Ticker

6/recent/ticker-posts

Wace Malikiyya Ya Kamata Ahlus Sunna Su Bi?

Bai kamata ka ce ba ruwanka da Mazhaba ba, saboda Malamai suna fahimtar Addini ne bisa ka’idojin da wadannan Imamai jagororin Mazhaba suka shata. Wato su Imam Abu Hanifa, Imam Malik, Imam Shafi’iy da Imam Ahmad. Wannan ya sa kusan dukkan Malaman Muslunci za ka samu kowa akwai Mazhabar da yake dangantuwa gare ta a Fiqhu. Hatta Malaman Hadisin, kusan kowanensu yana da Mazhabar Fiqhu da ake danganta shi gare ta. Sai dai da yawansu sun kai matsayin Ijtihadi a cikin Mazhabobin nasu.

Kuma Mazhabar Malik tana da fifiko a kan sauran Mazhabobin. Shaikhul Islam ya ce:

"ويمكن المتبع لمذهبه أن يتبع السنة في عامة الأمور؛ إذ قل من سنة إلا وله قول يوافقها، بخلاف كثير من مذهب أهل الكوفة؛ فإنهم كثيرا ما يخالفون السنة، وإن لم يتعمدوا ذلك. ثم من تدبر أصول الإسلام وقواعد الشريعة وجد أصول مالك وأهل المدينة أصح الأصول والقواعد".

مجموع الفتاوى (20/ 328)

“Mai bin Mazhabar Malik zai yiwu ya zama yana bin Sunna a dukkan lamuran Addini. Don zai yi wahala ka samu wata Sunna face Malik yana da kauli da ya dace da ita, sabanin da yawa a Mazahabar Kufa (Abu Hanifa); su kam da yawan lokuta za ka samu suna saba Sunna, ko da bai zama da ganganci ba. Sa’annan duk wanda ya nazarci ginshikan Muslunci da ka’idojin Shari’a to zai samu cewa; ginshikan Mazhabar Malik da Almajiransa ‘yan Madina sun fi ingancin ginshikai da ka’idoji”.

Akwai wani abu da ya kamata mutane su sani; ita Mazhabar Malikiyya makaranta makaranta ce, sun kai makarantu guda biyar:

1- Makarantar Madina.

2- Makarantar Misra.

3- Makarantar Iraq.

4- Makarantar Magrib.

5- Makarantar Andalus.

To ita makaranta ta farko, wato “Makarantar Madina”, bayan ita ce uwa, ita ce kuma wacce ta ginu a kan bin Sunna da Hadisi. Ita ce makaranatar almajiran Malik wadanda suka gaje shi, irin su Usman bn Kinana, wanda ya hau kujerar Malik, da Ibnu Nafi’u, Ibnul Majishun da Mudarrif bn Abdillah d.s.

Ibnu Wahab - duk da cewa; shi dan Misra ne - ana kirga shi cikin Makarantar Madina, saboda Manhajinsa irin nasu ne.

Amma ita kuma Makarantar Misra, ta fi riko da aikin “Ahlul Madina” da kiyasi da ra’ayi. Wato makarantar su Abdurrahman bnl Qasim, Ibnul Hakam, Asbag da sauransu.

Abin da zai nuna maka banbancin wadannan makarantu guda biyu shi ne abin da aka ruwaito daga Yahya bn Yahya al-Laithiy kamar haka:

"قال يحيى: كنت آتي عبد الرحمن بن القاسم، فيقول لي من أين يا أبا محمد؟

فأقول له: من عند عبد الله بن وهب.

فيقول لي: اتق الله، فإن أكثر هذه الأحاديث ليس عليها العمل.

ثم آتي عبد الله بن وهب، فيقول لي من أين؟

فأقول له: من عند ابن القاسم.

فيقول لي اتق الله، فإن أكثر هذه المسائل رأي".

ترتيب المدارك وتقريب المسالك (3/ 387)

“Yahya ya ce: Na kasance ina zuwa wajen Ibnul Qasim, sai ya tambaye ni; daga ina ka tafo?

Sai na ce: daga wajen Abdullahi bn Wahab.

Sai ya ce: ka ji tsoron Allah! Lallai mafi yawan wadannan Hadisan fa “Ahlul Madina” ba sa aiki da su.

Idan kuma na je wajen Ibnu Wahab, sai ya tambaye ni; daga ina ka tafo?

Sai na ce: daga wajen Ibnul Qasim.

Sai ya ce: ka ji tsoron Allah! Lallai mafi yawan wadannan mas’alolin fa ra’ayi ne kawai”.

To kasancewar “Mudawwana” ta Ibnul Qasim ita ta fi shahara, ta watsu wuri-wuri, shi ya sa 'yan baya suke gabatar da Ibnul Qasim a kan sauran almajiran Malik, kuma suke gabatar da “Mudawwanar” a kan sauran littatafan da suka ruwaito ra’ayoyin Malik ta hanyar almajiransa, kamar “Mustakharajah” ta al-Utbiy, da “Wadhiha” ta Ibnu Habib, haka kuma suke gabatar da Makarantar Misra a kan sauran makarantin, har Makarantar Madina, alhali Makarantar Madina ita ce uwa, jagororinta su ne suka gaji Malik, kuma su suka fi bin Sunna da Hadisi.

Misali a kan wannan, idan ka dauki mas’alar “Dora hanun dama a kan na hagu” a cikin Sallah, riwayoyi daga sauran Almajiran Malik wadanda suka saba wa Ibnul Qasim suna da yawa. Almajiran Malik, su Mudarrif, Ibnul Majishun, Ibnu Nafi’u, Ashhab, Ibnu Wahab, duka sun ruwaito HALASCI, MUSTAHABBANCI, da SUNNANCI daga Malik, amma Malaman Malikiyya ‘yan baya, irin su Khalil a cikin “Mukhtasar” sai suka gabatar da riwayar Ibnul Qasim ta KARHANCI a kan ta sauran, duk da cewa; nasu riwayoyin ne suka dace da Sunnar Annabi (saw) da Sahabbansa. Kamar yadda Sahnun a cikin "Mudawwanar" ya ce:

"قال سحنون عن ابن وهب عن سفيان الثوري عن غير واحد من أصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم: أنهم رأوا رسول الله صلى الله عليه وسلم واضعا يده اليمنى على اليسرى في الصلاة".

المدونة (1/ 170)

Ma'ana; an ruwaito daga Sahabbai da dama; sun ga Manzon Allah (saw) yana dora dama a kan hagu a cikin Sallah.

Shi ya sa Ibnu Abdilbarr ya ce:

"قال أبو عمر: لم تختلف الآثار عن النبي صلى الله عليه وسلم في هذا الباب، ولا أعلم عن أحد من الصحابة في ذلك خلافا".

التمهيد لما في الموطأ من المعاني والأسانيد (20/ 74)

"Riwayoyi daga Annabi (saw) ba su saba ba a wannan babi (dora hanu a Sallah), kuma ban san wani cikin Sahabbai da ya saba ba".

Kuma ya ce:

"قال أبو عمر: قد ذكرنا أن الصحابة لم يرو عن أحد منهم في هذا الباب خلاف لما جاء عن النبي صلى الله عليه وسلم فيه".

التمهيد لما في الموطأ من المعاني والأسانيد (20/ 76)

Saboda haka mu a nan Nigeria da sauran kasashen Afirka ta yamma duka Makarantar Misra ta Ibnul Qasim ce ta iso mana, wannan ya sa za ka ga a cikin Malikiyyar tasu akwai ra’ayoyi da yawa, wadanda suka saba Hadisai ingantattu. Shi ya sa Ibnu Taimiyya ya ce:

"إن مدونة ابن القاسم أصلها مسائل أسد بن الفرات التي فرعها أهل العراق، ثم سأل عنها أسد ابن القاسم. فأجابه بالنقل عن مالك، وتارة بالقياس على قوله، ثم أصلها في رواية سحنون، فلهذا يقع في كلام ابن القاسم طائفة من الميل إلى أقوال أهل العراق، وإن لم يكن ذلك من أصول أهل المدينة. ثم اتفق أنه لما انتشر مذهب مالك بالأندلس، وكان يحيى بن يحيى عامل الأندلس، والولاة يستشيرونه، فكانوا يأمرون القضاة أن لا يقضوا إلا بروايته عن مالك، ثم رواية غيره، فانتشرت رواية ابن القاسم عن مالك لأجل من عمل بها، وقد تكون مرجوحة في المذهب وعمل أهل المدينة والسنة، حتى صاروا يتركون رواية الموطأ الذي هو متواتر عن مالك، وما زال يحدث به إلى أن مات لرواية ابن القاسم، وإن كان طائفة من أئمة المالكية أنكروا ذلك".

مجموع الفتاوى (20/ 327 - 328)

Ma’ana; "Mudawwana" asalinta mas’aloli ne na ‘yan Iraq (Abu Hanifa) sai Asad bn Furat ya je wajen Ibnul Qasim da su (ana kiransu "al-Asadiyya"), shi kuma ya ba shi amsa da maganganun Malik, wasu kuma da ra’ayoyinsa. Wannan ya sa za ka samu Ibnul Qasim yana karkata zuwa ga ra'ayi, Manhajin 'yan Iraq, wanda ya saba Manhajin 'yan Madina...

Har ya kai ga a Andalus ana sanya ka’idar cewa; a Alkalanci dole ana gabatar da "Mudawwana" a kan sauran riwayoyi daga Malik. Duk da cewa; akwai ra’ayoyin da suke Marjuhai ne, wasu sun saba aikin "Ahlul Madina" ko Sunna. Har ya kai ga an bar "Muwadda" an koma riko da "Mudawwana".

Saboda haka, da wannan za ka fahimci cewa; abin da ya kamaci Ahlus Sunna a Nigeria shi ne bin Mazhabar Malik, Makarantar Madina, saboda ita ce mai aiki da Sunna, kuma ta fi bin Usul na Malik.

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments