Citation: Isah Abubakar KAROFI, Lawal ALIYU & Sabi’u Alti ƁATAGARAWA (2021). Sharhin Wasu Karin Maganganu Masu Ɗauke Da Sunayen Bishiyoyi. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 9, Issue 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
SHARHIN WASU KARIN MAGANGANU MASU ƊAUKE DA SUNAYEN BISHIYOYI
Isah Abubakar KAROFI
Lawal ALIYU
Sabi’u Alti ƁATAGARAWA
Tsakure
Hikimar karin magana a wajen al’ummar Hausawa ba ta tsaya a kan
gajarce zance kaɗai ba domin da yawa daga cikin wasu karin
maganganun sukan zo da hikimar bayyana bishiyoyin da suke a cikin
farfajiyar ƙasar Hausa. Irin waɗannan albarkatun ƙasa dangin bishiyoyi
mutane sukan ci daga ‘ya’yansu. Wasu kuma, a kan yi amfani da su bayan an
sarrafa su ta hanyoyi daban-daban. Wannan nazari ya yi cikakken bayani a kan
bishiyoyin da ake da su shimfiɗe a cikin karin
maganganun Hausa. Bayan haka, binciken ya yi ƙoƙarin zaƙulo wasu karin maganganu
waɗanda suka zo da sunayen bishiyoyi daban-daban
kamar tsamiya da bagaruwa da kanya da ƙaya da giginya da sauransu. Binciken ya gano karin maganganu har
guda talatin da shida a ƙarƙashin bishiyoyi guda goma sha shida da aikin ya ƙunsa. An kuma yi amfani da hira da masana adabi da masana
albarkatun ƙasa musamman masana albarkatun da suka shafi
bishiyoyi da dangoginta domin samun wasu muhimman bayanai da takardar ta ƙunsa. Daga ƙarshe, an yi sharhi game
da karin maganganun da aka zo da misalansu a cikin takardar.
Muhimman Kalmomi: Karin
magana da Bishiyoyi
1.0 Gabatarwa
Karin magana, wasu
maganganu ne na musamman waɗanda suke ƙunshe da ɗimbin hikimar da ba kowa ne mutum yake iya fahimta ba, ba tare da
an fassara masa ba. Akwai adadi mai yawa na irin waɗannan karin maganganu waɗanda suka zo da sunayen
bishiyoyin da ake da su a ƙasar Hausa. Wasu daga cikinsu suna ƙoƙarin bayyana tasirin bishiyoyin da muhimmancinsu
ga rayuwar Hausawa. Wasu bishiyoyin nuni suke a kan fifiko idan aka kwatanta su
da wasu. Don haka, manufar takardar ce ta yi duba a cikin farfajiyar karin
magana ta zaƙulo wasu karin maganganunun da suka zo da
sunayen bishiyoyin da ake da su a ƙasar Hausa domin a yi
bayaninsu dalla-dalla. Sannan kuma, a yi sharhin karin maganganun.
Masana adabi irin su;
Umar (1987, sh. 21) da Yahaya da Zaria da Gusau da ‘Yar’aduwa (2004, sh. 30) da
Birniwa (2005, sh. 57) da Junaidu da ‘Yar’aduwa (2007, sh. 79) da Ɗangambo (2008, sh. 38) sun yi tarayya wajen bayyana ma’anar karin
maganar kamar haka:
“Dabara ce ta dunƙule magana mai faɗi cikin hikima ta yadda za a isar da saƙo mai ma’ana kuma gamsasshe”.
Amma a fahimtar masu
bincike, karin magana tana ɗaya daga cikin rassan
azancin baka na Hausa, wadda takan zo a gajarce cikin hikima mai ɗauke da tarin ilimi idan aka yi fiɗarta dalla-dalla.
2.0 Ma’anar Bishiya
CNHN (2006. 48) ya
bayyana ma’anar bishiya da “Itace da yakan tsiro ya girma a daji ko gari, wasu
kuma ana dasa su”. Karofi da Aliyu (2018, sh. 170) sun bayar da ma’anar itace
ko bishiya da wani nau’in halitta da take fitowa a wani wuri ko muhalli waɗanda sukan fara daga tsiro ta hanyar shuka ko dasawa ko kuma
fitowa da kanta. Sannan ta yi tsawo tare da manya-manyan rassa da yawan ganyaye
da kuma dogayen jijiyoyi waɗanda suke nutsewa cikin ƙasa domin samun ruwa. Sun ƙara da cewa wasu itacen
sukan yi tsawo sosai, wasu kuma gajeru ne.
A fahimtar masu bincike,
bishiya takan tsira daga ƙasa ta hanyar shuka ko kuma fitowa a sakamakon
an yada iri ko ƙwallon ‘ya’yan itatuwan da mutum ko dabba ko
tsuntsaye suka ci. Itace ko bishiyoyi suna da fitattun siffofi kamar haka;
gangar jiki da rassa manya da ƙanana da ganyaye da kuma
furanni a yayin da suke yin ‘ya’ya.
Kabir (2013, sh. 251)
ta ƙara fito da bayyanai dangane da yadda yanayin
itace ko bishiyoyi suke a ƙasar Hausa. Ta ce, akwai waɗanda za ka samu shuka su ake yi a kula da su. Misali, itatuwan
gida akwai kuma waɗanda za ka taras cewa ba wani yake shuka su ba.
Babu kuma mai kula da su, kamar itatuwan daji. Ƙasar Hausa cike da tsirrai iri daban-daban masu amfani ga mutane
da dabbobi da tsuntsaye da ƙwari wasu shuka su ake
yi, wasu kuwa fitowa suke yi da kansu a cikin gari ko dazuka.
3.0 Alaƙar Bishiyoyin Ƙasar Hausa da Karin
Magana
Alaƙar da take tsakanin karin magana da itatuwan ƙasar Hausa alaƙa ce ta ƙut da ƙut domin ita karin magana rumbu ce mai taskace dukkan ƙoƙarin al’umma ta ɓangarori daban-daban, su kuma itatuwa kasancewarsu ɗaya daga albarkatun ƙasa da suke zagaye da
al’ummar Hausawa kuma Hausawan suke sarrafa su domin samar da abubuwan da
rayuwa ta dogara da su. Haka kuma, karin maganganun da suke fitowa daga bakunan
Hausawa sun kasance wata kafa da take adana sunayen itace ko bishiyoyi da kare
su daga salwanta. Babu shakka, karin magana na ɗaya daga cikin ayyukan fasahar al’umma kuma da su ne Hausawa suke
amfani wajen adana hikimarsu da albarkatunsu da tarihinsu da kuma tattalin arziƙin ƙasar Hausa har zuwa ga ‘yan bayanta.
4.0 Bayanan Wasu Bishiyoyin Ƙasar Hausa da Sharhin Karin Maganganunsu
A wannan ɓangaren, an kawo bayanai ne a kan wasu zaɓaɓɓun bishiyoyi da suka fito a cikin karin
maganganun da aka zaƙulo a yayin gudanar da wannan bincike. Sannan
kuma, a ka bijiro da sharhi a kan misalan karin maganganun da aka zo da su a
cikin aikin kamar yadda za a gani a ƙasa.
4.1 Bagaruwa
Bagaruwa bishiya ce da take da tsawo da yawan
ganyaye. Bagaruwa tana da rassa sirara da suke baibaye da
ganyaye, kuma akwai ƙaya a jikin rassanta. Bagaruwa tana
yin ‘ya’ya a cikin sanho mai ƙwari. Da farko sanhon
kore ne, amma idan suka nuna suna komawa ruwan toka-toka. Haka kuma, idan
‘ya’yan sun nuna suna bushewa ƙayau, domin idan aka
girgiza har wata ƙara suke (Kabir , 2013, sh. 255). Ƙarar da bagaruwa takan yi tana kama da ƙarar kacau-kacau. Majema a ƙasar Hausa suna amfani
da bagaruwa wajen yin jimar fatu.
Inuwar bagaruwa ga inuwa ga ƙaya,
Idan da bagaruwa abin
kirki ce, da ba a ba majemi ita (Gwammaja, 2018, sh. 105).
Waɗannan karin maganganu sun fito da yanayi da sigar bagaruwa. Bagaruwa bishiya
ce mai tsinin ƙaya duk da cewa idan ta yi ganye tana da inuwa,
amma inuwar ba a raba ta da ƙaya. Don haka, inuwarta
na da wuyar a zauna ƙarƙashinta. Haka
kuma, bagaruwa aba ce mai hatsari ga mutum shi ya sa ta fi
shahara a tsakanin majema. Haka kuma, karin maganganun suna nuna alherin mutum
da kuma sharrinsa.
4.2 Ɓaure
Ɓaure ice ne mai girma ƙwarai yana da nono da
rassa manya da ƙanana da kuma ganyaye koraye matsakaita. Ɓaure yana
yin ‘ya’ya ƙanana masu taushi. Idan ‘ya’yan sun nuna sukan
canza launi ja-ja.Mutane ba su cin ‘ya’yan ɓaure.Ɓaure yakan
yi kakkaɓa a lokacin bazara[1].
Idan ana cin ɓaure a
bar tona cikinsa (Gwammaja, 2018, sh. 104).
Wannan karin maganar da
take a sama, tana nuna ɓaure a cikinsa yana da wasu abubuwa kamar ƙwari, wato abin ƙyama. Don haka, idan an
zo cin sa to, a bar tona cikinsa domin yin hakan zai iya haifar da wani lahani
ko matsala. Haka kuma, karin maganar tana ƙarin haske a kan idan
mutum zai yi wani aiki na gari ya bar tuna wani sharri da aka yi masa.
4.3 Gamji
CNHN (2006, sh. 153) ya
bayyana gamji da “Wata ƙatuwar bishiya da ake
samun danƙo a jikinta”. Gamji bishiya ce
mai girma sosai an fi samun gamji a cikin daji yana da jiki ja-ja da kuma nono
a jikinsa. Ɓaure yana da manya da ƙanana rassa da kuma
ganyaye kore masu ɗan faɗi. Ganyayensa suna kakkaɓewa a lokacin hunturu. Gamji yakan yi toho a
lokacin rani da damuna. Dabbobi sukan ci daga ganyayensa da suka zuba ƙasa ko kuma idan an saro shi[2].
Ga misalin karin maganar da ta zo da sunan gamji:
Gamji mai toho rani da damuna,
Sara da sasssaƙa ba ya hana gamji toho (Gwammaja, 2018, sh.
119).
Waɗannan karin maganganu da suka zo a sama, suna nuna yanayi da ɗabi’ar gamji ta fuskar nuna juriya a yayin da
yake ta fama da sara da sassaƙa ga ‘yan mai ganye, amma bai hana shi yin toho
rani da damuna. Hakan yana nuna yadda mahassada suke nuna wa mutum hassada,
amma ba za su iya hana masa ci gaba ba.
4.4 Giginya
Giginya itaciya ce mai tsawon gaske. Giginya jikinta
yana da kaushi. Gayenta kamar ganyen kaba yake kuma tana da ƙayoyi baƙaƙe masu lanƙwansa a jikin icen da yake ɗauke da ganyen. Tana yin
‘ya’ya manya-manya, idan sun nuna, sukan yi ja ana kuma shan su, suna da zaƙi sosai (Kabir, 2013, sh. 256).
Ana kuma sayar da
‘ya’yan giginyar a yara-yara da kasuwanni a ƙasar Katsina domin masu
sha’awarta, musamman yara[3].
Inuwar giginya na nesa kan
sha ta (Gwammaja, 2018, sh. 104).
Karin maganar tana nuni
ne da yadda giginya take da tsawo. Don haka, duk wanda yake kusa da ita ba ya
shan inuwarta, sai dai wanda yake nesa da ita. Ya yi dai dai da mai arziƙin da na kusa da shi ba su karuwa da dukiyarsa, sai dai na nesa da
shi kan mora.
4.5 Ice/Itace
Itace ko ice suna ne na jam’i wanda
yake nuni da bishiya mai rai ko busasshiya kuma abin makamashi wanda ake yin
girke-girke da shi[4].
Ba a hawan ice ta ƙasansa a sauka a reshe, Ta inda aka hau ice ta
nan ake sauka,
Iska ba nauyi gare shi
ba, sai dai kada itace,
Saran bisa ba ya kashe itace,
Sara ɗaya ba ya kashe itace,
Ice tun yana ɗanye ake lanƙwasa shi (Gwammaja, 2018, sh. 104).
Waɗannan karin maganganun suna bayyana ice da wani
abu wanda yake da rai. Sannan kuma, karin maganganun suna ƙunshe da ma’ana iri daban-daban. Suna dai nuna muhimmancin asali.
4.5 Icen Ƙarya
CNHN (2006, sh. 278) ya
bayar da ma’anar icen ƙarya da “Wani ice mai yawan fure ba ganye”.
Ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya (Gwammaja, 2018, sh. 127).
Karin maganganun suna
nuni ne a kan illar yin ƙarya da sakamakonta wanda hakan ya yi daidai da
yadda bishiyar ƙarya take yin fure farfat, amma cikin ‘yan kwanaki kaɗan, sai furen ya kakkaɓe, icen ya koma tamkar
bai taɓa yin furen ba. To, haka ma ƙarya take ba ta yin tasiri ko tsayi a duk inda aka yi ta.
4.6 Kaba
Kaba tsiro ne marar tsawo, yana da ganye mai tsawo da
marar faɗi kamar wuƙa. Kaba tana da ƙaya a gefen ganyen kamar na goruba da giginya. Haka nan kuma,
ganyen kaba yana da tsini daga ƙarshe (Kabir, 2013, sh.
256). Malaman zaure da almajirai suna sarrafa kaba domin samar da tauwadar
rubutu. Haka kuma, ana sarrafa ganyen kaba a samar da faifai da tabarma da lefe
da malfa da makamantansu.
Da ma iska ya tarar
da kaba na rawa,
Dai dai ke nan, kaya sun
tsinke gindin kaba,
Da sauran rina a kaba (Gwammaja,
2018, sh. 94).
Karin maganganun suna
fito da ɗabi’ar kaba a matsayinta maɗauri kuma mazaunin rina wanda da wuya a raba kaba da
rawa (kaɗawa) da rina a kowane lokaci. Hakan yana daɗa fito da alaƙar da take tsakanin kaba da
rawa da kuma rina. Don haka, karin maganganun suna nuna abin da ya faru shi ne
aketsammani.
4.7 Kanya
CNHN (2006, sh. 232) ya
bayyana kanya da “Wata irin bishiya mai ‘ya’ya masu zaƙi da ake sha”. Kanya bishiya ce wanda aka fi
yawan samunta a cikin daji. Kanya tana yin girma sosai,
jikinta baƙi-baƙi ne mai ɓawo-ɓawo ba ta da nono, amma tana da ƙwarin jiki wannan yasa masassaƙa suke sassaƙa kayan aiki da ita. Kanya tana yin ‘ya’ya masu
yawan gaske a lokacin bazara. ‘Ya’yanta idan sun ƙosa jajaye ne masu zaƙi a cikin ‘ya’yan akwai
wasu ‘yan ƙwallaye masu ruwan ɗorowa masu tauri. Mutane da dabbobi suna cin ‘ya’yan kanya.
Ga misalan karin maganganu da suka zo da sunan kanya:
Zuba sai ka ce kanya,
Ramuwar maɗi masakin kanya[5].
Karin maganganun suna
fito da yadda kanya nunanna ta ɗara maɗi daraja a tsakanin masu shanta. Da kuma yadda kanyar take zubar
da ‘ya’yanta a ƙasa, wato kakkaɓa ba adadi a yayin da
ta ƙosa. Hakan, yana nuni da yadda mutum yake yawan
magana barkatai tamkar yadda kanyar take zuba ba adadi. Sannan kuma, karin
maganar ramuwar maɗi masakin kanya tana nuni da
yadda mutum yake rama abin da wani ya yi masa fiye da yadda aka yi masa, wato
sai annunka.
4.9 Kuka
Kuka itaciya ce mai girma sosai tana yin rassa da
yawa, kowanne reshe yana ɗauke da ƙananan rassa da ganyaye
masu yatsu ƙanana kuma tana yin ‘ya’ya manya-manya a cikin
kwabsa. ‘Ya’yan kukar da suke a cikin kwabsar da su ne Fulani masu
sayar da nono suke kaɗa nono domin ya yi kamri kafin su sayar a
kasuwanni ko yara-yara ko gida-gida. Ganyen kuka kore ne mai
‘yan jijiyoyi ƙanana kamar layuka. Ana yin miya da ganyen kuka
bayan an dakaan samar da garinta. Kuka tana da yauƙi idan aka kaɗa ko haɗa ta da ruwa. Miyar kuka
sananniya ce a gidajen Hausawa domin ita ce miyar da ta fi karɓuwa a tsakanin al’ummar Hausawa na ƙauye da na birni. Ana kasuwancin kuka a mafi yawancin
kasuwannin ƙasar Hausa har ƙetarawa ake yi da ita a wasu sassa na duniya domin karɓuwar da ta samu a tsakanin Hausawa mazauna ƙasashen waje[6].
Ga wasu misalan karin
maganganun da suke ɗauke da sunan kuka:
Rashin kuka kansa a kaɗa tafasa,
Da ƙadangare ya hau kuka, ai ba tsarar uwarsa ba ce,
Ɗan kuka mai ja wa uwa tasa jifa
(Gwammaja, 2018, sh. 98-99).
Karin maganganun da suke
a sama, suna nuna girman da kuka take da shi, sannan ‘ya’yan
da take yi su suke ja mata Fulani ko makiyaya suke jifarta. Ya yi daidai da
idan mutum ya janyo wa iyayensa wata fitina. Ɗayar kuwa, tana nuni da yadda mutum yake neman abin da ya fi ƙarfinsa, amma ya dage yin sa.
4.10 Kurna
Kurna kamar magarya bishiya ce mai ƙaya. Tana kama da magarya ƙwarai sai dai ita kurna
ganyenta ƙanana ne kuma ƙayar tana jikin rassan bishiyar. Ganyenta ya yi kama da zanen
filawa, kuma akwai wani zane a tsakiyarsa. Kurna tana yin
‘ya’ya ƙanana (Kabir, 2013, sh. 257).
Bugu da ƙari, ‘ya’yan kurna suna da ƙwallo ɗan ƙarami wanda yake lulluɓe da wata tsoka mai zaƙi, sannan sai kuma ɓawo mai ruwan ƙasa-ƙasa da yake lulluɓe da ita. ‘Ya’yan kurna sun fi
‘ya’yan magarya girma da daɗin sha. Misalin karin
maganar da aka ambata sunan kurna da sharhinta.
Ko da girgiza kurna ta fi magarya [7].
Karin maganar tana nuni
ne a kan fifiko tsakanin abu biyu masu kama da juna ta fuskar muhimmanci.
4.11 Ƙaya
CNHN (2006) ya
bayyana ƙaya da “Wani tsinke-tsinke ne mai tsini wanda yake tsirowa a jikin
bishiya kamar ta bagaruwa ko aduwa ko kuma ƙashin kifi ko tsinkaye da yake bayan beguwa da bushiya”.
Ƙaya ita ce duk wani abu mai siffar tsinke-tsinke mai tsini da ake samu
a jikin bishiya ko tsiro ko jikin dabba. Don haka, duk wani tsinke mai tsini da
yake a jikin tsiro da zai iya yi
wa mutum rauni ko lahani shi ake kira da ƙaya (Kabir, 2013, sh. 254).
Ga wasu misalan karin
maganganun da suka fito da sunan ƙaya da sharhinsu: An yi gudun rauni, an faɗa a ƙaya,
Arziƙi rigar ƙaya,
Dangi rigar ƙaya,
Ko da biri ya zama wawa,
ba ya yi wasa da itace masu ƙaya ba (Yusuf, 1998, sh. 33).
Waɗannan karin maganganu suna ƙara fito da illar
da ƙaya take da shi na yi wa mutum ko dabba rauni. Arziƙi rigar ƙaya, hakan yana nuni da idan Allah ya ba mutum arziƙi ko dangi da yawa to, sai ya fuskanci matsi daga wajensu.
4.12 Maɗaci
CNHN (2006, sh. 313) ya
kawo ma’anar maɗaci da “Wata doguwar bishiya wadda itacenta suke da ɗaci ainun, ana yin magani da ganyensa da sassaƙensa, kuma ana yin katako da itacensa”.
Ga wata karin magana da
ta zo da sunan maɗaci:
Karatu na zangi
moriyarka da nisa, farkonka maɗaci, ƙarshenka zuma[8].
Karin maganar tana nuna
matsayin karatu, farkonsa wuya, ƙarshensa daɗi. A nan an danganta
Maɗaci da
wuya, wato ɗaci, zuma kuma daɗi.
4.13 Magarya
Magarya itaciya ce mai ƙaya, ganyenta yana kama da ganyen kurna. Haka
kuma, magarya tana da rassa sirara masu yawa a gindi ɗaya masu ɗauke da ƙaya mai tsini da dafi.
Tana ‘ya’ya a jikin rassanta kuma ana shan su. (Kabir, 2013, sh. 258).
Haka nan kuma, ‘ya’yanta
‘yan ƙanana ne kamar kashin awaki kuma jajjaye ne idan
sun nuna. Magarya tana da ɗan ƙwallo ɗan ƙarami a cikinta a
samansa akwai ‘yar tsoka ‘yar kaɗan mai zaƙi, sai dai ‘ya’yanta ba su kai kurna zaƙi da tsoka ba. Bayan haka, wani abu da ya ƙara bambanta kurna da magarya shi
ne sauƙin girgiza da kurna ta ɗara magarya a yayin ɗibar ‘ya’yansu.
Ka ɗaure akuyarka gindin magarya (Gwammaja, 2018, sh.
109).
Karin maganar tana nuna
rashin shakku a yayin da aka ba da ajiyar wani abu, wato samun tabbas ga wani
abu.
4.14 Sarƙaƙƙiya
Sarƙaƙƙiya itace ce wadda aka fi samu a cikin duwatsu, tana da ƙaya ‘yar guntuwa mai ‘yar lanƙwasa a kanta. Ana
danganta ta da jayayya ba don komai ba sai don yawan rikicinta a lokacin da
wani mutum ko dabba ya taɓa ta duk sai ta kama jiki ko suturar mutum ta
ko’ina idan ya cire nan ɓangaren sai ta kama wani ɓangaren kuma da haka duk sai ta yi wa mutum ko dabba rauni[9].
Ga misalin karin maganar da aka ambata sunan sarƙaƙƙiya:
To, sarƙaƙƙiya uwar
jayayya ((Yusuf, 1998, sh. 41).
Karin maganar tana nuni
a kan son yin jayayya a tsakanin mutane.
4.15 Taura
CNHN (2006, sh. 433) ya
kawo ma’anar taura da “Wata irin bishiya mai ‘ya’ya kamar
na gawasa”.
Ɗan taura biyu, ba ya taunuwa
gaba ɗaya (Gwammaja, 2018, sh. 122).
Karin maganar tana nuni
a kan abubuwa guda biyu muhimmai ba su gamuwa a lokaci ɗaya, sai an ba kowane lokacinsa. Hakan ya yi daidai da ƙwallon taura guda biyu ba su haɗuwa ga mutum cikin jin daɗi.
4.16 Tsamiya
CNHN (2006, sh. 451) ya
bayyana tsamiya da “Wata irin bishiya mai ƙananan ganyaye da ‘ya’ya dogaye masu tsami. da ake jiƙawa a yi kunu da ruwan ko a sha don magani”.
Ga misalan wasu karin
maganganu waɗanda suka zo da sunan tsamiya kamar
haka: Idan za ka yi lilo/shillo, ka yi a tsamiya, in ka yi a sabara ta
karye, Ɗan kuka ba ya zama ɗan tsamiya (Gwammaja, 2018, sh. 97).
Ungulu ta koma gidanta
na tsamiya (Gwammaja, 2018, sh. 123).
Karin maganganun suna
nuni da yin aikin daidai shi ya fi muhimmanci fiye da rashin daidai.
Haka kuma, ungulu ta
koma gidanta natsamiya tana nuni ne da mutum ya koma inda ya fito
tun farko.
5.0 Kammalawa
Wannan takardar ta yi
duba ne a cikin farfajiyar karin magana inda aka zaƙulo wasu muhimman bayanai waɗanda suka taimaka wajen
kammaluwar wannan bincike. Muhimman abubuwan da takardar ta tattauna a kansu
sun haɗa da ma’anar karin magana daga masana
daban-daban da ma’anar bishiya da alaƙar bishiyoyi da karin
magana. Bayan nan kuma, an yi bayani mai ma’ana a kan bishiyoyi goma sha shidda
(16) waɗanda dukkaninsu ‘yan asalin ƙasar Hausa ne ba baƙi ba daki-daki. Sannan
kuma aka gina karin maganganu aƙalla guda talatin da shidda (36) a kansu. Haka
nan kuma, an yi sharhi mai gamsarwa a kan zaɓaɓɓun karin maganganun dalla-dalla domin amfanin masu karatu ko
nazari da kuma masu bincike. Daga ƙarshe, an kammala
takardar tare da bayar da shawarwari domin ciyar da wannan ɓangaren gaba.
6.0 Shawarwari
Azanci da hikimomin
Hausawa suna da matuƙar muhimmanci ƙwarai wajen adana ƙoƙarin da magabata suka yi wa wannan al’umma ta Hausa, don haka
akwai buƙatar a ƙara zage damtse domin
ciyar da wannan ɓangare gaba da kare shi daga salwanta domin ‘yan
baya su ma su ci moriyar da na gaba suka samu har ake koyi da irin gudummawar
da suka taka a lokacinsu. Don haka, akwai shawarwari da ya kamata masu bincike
da nazari ya dace su ɗauka domin haƙa ta cim ma ruwa a ɓangaren ko bagiren karin maganar Hausa.
Shawara ta farko,
farfajiyar karin magana aba ce mai faɗi ƙwarai, akwai buƙatar a ƙara faɗaɗa nazari ko bincike a sauran ɓangarorin da suka shafi tarihi da tattalin arziƙi da siyasa ko tsarin mulki da abincin gargajiya da dabbobi da
tsuntsaye da ƙwari da sauransu, domin a zaƙulo irin waɗannan karin maganganu da aka gina ruhinsu da
abubuwan da aka zayyana a sama, sannan a fito da sharhinsu ta yadda za su
amfanar da sauran masu nazari da karatu a mataki na ilimi daban-daban.
Shawara ta biyu, ya
kamata masu tsara manhajar karatu na gaba da sakandare su yi la’akari da ɗumbin hikimomi da karin maganar Hausa ta ƙunsa su samar da wani kwas mai zaman kansa wanda za a dinga koyar
da hikimomi da sharhin karin maganganun Hausa kawai ba tare da an gwama shi da
wasu ɓangarori na adabin baka ba. Yin haka zai
taimaka ƙwarai wajen fito da tunanin Bahaushe a kan karin
maganganu da dama suka shafi duniya da lahira da addini da cigaban ƙasa da sauran makamantan waɗannan.
Shawara ta uku, ta shafi
masana da marubuta adabin baka na Hausa da su lura da cewa rubutu a kan karin
magana yana samun koma baya saboda ƙarancin masu rubutu a
wannan zamanin. Marubuta da yawa sun fi mayar da alƙalummansu na rubutu a ɓangaren rubutun zube
wato, ƙagaggun labarai na Hausa da na waƙoƙi fiye da karin magana, wannan dalili ya sanya
an bar wani wawasheshen giɓi wanda ya gagara cikewa in ba an ɗauki matakin gaggawa ba to, matsalar ci gaba za ta yi ba raguwa
ba. Ga shi farfajiyar karin magana kome da ruwanka ce, ta ragaɗe lungu da saƙo na rayuwar Bahaushe
ko’ina ka duba ta yi ruwa ta yi tsaki. Don haka, akwai buƙatar masana da marubuta su yi shiri da zai taimaka wa ɓangaren karin magana domin haƙa ta cim ma ruwa ta
fuskar samun sharhin karin maganganun da suke fitowa daga bakunan Hausawa domin
wasu karin maganganun faɗarsu akwai ake yi ba a san yadda sharhinsu yake
ba.
Manazarta
Birniwa, H.A. (2005). Tsintar dame a kala: Matsayin karin magana a
cikin waƙoƙin siyasa. Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies.
C.N.H.N. (2006). Ƙamusun Hausa. Ahmadu Bello University Press.
Ɗangambo, A.
(2008). Rabe raben adabin Hausa. Amana Publishers.
Gusau, S.M. (2008).Waƙoƙin baka a ƙasar
Hausa:Yanaye-yanayensu da sigoginsu. Benchmark Publishers.
Gwammaja, K.D. (2018). Jagoran nazarin karin magana.
K.D.G. Publishing Company.
Junaidu, I. da ‘Yar’aduwa, T. M. (2007). Harshe da adabin
Hausa a kammale. Spectrum Books.
Karofi, I.A. da Aliyu, L. (2018). Itatuwa masu guba a ƙasar Katsina. Kadaura Journal of Hausa Multi Disciplinary
Studies vol.1, No. 4. 170.
Kabir, M. M. (2013). Rashin sani kaza ta kwana akan dami: Tsokaci
a kan tsirrai da itatuwan ƙasar Hausa. Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa (Deterioration of Hausa Culture). 247-260.
Umar, M.B. (1987) Dangantakar adabin baka da al’adun
gargajiya. Triumph Publishers.
Yahaya, I.Y. da Zariya, M.S. da Gusau, S.M. da ‘Yar’aduwa, T.M.
(2004). Darussan Hausa don makarantun sakandire littafi na biyu. University
Printing Press.
Yusuf, Y. (1998). Hausa
a dunƙule. Triumph Publishers, Gidan Sa’adu Zungur.
[1] Hira da Bawale Nakumbo, 12/3/2021.
[2] . Hira da Bawale Nakumbo, 12/3/2021.
[3] . Hira da Bawale Nakumbo, 12/3/2021.
[4] . Hira da Abdullahi Yakubu Darma,
11/3/2021.
[5] . Hira da Abdullahi Yakubu Darma,
11/3/2021.
[6] . Hira da Sabi’u Alti Ɓatagarawa, 17/3/2021.
[7] . Hira da Shehu Yakubu, 11/3/2021.
[8] . Hira da Shehu Yakubu, 11/3/2021.
[9] . Hira da Bawale Nakumbo, 12/3/2021.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.