Citation: Tijjani SALISU & Abubakar BABANGIDA (2021). Harshe Da Mu’amala A Wajen Ƙasar Hausa: Bunƙasar Kalmomin Cinikayya A Cikin Kasuwar Gashuwa. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 9, Issue 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
HARSHE DA MU’AMALA A
WAJEN ƘASAR HAUSA: BUNƘASAR KALMOMIN CINIKAYYA A CIKIN KASUWAR GASHUWA
Na
Tijjani SALISU
Abubakar BABANGIDA
Tsakure
Wannan muƙalar ta ƙudurianiyar gano tasirin harshen Hausa a kan wasu harsuna a
wajen ƙasar Hausa musamman ma ta hanyar bunƙasar ko ƙirƙirar wasu kalmomin Hausa a cikin harkokin kasuwancin mutanen
Gashuwa”. Muƙalar ta ɗauki aikin Yakasai (2012) abin kwatanci ga wannan aiki. Wannan
bincike ya yi amfani da hanyar ganawa ta kai tsaye da ‘yan kasuwa a ɗaiɗaikunsu tare da amfani da lura da su a fakaice
wajen tattaro bayanan wannan aiki. Daga cikin abubuwan da wannan muƙala ta bankaɗo sun haɗa da ire-iren kalmomin fannu da ɓangarorin yan kasuwa ke amfani da su wajen harkokinsu na yau da
kullum tare da fashin baƙin waɗannan kalmomin. Daga
cikin abin da sakamakon wannan bincike ya gano su ne, lallai suna amfani da
kalmomin da sai su ya su ne, da masu mu’amala da su ne suke fahimtar me ake
nufi. Misali; Talla tana nufin doguwar mace da muhammadiyan tana nufin yin
sassauci da kayan ruwa yana nufin maganin ruwa na yara; haka ma kalmar lami na
nufin bashi, yayin da kalmar tare na ne, ke nufin mai latsi ne ba mai saye ba;
muƙalar ta gano cewa Hausar da ake amfani da ita a
cikin gari ta bambanta da ta ‘yankasuwa, a cikin kasuwar ma, kowanne rukuni
kalmominsu sun bambanta da juna.
1.0 Gabatarwa
Idan ana magana game da
ainihin asalin ƙasar Hausa za a iya lalubo ta a cikin Afirika ta
yamma, wato farfajiyar nan da ke tsakanin dazuzzukan da ke kurkusa da gaɓar tekun atilantika daga kudu cikin Nigeriya zuwa hamadar sahara a
Arewa. Ƙasar Hausa tana nan idan aka duba taswirar
Afirika za a samu ƙasar Hausa a tsakanin layi na goma sha biyar
(15N) zuwa na goma sha takwas (18N) na Arewa da ikwaita, kuma ƙasar tana tsakanin layi na takwas na (8E) da na goma sha biyu
(12E) a Gabas da layin Greenwhich (Adamu, 1997, sh, 11).
A bisa bayanan da suka
gabata za mu iya cewa ƙasar Hausa a yau tana nan a cikin Afirika ta
yamma a arewaci Nijeriya kuma akwance taketa taɓo har cikin ƙasar Njar wajen su maraɗi da wasu yan garuruwa,
haka ma daga gabas ta yi iyaka da tsuhuwar jihar Borno (wanda ya haɗa da jihar Yobe da wasu ɓangarori na kudancin
jihar Bauchi) daga yamma kuwa ta yi iyaka da ƙabilun gwari da kuma ƙabilun kudancin
Zariya. Ƙasashen Hausawa kuwa sune kamar su kano,
sakkwato, Katsina, Daura da Zariya da ma arewacin jihar Bauchi. Cikin Njar kuwa
alwai su Damagaram, Dogon Dutse, Kwanni da sauransu (db Abubakar 1983)
Dangane haka duk inda bai
faɗa cikin wannan farfajiyar da masana suka ambata
ko zayyana ba to lalle ne yana wajen ƙasar Hausa musamma ma
nan yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya in ban da Arewacin jihar Bauchi.
Saboda haka duk wurin da
aka samu jama’a, za a tarar ana mu’amala iri-iri a wurin. Kuma babu yadda za a
yi mu’amala ta kasuwanci ba tare da harshe ba. Saboda haka, ta tabbata cewa
harshe da al’umma da kuma mu’amala da kasuwanci tamkar jini ne da tsoka. A
harkar kasuwanci, ɗaya ba ya tafiya ya bar ɗaya. Kuma ya zama wajibi idan al’ummai suka haɗu da nufin kasuwanci, ta sanadiyar keɓanta, dole a samu bambancen kalmomin rukuni a tsakanin su.
Yahaya da wasu, (1992) sun bayyana kasuwanci da cewa, hanya ce ta
amfani da azanci da hikima a sarrafa albarkatu da ni’imomin da ɗan adam ya mallaka don tunanin yau da kullum.
CNHN, (2006) cewa aka yi, harshe hanyar magana ce tsakanin al’umma
iri ɗaya. Shi kuwa Yakasai, (2012, sh. ɗɓi) ya ƙara tabbatar da cewa harshe mahimmiyar kafa ce
ta sadarwa cikin zamantakewa. Wato idan aka yi amfani da harshe a wajen
sadarwa, to shakka babu za a samu yana damɓare da al’ada ta hanyoyi
daban-daban. Shi kuwa Hornby, (1948) a cikin Yakasai (2012) cewa ya yi
al’umma ɗaukacin mutane ne da kuma al’ada da ɗabi’u iri ɗaya.
Za mu iya tabbatar da cewa,
kasuwanci ba ya yiwu wa sai da harshe da al’umma da kuma mu’amala. Dandazon
jama’a ne ke haɗuwa wuri guda, ya Allah ƙabilu guda ko kuma ƙabilu mabambanta domin
cim ma manufa ta wani ɓangaren rayuwa. Cuɗayar kuwa, tana
kasancewa a rukuni daban-daban a tsakanin su. Saboda haka, wannan takarda,
ta ƙudirci bayyana yadda lamarin ke kasancewa a
kasuwancin mutanen Gashuwa. Al’ummar wannan wuri suna amfani da Hausa a
matsayin harshen kasuwanci da ma wasu ɓangaririn rayuwa. A
dalilin keɓewa da suke yi, ya haifar da yin amfani da wasu
kalmomi waɗanda kowane rukuni da nasu, kuma sai su kansu da
masu mu’amala da su ne ke fahimta.
1.1 Ma’anar Harshe
A kulli yaumin magana muke
yi, ya Allah da fatar baka ko a rubuce ko kuma ta hanyar ishara duk domin isar
da saƙo a tsakaninmu. Saboda haka a nan za mu iya cewa
harshe hanya ce ta isar da saƙo a tsakanin al’umma kuma sahihiyar baiwa ce da
ubangiji ya ba wa ɗan adam. A ƙamusun Hausa, (2006) an
bayyana harshe da cewa, “hanyar magana tsakanin al’umma iri ɗaya. Shi kuwa Abubakar, (2006, sh. 12-15) cewa ya yi, “harshe kafa
ce ta sadarwa a tsakanin al’umma, kuma yana haɓaka ya bunƙasa har ya tsallaka mahallin da ba nasa ba. Ya kafa hujja da yadda
harshen Hausa yake ci gaba a makarantu da ƙasashen Afrika da duniya
baki ɗaya. Kuma ya ƙara da cewa ƙabilar Hausawa suna da yawan jama’a, wannan ya yi dai-dai da abin
da Newman, (1973, sh. :ɗɗɗɓii) yake cewa:
Hausawa yawansu ya kai milliyan talatin da biyar
kuma suna rayuwa a wani guri da ake ce masa ƙasar Hausa a Arewacin Nijeriya da Kudancin Nijer. Kamar Kano da
Sokoto da Daura da Dogondutci da Gobir da Tohoua da sauransu
Newman (1973) a bayaninsa yana ƙara jaddada mana yawan ƙabilar Hausawa da kuma
girman ƙasa da suke da shi. Wannan ya ƙara tabbatar mana da cewa, Hausawa ba a wuri ɗaya suke rayuwa ba, Kuma harshensu, harshe ne mai ɗauke da al’umma a sassa daban-daban.
Denham da Lobeck, (2013,
sh. ɗiɗ) sun bayyana harshe da
cewa abu ne rayayye idan aka yi la’akari da yadda muke magana a tsakaninmu da
kuma yadda yake canja mahali ko canji na magana ko furuci a tsakanin mutane duk
da ma ba kowa ba ne yake yin amfani da shi. Wannan ya yi dai-dai da abin da
Yakasai, (2012, sh. 2) yake cewa:
“Baiwar da ɗan adam yake da ita ta amfani harshe ita ce ta babban abin da ya
bambanta shi da dukkan sauran halittu, har ya fifita shi bisa kansu kodayake
dabbobi ma suna da tunani irin nasu, wanda kuma suke bayyanawa cikin hanyar
sadarwa irin daban- daban babu wata dabba da take da hanyar sadarwa irin
wadda ɗan Adam yake amfani da ita, wato harshe “.
Wannan bayanin na Yakasai (2012) yana ƙara mana haske dangane da yadda harshe yake kasancewa baiwa
ga ɗan adam. Kuma ya ƙara tabbata da bayanin su Denham da Lobeck, (2013) na cewar ba
kowa ba ne yake amfani da harshe, har ila yau kuma, sun ƙara bayyana mana cewa lallai harshe yana da mihimmanci
saboda ɗan adam ne kaɗai yake amfani da shi.
Shi kuwa ɗan adam babu ya shi a cikin haluttun da Allah ya
halitta.
1.2 Ma’anar Mu’amala
Ma’amala gamayya ce ta al’umma wanda za su iya kasancewa al’umma
guda ko ‘yan dangi ɗaya ko kuma daga sassa daban-daban domin cuɗanya a tsakaninsu saboda samun biyan buƙatar rayuwar yau da gobe.
CNHN, (2006) cewa aka yi
mu’amala ita ce gudanar da wata harka da wani mutum. Sai dai kuma Boyd,
(1969) ƙarin haske ta yi, inda ta tabbatar da cewa
ma’amala ta wanzu tsakanin Hausawa da Fulani Torankawa Mutanen Futa-turo
ta ƙasar Sengal. Tun lokacin kakan Usmanu Ɗanfodiyo mai suna Musa Jakolo. Wanna ma’amalar ta haifar da ƙara jaddada addinin Musulunci da auratayya tsakaninsu da Hausawa.
Shi kuwa Gazali, (2005) cewa ya yi tabbas mu’amala za ta iya
kasancewa ta fuskar kasuwanci ko neman ilimi da addini. Har ila yau ya tabbatar
da cewa, a sakamakon ma’amala, an samu dangantaka mai ƙarfin gaske tsakanin Barebari da Hausawa.
Haka Yahaya, (1989) ya tabbatar da cewa a sakamakon mu’amala
tsakanin Hausawa da Larabawa da Turawa, ya sa Hausawa sun koyi rubutun
mahammadiya da ajami cikin harrufan Larabci da kuma rubutun boko. Shi kuwa
Dalsgart da wasu, (1975) cewa suka yi, mu’amala ita ce gamayyar al’umma biyu ko
fiye da haka domin ɗaukar mataki a kan wani al’amari na daban.
Sai dai kuma Berber da wasu, (1996) cewa suka yi mu’amala haɗaka ce ta mutane biyu ko fiye domin isar da saƙo a tsakaninsu ko kuma tuntuɓar junansu domin kaiwa
ga cimma nasara ko buri. bisa la’akari da waɗannan bayanan za mu iya
kafa hujja da tabbatar da cewa, lallai ma’amala tsakanin mutane mihimmin
al’amari ne. kuma ya zama wajibi wani harshe ya yi tasiri a kan wani.
1.3 Mu’amala Ta Fuskar Kasuwanci
Masu iya magana kan cewa
“kasuwa a kai miki dole”. Domin nan ne wurin da aka fi sani wajen gudanar da
kasuwanci da samun abin masarufi. Kuma yin ma’amala a wannan wurin ya zama
wajibi, saboda gamayya ce ta mutane daga harsuna da al’adu daban-daban da nufin
neman abin rufawa kai asiri.
A CNHN, (2006) an bayyana
ma’anar kasuwanci da saye da sayarwa. Sai dai kuma Yahaya da wasu, (1992) sun
bayyana sana’a da cewa, hanya ce ta amfani da azanci da hikima a sarrafa
albarkatu da ni’imomin da ɗan adam ya mallaka don tunanin yau da kullum.
Kowa ya san da ƙasar Hausa cike take da harkokin kasuwanci. Ƙasa ce kandamemiya mai girma da faɗin gaske kuma ta haɗa garuruwan Arewacin Nijeriya da Kudancin Nijer. Daulolin Hausa
bakwai zuwa takwas ana aiwatar da ma’amaloli na cinikayya. Ga misali kamar Kano
da Katsina da Sokoto da Maraɗi da Kebbi da sauransu duk ana gudanar da
harkokin kasuwanci. Haka zalika a ƙasashen Yammacin Afrika
Hausa ta yi wa sauran harsunan wurin babakere, dalili shi ne dole sai da
harshen Hausa ake gudanar da kasuwanci a waɗannan mahallan. Ko da
rubutu za a yi, a resiti ko shaida ko jimillar kayayyaki dole sai da harshen
Hausa ake rubutawa a wannan ƙasashen misalan irin waɗannan ƙasashen sun haɗa da Ghana da Nijer da
Kamaru da Burkina Faso da Kodebuwa da Cadi duk ana harkar kasuwanci ne da
harshen Hausa. Wannan ya kai mu ƙara fahimtar cewa,
harshen Hausa ya kai a ce masa shi ne harshen da ya fi kowanne harshe bunƙasa a waɗannan ƙasashe (Adamu, 1997, sh.
11)
1.4 Taƙaitaccen Bayani A Kan Gashua
Garin Gashua shi ne helkwatar ƙaramar hukumar Bade a
cikin jihar Yobe a Arewa maso Gabashin Nijeria. Garin yana ƙunshe da gamin gambizar ƙabilu daban-daban kamar
goma sha biyu (12) waɗanda suka haɗa da Badawa da Hausawa
da Barebari da Fulani da Yarabawa da Inyamure da Kare-kare da Gizimawa da Margi
da Bura da ma yan ƙabilar Tibi. Hausawan da suke zaune a wannan
yanki galibinsu sun yiwo hijira ne daga wurare kamar Bauchi, Haɗejia, Kano da kuma Sakkwato. (Grema da Kukuri, 2012, Sh.115).
Garin Gashuwa kuwa ya
kasance gari mai tattare da ‘yan kasuwa kusan za a iya cewa yana ɗauke da manyan ‘yan kasuwar da za a iya alfahari da su a Arewa
maso Gabashin ƙasar nan. Kuma ana aiwatar da harkar kasuwanci
ne da harshen Hausa a wannan wurin. Garin yana da kasuwanni iri-iri kamar
kasuwar dabbobi da kasuwar kayan ɗanye da kasuwar hatsi da
duk dangin tsaba da kasuwar kifi da sauransu. Al’ummar Gashuwa suna son
kasuwanci wannan yana da nasaba da shigar Hausawa garin, da kuma tasirin da
suka yi bisa kowa a wurin. Saboda sai da Hausa ake gudanar da ma’amalar
kasuwanci a cikin garin. Ga kuma ƙabilar Inyamurai da
Yarabawa duk al’umomi ne masu sha’awar kasuwanci kuma masu yin sa (Grema da
Kukuri, 2012, sh, 116) .
1.5 Manufar Bincike
Muƙalar ta ƙuduri aniyar yin tsokaci a kan ma`anar harshe da
mu`amula ta fuskar kasuwanci a garin Gasua da nufin gano ire-iren kalmomin da
ake amfani da su a wannan fannin tare da kawo ma`anonin kalmomin a
daidaitacciyar Hausa.
2.0 Bitar Wasu Ayyuka Magabata
Yakasai (2012, sh, 110) ya ce a rayuwar yau da kullum ta Bahaushe
ita ta haifar da Hausar rukunin masu sana`a wadda take cike da kalmomi irin na
fannu. Haka kuma duk in da ka zagaya ba za ka ji ana amfani da su ba sai a
Hausar rukunin masu sana`ar, kamar yadda za mu ga misalai a cikin wasu kalmomin
gama garin yan kasuwa:
Misali na 1:
|
Kalmomin
kasuwanci |
Ma`ana |
|
i. saye [sajee] |
ka bayar da kudi ka karbi wani abu |
|
ii. sayarwa [sajarwa] |
ka bayar da wani abu a baka kudi |
|
iii. tayi [taji] |
ka fadi abin da za ka biya abu ko
a bar maka ko a hana ka, a nemi ka kara |
|
iv. albarka [albarka] |
neman kari daga yadda mai saye ya
taya |
|
v. an sallama [an sallama] |
an amince da yadda mai saye ya
taya abin |
|
vi. iƙala [iƙaalaa] |
neman warware ciniki bayan an
kulla shi |
Hassan (2016, sh, 29) ya yi tsokaci a kan Hausar rukuni-rukuni iri
ta zawarawa a garin Dutsin-ma da kewaye. Haka nan ya kawo misalan wasu keɓaɓɓun kalmomi da zawarawa ke amfani da su wajen
sadarwar su ta yau da kullum a cikin mu`amalolinsu wanda yake ba za ka ji
wadannan keɓaɓɓun kalmomi ba a ko’ina
ba sai a wajen zawarawa su ya su. Ga kaɗan daga cikin kalmomin:
Misali na 2:
|
Kalma |
Ma`ana
ta yau da kullum |
Keɓaɓɓiyar
ma`ana |
|
i. tulu |
abun ɗebo ruwa na ƙasa |
bazawari mai ƙaton kai |
|
ii. kashe wuta |
zuba wa wuta ruwa |
kashe wata fitina domin komawa
gidan tsohon miji |
|
iii. kwasa |
ɗebe wani abu |
bazawarin da aka mayar jaki wanda
ba a so kuma ana karɓar abin hannunsa |
|
iv. wan (one) |
a nan “wan” tana nufin ɗaya |
bazawari wanda yake sakin bakin
aljihu wato mai kyauta |
|
v. ƙarfe |
a nan ana nufin taman ƙarfe |
bazawarin da baya kyauta, wato
bazawarin da yake mai ƙanƙamone |
|
vi. reza |
abu mai kaifi sosai |
bazawara mai yawan son kuɗi da
abin duniya |
Azare (2016, sh, 116) ya ƙara da cewa idan aka yi dubi na kaƙiƙa akan irin keɓaɓɓun kalmomin da matan
aure yan boko suke amfani da su wajen sadarwarsu ko kuma mu`amalolinsu na yau
da kullum za mu ga cewa akwai yan bambance-bambance tsakaninsu da takwarorinsu
waɗanda ba su yi ilmin zamani ba waɗannan yan bambance-bambance kuwa suna da nasaba ta kai tsaye da
ilmin zamani. Ga wasu daga cikin irin waɗannan kalmomi:
Misali na 3:
|
Keɓaɓɓun
kalmomi |
Ma`ana
ta yau da kullum |
Keɓaɓɓiyar
ma`ana |
|
i. tunkiya |
dabbar gida (sheep) |
kishiya (co-wife) |
|
ii. gida ya yi dirai |
gida ya bushe |
ƙarshen wata ba kuɗi; kayayyakin
masarufi sun ƙare |
|
iii. sandar girma |
sandar da ake bai wa masu sarauta |
mazakutar namiji |
|
iv. gimbiya |
yar sarki |
matar da miji ya fi so |
|
v. ba sabis |
babu hanyoyin sadarwa ta iska |
mijin da ba ya iya biya wa matarsa
buƙata |
|
vi. ofis |
muhallin gudanar da aikin gwamnati |
madafa (kitchen) |
Umar da Musa (2017, sh.12) sun yi tsokaci a
kan Hausar rukuni wadda ta shafi irin Hausar ɗalibai ko kuma irin keɓaɓɓun kalmomin da ɗalibai ke amfani dasu a
jami`o`i musamma ma Jami`ar Usman Ɗan fodio da ke Sakkwato,
wasu daga cikin irin waɗannan keɓaɓɓun kalmomi su ne kamar haka:
Misali na 4:
|
Kalmomi |
Ma`ana
ta yau da kullum |
Keɓaɓɓiyar
ma`ana |
|
i. wanki |
kawar da dauɗa daga jikin tufa ko
wani abu |
maguɗin jarrabawa |
|
ii. farin wata |
hasken da yake bayyana a sama idan
dare ya yi |
samuwar bayanin jarrabawa kafin
lokacinta |
|
iii. sha |
shan wani abu ko saurare |
hadda ta karatu |
|
iv. dogon wuya |
wuya mai tsawo |
leƙen aikin na gaba a yayin
jarrabawa |
|
v. layun tsari |
wani abu da ake rufawa a rataya
domin magani |
shiga jarrabawa da amsa |
|
vi. direba |
mai tuƙa mota |
jagora a wajen jarrabawa |
3.0 Hanyoyin Da Aka Bi Domin Tattaro Bayanai
Hanyar da aka bi domin tattaro bayanai ita ce ta ganawa kai tsaye
da yan kasuwa a ɗaiɗaikun su tare da lura da
yadda suke gudanar da al`amuransu a fakaice ba tare da sun gane cewa ana lura
da su ba.
4.0 Ƙalailaicewa
Kamar yadda aka sani ne
kasuwa muhalli ne da yake ɗauke da jama’a kala-kala domin samun abin
masarufi. Duk wanda aka gani a kasuwa ya je ne domin biyan buƙatarsa ko ya saya, ko kuma ya sayar. Su kuwa ‘yan kasuwar Gashuwa
a dalilin zamansu wuri guda domin gudanar da mu’amalarsu ya haifar musu da yin
amfani da wasu kalmomi ko kalamai a cikin zancensu na yau da kullum, wanda sai
a junansu ne kawai suke fahimtar sadarwar, ko masu ma’amala da su. Wannan ma
yana ƙara tabbatar da cewa, ta fuskar kasuwanci Hausa
ta yi tasiri a kan sauran harsunan da suke rayuwa a garin na Gashuwa. Ga
misali:
Misali na 5: Hausar Fannoni Daban-Daban
|
Kalma |
Ma`ana |
Daidaitacciyar
Hausa |
|
Gàjere |
wandà
yakè da gazàwaa |
mài
rauni |
|
Taa
yì maî |
an
samú ribà |
cîn
ribà |
|
Na
hàu shi |
cîn
ribà kan mai sàya |
na
ci ribà |
|
Ya
hàu ni |
cîn
ribà akan mai kaya |
na
faɗi |
|
Ya
fakè ni |
ya
sacè mîn kaya |
ya
mîn satà |
Sai dai a cikin kasuwar ta
Gashuwa ma’amalar a tsakanin rukunin mutane ta bambanta ƙwarai da gaske, saboda ana samun fannoni mabambanta a cikin kasuwa
guda, hakan ne ya haifar da kowanne bakin wuta da irin nasa hayaƙi. Kowanne fanni na ‘yan kasuwar Gashuwa, suna amfani da wasu
kalmomi a ciki Hausarsu da ta sha bamban da ta takwarorinsu ga misali Hausar
masu sana’ar kafinta ta bambanta da Hausar masu magani, haka ta masu sana’ar
koli, ta bambanta da ta masu sana’ar goro. Wannan ma tasiri ne sosai da harshen
Hausa ya yi a ƙasar da ba tasa ba (Babangida, 2018, sh, 23)
Wani abin lura kuwa, da
irin wannana nau’in maganganun shi ne kalmomin Hausar da ‘yan kasuwar Gashuwa
suke amfani da su, sun sha bamban da na ‘yan kasuwar Damaturu da na Nguru da na
Sokoto duk da ma an fi samun irin waɗannan ma’amalolin a
birane. Domin tabbatar da wannan batu, ga ma abinda Ɗantumbishi (2005, sh. 70-86) yake cewa:
|
“An fi samun cuɗanyar al’umma
a birane kamar hulɗa ta ciniki
da ma’amala saboda |
|
haka samun ‘yan bambance-bambancen harshe da salon sarrafa harshe kan taso”. |
Wannan bayanin Ɗantumbushi (2005), yana
mai tabbatar da cewa; an fi samun hada-hada a birane saboda a nan ne ake samun
al’ummu masu tarin yawa. Saboda haka, a wajen yin ma’amala a tsakanin jama’a,
dole ne a samu wani harshe ya yi tasiri a kan saura kuma samun canje-canje a
cikin harshen da yake da tasiri a tsakanin wannan al’ummar ya za wajibi.
A Kasuwar Gashuwa akwai
wani yanki na jama’a da ake yi masa laƙabi da ‘yan magani.
Kalmomin da ake amfani da su a Hausar wannan rukunin ta bambanta da ta wasu
yankunan na cikin kasuwar. A sakamakon keɓewa da suka yi, ya
haifar da wasu ‘yan canje-canje a tsakaninsu da sauran ‘yan-kasuwar garin; a
ma’amalarsu ta yau da kullum. Haka kuma masu maganin gargajiya Hausarsu ta
bambanta da masu maganin zamanin. Wannan ma hujja ce da take tabbatar da
tasirin harshen Hausa ga sauran harsunan da ke garin Gashuwa. A cikin kasuwar
Gashuwa ‘Yan maganin gargajiya wani nau’i ne na jama’a, mafi akasari ana
samunsu a wajen kasuwa masu sana’ar maganin gargajiya a garin Gashuwa gada suka
yi a wurin iyaye da kakanni. A sakamakon keɓanta da suke yi sukan yi
amfani da wasu kalmomi a cikin Hausarsu ta sanadiyar haka ne suka bambanta da
sauran takororinsu ‘yan kasuwa ta yin amfani da waɗannan kalmomi a tsakaninsu. Ga misali:
Misali na 6: Hausar masu maganin gargajiya
|
Kalma |
Ma`Ana |
Daidaitacciyar
Hausa |
|
Hùdàjje |
kamùn
mayu |
wanda
aka huda |
|
Shiɗaɗɗè |
kamùn
danshi |
wanda
bay a hayyacinsa |
|
Hàkar
dajì |
magàni
mài wuya |
harkar
da ake yi a daji |
|
Hùhu-làhu |
mài
cùtar basir |
wato
fanko |
|
‘Yar
lisu |
cùtar
shawara |
cuta
mai sa barci |
|
Tòmashe |
wàrkakken
ràuni |
warkewa
daga ràuni |
Haka ma masu sayar da maganin zamani a garin Gashuwa, a sanadiyar
keɓanta da suka yi, ya haifar musu da yin amfani da
wasu kalmomi lokacin cinikayyarsu ko kuma zamantakewa a tsakaninsu. Hausar
wannan rukunin ta sha bamban da Hausar ‘yan maganin zamani. Ga misali:
Misali na 7: Hausar Masu Maganin Zamani
|
Kalma |
Ma`ana |
Daidaitacciyar
Hausa |
|
Farin
kàya |
kàyan
maràsaa lafiya |
fararen
tufafi |
|
Baƙin kaya |
Ƙwàya |
baƙaƙen tufafi |
|
A
kàrci ƙasà |
maganìn
ciwòn kâi |
kartar ƙasa da wani abu |
|
Fasinjàna |
mài
sayàn kayanà |
mài
hawa motar haya |
|
Kà
ragè mîn |
kà
yi minì sauƙi |
kà
sassàuta farashi |
|
Kayan
matà |
magànin
jima’ìn matà |
magànin ƙarfin matà |
|
Kayan
maza |
magànin
jima’ìn maza |
magànin ƙarfin maza |
|
Kayan
ruwa |
magànin
ruwa na yaran |
sinadari
mai haɗe
da ruwa |
|
Igiyàa |
mesàr
dirif |
abin ɗaure wani abu |
|
Injakshin |
àllurar
màye |
àllura |
Sai kuma kafintoci, suma
sanadiyar keɓewa da suke yi wuri guda don yin kasuwancinsu,
suna yin amfani da wasu kalmomi a cikin ma’amalarsu ta yau da kullum. Hausar
wannan nau’i ta ‘yan-kafinta ita ma ta bambanta da sauran rukunin jama’ar cikin
kasuwar. Ga misali:
Misali na 8: Hausar Kafintoci
|
Kalma |
Ma`Ana |
Daidaitacciyar
Hausa |
|
Mahammadiyya |
Daidai
wa daida |
Adalci |
|
Na
turè shi |
an
ci ribar aiki |
ture
mutum |
|
Zân
kwarfè shi |
zân
sàmu riba |
kwashe
wani abu |
|
Cuku-cuku |
hà’incìn
aiki |
abin
dab a gaskiya |
|
Kà
zaunà a kansa |
kà
gàllaza masa |
zama
a kan wani abu |
|
Sàra |
inkiyar
yin tsàda |
sari
wani abu |
|
Ɗàga ƙafà |
Sauƙi |
Sassauci |
|
Ɗàga ƙafà hakà ne |
Tsàda |
Gàllazà |
|
Sallah |
maràr
salla |
wani
nau`in ibada |
|
Ƙàbilà |
rashin
sanin harka |
Bàre |
Akwai wani ɓangare na masu sana’ar goro, su kuma mafi
yawancinsu Hausawa ne da Barebari.Wurin da suke sana’ar yana ɗaya daga cikin mahallai masu girma da kuma yalwar jama’a.
Sanadiyar keɓe kansu da suka yi, ya haifar musu da samuwar
wasu kalmomi a tsakaninsu, kuma suna amfani da su a cikin Hausarsu musamman
lokacin cinikayya a tsakaninsu da masu sayayya. Wannan ma ya ƙara fito da tasirin Hausa a mu’amalar kusuwanci a garin Gashuwa.
Saboda haka; sai su kaɗai ne suke fahimtar junansu. Ga misali:
|
Misali na 9: Hausar Yan Goro Kalma |
Ma`ana |
Daidaitacciyar Hausa |
|
Met |
mai ciniki |
abokin ciniki |
|
Kùsu |
rashin jìtuwa |
ɓera |
|
Daushe |
ingancì |
abin day a kwan biyu |
|
Tallà |
ta burge |
tallata haja |
|
Tà yî |
doguwa |
au ya yi daidai |
|
Manic |
mài kawo kaya |
mài jarì sosai |
|
Sabon huji |
baƙon
sana’a |
sabon zuwa |
|
Rànsa |
nairà ashirin |
nàira ashirin |
|
Dam |
nàira dubu |
ƙarar wani abu |
|
Lami |
Baashiì sa |
babu ɗanɗano |
|
Tsìni |
Babu |
abu mai tsini |
|
Dir |
sabon tashe |
sabon tashe |
|
Gobso |
gorò maràr kyau |
màtacceen goorò |
|
Musà |
Ɓàrawo |
musu |
A ɓangaren masu sana’ar koli kuwa, Kalmomin da suke
amfani da su a rukuninsu sun bambanta da sauran ‘yan kasuwar, sukan sarrafa
kalmominsu a cikin maganganunsu na yau da kullum, wanda sai a junansu ne kaɗai suke fahimtar saƙonsu a matsayin masu
sana’a a rukuni guda. Hatta mata masu sana’ar a cikin gida, idan suka zo
sayayya a kasuwa; sukan yi maganganu wanda sai su da kansu ne kawai suke
fahimtar abin da suke nufi. Kuma cikin harshen Hausa. Misali:
Misali na 10: Yan Koli
|
Kalma |
Ma`ana |
Daidaitacciyar
Hausa |
|
Tarena
ne |
mài
tàyi bâ sayà |
mài
latsi |
|
Dede
nè |
farashìn
hakà nè |
Gàskiya |
|
Iki
nè |
farashìn ƙarya |
Cùta |
|
Zàge
nè |
wandà
bâ yà cìniki |
maràr
cìniki |
|
Ƙuri nè |
ɗan kallo nè |
ɗan kallo nè |
|
Girbè
shi |
na
cî rìba a kansa |
sare
wani abu |
|
Atàsayis |
ba
zâi sàya ba |
ya
fasà sàya |
5.0 Kammalawa
A wannan muƙala, an nuna yadda harshen Hausa ya yi tasiri a
garin Gashuwa. Har ya zama shi ne mahaɗi a tsakanin ‘yankasuwar
garin. Babu yadda za a gudanar da harkar kasuwanci a wannan mihimmin garin in
ba da harshen Hausa ba. A sakamakon haka ne, aka samu Hausar rukuni a ɓabgarori da dama a harkar kasuwancin waɗannan al’ummai. Wanda sai kana mu’amala da su za ka fahimci abin
da suke magana bisa kansa. Waɗannan keɓaɓɓun kalmomi kuwa sun haɗa da Hausar masu maganin
gargajiya inda ake samun kalmomi kamar ‘hudajje’ ma`ana kamun mayu, da Hausar
masu maganin zamani a inda ake samun kalmomi kamar ‘baƙin kaya’ ma`ana kayan maye da kuma Hausar masu sana`ar kafinta a
inda ake samun kalmomi kamar ‘saraa’ ma`ana yin tsada, haka ma Hausar yan goro
akan samu kalmomi kamar ‘lami’ ma`ana bashi, da ma Husar yan koli in da ake
samun kalmomi kamar su ‘zagee ne’ wato marar ciniki. Waɗannan batutuwa da ma wasu sun fito da irin tasirin da harshen
Hausa yake da shi ba wai a yankin ƙasar Hausa kawai ba har
ma da wasu sassa da ke wjen ƙasar Hausa.
Manazarta
Abubakar, A. (2006), Matsayin nazarin harshen Hausa a
yau. Algaita journal of current research in Hausa Studies, vol.1, (4). 12-15
Adamu M. T. (1997).
Asalin Hausawa da harshensu. Ɗan Sarkin kara
publishers
Azare Y.M. (2016).
Language in diɓersity: A look at the role of women towards
language deɓelopment in Hausa sociolinguistics setting, Yobe
Journal of Language, Literature and Culture, Vol.4. 116.
Berber, B. da wasu (1996), An American ciɓic forum, ciɓic society between market indiɓidual and political community, Social Phylosophy and Policy.
Cmbridge University Press.
Boyd, J. (1969). The flame of Islam. Northern Nigerian
Publishing Company.
CNHN, (2006), Ƙamusun Hausa na Jami’ar
Bayero. Ahmadu Bello
University Press.
Dalsgart, K. (1975). Art interaction with light. Oɗfort University Press.
Ɗantumbishi, A. M.
(2005). Harshen al’umma da kuma zumunci. Ɗunɗaye Jounal of Hausa Studies, Vol. 1 (2). 70-86.
Denham, K. da Lebock, A. (2013). Linguistics for eɓeryone an introduction. Internationa Edition. Wadsworth, Cengage
Learning.
Garzali, B. (2005), The Kanuri in diaspora, Fuculty of
Arts, University of Maiduguri.
Grema M. and Kukuri M. M. (2012). Ɓariety of Hausa spoken in Gashua town. Language,
Literature and Culture, Festschrift in Honour of Prof. Abdulhamid Abubakar.
Hassan, S. (2016).
Hausar zawarawa a garin Dutsin-ma da kewaye. Yobe Journal of Language,
Literature and Culture vol.4, 29-30.
Newman, P. (1973). Chad
classification and reconstruction. Affroasiatic Linguistics, 5(1), 1-42.
Umar M. M. da Musa S. (2017). Aro da ƙirƙira: Nazarin samuwar sababbin kalmomin kimiyya a
Hausa; Yobe Journal of Language, Literature and Culture, Vol.5, 11-18
Yakasai, S. A. (2012). Jagoran nazari walwalar harshe. Usmanu Danfodiyo
University Press.
Yahaya, I. Y. (1988). Hausa a rubuce: Tarihin
rubuce-rubuce cikin Hausa. Northern Nigeria Publishing Company.
Yahaya, I. Y. da Musa, T. ‘Y. da Muhd, Z. (1992). Darrusan Hausa
don manyan makarantun sakandare. University Press.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.