Ya ba ni amsa, sanadin da ya sa na yi dariya sannan na
ce.
“Wannan
ai ba maganin rashin lafiya ba ne, Ka Fi Ɗan’uwa Taya Aiki kenan.
Idan babu irin waɗannan magungunan ta yaya
zamu iya da irin waɗannan ayyukan?”
Ina
gani ya ƙwalalo ido kamar ya ga abin tsoro.
“Wannan
ai motar da za ta sauke ka a tashar shaye-shayen kayan maye ka shiga, magani ba
an yi shi ne domin a dinga shan shi kamar abinci ba, larura ce ke sanya amfani
da shi.” Ya ci gaba da cewa.
“Akwai
abin da a Turance ake kira da Drug Abuse da kuma Drug
Misuse. Idan masanin magani Famasist ya ba da magani, yana faɗan
adadin yadda za a sha maganin, lokutan da za a sha, da duk bayanin da ya kamata
mai amfani da wannan magani ya kiyaye. Rashin bin ƙa’idojinsa
ga mara lafiya, shi ne Drug misuse. Shi kuma amfani da magani don cimma
wata manufa ba rashin lafiya ba kamar dai yadda kake yi yanzu shi ake kira Drug
Abuse. Sannan kuma kowannen su akwai irin illarsa ga lafiya.
Su
irin waɗannan
magungunan da kake sha suna cikin waɗanda
ake iya samu kai tsaye ba tare da rubutun ƙwararre
ba, su ake kira da Over the counter drugs, amma ka sani, sayar maka ba
lasisin amfani da su ba tare da sani ko shawarar ƙwararru
ba ne a gareka.
Su
ne magungunan ciwo marasa alaƙa da
kitse wato NSAIDs, suna yin aiki ne ta hanyar dakatar da samar da
sinadaran da ke tunzura faruwar ciwo, ciki har da sanannen sinadarinnan ‘Prostaglandins’
(PG). Sai dai bayan tunzura ciwo wasu daga nau’o’in wannan sinadaran da su ƙwayoyin suke hanawa suna da matuƙar amfani ga jiki. Misali, bincike ya
nuna cewa ƙarancin PGI2&PGE2
da magungunan ke haddasawa yana haifar da ciwon ƙoda
na bagatatan Acute Renal Failure.Kusan wannan ya sa za ka ga da yawan
masu shaye-shayen ƙwayoyi
ciwon ƙoda ne yake yin ajalinsu, to don Allah
mene ne abin daɗi ko burgewa a shan abin da
a ƙarshe shi ne ajalinka?
Sannan
kada ka ɗauka
wai illar ta tsaya ne a iyaka ciwon ƙoda,
ƙarancin PGI2&PGE2 sanadiyyar yawan
amfani da irin waɗannan magungunan na daga
cikin manyan dalilan da kan iya haifar da cutar gyanbon ciki (Ulcer/PUD)...”
“Kuma
fa gaskiyarka! Don wallahi ina da olsa.” Audu Lauje ya katse shi.
“Ai
indai za ka jiɓinci shan waɗannan
magungunan ba bisa ƙa’ida ba, to ka tabbata kana
kira wa kanka matsaloli ne iri-iri waɗanda
idan ba ka yi sa’a ba su za su jawo ƙasa
ta rufe ka.”
Gaba ɗaya
sai muka shiga kallon-kallo a tsakaninmu, ban san abin da yake ran sauran
abokan aikin nawa ba, amma ni dai kam na ɗan
firgita da lamarin, don ko kaɗan ban shirya mutuwa da ƙuruciyata ba.
“Idan
kuma ba mu sha ba yaya za mu yi da gajiyarmu? Ta yaya za mu samu irin wannan
kuzarin mu fafata aiki?” Kamar ya san tambayar da ke raina kenan ya fara kawo
mafita.
“Ina
ba ku shawarar ku dinga bin komai a sannu, kada ku wahalar da jikinku ku ce
lallai sai kun gama aiki mai tarin yawa a rana ɗaya.
Bayan kun yi aiki kun gaji akwai buƙatar
ku dinga kwanciya kuna bacci jikinku ya samu hutu sosai, hakanan a maimakon kuɗin ƙwayoyin da kuke saya masu yawa, ku samu
kifinku na naira ɗari,
wata rana kuma sai ku nemi kayan marmari, insha Allahu garkuwar jikinku za ta ƙaru ku ji ƙarfi
ba sai kun sha ka fi ɗan’uwa taya aiki da kuke faɗa
ba.” Ya yi shiru yana kallon mu kamar mai yin nazarin ko mun gamsu, jin ba mu
tamka ba ya ci gaba.
“Ko
za ku sha magani to ku sha bisa ƙa’ida, amma idan har kuka ci
gaba da shan shi a haka ina jiye muku tsoron abin da ake kira ‘Drugs
Addiction’, ko kuma idan kun fara manyanta, garkuwar jikinku ta yi rauni ku
biya bashi...”
Tun
a wancan lokacin ya kamata na yi aiki da shawarar Dakta Sulaiman, to sai dai da
yake an ce wanda ya yi nisa ba ya jin kira ko kaɗan
ban yi amfani da shawarar tasa ba, wanda kuma ba na ko tantama silar ƙara taɓarɓarewar
komai kenan na zama cikakken ɗan marisa ba tare da na
farga ba.
Dakta
ya faɗi
wata kalma wai Drugs Addiction wacce
na so na tambaye shi ma’anarta na sha’afa, abin da ban sani ba a lokacin tuni
na gama lumewa har wuya a cikin rijiyar ma’anarta...
A
farkon lamari Ka Fi Ɗan’uwa ɗaya
yana iya yi wa batirina ful caji har ma na wuni zunbur ina yin aiki, sannu a
hankali kuma sai ya zamana cewa ɗaya
ya yi mini kaɗan ta yadda ko kistata ba ya iya yi wa
injin nawa. Hakan ta sa na fara afa biyu, waɗanda
su ma ba a ɗauki wani lokaci ba suka daina yi mini
tasiri. A haka na koma uku, na koma huɗu,
har ma na koma afa shi kamar na samu gyaɗa
marau-marau.
Kodayake
ina yawan tuno illolin da Dakta Sulaiman ya zayyano mini da shan ƙwayoyi ba bisa ƙa’ida
ba ke jawowa, kuma sosai ina so na daina sha ko zan kuɓuta.
To amma fa duk ranar da ban afa su ba wai ni don na daina, a ranar ba na iya
tsinana komai, don hatta lagwani sai ya shafa mini lafiya wajen kwanciya da
kasala. Ji nake yi ma kamar zan mutu idan ban sha ba, ta yadda duk inda yake
sai na je na nemo na afa.
Sai
a lokacin na fahimci lallai na yi wa kaina babbar illa na bar zane tun ranar
gini, don tuni na zama Addicted ɗin
da aka ce mini ma’anarta kenan.Sai na zama a irin yanayin gaba kura, baya
sayaki. Idan na sha na shiga uku, idan ban sha ba ma na shiga jalala.
Sannu
a hankali kirarin da nake yi wa maganin cewa ya fi ɗan’uwa
taya ni aiki sai ya tashi a banza, ya zamana cewa ko hambuɗar
shi zan yi kamar dambu ba ya taya ni aikin irin yadda yake yi mini a baya. To a
nan ne da na koka wa abokanan cin mushena suka tallata mini wasu sababbin kayan
aikin cewa na watsar da Ka Fi Ɗan’uwa na gwada su wai buƙata za ta biya. A nan na san wata ƙwaya DUNIYA LEBUR, a nan na san KANO A ƘAFA, a nan na san A YI NAN-A YI NAN da
wata ƙwaya wai ita SHA FARA KA GA ALJAN.
Ai
kuwa na ga aljan ɗin a ranar da na fara shan
ta, don kuwa abubuwan da aka ce mini ni ne na aikata su bayan na sha ta har
yanzu idan na tuno yadda nake da hankali da mutuncina a idon jama’a, gani nake
yi kamar ƙarya ake yi mini. Ni
da nake da tsananin kunyar da ko riga ba na iya cirewa a cikin jama’a, an ce a ranar zigidir na
yi haihuwar uwata ina ta kwarara ihu da sambatu marasa kan gado, don tsananin
abin kunya an ce wai sirikina da nake son ‘yarsa
shi ne da kansa ya yi mini dabara ya ɗan
sakaya mini tsiraicina da na kasa a faifai.
Abubuwa
biyu ne suka sa na ƙara
gamsuwa da abin da aka ce na aikata, na farko yadda na farka daga baccin da ban
san lokacin da na yi ba, na ga jikina ba kaya sai ɗan
wandon da sirikin nawa yaɗaura mini a ƙugunaɗaurin
bante. Na biyu kuma yadda na ga wasu da suka sha ƙwayar
a gabana wata rana su ma suna tamɓele.
Na
ga mijin da ya sha ya yi wa matarsa dukan kawo wuƙa
jami’ai suka kama shi, na ga ɗan
da ya sha ya yi wa iyayensa zagin tsamen nama suka ce ya je ya gani, na ga
direban da ya sha ya je ya yi hatsari da fasinjojinsa har ya kashe wasu, na ga ƙanin da ya sha ya farke yayansa da wuƙa a ciki ya mutu. Amma duk da haka don
rashin lissafi irin na ɗan’adam, mutum ba ya
hankalta, mu zame masa madubin gani-ga-wane ya gujewa shan ta, shi ma sai ya
afko cikinmu ya taya mu nadama
Haka mahaifiyata za ta saka ni a gaba, hawaye na ambaliya
daga ƙoramar saka tozalinta tana yi mini nasihar na nutsu na
daina shaye-shaye, amma tunda ba ta ɗauki ainahin hanyar gyaran irinmu bako na yi mata alƙawari ba na iya dainawar idan na kaɗaita.
Su kuwa jama’ar gari kullum tsakanina da su sai mugun
fata, babu mai tunanin yi mini addu’a ko ya ɗora ni a kan hanyar
da zan daina, don hatta Farida sanyin idaniyata, tunda mahaifinta ya ga irin taɓarar da na yi ranar
da na sha wannan ƙwayar ya raba ni da ita, ya yi mata
aure.
A daidai lokacin da kowa ke guduna ana ƙyamata aka daina ba ni aikin ƙarfin da nake yi kamar da, a daidai lokacin ne na haɗu da Musa Jagwado
dilan tabar wiwi wanda shi kuma ya ja ni a jiki sosai. Tunda
Ubangiji Ya halicci zuciya da son mai kyautata mata, irin yadda Jagwado ke
kyautata mini sai na mayar da umarninsa kamar ayar Allah.
A
wurinsa na koyi sha da dillancin tabar wiwi, har ƙasashen
ƙetare muke fita mu shirya auren bogi,
idan za mu tawo da amarya a cikin tawagar bogi mu saka kayan mayen da muka saro
lodi guda mu tsallako boda, don kuwa idan aka ga akwatunan aure da mata masu
rakiya, muna samun rangwame a mana kara ba tare da an binciki kayan ba.
Wani
lokacin kuma safayar tayar motarmu muke cire tub ɗin,
sai mu cika ta fal da miyagun kaya. Wani lokacin kuma kujerun motar muke
rarakewa mu yi musu riga mai zif mu loda kaya mu tsallako boda da su mu shigo
muna sayar wa da matasa muna gurɓata
musu tunani.
Muna
bin hanyoyi da dama wajen basaja, bugu da ƙari
kuma muna bin Malamai wajen neman asirin saɓani
da rufa ido. Shi ya sa na daɗe ina murza zarena yadda
nake so, bai taɓa tsinke mini ba sai da
Farida ta dawo cikin rayuwata a karo na biyu, bayan auren da ta yi na farko ya
mutu.
Mara
gaskiya ko a kan doki yake sai ya yi ɗingishi,
hakan
ce ta sa ina ganin Farida a ranar jikina ya fara ɓari.
Har sun gama duba jakata ba su samu wani abu na zargi da za su kama ni da shi
ba, amma ta harba roket ta ɓaro jirgina a matsayinta na
ma’ajin sirrina.
Da
ma tun da na ga ta fito daga motar jami’an ta nufi wajen kwandastan motarmu,
tana tambayar shi da me na hau motar bayan jakata, ya sanar da ita cewa na hawo
da ƙatuwar talabishin ɗita,
na san lallai tunɓur take so ta yi mini a
gaban jami’ai su kama ni. Ai kuwa sai aka buɗe
mata bayan motar, aka nuna mata ƙatuwar
talabishin ɗin.
Da ɗan
gari ake cin gari, ni ma da taimakon Farida aka ci ni da yaƙi. Ita ce ta saka jami’an suka fasa robar
talabishin ɗin, wacce na cire duk kayan cikinta na
loda kayan maye don kautar da tunanin masu tunani a kaina. Saboda ko tare ni
aka yi da ma ina da risitinta, shi nake nunawa na ce gyara zan kai ta, idan ta
kama ma nakan ɗan ba da eating nose na wuce.
A
haka suka ƙwale ni,
ni ɗaya ƙwal, a
cikin ƙwalleliyar
rana, ina ta ƙwalalo, ƙwala-ƙwalan
idanuwana, kamar ƙwale
ko
ƙwallon, ƙwaleliyar ƙwara...”
Ya
yi shiru ganin yadda ɗaliban da yake ba wa labari
suke kallon shi, na yadda ya jero luguden kalmomi da harafin ‘ƙwal’. Murmushin da ke kwance a
fuskar da yawansu shi ya tabbatar masa ya burge su. Ba tare da wani ya tamka ba
kuma ya ci gaba.
“Shi
ya sa duk rana irin ta yau 26 ga watan Yuni, majalisar ɗinkin
duniya ta ware domin yaƙi da
shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
A saboda haka ne kuma muke yawo makarantu don wayar da kan matasa a duk irin
wannan rana silar ba ku labarina kenan
don ku hankalta...”Ya sake yin gyaran murya ya ɗora.
“Akwai
masu ganin cewa duk wanda ya fara shaye-shaye ba zai iya dainawa ba, mutuwa ce
kawai za ta raba suya takalmin kaza. Abin da suka manta shi ne, babu cutar da
ba ta da magani, sai dai idan ba a san maganin ba.
Sahihin
maganin shaye-shaye kuwa shi ne a
kai mai yi gidan gyaran hali wato Rehabilitation Center. Sai dai da
yawan mutanenmu ba su waye da hakan ba, amma ita sanyin idaniyata Farida ta san
haka sarai, shi ya sa suka haɗa wata yarjejeni da jami’an
NDLEA suka kama ni.
A
maimakon su gurfanar da ni a Kotu sai suka ƙwace mini dukiyata, suka damƙa mata ni a matsayin dama ta ƙarshe, cewa ta gwada sauya ni zuwa mutumin ƙwarai kamar yadda ta yi musu alwashi
kafin ta taimaka musu. Saɓanin
haka kuma idan suka sake kama ni a gidan maza zan ƙarasa rayuwata. Da wannan damar ta yi
amfani ta ribace ni ta kai ni gidan gyaran hali.
Da
ma an ce so hana ganin laifi, son da nake yi mata ne, da kuma irin
kulawar da ta dinga ba ni ya taimaka mata tun ina jin haushinta har na dawo na
saduda.
A
gidan na ga yadda ake amfani da dabaru iri-iri wajen raba mutane da
shaye-shaye. A matakin farko akwai nasiha daga Malamai, bayan sun gama faɗa
mana abin da shari’a ta ce na haramcin kayan maye kuma, akwai addu’o’i da suke
yi mana na neman shiriya.
Daga
nan kuma akwai masana da suke amfani da dabara da iliminsu wajen sauya mana
tunani Cognitive Behavioural Therapy (CBT). A nan suka faɗa
mana illolin shaye-shaye ta yadda ni da kaina na
sake tsanar ɗabi’ar.
Sannan
kuma akwai magungunan da suka dinga ba mu, waɗanda
za su rage raɗaɗin
rabuwa da magungunan da muka saba da su Addicted.
Misali, amfani da Methadone ga waɗanda
suke amfani da Opioids irin su Codiene, Morphine da sauran su.
Su
kuwa masu shan barasa akwai irin maganin da na ga ana ba su, wanda indai har
sun sha shi to ba za su iya sake shan giyar ba. Idan suka sha kuwa a take za ka
ga suna ta amai, wasu kuma ciwon kai mai zafi ya rufe su, wanda kuma hakan ne
yake sakawa ta dole su haƙura
da ita idan suka ji a maimakon ta bugar da su tana saka su amai da ciwon kai.
Sunan maganin da ake ba su Disulfiram.
Akwai
maganin Benzodiazepines, shi kuma ana amfani da shi ne wajen saka mutane
bacci a lokacin da suke jin cewa indai har ba su cika tumbinsu da kayan maye ba
za su iya mutuwa, kamar dai irin yanayin da na ce muku ina ji idan ban hau
gajimare ba da farko.
Shi
ya sa indai an kai mai shaye-shaye gidan gyaran hali, kuma zai bayar da haɗin
kai dole ma ya daina yin shaye-shaye cikin ƙanƙanin lokaci. Saboda akwai iri-irin
hanyoyi da suke amfani da su masu tasiri sosai.” Ya sake yin shiru yana kallon
tarin matasan ɗaliban da yake ba wa labarin, bayan
gyaran murya ya ci gaba.
“Ku
ne matasa, ku ne ƙashin
bayan kowacce al’umma.
Idan kuka gyaru to al’umma
ta gyaru, idan kuka ɓaci ma al’umma ta ɓaci.
Don haka ahir ɗinku da yin shaye-shaye! Masu ɗauka
cewa akwai mafita a cikin yin shaye-shaye yaudarar kansu kawai suke yi, babu
wata mafita a cikinsa sai tarin illoli da nadamomi marasa ƙarshe. Zan
zayyano muku wasu kaɗan daga cikin illolin
shaye-shaye yanzu.
Shaye-shaye
yana hana haihuwa Infertility. Saboda aikin da sinadaran kayan mayen
kanyi akan sinadarin Gonadotropin hormone-releasing hormone(GnHR)
yana rage yawan sinadaran Luteinizing Hormone(LH) da Follicle-Stimulating
Hormone (FSH). da kuma na Testosterone.
Ko
kuma a dinga yinɓarin juna-biyun idan an
samu, ko a haifi yaron da wata illah,ko nakasu a jikinsa.
Shaye-shaye
yana rage garkuwar jiki, saboda da yawa daga cikin waɗannan
magunguna suna aiki akan ƙwayoyin
halittar garkuwar jiki na T-helperda kuma na T-Suppresor wanda
yake kawo raguwar garkuwar jiki, shi kuma idan garkuwar jiki yayi ƙasa to cututtuka da dama zasu iya shiga
jiki.
Shaye-shaye
yana kawo ƙanƙancewa da yin jajir na idanu, yana ma
rage ƙarfin gani na idanun. Hakan na faruwa ne
sakamakon illar da magungunan suke yi akan Occulomotor tare da
jijiyarsa.
Yin
shaye-shaye yana sa mutum ya yi ta bacci mara kan-gado kamar manja a sanyi, ya
yi ta yin alamomin hauka, kamar su soshe-soshe, tafiya a bauɗe
kamar ƙaguwa.
Ga
kuma illa ta zahiri da yake yi wa mutum a cikin al’umma, babu wanda zai yarda
da kai idan kana shaye-shaye balle har ya ba ka amana, ko ba kai ka aikata
laifi ba ana iya cewa kai ne tunda kai ake gani a mutumin banza mai haɗiɗiyar
KA FI ƊAN’UWA
TAYA AIKI, don haka matasa a kula. Na gode”
Yana gama jawabin ɗaliban suka hau yin tafi
cike da gamsuwa da bayanansa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.