Daga
Muhammad Abubakar Zabi
Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
08136844199
muhammadabubakarzabi@gmail.com
1.0 GABATARWA
Hausawa al’umma ce da ta
ginu bisa matakan rayuwa har guda uku. Da farko Hausawa sun gudanar da
rayuwarsu bisa tsarin al’adun gargajiya wanda ya fara tun daga haihuwa da aure
da kuma mutuwa. Hatta bautarsu a gargajiya suka gudanar da ita a wannan matakin.
Haka kuma, sun gudanar da rayuwa bayan karɓar addinin musulunci duk da haka ba su watsar da
al’adunsu na gargajiya ba. Bayan zuwan turawan mulkin mallaka rayuwarsu ta
gudana bisa sabon tsari. Duk da waɗannan sauye-sauyen matakan rayuwa bai sa Hausawa sun
watsar da al’adunsu ba. Akwai hanyoyi da dama da za a iya dubu ire-iren al’adun
Hausawa, ɗaya daga cikin hanyoyin
ita ce hanyar nazarin nomansu na gargajiya wanda suke amfani da shi tun matakin
rayuwar farko har ya zuwa wannan zamani da kuma irin tasirin zamanin da aka
samu a cikin harƙar noma a yau.
Abin da wannan bincike
ke son zaƙulowa shi ne taƙaitaccen tarihin Hausawa
sannan a waiwayi babbar sana’ar da Hausawa ke dogaro da ita wajen samar da
abincinsu da sauran al’amurran rayuwa don fito da wasu muhimman abubuwa. Daga
bisani takardar za ta duba ma’anar tattalin arziki, da kuma yadda tattalin Bahaushe
yake bunƙasa. A ƙarshe a duba irin
tasirin da barazanar zamani a ɓangaren noma a ƙasar Hausa, tare da duba
yadda zamani ya kawo koma baya ga tattalin arziki da aka samu a harkar noma.
1.1 HAUSAWA
Dangane da asalin Hausawa akwai ra’ayoyi
mabambanta a bayanin Dr. Mahadi Adamu (2010) mawallafin littafin “the Hausa
factors in West African History” a cikin darasin Yakasai cewa ya yi Hausawa su
ne mutanen nan waɗanda ƙasar Hausa ce ƙasarsu ta asali ko kuma
mutanen da suka shaƙu da al’adun Hausa”
A darasin Yakasai na aji
M. A ya kawo cewa wasu, cewa suka yi asalin Hausawa ya fara ne ta hanyar wani
mutum wanda ake ce masa Bayajidda (dan Abdullahi sarkin Bagadaza) wasu masana
kuwa suna cewa asalin sunansa Abu-yazid daga baya Hausawa suka mayar da sunansa
Bayajidda.
Shi kuma Dr. Hambali
Jinju a cikin darasin M. A na Yakasai 2015 yana ganin cewa dangane da tarihin
Hausawa tun gabanin zuwan baƙi, ana iya cewa a can daman akwai Hausawa a Daura tun
gabanin zuwan baƙi, a ƙalla shekaru dubu biyu
kafin farkon tatsuniyar Bayajidda. Sashen Hausawa da suka zo da Hausa a
cikin ƙasar Hausa sun fito ne daga masar ne, bayan ita masar
ta ya mutse, saboda yaƙe-yaƙe da waɗansu ƙasashe suka kai mata.
Har illa yau mutanen masar baƙar fata ne, kuma sarakunansu (Fir’auna) baƙaƙe ne har lokacin sharia
gida na ashirin da huɗu, su waɗannan mutanen Masar su
ne suka yi ƙaura zuwa Afrika ta yamma. Sun zauna bakin tafkin Chad
wanda a da can yana cike da ruwa ake waye kuma akwai daji da namun daji
iri-iri. Farare na Hamada sukan kawo hari da sannu Hausawan asali suka neman
mazauni.
A lokacin da suka fito
daga Masar suna ɗauke da harshen
Masiranci wanda ya sauya cikin tarihi ya zama Hausa.
Bunza A. M. 2011.kuma
cewa ya yi Hausawa su ne wanda uba da uwa da kaka, kakannin duk Hausawa to
wannan shi ne Bahaushe, amma idan an samu saɓanin haka misali uba Bahaushe uwa kuwa wata ƙabilar dabam to ya zama
barbarar yanyawa.
Yakasai 2015 cewa ya yi
tushen Hausawa bai wuce tsakanin Kano, Hadeja da Daura ba, daga nan ne suka
watsu zuwa wajajen Katsina, da Zazzau da Zamfara da kuma Kebbi.
A ganin Ɗanmasanin Kano da Mai
tama sule (2000). kuwa asalin Hausawa daga Habasha ne, garin cewa Habasha ne a
ka yi tuntuɓen harshe aka ce Hausa,
kuma maimakon Habashawa ne aka samun Hausawa. Asalin Hausawa dai na nan ƙasar Hausa tun asali,
kuma sun samu bunƙasar harshe da al’adu tun da daɗewa.
Bisa ga yadda masana da
manazarta suka ce za mu iya cewa, Asalin Hausawa shi ne, mutumin da yake jin
harshen Hausa, iyayensa Hausawa ne. kuma al’adun Hausawa sun yi tasiri gare
shi. ko da kowa ba a ƙasar Hausa yake zaune ba, to ya zama Bahaushe.
1.2 SANA’AR NOMA A ƘASAR HAUSA
Tun da Allah ya
halicci ɗan Adam ya samar masa da
sana’o’i iri-iri domin su kasance abin dogaro a gare shi wajen rayuwarsa ta yau
da kullum, saboda haka Hausawa a matsayin su na masu ƙoƙarin neman na kansu suka
riki noma babban muhimmi abu wanda yake kusan shi ne ƙashin bayan tattalin
arzikin ƙasarsu, kasha saba’in daga cikin ɗari na mazauna ƙasar Hausa manoma ne. Ba
shakka noma sana’a ce mai tarin albarka, wanda Bahaushe ya gada Iyaye da
kakanni saboda haka ne ake masa kirari da cewa “na duƙe tsohon ciniki” Da noma
ne al’ummar Hausawa suke samun abinci da abubuwan more rayuwa.
Hausawa sun kasa noma
zuwa gida biyu ta fuskar yanayin shekara. Akwai noman rani da noman damina.
Haka kuma ta fuskar abin da suke nomawa shi ma sun kasa shi biyu, wato noman
abinci da noman kadarorin sayarwa. Ga fasalin noman Hausawa:
·
Noman
ci
·
Noma
na sayarwa
Ire-iren noma a kasar
Hausa.
·
Noman
Damina
·
Noman
Rani
1.3 MA’ANAR TATTALIN
ARZIKI
Tattalin arziki abu ne
da ke ɗauke da ma’ana mai faɗi. Musamman idan
aka ɗauki Kalmar aka haɗa ta da wasu kalmomin
harshe. Misali tattalin haɗin kai, ko tattalin
fitina ko tattalin shirin aiki ko tattalin arziki kowace kalma a nan ma’anarta
daban, amma ƙunshiyar su ɗaya ce, wato tattali. Masana da manazarta sun bayyana
tattalin arziki da cewa
Umar (1983:1-2) ya
bayyana tattalin arziki da cewa
“Tsari ne na inganta ko
bunƙasa hanyoyin
shigar kuɗi da sauran abubuwa buƙatun
ɗan Adam, musamman abinci
da muhalli da sutura”
Shi kuwa kabakawa, B.U
(2012:37) cewa ya yi
“Tattalin arziki
ya ƙunshi tsarin samar
da abubuwa buƙata da yadda ake
rarraba su tsakanin
jama’a da kuma sigar
yadda ake amfani da su”
Auta, A.L.(2006:196)
cewa ya bayyana kalmar tattali arziki da cewa:
“Abubuwa guda uku ne
suka zama shika-shikan
ganuwar tattalin arzikin
Bahaushe da suka haɗa
da sana’o’i da kasuwanci
da ƙwadago, ga sarakuna
kuma a ɗauri ga haraji da
jangali da sauransu”
A nan ana iya cewa
tattalin arziki shi ne duk wata hanyar samun kuɗi da kuma adana su, da gudanar da sana’o’in da al’umma
ke aiwatarwa ta hanyar amfani da abubuwan da al’umma ke buƙata na gudanar da
rayuwarsu ta yau da kullum in aka kula da su bisa tsari shi ake ƙira tattalin arziki.
1.4 BUNƘASAR TATTALIN ARZIKI
BAHAUSHE.
A gargajiyance akwai
hanyoyin da yawa da Bahaushe ke bi don haɓaka ko kawo ci gaban tattalin arzikinsa. Waɗanda suka haɗa da sana’o’insa tare da
yanayin tsarin zamantakewarsa. Idan aka dubi waɗannan sai a ga cewa wasu muhimman hanyoyi ne da
Bahaushe ke bi don bunƙasar hanyoyin tattalin arzikinsa.
Sana’o’in gargajiyar
Hausawa su ne mafi girman tafarkin tattalin arzikin da Bahaushe ke bi don samar
wa kansa abubuwan da yake buƙata don gudanar rayuwarsa ta yau da kullum. Da sana’a
yake sarrafa dukkan albarkatun ƙasa da sauran ni’imomin
da Allah (S.W.A) ya yi masa, kuma sauran abin da ya samu a sana’arsa yake
musanyawa ya mallaki abubuwan da bai da su a yanayin ƙasarsa.
Babbar sana’ar Bahaushe
ita ce noma, wanda wannan sana’ar ta samar da sana’o’i da yawa. Wanda haka ya
taimaka wajen bunƙasar tattalin arzikin Bahaushe. Ga kaɗan daga cikin sana’o’in
da sana’ar noma ta samar:
·
Ƙira
·
Sassaka
·
Tubka
·
Kaɗi
·
Dakau
·
Fatauci
·
Kiɗa da waƙa
·
Dako
·
Ƙwadago
·
Sakai
·
Awo
·
Ujula
·
Tauri,
sussuka, koda
·
Kiwo
– wajen amfani da kashinsu (Toroso) a matsayin taki
·
Sana’o’in
mata
·
Toye-toye
·
Dafe-dafe
·
Ɗinki-ɗunke
1.5 TASIRIN ZAMANI
A ƁANGAREN NOMA A ƘASAR HAUSA.
Hausawa suna yin noma
iri biyu, na abinci da na sayarwa. Kayan noma na abinci sun haɗa da gero da dawa da
masara da maiwa da sauransu. Waɗanda ake nomawa domin
sayarwa sun haɗa da auduga da gyaɗa da wake da riɗi da sauransu. Ƙasar Hausa tana da
albarkar noman wasu abubuwa kamar Rogo da Dankali da ‘ya’yan itatuwa irin su
Mangwaro da Gwaba da Gwanda da sauransu (Yola, M.M. 2014: 508-509).
Zamani ya yi tasiri
kwarai da gaske a kan sana’ar noma domin bayan shigowar Turawa ƙasar Hausa an samu sauƙi a kan yadda ake yin
noma ta hanyar amfani da Shanu ko Motar huɗa, sannan kuma an samu sinadarin da zai taimaka wa
shukar da aka yi ta fito da wuri ta hanyar amfani da “Takin zamani” Hatta ga
iri da ake amfani da su wajen shuka zamani ya zo da masu saurin fitowa. An kuma
samu magungunan ƙwari da ake amfani da su wajen yi wa shuka feshi. Haka
yake sakamakon tasirin zamani ya jawo yanzu a ƙasar Hausa ana samun iri
wanda kafin damina ta wuce za a iya shuka shi sau biyu. Wato irin baya wuce
kwana 35-40 kamar Wake, Gurjiya da sauransu. Haka kuma a karni na 21 an samu ci
gaban da za a samu dawa ko Masara ta fito da kayuwa kamar uku ko huɗu ita kuma Masara saboda
tasirin zamani an samu mai yin goyo da yawa a jiki kara guda.
An samu Ƙarin wani nau’in noma
tare da yadda ake gudanar da shi wato “Nnoman rani” Hausawa da ke zaune kusa da
fadama ko gulbi ko kogi su ne waɗanda suka fi yin noman rani. Wannan noma ne da ake yi
wa ban ruwa ta hanyar amfani da “Jigo” Zamananci ya sa yanzu da na’ura wuta ake
ban ruwa wato inji mai amfani da man fetur ko gas (Yola, M.M 2014: 508-509)
Ta ɓangaren noman rani a
wannan ƙarni na 21 an samu tasirin zamani a cikin sa ainun ta
fuskar abin da ake nomawa da kuma kayan aikin. Yanzu kamar tumatir, tattasai,
taruhu, masara, a wannan lokaci shi ma an samar da irin da zai dace da wannan
yanayi, wanda zai nuna da wuri. Sai kuma ta ɓangare itatuwa, shi ma wannan ɓangare zamani ya yi
tasiri a kansa ainun, domin a zamanin da kamar itacen Dibino, Mangwaro, Gwanda,
Kashu, Gwaba da sauran itatuwa. Za a shuka, amma kafin a amfana da su za a
jima, a wannan zamanin kuwa za a ga har dibino da ake cewa in ka shuka sai dai ‘ya’yanka
su amfana, to yanzu an samu na zamani wanda cikin shekara guda zuwa biyu zai
yi, har al’umma su amfana da shi.
Ta fuskar yanayin adana
kayan da aka noma shi ma zamani ya yi tasiri bisa. Alal misali a zamanin da
al’ummar Hausawa kan yi amfani da Rumbu ko kuma su bar abin cikin konsonsa. A
wannan zamani abin ba haka yake ba. Zamani ya zo da abubuwa adana amfani ta yadda
wasu suna amfani ne da magani, wasu kuma suna amfani da rumbun gwamnati wato
“silo” da akwai abubuwa da dama da zamani ya zo da su.
Haka kuma ta ɓangaren abin da ya shafi
kayan aikin gona, shi ma wannan zamani bai bar shi a baya ba. Domin a zamani da
a kan yi amfani da Fartanya, Magirbi, Sungumi, Garmar huɗa da sauransu. Amma a
wannan zamani sai ga shi shukar kan ta akwai inji mai yenta, noma akwai matar
noma, da kuma girbi. Ta kai ma har sussuka akwai inji mai yi. A wannan karni na
ashirin ɗaya an samu ci gaba
domin yanzu a kan samu mota guda da za ta yi shuka da girbi kuma ta yi sussuka
a lokaci guda.
1.6 BARAZANAR ZAMANI A
KAN SANA’AR NOMA A ƘASAR HAUSA.
Zamani yana barazana
wajen koma baya ga tattalin arzikin Bahaushe ta fuskoki da dama.
1-
Domin
a zamanin da a kan ɗebe mutane da yawa wajen
zuwa aikin ƙwadago su samu abin da za su dogara da shi, domin
sarrafa rayuwarsu cikin sauƙi. Yanzu lamarin ya canja, aikin da mutum ɗari za su yi, inji zai
iya aiwatar da shi cikin lokaci kaɗan.
2-
Zamani
ya haifar wa da Bahaushe ya daina noman ci, sai dai noman sayarwa. Sakamakon
haka ya sa, Bahaushe baya iya ciyar da kansa sai ya yi oda. Domin ya fi mayar
da hankali ga noman da zai samu kuɗi, ga noma abin da zai ci. Wannan barazanar zamani ne
ga al’ummar Hausawa, domin koma baya ne ga su kansu.
3-
Zamani
yana barazana a kan tattalin arzikin Bahaushe, shi dai ya samu kudi da wuri.
Maimakon ya je ya yi noma. Misali yanzu an fi son a yi aikin albashi ko kuma
zuwa wani aikin da za a yi shi nan take a samu kuɗi,
4-
Barazanar
da zamani ya kawo wa matasa sun dogara da kananan sana’o’i, misali achaɓa, wankin takalmi, ko
cajin waya, maimakon noma don bunƙasar tattalin arzikinsu,
da ma ƙasar su baki ɗaya.
5-
Wannan
barazanar zamani a kan tattalin arzikin Bahaushe da ya sa matasa suke kwararowa
birane domin samun rayuwa ta jin daɗi, maimakon su koma kauye su yi noma, su bunƙasa tattalin arzkinsu.
Domin a ƙauye ne ake noma ba birni ba.
6-
Haka
kuma abin da zamanin ya zo da shi ta fuskar takin zamani da ake amfani da shi
yana kashe ƙasa. Da kuma illa ga jikin mutane. Maimaikon da ka
noma buhu biyar, to in shekara ta juyo da kyar za ka samu buhu biyu a gonar;
matuƙar ba ka sa Takin zamanin ba.
7-
Haka
kuma ta ɓangaren magunguna da ake
feshi a amfanin gona, yana kawo illa ga jikin ɗan Adam. Misali kamar masu kiwo
kaji, suna amfani da wata allura wato, “Stylbesterol hormone”. Wannan allura
ana yi wa kaji domin ƙara kuzari da girma; duk mutumin da ya ci kajin za iya
samun ciwon kansa. Haka kuma akwai wani maganin feshi da ake amfani da shi wato
“thermic” shi kuma yana jawo gurɓatar yanayi.
2.1 KAMMALAWA
Wannan aiki ya yi Magana
ne a kan noman Hausawa na gargajiya da kuma na zamani, da kuma irin tasirin
zamananci. Da farko an duba su waye Hausawa da asalinsu . Sannan sai aka duba
tattalin arziki a ƙasar Hausa. Da kuma hanyoyin bunƙasar tattalin arzikin
Bahuashe. Daga ƙarshe aka duba tasirin da zamanin ya kawo ta fuskoki
guda biyu wato, ci gaba da ya kawo da kuma ci bayan da ya kawo.
Takardar ta gano cewa
zamananci ya yi tasiri ƙwarai da gaske a cikin harƙar noma, wanda za a yi
cewa an samu tasiri mai kyau da maras kyau. Tasiri mai kyau shi ne, inda aka
samu ƙarin hanyoyin inganta harƙar noma. Haka ta gano
cewa zamani na barazana ga tattalin arzikin Bahaushe matuƙar ba a sake wasu dabaru
ba. domin, zamani yana neman kawo cikas wajen rashin aikin yi tsakanin al’ummar
Hausawa. Da kuma haifar da wasu cutattuka a jikin mutane ta hanyar yin amfani
da magunguna da zamani ya zo da su.
MANAZARTA
Abdulrahaman, A. (2005) “Bukukuwan
Gargajiya na ƙasar Hausa Madubi ne na Ƙyallaro Rayuwar Hausawa
ta Asali” Aikin jinga da aka Bayar. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan
Nigeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Adamu, M. (1978) “The Hausa Factor in
West African History”. Zaria: Amadu Bello University Press.
Adamu, M. T(1997) “Asalin Hausawa da
Harshensu”, Kano Ɗan Sarki Publisher
Adamu A. U. (2005)
“Hausa da Hausanci a ƙarni Na 21: Ƙalubale da Madosa”.
Takarda da aka gabatar a taron wuni guda kan jama’a game da haraƙar fim, Kano: Cibiyar
Nazarin Al’adun Hausawa.
Amfani. A. H (2004) “The Development From
Colonial Period to Modern Day States” Ɗundaye Journal Of Hausa
Studies, Department of Nigeria Languages. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo
Alhassan, H. (1982) Zaman
Hausawa 2. Islamic Publication Bureau, Lagos.
Auta, A. L (2006) “Tattalin Arzikin
Al’umma: Nazairin Sana’o’i da Kasuwancin Hausawa” A cikin Algaita, Kano :
Jami’ar Bayero
Bagudo, F. A. (2009) “Gudummuwar Matan
Sokoto Wajen Bunƙasa Tattalin Arziƙin ƙasa”. Kundin Digiri Na
Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
Bello, A. Y (2006) Kirarin Abincin Hausawa
da yadda ake yin su a jahar Saƙƙwato” kudin digiri na farko, Jami’ar
Usumanu Danfodiyo.
Bunza, A. M (2011)
“Sakkwato ce Asalin Hausa In ji Naranbaɗa Laluben Gudumuwar Makaɗa a kan Asalin Bahaushe da Harshensu” Takardar da aka
gabatar a taron ƙara wa juna Sani. Katsina: Jami’ar Umaru Musa Yar’adua
Bunza, A. M (2014)
“Katsina rumfar Hausa Gamji Matattar Tsuntsaye” Takarda da aka gabatar a
taron ƙara wa juna Sani. Katsina: Jami’ar Umaru Musa Yar’adua
Bunza, A. M (2014)
“Matakan Kyallaro Asalin Bahaushe: (Ruwa Na ƙasa Sai Ga Wanda Bai
Tona Ba) Takardar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sanin
a ƙasa-da ƙasa na Farko a Jami’ar
Kaduna.
Bunza, A. M (2014)
“Bitar karatun Hausa A Ƙarni Na Ashiri da Ɗaya 21(wuri da
Babu Ƙasa ake Gardamar Kokuwa)” Takardar da aka Gabatar a
Sashen Nazarin Harsuna Nijeriya, Kano: Jami’ar bayero
Bunza, A. M (2015) “A ji
Bahaushe, A ga Bahaushe, A san Bahaushe Ya Yi ( Tsakuren Ficen Bahaushe da
Tasirinsa a Duniyar Ƙarninsa)” Takardar da aka gabatar a walimar dr.
Ibrahim Sarkin Sudan Kwantagora Zuwa Associate Professor A ƙangaren Al’ada.
Funtuwa, S. A. (2006) “Ƙananan Sana’o’in Hausawa
Da Yadda Ake Aiwatar Da Su: Nazari Na Musamman a Kan Sana’ar Ƙwadago Da Ate, da Dako,
da Yankan Farce, da Gyartai”. Kundin Digiri Na Ɗaya. Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto.
Kabakawa, U.B (2012) “ Mahangar makaɗan baka dangane da
tattalin arzikin Hausawa” Saƙƙwato. Kundin Digiri na biyu, sashen koyar
da harsunan Najeriya, Jami’ar Usumanu Ɗanfodiyo.
Yakasai, S. A (2015) Darasin ajin M.A na
(Hau 801) Historical Linguistics. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Yola, M.M (2014) Sana’o’in Hausawa na
gargajiya: “Garkuwar adabin Hausa”:A festschrift in tribute to Abdulƙadir Ɗangambo.
Zabi, M. A (2014)
Matsalolin Amfani Da Maganin Kwari A Kayan Gona Unpublished
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.