Ticker

6/recent/ticker-posts

Warwarar Tubalan Ginin Turken Wakar Al’almajiri’ Ta Haruna Aliyu Ningi

Citation: Umma Ado ABBAS (2021). Warwarar Tubalan Ginin Turken Waƙar Al’almajiri’ Ta Haruna Aliyu Ningi. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 9, Issue 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

WARWARAR TUBALAN GININ TURKEN WAƘAR’ALMAJIRI’ TA HARUNA ALIYU NINGI

Na

Umma Ado ABBAS

Tsakure

Wannan takarda ta yi nufin yin nazarin tubalan ginin turke da Haruna Aliyu Ningi ya yi amfani da su a waƙarsa ta Almajiri wajen isar da manufarsa ga masu sauraro. Takardar ta samu jagoranci daga mazahabar waƙar baka Bahaushiya ta Gusau (2015). An yi amfani da hanyoyin bincike waɗanda suka haɗa da samo matanin waƙar kai tsaye daga wurin Haruna Aliyu Ningi. Takardar ta fito da muhimman tubala guda takwas (8) waɗanda Haruna Ningi ya yi amfani da su wajen gina manufar waƙar da kuma isar da saƙonsa ga masu sauraro.

Keɓaɓɓun Kalmomi: Warwara, Tubali, Turke, Waƙa, Almajiri, Haruna Ningi

1.0 Gabatarwa

Waƙa hanya ce da ake amfani da ita wajen isar da saƙo cikin sauƙi. Wannan ne ma ya sa a duk lokacin da ake son bayyana wani muhimmin saƙo ga al’umma, sai an bi ta hanyar waƙa. Za a fahimci haka idan aka yi la’akari da yadda mawaƙa suke taka rawa wajen bayyana manufar gwamnati da tallata wata haja da sanar da bikin ɗaurin aure da fito da abubuwa na wayar da kan al’mma da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum. Gusau (2003, sh. ɗiii) ya bayyana waƙar baka da cewa, “Zance ne na hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaituwa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da amshi”. Shi kuwa Satatima (1999, sh. 24) ya bayyana cewa waƙar baka ita ce, “Wadda ake rerewa don jin daɗi a ajiye ta a ka kuma a yaɗa ta da baka”. A wurin Mainasara (2016, sh. 9) yana ganin, “waƙar baka wani zance mai ƙunshe da azanci da ake shiryawa bisa wasu ƙa’idoji na musamman don isar da wata manufa ko saƙo ga al’umma”.

A wannan takarda an yi nazari ne a inda aka fito da tubalan ginin turke da Haruna Aliyu Ningi ya yi amfani da su a waƙarsa ta’Almajiri’ wajen isar da saƙonsa ga masu sauraro.

1.1 Taƙaitaccen Tarihin Haruna Aliyu Ningi

An haifi Haruna Aliyu Ningi ranar Talata 22/11/1972 a ƙauyen Rumbu da ke cikin ƙaramar hukumar Ningi ta jahar Bauchi. Haruna ya yi karatun allo a wurin mahaifinsa wanda a wurinsa ne ya sauke Alkur’ani, tare da karantar sauran littattafai waɗanda suka haɗa dai littattafan Fiƙihu da Hadisai da sauran littattafai na addini. An saka Haruna a makarantar firamare ta garin Rumbu daga shekarar 1977-1981. Ya samu nasarar shiga makarantar sakandire da take garin Bura daga 1981 zuwa 1986. Haruna ya ci gaba da karatu mai zurfi a makarantar Kimiyya da Fasaha da ke Ƙauran Namoda, a inda ya samu shaidar Dufuloma a ɓangaren harkokin kuɗi (Financial Studies) a shekarar 1996. Bayan gama karatun ne kuma sai ya faɗa harkar siyasa.

Haruna ya fara waƙa ne a shekarar 1996 a lokacin siyasar UNCP da DPN. Shahararrun waƙoƙin Haruna su ne waƙar “PDP jam’iyata” da “Ku faɗa wa Obasanjo; Mu kan ba mu yarda ta zarce ba” da kuma “Shegiyar uwa mai kashe’ya’yanta PDP” da sauransu. Haruna bai gaji waƙa ba domin mahaifinsa malami ne, to amma da yake Allah ya ƙaddara zai zama mawaƙi sai ya tsinci kansa a cikin harkar. Haka kuma ba wanda ya koya masa waƙa, kawai dai Allah ne ya haska tauraronsa, shi ya sa ma ba shi da wani wanda zai ce shi ne maigidansa a harkar waƙa, sai dai abokan hulɗa kawai. Amma kuma akwai mutumin da yake ganin da Allah ya haɗa su, to da ya zama uban gidansa ko da kuwa bai koya masa komai ba. Wannan mutumi shi ne Auwalu Isa Bunguɗu. Haruna makaɗi ne da yake aiwatar da waƙoƙinsa da kayan kiɗan zamani tare da’yan amshi a sitidiyonsa mai suna Baushe Media da ke garin Bauchi (Muhammad, 2019, sh. 4).

2.0 Turke a Waƙar Baka

Masana da manazarta da dama sun yi rubuce-rubuce a kan ma’anar turke. Daga cikinsu akwai, Gusau (2008, sh. 370) ya bayyana cewa turke na nufin, “Saƙon da waƙa take ɗauke da shi. Idan an ce saƙo kuma ana magana ne kan manufar da ta ratsa waƙa tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta: Wannan saƙon kuma yakan zo cikinta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kansa ba. Ashe ke nan, saƙon da makaɗi yakan zaɓa ya gina waƙarsa, ya tauye kansa da kansa ya zuba ɗiyanta bisa wasu zaɓaɓɓun kalmomi da za su doshi wata babbar manufa ɗaya, shi ake kira turke”.

Abba da Zulyadaini, (2000, sh. 45) sun bayyana jigo (turke a waƙar baka) da cewa: “Jigo[1] na nufin saƙon da mawaƙi yake so ya isar cikin waƙarsa ga jama’a”.

A nasa ra’ayin (Muhammad, 2012, sh. 65). ya bayyana turke da cewa shi ne: “Saƙon da makaɗi yakan zaɓa ya gina waƙarsa, cikin tsari bisa wasu zaɓaɓɓun kalmomi inda za a doshi wata babbar manufa ɗaya, shi ake kira turke.”

Daga waɗannan ra’ayoyi na mabambantan masana, a iya cewa turke na nufin manufar waƙa, wato saƙon da mawaƙi yake son ya isar ga masu sauraro.

2.1 Tubalan Ginin Turke

Tubalan ginin turke na nufin, wasu maganganu da aka bi aka ƙuƙƙulla waƙa da su don ta ƙara tsawo, amma ba su ne babbar manufar waƙar ba (Gusau, 2003, sh. 30).

Har ila yau, Gusau (2008, sh. 374) dangane da ma’anar tubali ya ci gaba da cewa:

A waƙoƙin baka na Hausa akan jajjefa wasu ƙananan maganganu na daban ƙari a kan wasu manyan manufofin da aka gina su a kansu. Makaɗan baka sukan yi amfani da waɗannan ƙananan zantuka ne su ƙuƙƙulla waƙa don ta ƙara tsawo, sai dai lalle ne su dace da babbar manufar waƙa. Sannan kowanne babban turke, akwai nau’o’in ƙananan turakun da suka dace da shi

Satatima (2009, sh82) da ya zo bayyana ma’anar tubali cewa ya yi:

Cikin hikima ne mawaƙan baka sukan zaɓi turken waƙarsu su kuma ƙayatar da shi ta amfani da ƙananan turaku wato tubalan ginin turke, ko kuma raɓa dannin turke kamar yadda wasu sukan kirasu. Alal misali idan waƙa turkenta yabo ne, to sai ka ga mawaƙi ya taɓo nasaba da riƙo da addini da kyauta ya lanyace wannan yabo nasa da shi.

Dangane da ma’anonin da masana suka kawo, a iya cewa tubali na nufin ƙananan saƙonni da mawaƙan baka kan yi amfani da su a cikin waƙoƙinsu domin taimakawa wajen fito da babban turke. Kaɗan daga cikin tubalan akwai yabo, zambo, habaici, zuga, kirari da makamantansu.

2.2 Bayani a Kan Almajiri

Asalin kalmar’Almajiri’ ta samo asali ne daga harshe Larabci wato ‘‘Al-muhajiri’ da take nufin wanda ya yi hijira daga wani wuri zuwa wani wurin. Wannan shi ne sunan da ake kiran Sahaban Manzo (S.A.W) da suka yi ƙaura daga Makka zuwa Madina. A ma’ana ta zahiri kuwa almajiri shi ne mutumin da ya ƙaura daga garinsu zuwa wani wuri da nufin ya yi karatu, tare da sauke Kur’ani mai tsarki. Wannan tsari na almajiranci ya fara tun lokaci mai tsawo da ya wuce a inda Hausawa da Fulani suke tura’ya’yansu makarantar allo don su haddace Alkur’ani da sauran littattafan ilimi (Mashema da Idris da kuma Musa, 2018, sh. 1).

Mashema da Idris da kuma Musa (2018, sh. 1) suka ci baba da cewa, “Tasirin karatun Alkur’ani na almajiranci a ƙasar nan ya fara ne a ƙarni na goma sha ɗaya, a wannan lokaci masarautun Borno da na Sakkwato suka samar da makarantun allo a inda ake karantar da karatun Kur’ani. Masarautun nan (Borno da Sakkwato) sun taka rawa wajen koyar da Kur’ani. Da yawa daga cikin mashahuran malaman arewacin ƙasar nan da kuma wasu ɓangarori na Afirka sai da suka yi karatu a irin waɗannan makarantu na allo kafin su zama’Hafizai’ (waɗanda suka haddace Kur’ani).

3.0 Hanyoyi da Dabarun Gudanar da Bincike

Kowane irin bincike na ilimi da za a gudanar akan zabi hanyoyi da dabaru da ake yin amfani da su domin ganin wannan bincike ya kai ga samun nasara. Hanyoyi da dabaru da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike sun haɗa da samo matanin waƙar, kuma daga bisani aka juye ta a rubuce domin samun sauƙin nazari. An tattauna da makaɗi Haruna Aliyu Ningi a inda aka yi masa tambayoyi a kan abin da ya shafi waƙar.

Ningi ya bayyana cewa ya yi wannan waƙa ne saboda ya jawo hankulan Gwamnoni su gane cewa hana almajiranci ba shi ne mafuta ba. Ya aiwatar da waƙar ne a situdiyonsa mai Suna Baushe Media da ke garin Bauchi. Waƙar tana da ɗiya guda goma sha uku (13).

4.0 Tubalan Waƙar Almajiri ta Haruna Aliyu Ningi

Haruna Aliyu Ningi ya yi amfani da tubala mabamabanta a waƙar almajiri domin samun sauƙin isar da saƙon da ta ƙunsa ga masu sauraro. Daga cikin tubalan da ya yi amfani da su akwai:

4.1 Mai da Martani

 Martani na nufin magana ko jawabi a kan wani abu da wani ya yi. Dubi yadda Haruna Aliyu Ningi ya mayar wa da gwamnoni maratani a kan ƙudurinsu na hana almajiranci a jahohinsu. Ga abin da yake cewa:

 Jagora: Ni almajiri ne,

: Kai ma almajiri ne,

: Kuma almajirai ne,

: Ai waƙar almajiri ce,

: Gwamnoni kun ji kunya,

: Kuna sukar almajiranci.

: Amma kuma ga jaharku,

: Ana buga harkar karuwanci.

(Haruna Ningi: waƙar’Almajiri’ ɗa na 1).

A nan Haruna ya mayar wa da gwamnonin Arewacin Nijeriya martani ne a kan ƙudirinsu na hana bara (almajiranci) a jahohinsu, alhalin sun kyale abubuwan da suka fi almajirancin illa kamar su karuwanci ana gudanar da su a jahohinsu. Haruna ya fito ƙarara ya nuna wa gwamnonin cewa sun ji kunya, sun bar abubuwan da suka saɓawa al’adu da ɗabi’un Hausawa da ma addinin Musulunci ana gudanar da su a jahohinsu, amma kuma suna ƙoƙarin hana almajiranci.

4.2 Asali

 CNHN (2006, sh. 20) ya bayyana kalmar asali da cewa tana nufin “mafari ko tushe ko salsala”. Haruna Ningi a ƙoƙarinsa na fito da manufa da saƙon waƙar ya bayyanaa abin da ake nufi da almajiranci, da yadda aka sami sauye-sauyen zamani a kan tsarin na almajiranci, a inda yake cewa:

 Jagora: Farko ga tambaya mu ji menene almajiranci?

: Daga kan almajiri aka san kalmar almajiranci,

 ‘Y/Amshi: Shi ko almajiri mabiɗin ilimi ne in ka gan shi,

: Kuma ko da taimako ne sai in kai ra’ayi ka ba shi.

 Jagora: Wasu ne suka ɓata harkar,

: Masu jidon yara ƙanana,

: Su saka su bara a titi,

: Wai haka ɗin sun ɗau amana,

(Haruna Ningi: waƙar’Almajiri’ ɗa na 3-4)

A nan makaɗi Haruna Ningi ya fito da asalin menene almajiranci ta samu ne daga almajiri, sannan kuma almajiranci hark ace ta neman ilimin addinin Musulunci. Haka kuma ya ci gaba da sanar da masu sauraro cewa almajiri bai tilasa wa mutane su taimaka ma sa ba, har sai in suna da ra’ayi na su taimaka masa. Amma sai wasu suka ɓata wannan harka ta almajirancin a inda suke ɗauko yara ba tare da damuwa da ci da sha da makwancinsu ba. Suka sake su kawai a gari kwararo-kwararo suna bara.

 4.3 Shawara

CNHN, (2006, sh. 411) ya bayyana ma’nar shawara da nasiha ko tattaunawa a kan wasu matsaloli tsakanin mutum biyu ko fiye. A ƙoƙarin Haruna na isar da saƙon waƙar ya ba da shawara a kan yadda za a gyara harkar almajiranci kamar haka:

 ‘Y/Amshi: E! Lalle na fahimta ta nan haka illar ta fara,

Sai dai ko mai ya faru abin da ya dace sai a gyara,

: Kwarai!

 Jagora: Ni ma na yarda a gyara ya fi ya fi a ce a rusa,

: Gyaran abu in ya ɓaci a nan sai mai hange na nesa,

: Domin in za a gyara za ai don an ba da amsa.

 (Haruna Ningi: waƙar’Almajiri’ ɗa na 5)

A nan Haruna yana ba wa gwamnoni shawarar cewa duk lallacewar da harkar almajiranci ya yi, bai kamata a hana yin sa ba, maimakon a hana gwanda a zauna a yi nazarin abubauwan da suka sa harkar ta lallace a gyara su. Haka kuma yana nuna in za a yi gyaran sai an kalli harkar da idon basira kafin a kai gyara ta.

4.4 Nuna Takaici

CNHN (2006, sh. 420) ya bayyana takaici da jin haushi wanda ɓacin rai yakan kawo. Haruna Ningi ya nuna takaicinsa na yadda gwamnoni suka kau da kansu a kan abubuwan alfasha da ake aikatawaa a jahohinsu, suka tsangwami harkar almajiranci. Ga abin da ya ce:

 Jagora: Abin ne babu tsari,

: Babu kishi,

: Babu darajawa,

: Ba mutunci,

: Mun yarda bara a daina,

: Tun da a tsari ta haramta,

: Amma almajiranci kar a hana don ya halarta.

 (Haruna Ningi: waƙar’Almajiri’ ɗa na 7)

A wannan misalin da aka kawo na ɗan waƙar da ya gabata, Haruna Aliyu Ningi ya nuna takaicinsa a kan yadda gwamnoini suke son su kawo tasgaɗo a kan harkar almajiranci alhali ga abubuwan alfasha nan ana aikatawa, amma ba ɗau mataki a kai ba. Haka kuma ya nuna yadda yake ganin rashin tsari da kishi, sannan kuma ba daraja da mutunci a cikin hana harkar almajiranci. Tsari a nan na nufin rashin dacewa. Kishi kuwa shi ne rashin tsayawa da nuna ƙwazo a kan wani abu. Daraja kuwa tana nufin rashin girmamawa. Ita kuwa kalmar mutunci a nan tana nufin halin girma. Haruna ya yi amfani da waɗannan kalmomin ne duk don ya nuna takaicinsa a kan yadda gwamnoni suka tsangwami harkar almajiranci.

4.5 Habaici

Habaici shi ne yin amfani da wasu kalmomi a fakaice don a musgunawa wani, a ɓata masa rai, ya ji haushi. A wajen yin habaici ba a fitowa fili a nuna da wanda ake yi, sai dai a yi amfani da kalmomin sakayawa irin su’wane’ da’wani’ da’wasu’ da sauransu (Muhammad, 2019, sh 121). Ga misali inda Haruna Aliyu Ningi ya yi habaici a waƙarsa ta Almajiri kamar haka:

Jagora: Gwamnonin nan da sata sun ɗara ɓeraye aradu,

: Su dai su gani su ɗauka ,

: Hakkin kowa su taka,

Wani gwamna har da duka,

: Wai ai shi ba yi shakka,

: Sun girma a cin amana,

: Masu idanun dubarudu.

 (Haruna Ningi: waƙar’Almajiri’ ɗa na 8)

ƙoƙarin Haruna Ningi na isar da saƙon waƙarsa, a nan ya yi wa wani daga cikin gwamnonin Arewa habaici, a inda yake nuna masu sauraro cewa har dukan mutane yake yi. 

4.6 Yabon Ubangiji

Yabo shi ne ambaton kalmomin sambarka da nufin nuna amincewa da hali ko wani abin da mutum ya yi nagari. Ko kuma a iya cewa yabo wani lafazi ne da ake yi ga wani mutum domin a nuna halayensa da siffofinsa kyawawa da cewa abin so ne kuma abin ƙauna ne. (Gusau2008, sh. 376). Ubangiji kuwa shi ne mahaliccin komai, wato Allah (CNHN, 2006, sh. 14). Ke nan yabon ubangiji shi ne yin amfani da lafuza masu daɗi wajen nuna girmansa da buwayarsa da adalcinsa da sauransu. Haruna Aliyu Ningi ya yi amfani tubulin yabaon ubangiji wajen gina turken waƙar kamar haka:

 Jagora: Shi Allah adali ne,

: Kuma mai son mumini ne,

: Mai ƙyamar kafiri ne,

: Bai kunyar fasiƙi ne.

(Haruna Ningi: waƙar’Almajiri’ ɗa na 11)

A wannan ɗan waƙa da aka kawo a sama Haruna Aliyu Ningi ya yabi Allah (S.W.T) ha hanyar yi masa kirari, ya fito da sifofinsa, ta amfani da kalmomin yabo waɗanda suka haɗa da adali da son muminai da ƙyamar kafir, sannan kuma ba ya kunyar faskiƙi. Adali na nufin mai adalci. Shi kuwa mumini yana nufin wanda ya ba da gaskiya da Allah, ya kuma ke bin dokokin Musulunci. Kafiri kuwa shi ne wanda bai yarda da addinin musulunci ba. A inda kuma yake nufin ashararin mutum ko mai yawan yin aikin assha. Haruna Aliyu Ningi ya yi amfani da waɗannan kalmomin ne, ya yabi Allah ta hanyar fito da wasu siffofinsa.

4.7 Addu’a

CNHN (2006, sh. 3) ya bayyana addu’a da roƙon Ubangiji. Ke nan addu’a ita ce roƙon Allah ya biya mutum buƙatarsa. Haruna Aliyu Ningi ya yi amfani da tubulin addu’a a ƙoƙarinsa na miƙa saƙon waƙar ga masu sauraro. Ga abin da yake cewa:

 ‘Y/Amshi: Addu’a ce za mu yi ta,

: A kan kowane azzalumi ne,

: Ko da kuwa malami ne,

: Ko da mai unguwa ne,

: Sarki, attajiri ne,

: Ko mai mulkin jaha ne,

 Jagora: Ko mai mulkin ƙasa ne,

: Ko ko jami’in tsaro ne,

: Kowa ya rufe gun ibada,

: Saboda Coronar kasuwanci,

: In har mai shiryiwa ne,

: Jirgin sama in yah au, ka kaɗo wannan jirgin ya ƙone,

: In mota ce ya hau ka kifar wannan mota ta ƙone,

: In babur ne ka sa shi ya kama wuta shi ma ya ƙone,

: In bai da abin hawa, a cikin ɗaki nai ya ƙone.

(Haruna Ningi: waƙar’Almajiri’ ɗa na 12)

A nan Haruna Aliyu Ningi ya yi addu’a ne a inda yake roƙon Allah da ya hukunta duk wanda yake da hanu wajen hana yin Sallah a watan Azumi saboda cutar Corona, ko da kuwa wannan mutumin malami ne ko mai unguwa ko sarki ne shi ko mai kuɗi ne ko kuma gwamna ko shugaban ƙasa. Haka kuma Haruna ya yi masa addu’ar shiriya in har zai shiryu, in kuma bai shiryu ba Allah ya hukunta shi da irin abubuwan da ya jero a ɗiyan waƙar tasa.

4.8 Faɗakarwa

Faɗakarwa na nufin gargaɗi ko nasiha ko kuma ilmantarwa ko tarbiyantarwa tare da wayar da kai ko hannunka-mai sanda gami da tunasarwa (Kurawa, 2019, sh. 88). Ga abin da Haruna yake cewa a wani misali na ɗan waƙar kamar haka:

 Jagora: A hana mana jam’i a cikin Ramadan ai isgili ne,

: Saƙon farko ku ji shi,

: Kafin Coɓid 23 ta iso,

: Mu ci…... Uhmmmmm!!!

 (Haruna Ningi: waƙar’Almajiri’ ɗa na 13)

A nan Haruna yana yi wa waɗanda suka hana yin jam’i a watan Azumi saboda cutar Corona Ɓirus hanunka-mai-sanda, a inda yake gaya musu cewa abin da suka yi isgilanci ne, sannan kuma za su gane kuransu a zaɓen shekara ta 2023.

5.0 Kammalawa

Kamar yadda bayanai suka gabata a wannan takarda, an yi nazari ne dangane da yadda Haruna Aliyu Ningi yake amfani da mabambanta tubala waɗanda suka haɗa da mai da martini da asali da nuna takaici da shawara da habaici da yabon Ubangiji da addu’a kuma faɗakarwa wajen isar da manufar waƙarsa. A cikin takardar an kawo bayani kan ma’anar turke da tubalan ginin turke da kuma bayani a kan almajiri. An yi amfani da hanyoyi da dabaru waɗanda suka haɗa da samo matanin waƙar da hira da makaɗi Haruna Aliyu Ningi. Haka kuma an kawo misalai na waɗannan tubala tare da yin sharhinsu.

Manazarta

Abba, M. & Zulyaidaini, B. (2000). Nazari kan waƙar baka ta Hausa. Gaskiya Corporation Company.

CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa na jami’ar Bayero. Ahmadu Bello University Press.

Gusau, S. M. (2003). Jagoran nazarin waƙar baka. Benchmark Publishers.

Gusau, S.M. (2008). Waƙoƙin baka a ƙasar Hausa: yanaye-yanayensu da sigoginsu. Benchamark Publishers.

Gusau, S.M. (2011). Adabin Hausa a sauƙaƙe. Century Rearch and Publishers.

Gusau, S. M. (2014). Waƙar baka bahaushiya, Bayero University.

Gusau, S. M. (2015 A). Abdu Karen Gusau. Century Research and Publishing.

Haramde, M. M. (2014). The practice of almajiri: Prospect and socio-medical challenges in Northern part of Nigeria. Journal of African studies and Deɓelopment, 6 (7), 128-131.

Hussaini, B. (2009). Haruna Aliyu Ningi da wasu waƙoƙinsa. Ramadan Press.

Kurawa, M. A. (2019). Nazarin turke da awon baka a waƙoƙin Asharalle a Jahar Katsina. [Kundin digiri na Biyu]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeirya, Jami’ar Bayero, Kano

Lawal, N. (2016). Nazarin waƙoƙin makaɗan bege na Hausa. [Kundin Digiri na Biyu]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano

, B. L. & Idris, A. I. & Musa, Y. (2018). The chellenges of amajiri system of education to social peace Mashema in Nigeria: A cross-sectional inɓestigation. International Journal of Innoɓatiɓe Research and Adɓance Studies, 5 (8), 44-50.

Muhammad, A.S. (2012). Nazarin ayyukan makaɗa Sa’idu Maidaji Sabon Birni (1938-2000). [Kundin Digiri na Biyu]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Afrika. Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya

Muhamamd, H. I. (2019). Nazarin adon harshe a waƙoƙin sarauta na Haruna Aliyu Ningi. [Kundin Digiri na Biyu]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero, Kano.

Satatima, I. G. (2009). Waƙoƙin ɗarsashin zuciya na makaɗan baka. [Kundin digiri na Uku]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeirya, Jami’ar Bayero, Kano

Saulawa, B.S. (2017). Nazarin turken yabo a waƙoƙin Hafsatu Garba Nijar[Kundin Digiri na Biyu]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano

Taiwo, F. J. (2013). Transforming the almajiri education for the benefit of Nigerian society. Journal of Education and Social Research, 3 (9), 67-72

UsmanA. (2017). Tarkakken nazarin wasu waƙoƙin Sadiƙ Zazzaɓi[Kundin Digiri na Biyu]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero, Kano

Usman, H.S. (2016). Nazarin turken ta’aziyya a waƙoƙin Dr. Mamman Shata Katsina[Kundin Digiri na Biyu]. Sashen Koyar da Harsunan NijeriyaJami’ar Bayero.

Rataye na Ɗaya: Matanin Waƙar Almajiri

 Jagora: Ni almajiri ne,

: Kai ma almajiri ne,

: Kuma almajirai ne,

: Ai waƙar almajiri ce,

: Gwamnoni kun ji kunya,

: Kuna sukar almajiranci.

: Amma kuma ga jaharku,

: Ana buga harkar karuwanci.

 Jagora: E! Allah Rabbi Allah,

: Da ka sa mu mu dinga Sallah,

: Kai wa Manzo kamala,

 ‘Y/Amshi: Kwarai,

 Jagora: Da Sahabbai nai jimilla,

 ‘Y/Amshi: Na’am,

 Jagora: Ka hana mu da yin baɗala,

 ‘Y/Amshi: Kwarai,

 Jagora: Maganar ba ƙila-ƙala,

: Ga zance sala-sala,

 ‘Y/Amshi: Faɗi,

 Jagora: Da na ɗauko ba kasala,

: Wa za ya tayan in cilla,

: Ya iso har gun amilla,

: Gwamnoni kun ji kunya,

: Kuna sukar almajiranci.

: Amma kuma ga jaharku,

: Ana buga harkar karuwanci.

 ‘Y/Amshi: Subhanallah,

 Jagora: E!

 Jagora: Farko ga tambaya mu ji mene ne almajiranci?

: Daga kan almajiri aka san kalmar almajiranci,

 ‘Y/Amshi: Shi ko almajiri mabiɗin ilimi ne in ka gan shi,

: Kuma ko da taimako ne sai in kai ra’ayi ka ba shi.

 Jagora: E!

 Jagora: Wasu ne suka ɓata harkar,

: Masu jidon yara ƙanana,

: Su saka su bara a titi,

: Wai haka ɗin sun ɗau amana,

 ‘Y/Amshi: E! Lalle na fahimta ta nan haka illar ta fara,

: Sai dai ko mai ya faru abin da ya dace sai a gyara,

: Kwarai!

 Jagora: Ni ma na yarda Yaya a gyara ya fi a ce a rusa,

: Gyaran abu in ya ɓaci a nan sai mai hange na nesa.

 Jagora/’Y/Amshi: Domin in za a gyara za ai don an ba da amsa.

 Jagora: Makarantun ne na boko wa ya gina musu ne y aba su?

 ‘Y/Amshi: Ah to!

 Jagora: Gwamnati ce ta yi su,

: Sannan da kuɗin ƙasarsu,

 ‘Y/Amshi: Kwarai!

 Jagora: Bayan haka tai asusu,

: Da ta ɗauki ma’aikata da duka wata sai ta biya su,

 ‘Y/Amshi: Kundin mulkin ƙasarsu,

: Yin zaɓi shi ya ba su,

: Amma almajirai aka ƙi su a kan sun zaɓi nasu,

 Jagora: Ayya!

 ‘Y/Amshi: Amma kuma Jonathan ya yarda da su ɗin’yan ƙasa ne,

: Kuma dole suna da hakki za a kula su kamar su wane,

: Bayan yai makarantu sai suka wai kyale arne,

: To ai su kafirai ne sun ɗara kowane arne,

 ‘Y/Amshi: Kwarai!

 Jagora:’Yan kut……..

 ‘Y/Amshi: Haruna tsaya haka ban da zagi.

 Jagora: Abin ne babu tsari,

: Babu kishi,

: Babu darajawa,

: Ba mutunci,

: Mun yarda bara a daina,

: Tun da a tsari ta haramta,

: Amma almajiranci kar a hana don ya halarta.

 ‘Y/Amshi: Ɗanningi bugu da ƙari su ma sai sun daina sata,

: Domin illa ta sata ta fi bara girman haramta,

 Jagora: Ka gani.

 Jagora: Gwamnonin nan da sata sun ɗara ɓeraye aradu,

: Su dai su gani su ɗauka ,

: Hakkin kowa su taka,

: Wani gwamna har da duka,

: Wai ai shi ba yi shakka,

: Sun girma a cin amana,

: Masu idanun dubarudu.

 ‘Y/Amshi: Ai na gane shi mungu ɗan kuturu mai hura hanci,

: Don na ji yana faɗin sun rusa shirin almajiranci,

 Jagora: Amma kuma ga jaharsa,

: Ana buga harkar karuwanci,

: Shan maye ga kawalci,

: Bayan harkar dabanci.

 Jagora: Sun zo da Corona Ɓirus sun hana kowa kasuwanci,

: Domin sun zo da nasu su Da’u iyayen fasiƙanci,

: Sun kulle gidan ibada ka ji irin ɗanyan hukunci,

: Ku ma sun kulle kasuwanni, sun rufe gun harkar fatauci,

: Sun bar jama’a da yunwa

: Ba sunna babu aya,

: Ba sisi babu hanya

: Ba sa da Corona jinya,

: Wannan abu ya ƙazanta an shiga mummunan talauci,

 Jagora: Shi Allah adali ne,

: Kuma mai son mumini ne,

: Mai ƙyamar kafiri ne,

: Bai kunyar fasiƙi ne.

 ‘Y/Amshi: Addu’a ce za mu yi ta,

: A kan kowane azzalumi ne,

: Ko da kuwa malami ne,

: Ko da mai unguwa ne,

: Sarki, attajiri ne,

: Ko mai mulkin jaha ne,

 Jagora: Ko mai mulkin ƙasa ne,

: Ko ko jami’in tsaro ne,

: Kowa ya rufe gun ibada,

: Saboda Coronar kasuwanci,

: In har mai shiryiwa ne,

: Jirgin sama in yah au, ka kaɗo wannan jirgin ya ƙone,

: in mot ace ya hau ka kifar wannan mota ta ƙone,

: In babur ne ka sa shi ya kama wuta shi ma ya ƙone,

: In bai da abin hawa, a cikin ɗaki nai ya ƙone.

 Jagora: A hana mana jam’i a cikin Ramadan ai isgili ne,

: Saƙon farko ku ji shi,

: Kafin Coɓid 23 ta iso,

: Mu ci……. Uhmmmmm!!!



[1] Jigo ko turke suna magana ne a kan manufa ko saƙon da waƙa ta ƙunsa. Jigo kamar yadda masana suka kawo ya shafi rubutacciyar waƙa ne, shi kuwa turke ya shafi waƙar baka kamar yadda Gusau (2003) ya kawo. Amma a wurin Abba da Zulyadaini (2000) sun kalli jigo a manufar rubutacciya da kuma waƙar baka.

 Yobe Journal

Post a Comment

0 Comments