Ticker

6/recent/ticker-posts

Bori Da Malantaka a Wasu Daga Cikin Adabi Bakan Hausawa

Daga

Muhammad Abubakar Zabi
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
08136844199
Muhammadabubakarzabi@Gmail.Com

Da

Adamu Halilu
Sashen Nazarin Harsunan Afirka
Jami’ar Amadu Bello, Zaria
08032307714

Tsakure

Hausawa al’umma ce da ta ginu bisa matakan rayuwa har guda uku. Da farko Hausawa sun gudanar da rayuwarsu bisa tsarin al’adun gargajiya wanda ya fara tun daga haifuwa da aure da kuma mutuwa. Hatta bautarsu a gargajiya suka gudanar da ita a wannan matakin. Haka kuma sun gudanar da rayuwa bayan karɓar addinin musulunci duk da haka ba su watsar da al’adunsu na gargajiya ba. Bayan zuwan turawan mulkin mallaka rayuwarsu ta gudana bisa sabon tsari. Duk da waɗannan sauye-sauyen matakan rayuwa bai sa su Hausawa sun watsar da al’adunsu ba. Bori da Malantaka suna daga cikin hanyoyi da Hausawa suka ɗauka a matsayin hanyar warakar da al’ummarta. Aikin daga ƙarshe zai duba waye Bahaushe, sannan ya duba ma’anar Bori, da Malanta da kuma ma’anar magani tare da duba mene ne adabi. A duba ma’anar Bori da Malanta a taskar adabi, kamar waƙa baka, da Karin magana da sauransu.

1.0 Gabatarwa

Hausawa al’umma ce da ta ginu bisa matakan rayuwa har guda uku. Da farko Hausawa sun gudanar da rayuwarsu bisa tsarin al’adun gargajiya wanda ya fara tun daga haifuwa da aure da kuma mutuwa. Hatta bautarsu a gargajiya suka gudanar da ita a wannan matakin. Haka kuma sun gudanar da rayuwa bayan karɓar addinin musulunci duk da haka ba su watsar da al’adunsu na gargajiya ba. Bayan zuwan turawan mulkin mallaka rayuwarsu ta gudana bisa sabon tsari. Duk da waɗannan sauye-sauyen matakan rayuwa bai sa su Hausawa sun watsar da al’adunsu ba. Akwai hanyoyi da dama da za a iya duba ire-iren al’adun Hausawa, ɗaya daga cikin hanyoyin ita ce hanyar nazarin Bori na gargajiya wanda suke amfani da shi tun matakin rayuwar farko har ya zuwa wannan zamani da kuma irin tasirin zamanin da aka samu a cikin harƙar Bori a yau, wanda yanzu Malantaka ta maye gurbin bori.

Daga cikin al’adun gargajiya na Bahaushe, babu wani ɓangare da ya samu karɓuwa, da farin jinni ga manazarta ýan ƙasa da na waje kamar Bori. Rubuce-rubucen da aka yi kan Bori sun fi kowane rubuce- rubuce yawa a fannonin nazarin al’ada. Bunza (2015).

Bori wani nau’i ne daga cikin sassan addinin Bahaushe, wato Tsafi, camfi da kuma Bori. Don haka wannan nau’i na Bori ya samu karɓuwa a wajen Hausawa sosai, suna amfani da Bori da Malanta a matsayin wata hanya ta samun magani.

Bori dai a nahawun ma’ana, Kalmar ta ci sunanta. A farfajiyar adabi ba ta tsallake ma’anar wasa ba. A ɓangaren al’ada kuma wata hanya ce wadda al’ummar Hausawa suka yi Imani da ita Bunza (2015).

Aikin daga ƙarshe zai duba waye Bahaushe, sannan ya duba ma’nar Bori, da Malanta da kuma ma’anar magani tare da duba mene ne adabi. A duba ma’anar Bori da Malanta a taskar adabi, kamar waƙar baka, Karin magana da sauransu. Sannan sai a kammala aikin.

2.0 Asalin Hausawa A Taƙaice

Sanin asalin Bahaushe kundi ne mai faɗin gaske. Domin Bahaushe mutum ne mai daɗaɗɗen tarihi bisa doron ƙasa. Masana da dama sun ambaci haka akan wa za a kira Bahaushe. Masana ilimin kimiyyar harshe da tarihi da al’ada sun sha gwagwarmaya wajen gano wane ne Bahaushe. Haƙiƙa an daɗe ana ɗauki ba daɗi wajen bin diddigin gano Bahaushe na asali. Daga cikin irin waɗannan masana ilimin harsuna akwai, Schuh da Yalwa (1993) sun bayanna cewa:

Yaren Hausa harshen na ɗaya daga cikin Harshen Chadi (ɓangaren iyalan Afro-Asiatic). Sun bayyana cewa Hausawa na a yammacin Tafkin Chadi ne, amma sun warwatsu a wurare daban-daban. Daga cikin wannan akwai Arewacin Nijeriya da Nijar da Chadi. Haka kuma, Harshe ne da ya bunƙasa wajen kasuwanci a ƙasashen Afrika ta yamma, da Afrika ta tsakiya da kuma ɓangaren Arewa maso Yamma da Sudan.

Jinju, (1985) a nasa binciken ya ce:

Mutanen Masar baƙar fata ne kuma sarakunansu (Fir’aunoni ne), baƙaƙe ne har lokacin sarautar gida na ashirinda huɗu. Su waɗannan mutanen Masar su ne a ganina suka yiwo ƙaura zuwa Afirka ta yamma suna zaune a bakin tafkin Chadi wanda can da maƙil yake da ruwa. A wannan lokaci ne mutanen fara fata suka riƙakai masu hari, sai suka yi ƙaura suka canza wurin zama tare da harshen su na misiranci wanda ya canza ga tarihi ya koma Hausa.

Duka waɗannan bayanai ba su isa su tabbatar muna da asalin Hausawa da harshensu ba. Domin harshe kaɗai ba iya tabbatar da asalin mutum. Zancen zaman Hausawa a gaɓar Kogin Chadi da alaƙar harsunan gidan Chadi wani wuri ne da Hausawa suka zauna na ɗan lokaci, daga baya suka canza wurin zama.

Haƙiƙa Smith ya ce, wani abu game da wane ne Bahaushe, kasancewar kowane Bahaushe yana iƙirari da harshensa na Hausa a matsayin asali. Hausawa da dama sukan yi kamannu da junansu. Ra’ayin Smith ya so ya yi kama da na Adamu (1978) da yake cewa:

Hausawa ne daɗaɗɗun mazauna Hausa da dukkanin zuriyarsu ta fuskar maza, ko kuma waɗanda suke amfani da al’adun Hausawa da riƙe harshensu da addininsu.

Shi kuwa Bunza (1990) ya bayyana cewa:

Hausawa dai mutane ne da suke zaune a ƙasar Hausa tun

 farkonta, kuma suna da zuriya a cikinta har ya zuwa yau

Kazalika, suna magana da harshen Hausa ba su da wani

Harshen in ba Hausa ba, suna da ɗabi’u da al’adu irin na

Hausawa. Idan sun saɓa haka to barbarar yanyawa ne.

Kamar yadda muka gani cewa masana sun kawo wane ne Bahaushe: Bisa ga yadda masana da manazarta suka ce za mu iya cewa, Bahaushe shi ne, mutumin da yake zaune a ƙasar Hausa, ta fuskar launi kuma baƙi ne; kuma iyayensa Hausawa ne, idan kuma ba a ƙasar Hausa yake zaune ba, ya kasance yana jin Hausa, kuma wasu al’adun Hausawa sun yi tasiri a gare shi, to wannan shi ne Bahaushe.

2.1 Ma’anar Bori

Yana da kyau kafi a fara kallon ma’anar Bori, mu kalli Kalmar Bori. Kalmar Bori takan ɗauki ma’anoni daban-daban idan aka sarrafa ta yadda al’umma ke kallon ta. Bahaushe ya samu Kalmar Bori daga Kalmar “Bore”, Bore na nufin zanga zanga ta fito-na-fito, da nuna rashin yarda, da burin ta’adanci, domin ramuwar gayya, ko tawaye, ga wanda ba a so, ko zanga-zangar tabbatar da wanda ake so. Wasu suna ganin daga nan ne aka samo Kalmar bori.

A wata fassarar kuwa, ana hasashen Kalmar bori daga Borin tukunya, ko tuwo, ko fura, ke yi idan an ɗora ta a kan wuta ana girki. Yayin da ruwa suka tafasa zafi ya ci ƙarfinsu suka fara zaɓarɓaka, za a ga dahuwar/girkin ta shiga wasu halaye kamar haka.

- Za ta ture marfin da aka rufe.

- Ruwan za su fito waje da ƙarfi.

- Za ta riƙa fitar da kumfa.

- Wutar za ta mutu ta kowane gefe..

Idan girki ya shiga wannan halin, za a kira mai shi a ce zo da sauri tukunyarki ta fara Bori. Komai tafasar da ta yi idan ba a samu abu biyu ba, ba a cewa ta yi Bori.

- Faɗuwar marfi ƙasa

- Fitar kumfa a bakin tukunya

Haka yake ko a wajen ɗan Bori, matuƙar bai kai ƙasa baki na fitar da kumfa ba, ba a cewa an hau bori. Wata ƙila daga nan ne kalmar ta samo asalinta.

A wani ɓangaren kuma ana ganin cewa Kalmar Bori ta samu asali daga, Bauri na magani. Bauri sauyoyi ne da ganyen itace da ɓawo ake haɗawa cikin tukunya a tafasa domin a sha a matsayin magani. Wasu na ganin cewa Kalmar ta samo asali ne daga nan.

Bugu da ƙari, Hausawa na danganta Kalmar da abubuwa da yawa, kamar idan aka ɓata wa yaro rai, ya faɗƙasa yana kuka, yana shure- shure, a kan ce, a ƙyale shi Bori yake yi. Idan gyaɗa aka soya, wata ta lalace tun gabanin a soya idan aka ɓare aka ga abin ya bayyana, ana ce masa, “Borin gyaɗa”. kaɗan ke nan daga cikin hasashen da ake yi wa asalin Kalmar Bori. Daga nan kuma za mu duba mu ga mene ne Bori.

2.1.1 Bori

Wani nau’i ne da ya sa mu karɓuwa a cikin al’ummar Hausawa sosai. Haka kuma shi wannan fage ya samu karɓuwa a ɓangaren masana da manazarta na cikin gida da waje. Ga kaɗan daga cikin wasu ma’anonin Bori:

“Bori shi ne, shigar Iskoki a ɗayan gaɓoɓin

hanci ko baki ko kunne tare da haƙiƙance

bayyanar su a idon mai bori. Yawo da ake yi

da kai da rawar da ake yi da fizge-fizge hanaye

da gaɓoɓi na fitar hankali su ne bori”(Bunza 2015).

Haka kuma ya ƙara da cewa:

“Bori dai wata wasa ce ta gargajiyar Bahaushe

da ta keɓanta ga wasu ýan tsirarru da ke da

sha’awar kwaikwayar ɗabi’un Iskoki da hulɗa

da su . shigan Iskoki na haƙiƙa, ya wuce bori,

ya zama wata lalura ta daban. Don haka bori ba

haƙiƙa ba ne kwaikwayon shigan iska na haƙiƙa ne”(Bunza 2015).

Ya sake bayyana ma’anar da cewa:

“Bori wata babbar mafaka ce da mata suka

kafa domin ƙwato ýancinsu na zamantakewa

da mutuntaka ga hannun maza tare da ba da tasu

gudumuwa ga al’umma. Matan da ke bori ba su kai

shi matsayin addini ba domin ba su yi iƙiirarin barin

addinin da bori ya riske su da shi ba”(Bunza 2015).

Wata ma’ana ta Bori kuma:

“Bori wata dabarar warkarwa ce da Bokaye suka

yi fice da ita.

Bisa waɗannan ma’anoni da muka gani game da Bori, za a ƙara ganin cewa lallai bori wani fage na musamman wanda ake yinsa bisa wasu dalilai da daman-daban. Mun fahimci bori ana yin sa saboda neman Iskoki, da kuma wasa na nishaɗi, tare da mata ma suna yinsa domin isar da wani saƙon da yake damunsu. Haka kuma yake ana bori domin neman waraka, wato neman magani ga wata cuta da ta damu al’umma.

Don haka za mu iya cewa, Bori wani wasa ne da al’ummar Hausawa ke yi, ta hanyar amfani da garaya da gurmi da goge, tare da ka-ca-kau-ra, da rawa ta fitar hankali, domin nishaɗantarwa, da kuma nema magani ga wata cuta da ta addabi mutum. Tare da yadda mata ke yin amfani da Bori domin isar da saƙonsu ga wanda ya matsa musu, ko ya dame su ga wani lamari na daban. Da kuma neman Iskoki don samun abokan hulɗa.

2.2 Malanta

Wannan fage na Malanta ya samu kulawar malamai da suka yi rubuce-rubuce a kai. Ga kaɗan daga cikin abin da wasu suka ce game da Malanta.

Asalin Kalmar Malanta daga Larabci take ba Bahaushiya ba ce (Bunza 1999) gabanin bayyanar Musulunci a ƙasar Hausa wannan kalma babu ita, bayan da Musulunci ya samu karɓuwa, karatu ya samu gindin zama a ƙasar Hausa, Malantaka ta bayyana (Musa 1999).

Bunza (2004) cewa ya yi Malanta ita ce samun karatu sahihi mai tushe da aka naƙalto shi ga wani ko wasu masana bisa tsarin koyo da ɗalibtaka. Haka kuma, ya kasance an samu aminta ko yarda daga Malaminsa in da aka koyo shi ta cewa ɗalibin ya fahimci abin da aka koya yana da damar ya koya wa wani..

Imam (1933) shi kuma cewa ya yi daga cikin sifofinsa akwai tsarin suturarsa ta fuskar naɗi da kawaicinsa da kaɗaitarsa da kamun kansa da makamantansu. Duk da haka, kowane mutum na iya ya ari waɗannan sifofi da Gangan ko ɗabi’a har a yi masa zaton Malanta ko dai bai san komai ba.

BirniTudu (2013) Y aba da ma’anar malami kuma na nufi mutumin da ya koyi abu kuma ya koyar da shi. Malami yana ba da bayani ga wanda ya nemi a warware masa wani al’amari na ibada ko zaman duniya. A fagen addini shi ne mai kiran mutane zuwa ga addinin Allah ta hanyar yi musu wa’azi. A fagen sana’a shi ne madugu uban tafiya. A zamnatakewa, shi ne wanda ya fi shekaru. A hulɗa shi ne masani abin da na tare da shi ba su sani ba.

Dangane da yadda masana suka ce game da Malanta ita ce, Ɗalibi da ya je wajen wani malami domin koyon ilimi na addini ko na zamani, ko wani fannin wani abu na daban, kuma ya sami ilimin shi ma ya koyar.

2.3 Magani

Wannan fage na magani ya samu kulawar masana da mazarta ainun, wanda suka yi ta bayani game da ma’anar magani. Ga kaɗan daga ciki.

“Maganin gargajiya- shi ne yin amfani da itatuwa

ko rubutu ko addu’a ko sulkulle, don warkar da

wata cuta, ko neman wani amfani, ko gusar da

sharri, ko haddasa wani abu saboda biyan buƙata”.(Adamu 2012)

“Magani shi ne duk wani abu da za a yi, ko wata

hanya, ko kuma wata dabara da ake yi don gusar

da wata cuta daga jikin mutum ɗungurungum,

ko kuma kwantar da ita don kawo jin daɗi ga jiki

ko ga zuciya dan sauwaƙa duk wahala da damuwa

da ita cutar kan iya haifar Ahmad”, (1984:6).

“Magani- wata hanya ce ta warkar da ko

kwantar da ko rage wata cuta ta ciki ko ta

waje ko wadda aka samu ta haɗari ko kuma

neman kariya ga cuta ko abokan hamayya ko

neman ɗaukaka ta daraja ko ta buwaya ta hanyar

siddabaru da sihirce- sihirce na ban al’ajabi” (Bunza, 1990).

Kamar yadda masana da mazarta suka yi ta faɗi-ta-shi wajen kawo ma’anar magani, za mu iya cewa magani shi ne, duk wata hanya da mutum ya bi wajen yaye wata damuwarsa, da ta dami shi. Walau ta jinya ko ta buƙatun rayuwa.

3.0 Ma’anar Bori Da Malantaka A Taskar Adabi

Adabin babbar fitila ce ta hasko rayuwar al’umma da yadda take tafiyar da ita.

Haka kuma Ɗangambo ya ƙara da cewa Adabi shi ne madubi ko hoton rayuwar al’umma. Wannan ya ƙunshi yadda al’adunsu, ɗabi’unsu, harshensu, halayyar rayuwarsu da abincinsu, tufafinsu, maƙwancinsu, hulɗoɗinsu, tunaninsu da ra’ayoyinsu da sauran abubuwa da suka shafi dabarun zaman duniya don ci gaba da rayuwa; kai har ma da abubuwa da suka shafi mutuwa. Duk wata al’ada da ake nazari kan al’umma yana da kyau a lalube adabi a ji yadda ya Harare batun. A nan muna son mu duba Bori da Malantaka ta ɓangaren waraka mu ga me adabi ya ce game da shi, kamar waƙa, kirari, da Karin magana da sauran ɓangarori na adabi.

3.1 Bori Da Malantaka A Riwayar Mawaƙan Baka

Mawaƙan baka, adabi Bahaushe suke ƙara faɗaɗa wa ma’ana, da ƙara fito da shi yadda yake a cikin rayuwar al’umma. Domin nuna halin da ake cikin ko yadda al’umma suke. Ana samu Mawaƙa da dama sun yi waƙa a kan Bori, akwai Mamman Shata, Sa’adu Bori da wasu Mawaƙa da dama. Haka za mu ga yadda mawaƙan baka suke tabbatar mana da cewa lallai Bori nau’i ne na Magani, wanda mutum yake nema domin biyan wata buƙata ta daban. Wato jinya ko wata buƙata ta rayuwa. Ga wani misali a lokacin da ƙwaro daga cikin ƙwarin Gambo mai waƙar ɓarayi ke neman sa’a a kashe masa Tsoho Tudu cewa ya yi:

Jagora: An yi bori, an yi bori, an yi bori

:Na yanka awakina da kaji

:An ce sa’a ta samu babba

:Y ac ce “Dogon zango nab biyo Tudu”

:Wai shi ya biyo Tsoho dag Gyalange.

Wannan ya nuna cewa lallai Bori yana da tasiri cikin adabin Hausawa yadda har mawaƙa suke kawo shi a matsayinsa na magani a cikin al’ummar. Idan aka duba abin da ka faɗi a nan, za a fahimci cewa lallai bori wani nau’i ne daga cikin nau’ikan magani, domin ya nuna cewa ya nemo sa’a a wajen ýan bori. Ya ce ya yanka awaki da kaji domin neman dacewa.

Haka kuma domin sake tabbatar da lamarin bori da malantaka cikin adabin Hausa, ga wani ɗiyan waƙa da Narambaɗa yake yi wa wani ɗan sarauta da ya yi takara. Yana cewa:

Jagora: Ga wani ya kunna ya ga ba ƙafa

: ýan bori kai shi sun baro

:Saruru ya baddala abinai

Yara: Ya koma biɗan kwabon hura

Gindi: Ibrahim na Guraguri

:Maishinkahi bajinin zagi

:Mu dai Allah ya bar muna kaya

Ta kula da wannan waƙar za mu sake tabbatar da cewa bori magani ne, domin ana zuwa nema magani domin wata buƙatar rayuwa. Domin ya kawo cewa shi ɗan takarar ya je neman sa’a wajen ýan bori, suka damfare shi ya zama babu kwabo sai an taimaka masa. Ke nan Narambaɗa ya nuna cewa ana amsar magani a wajen ýan bori ko malamai, saboda haka ke nan za mu yarda cewa bori wani nau’i magani ne.

Haka kuma Mamman Shata Katsina ya nuna a cikin bakandamiyarsa cewa lallai bori da malantaka magani ne, ga misali kamar haka:

Gindi; Alolo mai ganga ya gode, yaran mai ganga sun gode.

: Ba malamai ba ne

:Ba bokaye ba ne

Ikon Allah ne,

Im bori ne

Mai zai hana boka ya yi ɗansa ya samu.

Ya nuna cewa, bori ma wata hanya ce ta neman magani, kamar yadda ya faɗi a cikin waƙarsa. Yadda boka ko malami ke bayar da magani in ya isa ya bawa ɗansa ya samu ɗaukaka irin ta sa. Haka kuma a cikin waƙar ya nuna Arzika cewa ya nemi magani a wajen malamansa domin magani ya biya buƙatar da ake nema. Ga waƙar kamar haka:

Wata rana antashe shi lolo

Naj ji Zabarmawa na ta Zaino! Zaino!

Zaino kowa ka cewa,

Ban san da Zabarmanci sannan,

Naj ji Nuhwawa na ebeci!

Ban san da Nuhwanci ko kwabo ba,

Naj ji Hulani na hwaɗinn Gujjo!

Ba jin Hillanci nikai ba,

Sai Ga Hausawa irin mu

Naj ji suna eho! Ɓarawo!

Nac ce ‘an yi ɓarna’

Wancen bawa ba kai shikai ba.

Na dubi dut rutsun kasuwan nan

Sai shina tahiya tai yanga-yanga!

Hay yas shigajirgi lahiya lau,

Wane jihwa ko bugawa!

Sai dai nuni ɗan gaton uwa,

Nac ce biya mallanmanka Arzika

Sun cika aiki babu wasa

Domin idan aka nazarci wannan ɗiyan za a fahimci cewa Arzika a kasuwa ya je ya yi sata amma ba a gan shi ba, domin a yanzu wasu suna kiran boka da malam, boka kuwa yana da nasaba da yan bori. Wannan shi ya sa na kawo wannan a matsayin misali.

Ga wani misali daga waƙar Ɗankwairo ta Sarkin Gombe yadda yake nuna cewa lallai bori da malanta wani nau’i ne na magani, domin ya nuna cewa idan yayan sarakuna suna neman sarauta sukan je gun yan bori da malamai domin neman magani ko sa’a gunsu

Sarauta tana wurin Allah

Sarauta tana wurin wanda jallah ya bai girma

Shehu ka biɗa ga Allah ka samu

Sai ga wani ɗan sarkin Gombe bai biɗa ga Allah ba

Ya sai babbakun tumakai

Ya sai babbakun shanu

Sai ya kiraye ýan bori

Kullum ana yi mai bori

Wawa bokaye sun kwashe masa ƙudinsa

Bokaye sun kwace kuɗinsa

Ba shi ga Allah ba shi ga Annabi

Ba shi da tsutsu ba shi ga tarko

Babu kuɗin kuma babu sarauta

Babu kuɗin kuma babu sarauta

Wannan ya nuna cewa ‘yan bori da malamai suna bayar da magani. Haka kuma Ɗan kwairo yana cewa ‘yan bori suna bayar da magani ga waɗanda suke nema. Wannan shi ya ƙara tabbatar mana da cewa lallai bori da malanta wani nau’i ne na magani.

3.2 Bori Da Malantaka A Riwayar Karin Magana

Karin magana kusan ya mamaye kowane fanni na rayuwar Bahaushe. Yana da wuyar gaske a ce ga sha’anin rayuwar da ba a samun Karin Magana ba, kuma wannan shi ya ba da damar kamar yadda harshe da al’ada kan sauya su bi zamani, to kwatankwacin haka Karin magana ke sauyawa. Don haka sau da yawa Karin magana na nuna yadda rayuwar Hausawa take da irin abubuwan da suke mallake da shi, da wanda ba na su ba.

Za mu duba wasu Karin magana da suke tabbatar mana da cewa Bori da malanta wani nau’i ne na magani. Ga misali kamar haka:

An huta Bori ya kashe Boka

In wata magana? An ce Bori ya kashe Boka

Yau da gobe karya ta boka

Da na sani takan kashe boka da malam

Da malamai da boka Allah ya fi su

Duhu ɗakin bori

Ɗakin bori, digar maganin gujajjen bawa

Boka ci kaji, magani sai Allah

Halin bori, halin godiya

Borin girka ba shi warka da mayunwaci

Idan muka duba waɗannan Karin magana za mu fahimci cewa lallai bori da malanta wani nau’in magani ne, don yana nuna mafitar lamari ko samun sauƙin abin da ya yi tsanani ko warware wata matsala ko biyan buƙata, da dai sauransu.

3.3 Matsayin Bori Da Malantaka A wajen Bahaushe

Bori yana ɗaya daga cikin hanyoyin bauta a lokacin gargajiyar Bahaushe. Baya ga Tsafi da Camfi, sai shi Bori da Hausawa suka yi Imani da shi a wancan lokaci na gargajiya. Wanda wannan hanya ce da ta samar wa Hausawa abubuwa da dama, baya ga hanyar bauta, Hausawa suna amfani da wannan hanya a matsanyin wata hanya ta samar musu da magani, da kuma kariya daga wasu abubuwan cutarwa. Baya ga lokacin gargajiya, Hausawa sun ci gaba da wannan hanya wajen samar wa kansu magani. Wanda a yanzu kuma malanta ta maye gurbin bori wajen bayar da magani da neman waraka ga wani al’amari na rayuwa.

4.0 Kammalawa

Wannan aikin bayan an yi gabatarwa an ɗan yi ƙoƙorin kawo waye Bahaushe, sannan ma’anar bori da Malanta da magani da ma’anar bori da malantaka a taskar adabi daga ƙarshe kuma bori da malantaka a riwayar mawaƙan baka, da Karin magana da kuma sanin matsayinsa a wajen al’ummar Hausawa. Wanda nazarin ya tabbatar mana da cewa lallai Bori da Malanta wani nau’i ne na bayar da magani, wanda yake nuna mana irin yadda bori da malanta suka yi tasiri a rayuwar al’ummar Hausawa, wanda suka ɗauke shi a matsayin wata hanya ta samar da magani ga al’ummarta. Ta kula da hanyar adabin Hausawa ya ƙara tabbatar mana da hakan, domin a cikin waƙoƙinsu da Karin maganganunsu duk akwai irin waɗannan maganganu da suke tabbatar mana da cewa bori da malanta wani nau’in magani ne a ƙasar Hausa. A kowane ɓangare na waƙa da Karin magana an ɗan kawo misalai da za su sake tabbatar mana da haka.

Manazarta

Abdullahi, I. S .S (2012). “Muhallin Magani A Adabin Bakan Bahaushe” A cikin Ɗunɗaye Journal Of Hausa Studies, Vol. 1, Number 4. Department Of Nigeria Languages, Usmanu ƊanfodiyonUniversity, Sokoto

Adamu, M. (1978) The Hausa Factor in West African History. Zaria: Amadu Bello University Press.

Adamu T. M (2014). Siddabaru A Ƙasar Hausa. Century publition Ltd, Kano.

Ahmad I. A (1984) Cututtukan ciki da magugunansu” Kundin BA, Sashen Nazarin Harsunan Nijriya, Jami;ar Bayero, Kano

Alhassan, H; Musa, U. I da Zarruuk, R. M. (1988). Zaman Hausawa Na Biyu Don Makarantun Gaba Da Firamare. Publications Bureau, Lagos

Birni Tudu, S.Y (2013) “Falsafar Malanta Cikin Littafin Ruwan Bagaja” Ruwan Bagaja In Perspectives. Eight Decades Of Hausa Masterpiece in Prose (1933-2013) zaria: University Press

Bunza, A.M. (1990), Hayaƙi Fid Da Na Kogo: Nazarin Siddabaru Da Sihirin Hausawa. Kundin Binciken Don Digiri Na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano

Bunza, A. M (1999) Gwagwamayar Malaman Ƙasar Hausa Da Turawan Mulkin Mallaka, Fassara daga Turanci Zuwa Hausa. Ulama and Colonializing translation, Editing And Introduction By Omar Bello Published by Milled stone Publishers, Sokoto

Bunza, A. M. (2002). Narambaɗa, Lagos: Ibrash Islamic Publicaiton Centre.

Bunza, A. M (2004) “Gwagwamayar Malam Mai Katuru da Malaman Ƙasar Hausa.(Darasi ga Malaman Yau Ƙalubale Ga Na Gobe)”. A Taron Ƙara wa Juna Sani a Bukukuwan Shekara 200 Da Kafa Daular Musulunci Ta Sakkwato

Bunza A. M (2006). Gadon feɗe al’ada. Tiwal Nigeria Ltd, surulere Lagos.

Bunza A. M (2015). “Mene ne Bori? Fashin Baƙin Ma’anarsa cikin Taskar Harshe, Adabi Da al’ada”. Takarda da aka gabatar a taro na musamman da cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Mutuntar ɗan Adam (CSNLF) Jami’ar Bayero kano ta Shirya mai taken BORI ADDINI KO AL’ADA ranar Talata 16 ga watan yuni 2015 a harabar cibiyar, Mazaunin dindindin.

Ɗanmaigoro, A. (2010) “Magungunan Gargajiya na Hausawa da Fulani”. Cikin Al’adu da Ɗabi’un Hausawa da Fulani”.

Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa, London: Edinburgh University Press, for International Africna Institute.

Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa, Kano: century Research and Publishing Limited.

Gusau, S. M (2014). Diwanin Waƙoƙin Baka: Juzu’I Na biyu, Kano: century Research and Publishing Limited.

Imam, A. (1933) Ruwan Bagaja. Zaria: NNPC

Jinju, H. (1985), “Asalin Hausawa Da Harshensa” Maƙala Da Aka Gabatar A Taron Ƙasashen Duniya Akan Hausa Da Adabi Da Al’ada. Jami’ar Bayero, Kano.

Malumfashi I; Ibrahim N. M (2014). Ƙamusun Karin Maganar Hausa. Garkuwa Publications, Kaduna.

Sallau, A.B.S.(2005) “A Sha a yi Wanka, Magani ga ɗan na Gada: Nazari da Tsokaci kan Magungunan Gargajiya na Wanzaman Hausawa a Wannan Zamani” Takarda da aka Gabatar a Sas1hen Hausa. Dutsin-ma: babbar Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita

Schuh, R.G. and Yalwa, L.D. (1993), Hausa (illustration of the IPA) Journal of the international Phonetic Assocition. 23 (2): 77-82.

Tremearne, A. J (1914) The Ban of the Bori: Demons and Demon Dancing in West and North Africa. London: Health Creation and Ouseley Ltd

Bori Da Malunta

Post a Comment

0 Comments