Daga
Muhammad Abubakar Zabi
Department of Nigerian
Languages and Linguistics
Sa’adu Zungur
University, Bauchi
08136844199
muhammadabubakarzabi@gmail.com
Da
Abdulsalam Alhaji
Jibrin,
School of Secondary
Education (Languages).
Aminu Saleh, College of
Education, Azare
abdulsalamalhajijibrin@gmail.com
Tsakure
Fulani da Hausawa
al’umma ce daɗɗiya wadda ban Allah ba
wanda ya san lokacin haɗuwarsu, sakamakon ƙarancin kayan rubutu a
wancan lokacin. Fulani na cikin ƙabilu na farko-farko da
Hausawa suka fara cuɗanya da su. Wannan shi
ya kawo bazuwar Fulani ko’ina cikin ƙasar Hausa. Shi ya sanya
wasu maƙwabtansu na nesa ke yi musu kallon abu guda. Haka kuma
shi ya samar musu da sunan Hausa-Fulani sakamakon daddediyar mu’amala wace ta
saka suka cakuɗa da juna, wanda yanzu
an kai fagen da Bafulatani ko Bahaushe ba zai iya tantance cewa shi kaza ne,
saboda an yi auratayya an kuma gauraya waje guda. Wanda zai yi wuya ka ƙirga kaka biyu ko uku na
zuriyarku ba ka tarar da wani sirki na Bahaushe ko Bafulatani ba. Ko ta wajen
Uwa ko ta wajen Uba. Wannan aikin zai waiwaci asalin Fulani a takaice da na
Hausawa da zamatakewa da suturar Fulani da kuma suturar Hausawa. A taƙaice wannan takarda za
ta duba yadda ake kallon Hausa Fulani a idon na kusa da na nesa.
1.0 Gabatarwa
Hausawa da Fulani, wasu
al’umma ce da Allah kaɗai ya san irin ajiyar da
ya yi. Ku san za a iya cewa haɗin Allah ne, wanda duk
ya ce zai raba Hausawa da Fulani to! Tamkar zai iya raba hanta da jini ne.
Dangantakar zamantakewar Hausawa da Fulani mahdi ne mai dogon zamani. Abu ne
mawiyaci a iya gano lokacin da Hausawa da fulani suka fara hulɗa. A ruwayar Maigandi
Attahiru (2003) masana irin su Malam Abdullahi Gwandu da Waziri Sakkwato da
suka yi faɗi tashin gane hakan sun
yi kirdadon gano cewa, Fulani na cikin ƙabilu na farko-farko da
Hausawa suka fara cuɗanya da su. Wannan shi
ya kawo bazuwar Fulani ko’ina cikin ƙasar Hausa. Shi ya sanya
wasu makwabtansu na nesa ke yi musu kallon abu guda kawai, kamar Iyamurai da
Yarbawa da sauransu ƙabilu na nesa. Haka kuma shi ya samar musu da sunan
Hausa-Fulani sakamakon daɗɗeɗiyar mu’amala wace ta haɗa juna, wanda yanzu an
kai fagen da Bafulatani ko Bahaushe ba zai iya tantace cewa shi kaza ne, saboda
an yi auratayya an kuma gauraya waje guda. Wanda zai yi wuya ka ƙirga kaka biyu ko uku na
zuriyarku baka tarar da wani sirki na Bahaushe ko Bafulatani ba. Ko ta wajen
Uwa ko ta wajen Uba.
1.1 Waiwaye
Funtua (2010) ya gabatar da muƙala mai taken Tufafin
Hausawa da Fulani na gargajiya. Bayan ya kawo gabatarwa sai ya kawo ire-iren
tufafin Hausawa na gargajiya. Yanda ya yi bayanin tufafin maza da mata, da kuma
tufafin da baƙi suka kawo. Alaƙar wannan muƙala da wannan takarda
shi ne ya taɓo wani abu daga cikin
abin da takardar take son duba wa wato tufafin Hausawa da Fulani, amma ta yadda
suka bambanta shi ne ta yadda shi yana Magana a kan tufafi ne ita kuma tana
Magana akan yadda na kusa da na nesa ke kallon Hausa fulani.
Shi kuma Ɗanmaigoro, (2010). Ya
gabatar da takardarsa mai taken Magungunan Hausawa da Fulani. Bayan ya kawo
gabatarwa sai ya duba Bokanci da Bori da Maita da Tsibbu da Magori da Ungozoma.
Sannan sai ya duba Magungunan sana’o’i, yanda ya duba Wanzamai da Maƙera da Mahauta da
Masunta da kuma Maɗora. Daga ƙarshe kuma ya kawo
muhimmancin magungunan gargajiya ga Hausawa da Fulani. Wannan takarda alaƙarta da wannan shi ne
yana Magana akan al’ummun Hausawa da Fulani, amma ta yadda a ka bambanta shi
ne, yana magana akan magani ita kuma wannnan takarda tana magana akan kallon da
makwabtan Hausa- Fulani ke yi musu.
Busa da Isa (2015) sun gabatar ta takardar
su mai taken kalmomin Makwabtan ƙabilu a harshen Hausa.
Yanda suka duba mene ne harshen Hausa da kuma Hausawa da makwabtansu, da
are-aren kalmomi daga makwabtan Hausawa zuwa harshen Hausa. Sai kuma su ka yi
bayani dangane da al’ummar Fulani da kuma kalmominsu da aka ara. Yarbanci da
kalmominsu. Da Barebari da kalmominsu da aka ara, da al’ummar Azbinawa da
kalmominsu da aka ara, da al’ummar Nufe da kalmominsu da aka ara, da
kumaal’ummar Gwari da kalmomin da Hausawa suka ara. Ita kuma wannan alaƙar da ke akwai tsakani,
yana magana akan harshen maƙwabtan Hausa, ita ma wannnan takarda tana magana akan
maƙwabta ne, don haka zuwan wannan takarda zai taimaka wa
aikin wajen kammaluwa.
1.2 Ra’i
Wannan takardar ta yi
amfani da Tsarin Mu'amala (Contact Theory) a matsayin hanyar nazari don gano
yadda hulɗa tsakanin mutane daga
al'ummu daban-daban ke shafar yadda suke kallon Hausawa da Fulani. An zaɓi wannan ra’i ne saboda
yana bayyana cewa, idan mutane suka yi mu'amala mai kyau, za su canza
ra'ayoyinsu game da juna."
1.3 Asalin Hausawa A Taƙaice
Sanin asalin Bahaushe
kundi ne mai faɗin gaske. Domin Bahaushe
mutum ne mai daɗaɗɗen tarihi bisa
doron ƙasa. Masana da dama sun ambaci haka akan wa za a kira
Bahaushe. Masana ilimin kimiyyar harshe da tarihi da al’ada sun sha gwagwarmaya
wajen gano wane ne Bahaushe. Haƙiƙa an daɗe ana ɗauki ba daɗi wajen bin diddigin gano Bahaushe na asali. Daga
cikin irin waɗannan masana ilimin
harsuna akwai, Schuh da Yalwa (1993) sun bayanna cewa:
Yaren Hausa harshen
na ɗaya daga cikin Harshen
Chadi (ɓangaren iyalan
Afro-Asiatic). Sun bayyana cewa Hausawa na a yammacin Tafkin Chadi ne, amma sun
warwatsu a wurare daban-daban. Daga cikin wannan akwai Arewacin Nijeriya da
Nijar da Chadi. Haka kuma, Harshe ne da ya bunƙasa wajen kasuwanci
a ƙasashen Afrika ta yamma, da Afrika ta tsakiya da
kuma ɓangaren Arewa maso Yamma
da Sudan.
Jinju, (1985) a nasa
binciken ya ce:
Mutanen
Masar baƙar fata ne kuma sarakunansu (Fir’aunoni ne), baƙaƙe ne har lokacin
sarautar gida na ashirin da huɗu. Su waɗannan mutanen Masar su
ne a ganina suka yiwo ƙaura zuwa Afirka ta yamma suna zaune a bakin tafkin
Chadi wanda can da maƙil yake da ruwa. A wannan lokaci ne mutanen farar fata
suka riƙakai masu hari, sai suka yi ƙaura suka canza wurin
zama tare da harshen su na misiranci wanda ya canza ga tarihi ya koma Hausa.
Duka waɗannan bayanai ba su isa
su tabbatar muna da asalin Hausawa da harshensu ba. Domin harshe kaɗai ba iya tabbatar da
asalin mutum. Zancen zaman Hausawa a gaɓar Kogin Chadi da alaƙar harsunan gidan Chadi
wani wuri ne da Hausawa suka zauna na ɗan lokaci, daga baya suka canza wurin zama.
Haƙiƙa Smith ya ce, wani abu
game da wane ne Bahaushe, kasancewar kowane Bahaushe yana iƙirari da harshensa na
Hausa a matsayin asali. Hausawa da dama sukan yi kamannu da junansu. Ra’ayin
Smith ya so ya yi kama da na Adamu (1978) da yake cewa:
Hausawa ne daɗaɗɗun mazauna Hausa da
dukkanin zuriyarsu ta fuskar maza, ko kuma waɗanda suke amfani da al’adun Hausawa da riƙe harshensu da
addininsu.
Shi kuwa Bunza (1990) ya
bayyana cewa:
Hausawa dai mutane ne da
suke zaune a ƙasar Hausa tun
Farkonta, kuma suna da
zuriya a cikinta har ya zuwa yau
Kazalika, suna magana da
harshen Hausa ba su da wani
Harshen in ba Hausa ba,
suna da ɗabi’u da al’adu irin na
Hausawa. Idan sun saɓa haka to barbarar
yanyawa ne.
Kamar yadda muka gani
cewa masana sun kawo wane ne Bahaushe: Bisa ga yadda masana da manazarta suka
ce za mu iya cewa, Bahaushe shi ne, mutumin da yake zaune a ƙasar Hausa, ta fuskar
launi kuma baƙi ne; kuma iyayensa Hausawa ne, idan kuma ba a ƙasar Hausa yake zaune
ba, ya kasance yana jin Hausa, kuma wasu al’adun Hausawa sun yi tasiri a gare
shi, to wannan shi ne Bahaushe.
1.4 Asalin Fulani A Taƙaice
Masana da suka yi rubutu
a kan asalin Fulani sun bayyana shi a zaman mai sarƙaƙiya kamar na Hausawa.
Daga cikin waɗanda suka yi
wannan ƙoƙarin sun haɗa da Malam Abdullahi Gwandu ƙanin Mujaddadi Shehu
Usmanu Ɗanfodiyo da Wazirin Gwandu.
Malam Abdullahi A cikin
littafinsa, Tazyin al-waraƙat cewa, Fulani sun fito ne daga tsatson Uƙubatu ɗan Nafi’u wanda ya ce
Balarabe ne kuma Sahabi Babba. Ya zo ƙasar Masar inda ya auri
ýar Sarkin garin mai suna Bujja Mugga sai suka haifi ýaýa huɗu waɗanda su ne asalin Fulani
da Fulatanci.
Shi kuma Wazirin
Sakkwato Malam Junaidu a littafinsa Tarihin Fulani cewa ya yi Fulani sun ta so
ne daga Durisininata ƙasar Sham har suka iso futa Toro ta ƙasar Sinigal suka zauna
garin har suka yi yawa. Nan ne a cewarsa Uƙubatu ya sadu da su har
suka shiga addinin musulunci. (Junaidu, 1978)
Ƙari ga wannan ra’ayin
Waziri Junaidu ya rawaito cewa akwai masu ra’ayi Fulani asalinsu zuriyar Rama
ne ɗan Annabi Ishaƙa ɗan Annabi Ibrahim (A.S)
ya kuma bayyana ta la’akari da wannan ra’ayi cewa, sun ta so ne daga futa Toro
da nufin komawa ƙasar Larabawa a ƙarƙashin jagorancin wani
babban Malami Musa jakollo. Daga cikin zuriyyarsa ne aka haifi Shehu
Usmanu Ɗanfodiyo. Sun zauna a ƙasar Gobir ana kiransu
da suna Torankawa saboda fitowa daga Futo Toro. (Junaidu, 1978)
Haka kuma bincike ya
nuna cewa zaman farko na Fulani yan yankin ƙasar Senegal ne na
Afirka ta yamma. Daga nan ne sannu a hankali suka ba zu zuwa ƙasashen chadi da Kamaru.
A cikin ƙarni na sha huɗu ne suka shigo ƙasar Hausa. Dalilin
shigowar Fulani ƙasar Hausa kuwa shi ne, sanadiyar ƙaura da suke yi daga
Senegal zuwa gabashi, domin neman makiyaya mai kyau. A cikin farkon ƙarni na sha shida akwai
al’umomin Fulani masu yawan gaske a ƙasar Hausa . sannu a
hankali kuma a cikin ƙarni na sha bakwai wasu Fulani da ke zaune ƙasar Hausa suka yi kudu
maso gabas har suka iso kogin Gongola suka mamaye wurin saboda yanayinsa na
dausayi da makiyaya mai kyau. Fulani ba su da wata sana’a wadda ta wuce kiwo. A
yau al’ummar Fulani sun haɗe da ta Hausawa har ma
ana ganinsu a matsayin al’umma ɗaya. (Funtua 2010)
Ta la’akari da yadda
masana da manazarta suka ce dangane da asalin Fulani za mu iya cewa,asalin
Fulani Larabawa ne wanda asalinsu a gabas ta tsakiya suke, kuma suna daga cikin
zuriyar Annabi Ibrahim (A.S). Saboda yanayi da kuma ƙaura-ƙaura ce na neman abinci
da wajen kiwo ya sa Fulani barin wajen su na asali suka zo yadda suke zaune a
yanzu.
1.5 Zamantakewa
Zamantakewa na nufin
kamar yadda sunan ya nuna daga Kalmar zama, wato abin nufi a nan shi ne zaman
tare, ya’allah ko dai ta fuskar zumunta ko makwabta, ko kuma ta fuskar yanayin
sana’a, ko da yake ma’anar takan iya wuce wannan idan aka yi la’akari da ire-iren
dangantakar da ake samu tsakanin al’umma.
Hausawa sun daɗe suna hulɗa da ƙabilun da ke zagaye da
su. Wannan kuwa ya faru ne a sanadiyar kasuwanci ko ƙaurace-ƙaurace. A cikin gida
Nigeriya za a iya kasa zamantakewar Hausawa da sauran ƙabilu zuwa gida biyu.
Gidan farko shi ne Hausawa da sauran ƙabilu da suke a rewancin
Nigeriya. A arewa harshen Hausa ya zama harshen ƙasa wanda da
sauran ƙabilu ne ke amfani da shi. Idan ƙabilu uku ko huɗu sun haɗu harshen da suke amfani
da shi wanda kowannensu na ji shi ne harshen Hausa. Don haka ma a jamhuriya ta
farko aka mai da harshen Hausa ya zama harshen da ake amfani da shi a majlisar
dokoki ta kaduna. Hausawa sun bazu ya zuwa sauran garuruwan ƙabilun arewacin Najeriya
irinsu Jos, da Adamawa, da Borno da Bauchi da Kaduna da kuma Niger da sauransu.
Haka kuma al’adunsu da suka haɗa da abinci da tufafi da
muhalli duka sun sami karɓuwa a jahohin Nigeriya,
da wanda ba na Hausa ba.
A ɓangaren zamantakewa kuma
da makwabtan Hausawa a kudanci da gabashin Najeriya kuwa, Hausa na da
kyakkyawar alaƙa ta kasuwanci da su. Da yake zamantakewar Hausawa
da ƙabilun da ke kewaye da su ta bambanta da yadda take da
jama’ar kudanci ko gabashi, wannan ne ya sa Hausa cakuɗuwa da waɗannan al’ummu, sai suka kakkafa unguwanni nasu
yasu-yasu. A kudanci Nijeriya. Hausawa kan kira waɗannan unguwanni da suna “Sabo” Don haka, ne suke da
sabo-Ibadan, Sabo- ile-ife. A kudancin Najeriya kuwa akwai unguwannin Hausawa
irinsu Agana Bodi da sauransu. A sakamakon zamantakewar Hausawa da Fulani, aka
samu alaƙa ta kusa sosai wanda har ta kai yanzu ba a iya
bambance Bahaushe da Bafulatani. Auratayya tsakanin Hausawa da Fulani, Fulani
suka wanke Bahaushe ya zama kyakkyawa mai kyan siffa, koma bayan a da Bahaushe
baki gajere mai
ƙaton kai.
1.6 Hausa-Fulani Gani
Daga Nesa
Bisa dukkan alamu
makwabtan Hausa-Fulani da suke nesa suna yi wa Hausa-Fulani kusan abu ɗaya, amma abin ba haka
yake ba, saboda duk wani Bahaushe da ya taho daga Arewa ko Bafulatani, wanda ya
yi karatu da wanda bai yi karatu ko ɗan kasuwa gani suke duk abu guda ne. Domin su ba sa
la’akari da wasu ɗabi’u ko halaye ko kuma
al’adu da ke bambanta su. In dai ba shanu suka ga mutum yana kiwo ba, ko
Bafulatana tana tallan nono ba; to kawai Hausa-Fulani ne. Su a kallonsu wanda
yake kiwo shi ne Bafulatani, amma duk wanda ya zo da saɓanin haka kawai za su kira shi da Hausa-fulni ne.
1.7 Hausawa A Idon Maƙwabtansu
Masu kallon Hausawa da
Fulani na kusa da alama kallonsu ya sha bamban da kallon da maƙwabtansu na nesa su ke
yi musu. Su makwabta na kusa suna iya bambance Bahaushe da Bafulatani ta waɗannan fuskoki:
-
Sunaye
-
Sutura
-
Muhalli
-
Al’adunsu
na bukukuwa da
-
Addini
1.7.1 Sunaye – Ta hanyar Suna maƙwabta na kusa na iya
bambanci Hausawa da Fulani. Ma’anar suna a fannu yana nufin wata keɓɓeɓiyar kalma da wata
al’umma ta yarda da ita domin ƙira ko ambaton wani
mutum ko wata dabba ko tsiro ko wani abu mai rai ko maras rai (mace ko namiji)
ta yadda za su bambanta da junansu ko makamantansu.
Masana da manazarta sun
tofa albarkacin bakin su game da ma’anar suna kamar haka:
CNHN (2006) sun bayyana
suna da cewa kalma ce da ake amfani da ita wajen ƙira ko ambaton wani abu.
Bargery (1963: 956) ya
ce suna kalma ce da ake ƙiran mutum ko bukin da ake yi a rana ta bakwai ta
haifuwar yaro ko yarinya a cikin al’ummar Hausawa.
Daga waɗannan bayanai, muna iya
cewa suna wani abu ne da mutune suke saka wa wani abu mai rai ko maras rai
domin ƙiransa da shi, a tantancewa da bambantawa.
Misalin Sunayen sun haɗa da:
Hausa Fulantanci
Gambo Haro
Juji Lari
jinjiri Yiɗi
Zinaru Innayo
Kyauta Toka
Kanta Kaku
Ayashe Junguɗo
Talle Bello
Magaji Shanono
Korau Juli
Tunau Ori
Haka kuma, ta waɗannan sunaye maƙwabtan Hausawa da Fulani
na kusa na iya tantace waye Bahaushe ko Bafulatani daga zarar an ambaci
sunansu.
Haka kuma, ta fuskar
suturar Hausawa da Fulani maƙwabtansu na iya bambance su. Ita dai asalin kalmar
sutura dai ararriyar kalma ce daga larabci(suturatu) da manufar tufafi da ke
rufe wa mutum al’aurarsa, wato dai duk tufafin da ke isar mutum Musulmi ga yin
sallah. Amma a wajen Bahaushe Kalmar tana da ma’anar tufafi isassu da za su
kare mutuncika daga tsiraici da kowanne iri ne, sababbi ne, ko tsofaffi in dai
sun kare tsiraici, ana kiransu sutura. Misalin tufafin sun haɗa da:
1.7.2 Tufafin Hausawa
Gyauto Wando Fatari
Zani Rawani Mayafi
Riga Taggo Fatala
Tufafin Fulani
Fulani kamar yadda aka
sani Makiyaya ne. Don haka akasarin tufafinsu ƙanana ne ba kamar na
Hausawa ba. Haka kuma Fulani suna rikon al’ada matuƙa. Dalili kenan ake
ganin ba su cika aron al’adun wasu baƙi ba ta fuskar
tufafi. Ɗan dama- dama a wannan lokaci yaransu sun ɗan ari suturar Turawa,
wato ƙanana riga da jeans. Sakamakon yadda tela yake ba su
wahala. Daga cikin tufafin Fulani akwai na maza da na mata kamar haka:
Tufafin Fulani maza
manya da yara, Fulani suna sa rigar saki ce mai kama da yar shara wadda aka yi
wa ado da ulu a wuya da gaba. Tana da aljihu biyu a gefenta. Sukan kuma haɗa ta da wando wanda ake
kira “ka-haye-ruwa” . Sannan su sa hula haɓar kada wadda ita ma aka yi wa ado da zaren ulu. Haka
kuma suna ya fa gwado a saman rigar sannan su rike sanda, da madubi, wani sa’in
da malafa da jallo. Mata kuma suna sa rigar saki ce wadda aka yi wa ado sosai a
gabanta da zaren ulu ja da kuma fasasshen madubi. Tsawon rigarsu bai wuce
cibiya. Suna ɗaura adiko a ka, su
kuma ɗaura zane da ake kira
mudukare. Fulani mata ba su da tufafi da yawa kamar na Hausawa.
Amma a wannan zamani, su
Fulani ba su aro kayan wasu daban ba, sai dai kayan Hausawa. Sakamakon
zamantakewar da ke tsakaninsu. Bisa ga yadda maƙwabtan Hausawa da Fulani
suke tare da su, da zarar sun ga tufafin za su iya bambance su, cewa wannan
Bahaushe ne ko Bafulatani
1.7.3 Muhalli
Muhalli yana nufin wajen
da al’umma ke zaune, suke gudanar da hidimomin rayuwarsu na yau da kullum a
wajen. Yanayin muhallin Hausawa da Fulani ya ɗan bambanta da juna, Bahaushe muhallin da yake zaune
za ka tarar da shi yana haɗe da ‘yanuwansa da
abokanai da sauran al’umma. Bafulatani kuma, yanayin wajen zamansa ya sha
bamban da na Hausawa domin shi kowa gonarsa yake zuwa ya yi gida da shi da
iyalansa. Aliyu (2015) Ta wannan tsarin ne maƙwabtan Hausawa da Fulani
na iya bambance su.
1.7.4 Al’adun
Bukukuwa
Al’ ummar Hausawa da
Fulami kamar kowace al’umma ta duniya tana da tata al’ada da ta gada kaka da
kakanni. Waɗanda suka bi don tafiyar
da rayuwarsu ta yau da kullum. Al’ada ta shafi dukkan matakan rayuwar Bahaushe
da kuma Fulani tun daga aure da haihuwa har mutuwa.
A cikin al’adun Hausawa
da Fulani, biki yana daga cikin abin da ke da muhimmanci a cikin hidimomin da
suke gudanar wa a rayuwarsu ta yau da kullum.
Bukukuwa:
A tsari na Bukukuwan
Hausawa da Fulani za a samun al’adu daban daban da suka keɓanta ga waɗanda bukin ya shafa
misali, a lokacin da za a fara gudanar da bukukuwan aure ko haihuwa ga al’ada
za a sami sunaye da suka shafi waɗanda bukin ya shafa misali.
a.
Amarya
a. Ɓagaɗo
b.
Ango
b. Angojo
c.
Yaro
na c. Ɓingeljo
d.
‘Yar
amarya
e.
Mai
jego
f.
Suruka
ko Sarakuwa
g.
yarbiƙi/ Ungozoma
Haka kuma, maƙwabtan Hausawa da Fulani
na iya tantance su ta wannan tsari, siffa da halaye da kuma wasu al’adunsu.
Misali, ta hanyar siffa duk inda ka ga Bafulatani fari ne akasari, haka kuma
gashinsu a murɗe yake. kuma ma fi
yawansu sirara ne, dogaye. Haka kuma ba su da sakin jiki, suna da kunya.
Bahaushen ƙwarai za a sami shi baƙi ne sosai, kuma zubin
kansa na da tsawo da kurungun kai mai ɗan jemo. Bunza (2015) Ta fuskar Gaisuwa, Tafiya da
Mu’amula da Auratayya da Mutuwa da Shugabanci da Sana’a da kuma Tsarin
gine-gine, duk waɗannan ɗabi’u makwabta
Hausa-fulani na iya bambance su ta waɗannan hanyoyi (Adamu 2015). Kuma zai yi wuya ka ga
Bafulatani ya ci maka abinci a kan hanya, amma Bahaushe ya sha bamban da
wannan ɗabi’a ta Fulani.
Haka kuma Bafulatanin
jeji za ka same shi da malafa da sanda da kuma jallon ruwa. Idan kuma saurayi
ne za ka same shi da madubi da sanda da kuma wuƙa. Wanda wannan halayya
ta sha bamban da ta Bahaushen ko da kuwa na jeji ne ba za ka same shi da waɗannan abubuwa ba. Ta
fuskar abincinsu kuwa, makwabtan suna iya bambance su. Ta fuskar abinci su,
Bahaushe yana da tuwo da Ɗan wake da Tubani da Dambu da Waina da Ɗanbagalage da Ƙuli-ƙuli da kwaɗo da kuma Daƙuwa da sauransu.
Bafulatani kuma za ka same shi da Fura da nono da Kunun kanwa da Kunun tsamiya
da Kwaɗon rama da Tantaɗi da Shaɓe da Kasambara, da
sauransu.
Ta ɓangaren furuci kuwa maƙwabtan Hausawa na kusa
na iya bambance su. Misali Bafulatani ya kan ce “Zan shi maimakon Zan ci”. Haka
kuma Bahaushe ba iya faɗin ƙosan sai dai ya ce
Kwasan. Duk waɗannan makwabtan Hausawa
na kusa suna iya bambance Hausawa da Fulani ta waɗannan hanyoyi da aka lissafa a sama. Koma bayan na
nesa. Sabi da ba sa tare da su. Balle su ga wasu ɗabi’unsu ko halaye domin su iya bambance waye Bahaushe
ko Bafulatani.
A takaice kallon da na
nesa ke yi wa Hausawa da Fulani a matsayin abu guda. Ya sa mu ne a sakamakon ba
tare da su suke ba a waje guda. Kuma sun tashi sun ga Hausawa da Fulani waje
guda, Da rashin sanin waye Bahaushe da Bafulatani, sannan kuma sun lura da
kowanensu Hausa yake yi. Haka kuma su a tunaninsu duk wani ɗan Arewa Hausa Fulani
ne. Haka kuma sun kula da cewa yanayin zamantakewarsu da auratayya tsakaninsu
duk guda ne. Kuma suna kishin junansu a waje. Don haka ne ma suke cewa
Hausa-Fulani. Amma na kusa na yi musu kallo ne, irin na mutum da makwabcinsa.
Domin tare suka tashi, Kuma za a iya cewa tare aka haife su har suka yi wayo
tare. Don haka ne, su kallon da suke yi ya sha bamban da wanda na nesa ke yi
musu.
1.9 Kammalawa
Kamar yadda aka gani
cewa, mun ga waye Bahaushe da kuma Bafulatani. Sannan muka ga irin zamantakewar
da ke a akwai tsakanin Hausa-fulani da makwabtansu. Bayan haka kuma mun ga irin
kallon da na kusa suke yi wa Hausawa da Fulani. Sannan mun ga yadda na nesa ke
yi musu kallo. Sannan sai muka duba ainihin suturarsu. Kamar yadda aka sani
cewa tun fil azal Hausawa da Fulani suna da tufafinsu na gargajiya, masu ƙima da ban sha’awa a
idanun sauran ƙabilun da suke kewaye da su.
Shawarwari:
* Ya kamata a ƙara yin mu'amala
tsakanin al'ummu daban-daban da kuma Hausa Fulani, domin haɓaka fahimtar juna.
* Ya kamata a gudanar da
ayyuka da za su haɗa al'ummu daban-daban,
domin kawar da rashin fahimta da kuma nuna halayen ƙauna da juna.
* Ya kamata a riƙa yin tattaunawa game da
al'adu da ɗabi'u daban-daban, domin
sauƙaƙe fahimtar juna.
* Ana bada shawara ga
al'ummu daban-daban da su ƙara hulɗa mai kyau da Hausawa da Fulani domin inganta fahimtar
juna da kuma kawar da ra'ayoyin da ba su dace ba.
Manazarta
Adamu, M. (1978), Hausa Factor In
West African History. Ahmadu Bello University Press, Zaria.
Aliyu, M. (2015) “Yanayi muhallin Hausawa
da Fulani A Ƙasar Katagum” Kundin N.C.E: Azare, Aminu sale, Collage
of education.
Bargery, G. P. (1933). Hausa-English Dictionary and English- Hausa
Bunza, A.M. (1990), Hayaƙi Fid Da Na Kogo:
Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa. Kundin Binciken Don Digiri Na Biyu.
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Bunza Aliyu Muhammad, (2015) “A ji
Bahaushe, a ga Bahaushe, a san Bahaushe ya yi Bahaushe. (Tsakuren ficen
Bahaushe da Tasirinsa a Duniyar Ƙarninsa)” Takardar da
aka gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Bunza Aliyu Muhammad, (2015) “Matakan
Kyallaro Asalin Bahaushe:( Ruwa na ƙasa sai ga Wanda Bai
Tona Ba)” Takardar jagora da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani
na ƙasa-da-ƙasa na farko a Jami’r
Jihar Kaduna, ƙarƙashin inuwar Hausa Studies Scholars Association,
kulawar Department of Nigerian Languages and Linguistcs bisa taken ‘The Hausa
People, Language and History: Past Present and Future’ Ranar 15-17 Disamba 2014
a Arewa House, Kaduna.
Funtua, A. I; Gusau Sa’idu Muhammad
(2010) Al’adu da ɗabi’u Hausawa da Fulani. Eds
Junaidu, (1978) Tarihin
Fulani. Zariya: NNPC Publisher
Jinju, H. (1985), “Asalin Hausawa Da
Harshensa” Maƙala Da Aka Gabatar A Taron Ƙasashen Duniya Akan
Hausa Da Adabi Da Al’ada. Jami’ar Bayero, Kano.
CNHN (2006). Kamusun Hausa na
Jami’ar Bayero Kano. Ahmadu Bello University Press.
Maigandi Attahiru, (2013) “Fulani da
Hausawan gundumar Sakkwato: Birɓishin dangantaka ta
share jini a koma wasa” Ɗunɗaye Vol. 1: Number 6:
Journal of Hausa Studies. Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University,
Sokoto.
Nashayya, B. M da Bisalla, B.A (2015) Who
Are The Hausa/Fulani? 1st International Conference Organized by
The Department Of Nigeria Languages And Linguistics, Kaduna State University,
Kaduna State.
Schuh,
R.G. and Yalwa, L.D. (1993), Hausa (illustration of the IPA) Journal of the
international Phonetic Assocition. 23 (2): 77-82.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.