Citation: Jamilu ALHASSAN & Hauwa Abubakar ISMA’IL (2021). Arulin Tashɗirin Waƙar ‘Hausa Mai Ban Haushi’ Ta (Dr.) Aƙilu Aliyu. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 9, Issue 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
ARULIN TASHƊIRIN[1]
WAƘAR ‘HAUSA MAI BAN HAUSHI’ TA (DR.) AƘILU
ALIYU
Na
Jamilu ALHASSAN
Hauwa Abubakar ISMA’I
1.0 Gabatarwa:
‘Tashɗirin Waƙar Hausa mai Ban
Haushi’ waƙa ce da mutum biyu suka samar da ita, (Dr.) Aƙilu Aliyu da Malam
Jamilu Alhassan. (Dr.) Aƙilu Aliyu shi ne mawaƙi na farko da ya
rubuta waƙar ta asali, mai ɗauke da baitoci 78. Daga baya Malam Jamilu
Alhassan ya yi tashɗirin waƙar ta dawo baitoci
156. Amma baitoci uku na ƙarshe, mai yin tashɗirin ne ya samar da su, domin yin ramzi.
“Tashɗiri shi ma aikin mutum biyu ne, ana yin sa ne
kuma da waƙa ‘yar tagwai, sai a yi mata ƙari. Yadda ƙarin zai kasance shi
ne, kowane baiti zai sami ƙarin ɗango biyu, sai ya zama baiti biyu. Ɗango na farko za a ƙara masa wani ɗango ya zama baiti ɗaya; ɗango na ƙarshe kuma a ƙara masa wani ɗangon amma ya zama
shi ne na ƙarshe. Baiti ɗaya an mayar da shi baiti biyu ke nan[2].”
Sa’id (2016, sh. 44).
A nasa aikin Muhammad (2019), shi ma ya taɓo maganar tashɗiri, inda ya bayyana
Tashɗiri da cewa, “Wannan
tsarin shi ne, idan mawaƙi ya rubuta waƙarsa ‘yar tagwai, sai
wani mawaƙin ya tsaga waƙar ya cusa nasa ɗango ko ɗangaye a tsakiyar waɗancan ɗangaye guda biyu suka
zama uku ko huɗu ko biyar.” Wannan ne ma ya sa ya raba Tashɗiri zuwa gida uku,
kamar haka: Tashɗiri Musallasa da Tashɗiri Rabiyya da kuma
Tashɗiri Muhammasa.
(Muhammad, 2019, sh. 22-24)
A tawa fahimtar Tashɗiri ana yin sa ne
kawai a waƙa ‘yar tagwai, inda za a tsaga baiti ɗaya ya koma biyu, ba
uku ko huɗu ko biyar ba. Domin
Kalmar Tashɗirin ta samo asali
daga kalmar ‘Shaɗara’ ta Larabci,
wacce take nufin tsagawa.
Babbar manufar wannan
takarda ita ce, auna waƙar Tashɗiri, a gano karin da ta hau daga cikin karuruwan nan goma
sha shida. Sannan a fito da zihafai da illolin da suka afka wa ƙafafuwan waƙar.
2.0 Karin Waƙar Tashɗirin Hausa Mai Ban
Haushi
Bello da Sheshe,
(2013, sh. 20) sun bayyana kari da cewa “wanzuwar ƙafafuwa masu bibiyar
juna cikin tsari, a baitin waƙa ko da baitin mai layi nawa ne.” A
kwai karuruwa goma sha shida na auna rubutacciyar waƙar Hausa, da suka haɗa da: Ɗawil da Madid da Basiɗ da Wafir da Kamil da
Hazaj da Rajaz da Ramal da Sari’i da Munsari da Hafif da Mulari’i da Muƙtalib da Mujtas da
Mutaƙarab da kuma Mutadarak.
Wannan bincike ya
gano cewa wannan waƙar an gina ta ne a kan kogin Kamil. wato 8+8+8, mai
alamci (ɓ ɓ – ɓ - / ɓ ɓ – ɓ - / ɓ ɓ – ɓ -). Za a gane haka
idan aka yi la’akari da waɗannan baitoci na ƙasa.
ɓ ɓ
- ɓ
- /ɓ
ɓ -
ɓ - /ɓ ɓ
- -4
Jama’a mu kar/kaɗe kunnuwan/mu na
zuci,
ɓ ɓ
- ɓ
- /-3 - ɓ -
/ ɓ
ɓ - -4
Mu
ji wanga zan/ce don mu bi/ shi mu amsa.
(Tashɗirin Waƙar HMBH*[3]*
bt. 7)
Idan aka duba wannan
baiti na sama, za a ga yana ɗauke da ƙafofi guda shida, ƙafa ta ɗaya da ta biyu na ɗangon farko sun fita
lafiya kamar haka: ɓ ɓ – ɓ -, wato ba wani
zihafi ko illa da suka shige su. Haka lamarin yake a ƙafar farko a ɗango na biyu. Amma
idan aka duba ƙafa ta uku a ɗango na farko da na biyu, za a ga suna da
sura kamar haka: ɓ ɓ - -4, wato illar Kaɗa’i ta shige su ke
nan. Kaɗa’i illa ce ta ragi
wadda take aukuwa a kan doguwar gaɓar da ke bisa turke, idan illar ta auku takan
mayar da doguwar gaɓar ta zama gajera
daga nan kuma sai ta haɗe wannan gajerar gaɓar da gajeriyar gaɓar da take kan turke
su zama daguwar gaɓa guda ɗaya. Ita kuma ƙafa ta biyu a ɗango na biyu, 3-
- ɓ -, zihafin Ilmari ne
ya shige ta, wannan ya sa ta koma 3- - ɓ – mai makon ɓ ɓ - ɓ -. Zihafin Ilmari matsala ce ta zihafi wacce
take faruwa a kan gajerun gaɓoɓi masu zaman kansu
daga farko, idan matsalar ta zo takan haɗe waɗannan gaɓoɓi biyu na farkon su zama doguwar gaɓa guda ɗaya. Wannan ya nuna
mana wannan waƙa ta Tashɗirin Waƙar HMBH, tana kan kogin Kamil 8+8+8
mai alamci ɓ ɓ – ɓ -.
Haka abin yake idan
aka duba wannan baiti na ƙasa. Don haka, duk ƙafar da aka yi wa
alama da lamba (3) to zihafin
ilmari ya shige ta, wadda kuma aka yi wa alama da lamba (4) to illar Kaɗa’i ce ta afku a
wurin. Misali:
ɓ ɓ
- ɓ
- /-3 - ɓ
- / -3 - -4
Zarafin da ma/maki, gwanin/ ban haushi,
ɓ ɓ - ɓ - /ɓ ɓ - ɓ - / -3 - -4
A
ga ɗan Are/wa da ba ya
ki/shin Hausa.
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 29)
Duk da cewar waƙar ta ginu a kan
kogin Kamil, hakan bai hana shigar zihafai da illa ba, sai dai wannan ba za ta
sa a canza wa tuwo suna ba. Wannan nazari ya gono cewa larura uku ce kawai ta
fito a wannan waƙa, kamar haka:
2.1
Zihafai A Arulin Hausa
Masana sun bayyana
ma’anar zihafi a Arulin Hausa. A fahimtar su, Bello da Sheshe (2013, sh.
38). “Zihafai dai jam’i ne na zihafi.
Abin da kuma ake kira zihafi shi ne “wata larura ce da take zuwa cikin ƙafa ta faɗa kan da’ira ba tare
da ta taɓa turke ba. abubuwan
da wannan larura ke yi a cikin ƙafa, sun kasu kasha uku.
1.
Tana iya samun da’ira ɗaya, mai zaman kanta,
ta shafe. Kamar a ƙafa ta takwas,
maimakon o o o-o o o-o sai a sami o o-o o o-o.
2.
Tana iya samun tagwayen da’ira, ta
shafe ɗaya ta bar ɗaya. Kamar a ƙafa ta takwas,
maimakon o o o-o o o-o sai a sami o o o o o-o.
3.
Tana iya samun da’irori biyu masu
zaman kansu, ta haɗe su wuri ɗaya ta mayar da su
tagwaye. Kamar a misalinmu na ƙafa ta takwas, maimakon o o o-o o
o-o sai a sami o-o o-o o o-o.
Zihafi ba lalle ne kuma ya kasance a waje ɗaya tak a cikin ƙafa ba. Ana iya samun
zihafi iri biyu a cikin ƙafa guda. Misali,
a ƙafa
ta shida, maimakon a sami o-o o-o o o-o sai a sami o o o o-o.
Watau an shafe da’ira ɗaya daga tagwayen
farko, kuma an shafe ɗaya daga tagwaye na
biyu.”
Shi kuma Dunfawa,
(2003, sh. 34), cewa ya yi, Sauyi (Zihafi), shi ne “canji da kan shiga cikin
wata ƙafa daga ƙafofin kari, wanda idan ya shiga sai
ya sake ma ƙafar tsari dana da wanda aka san ta da shi”. Amma Galadanci, (1975, sh. 6) cewa ya yi, “Deɓiations / Zihafai are changes which occur freely in the
feet without restriction, eɗcept that they are found only in the affiɗes of the feet and neɓer in the stems”.
Shi ma Zulyadaini,
(2017), ya bayyana Zihafi da cewa, “wata matsala ce da take faruwa a kan ƙafar waƙa, wadda idan wannan
matsalar ta afku takan sauya siffar ƙafar/ ƙafafuwan da suke ba
da Karin waƙa su fito ba kamar yadda aka san su ba”.
Ta la’akari da waɗannan ma’anoni da
masana suka bayar a sama, za a iya bayyana Zihafai da cewa wasu matsaloli ne da
ke far wa igiyar ƙafar waƙa su canja mata sura, sai dai ba sa
iya taɓa turken ƙafar.
Masanan sun raba
zihafai zuwa gida biyu, wato gwaurayen zihafai da kuma takwayen zihafai. Gwaurayen su ne: Habni da Ɗayyi da Ilmari da Waƙasi da Asabi da Aƙali da Ƙabli da Kaffi da kuma
Ta’aliƙi. Su kuma tagwayen su ne: Habli da Hazali da Naƙasi da kuma Shakali.
Zulyadaini (2003, sh. 34). A wannan waƙa zihafai biyu kawai
aka samu, da suka haɗa da:
2.1.1 Zihafin Ilmari
Masana sun bayyana
ma’ana da irin aikin da zihafin Ilmari yake yi, idan ya sauƙa a ƙafar waƙa. Bello da Sheshe
(2013, sh. 40), cewa suka yi, “Zihafin Ilmari shi ne, a sami ƙafa wadda gaɓoɓinta biyu, na farko,
gajeru ne masu zaman kansu, a haɗe su, su zama guda ɗaya mai tagwayen
da’ira. Za a sami wannan zihafi ne a ƙafa ta takwas
kawai.” Dala (2018, sh.14) a waƙe ya kawo nasa
bayanin, kamar haka:
“Da ILMARI zihafi ne,
Ƙafa ta takwas yake
zaune,
Gajerun fari sun manne,
Na ce halin zihafi ne,
Zihafi bai yi zafi ba.”
(Arulin Hausa a Waƙe, bt. 14)
Idan muka yi la’akari
da abin da masanan suka faɗa a sama, za mu fahimci cewa Ilmari matsala ce ta zihafi
wacce take faruwa a kan gajerun gaɓoɓi masu zaman kansu daga farko, idan matsalar
ta zo takan haɗe waɗannan gaɓoɓi biyu na farkon su
zama doguwar gaɓa guda ɗaya. Ilmari yana
shiga kogin waƙa ɗaya rak. wato kogin
Kamil, domin shi Ilmari ana samun sa ne kawai a ƙafa ta takwas ɓ ɓ – ɓ – idan ilmari ya
shige ta sai ta zama - - ɓ -. Duba wannan baiti
na ƙasa:
-[4]
- ɓ - /3- - ɓ - / 3- - [5]-
Saba da sa/mo gaskiya /duk nisa,
-3 - ɓ - /
ɓ ɓ - ɓ - / -3 - 4-
Sannan
ka tsar/kake zuciya /tattausa
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 1)
Idan aka duba wannan
baiti na sama da kyau, za a ga cewa ƙafofi biyar daga
cikin shida sun fara da doguwar gaɓa, wato (- - ɓ -), maimakon (ɓ ɓ – ɓ -) wannan yana nuna
mana cewa zihafin Ilmari ya sauka a kan gajerun gaɓoɓi biyu na farkon
kowace ƙafa ke nan. Ƙara duba wannan baiti
na ƙasa:
-3 - ɓ - /-3 - ɓ - / -3 - -4
Na gatsa han/cin gaskiya/ mai ganci,
-3 - ɓ - /-3 - ɓ - / -3 - -4
Ba
na nada/mar nuna ki/shin Hausa.
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 20)
A wannan baiti na
sama kuma, gaba ɗaya ƙafofi shidan ne suka
fara da dogayen gaɓoɓi, wato (-3 - ɓ -), maimakon (ɓ ɓ – ɓ -), wannan ya nuna
mana cewa duka ƙafofi shidan zihafin Ilmari ya shige su. Ga wani misali
kuma a ƙasa:
-3 - ɓ - / ɓ ɓ
- ɓ
- / -3 - -4
In
har akwai/ biyu masu jin/ Turanci,
-3 - ɓ - /-3 - ɓ - / -3 - -4
Ko
ko Buro/kin ko Fijin, / Ingausa.
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 41)
A wannan baiti na
sama kuma, ƙafofi biyar ne zihafin Ilmarin ya afka wa, domin su ne
suka fara da doguwar gaɓa, wato -3 - ɓ - maimakon su fara kamar haka, (ɓ ɓ - ɓ -). Wannan yana tabbatar mana da cewar waƙar “Tashɗirin Hausa mai ban
Haushi” akwai zihafin Ilmari a cikin ta. A taƙaice dai, duk ƙafar da aka ga an
mata alamar lamba uku daga sama (-3
- ɓ
-), to zihafin Ilmari ya shige ta.
2.1.2 Zihafin Waƙasi
Bello da Sheshe
(2013, sh. 41), cewa suka yi, “Zihafin waƙasi, ana samunsa ne a
ƙafar
da take farawa da da’irori biyu, masu zaman kansu, (gajerun gaɓoɓi biyu), watau a ƙafa ta takwas. Irin
wannan zihafi idan ya zo sai ya sami da’ira ta biyu ya shafe.”
A tasa fahimtar Dala
(2018, sh. 15) Zihafin Waƙasi yana shiga kogin waƙa ɗaya tak wato kogin
Kaamil, domin shi ma ana samun sa ne kawai a ƙafa ta takwas (0 0 00
0 00) idan waƙasi ya shige ta sai ya shafe gajeriyar gaɓa ta biyu daga farkon
ƙafar
sai ta zama ( 0 00 0 00).
Wannan na nufin
zihafin waƙasi yana afka wa gajeriyar gaɓa ta biyu a farkon ƙafa ta takwas ya
shafe ta. Duba wannan baiti na ƙasa:
-3 - ɓ - / ɓ ɓ - ɓ - / -3 - -4
Faufau
ba ka/ ga, ba ka ji mai/ yare ba,
ɓ5 - ɓ - /-3 - ɓ - / -3 -
-4
Yana gudun /yarensa
ko /ko ƙin sa.
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 40)
Idan aka lura da wannan baiti na sama, za a
ga ɗango na biyu ya fara
da ƙafa
kamar haka, (ɓ5 - ɓ -)
maimakon haka (ɓ ɓ
- ɓ
-), to zihafin waƙasi ne ya faɗa wa gajeriyar gaɓar nan ta biyu ya
shafe ta gaba ɗaya. Ga wani misalin:
-3 - ɓ - /-3 - ɓ - /
-3 - -4
Ka faɗi wan/nan, ungo ga/ mai sauƙi,
ɓ 5 - ɓ - / -3 - ɓ -
/ -3 -
-4
Mi
ye “kashe/reƙe” da har/shen Hausa?
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 82)
A farkon ɗango na biyu na wannan baiti na sama ma, zihafin
waƙasa
ya ƙara
sauƙa,
wannan ne ya sa ƙafar ta koma haka (ɓ5 - ɓ - ) a madadin ta zama haka(ɓ ɓ
- ɓ -).
Haka abin yake a wannan baiti na ƙasa:
ɓ5 - ɓ
- /ɓ ɓ
- ɓ - /
-3 - -4
A shekarar/ yabahin da sha/sha*[6] ke nan,
-3 - ɓ - /-3 - ɓ - / -3 -
-4
Miladiya /ai kun sani/ ‘yan Hausa.
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 158)
Ƙafar farko a ɗango na farkon wannan
baiti na sama, za mu ga ta kasance kamar haka (ɓ5 - ɓ -),
maimakon ta zama haka (ɓ ɓ
- ɓ -). Wannan ma yana nuni da gurbin da zihafi
waƙasi
ya sauka ne, inda ya rarumi gajeriyar gaɓa ta biyu ya laƙume ta. Irin wannan
zihafi bai fito sosai a waƙar ba, amma duk da haka an ba shi
lamba biyar, don haka, duk inda aka ga ƙafa mai kamar haka (ɓ5 - ɓ -),
to zihafi Waƙasi ya faɗa mata.
2.2
Illoli
A Arulin Hausa
Sa’id, (2016, sh. 16), ya bayyana Illa da cewa, “Wani canji ne da yakan
auku a ƙafar waƙa; sai dai ita Illa ta bambanta da Zihafi, domin idan an same ta a wata ƙafa ta baitin waƙa, to za ta ci gaba da aukuwa
ne a wannan ƙafar a duk sauran baitocin waƙar.” A taƙaice dai Illa wata matsala ce da take afkuwa a kan ƙafafuwan waƙa, a lokacin da suke afkuwa a
kan Karin waƙa, idan matsalar illa ta auku takan sauya siffar ƙafar waƙa, sai dai ba kamar zihafi ba,
ita illa tana afkuwa ko da a kan turke ne. Illa ta kasu gida biyu: akwai illar
daɗi akwai illar ragi. Illar daɗi/ƙari su ne: Tarfili da Tazyili da kuma Tasbigi. Illar ragi kuma su ne:
Hazafi da Ƙaɗafi da Ƙaɗa’i da Batari da Kashafi da Harmi. Zulyadaini (2003, sh. 40-44). A wannan
waƙa illa ɗaya tak, aka samu, ita ce:
2.2.1 Illar Ƙaɗa’i
Sa’id (2016, sh. 17)
cewa ya yi, “Ƙaɗa’ii na nufin Shafe
gurbi na uku a turken ƙafa, tare da haɗe gurbi na biyu da na ɗaya su koma doguwar
gaɓa.
Shi ma Dala (2018,
sh. 22) ya bayyana yadda Illar Ƙaɗa’i take, amma a waƙe ya kawo bayanin,
kamar haka:
“Akwai
ƘAƊA’I da illarsa,
Da
ke sauka a Turkensa,
Ya
karɓi ɗayan tagwayensa,
Ya
zo ya haɗe gajerunsa,
Su
tabbata doguwa babba.”
(Arulin Hausa a Waƙe, bt.70)
Ta la’akari da
bayanin nan da masanan suka kawo a sama, za mu iya cewa Illar Ƙaɗa’ii illa ce ta ragi
wadda take aukuwa a kan doguwar gaɓar da ke bisa turke, idan illar ta auku takan
mayar da doguwar gaɓar ta zama gajera
daga nan kuma sai ta haɗe wannan gajerar gaɓar da gajeriyar gaɓar da take kan turke
su zama daguwar gaɓa guda ɗaya. Duba wannan
baiti na ƙasa:
-3 - ɓ - /-3 - ɓ - /
-3 - -4
Ka
ɗebe al/farmarka ka/
warwatsar,
-3 - ɓ - /-3 - ɓ - /
ɓ ɓ - -4
Ka
ƙyale
tu/she, ga shi ka/ riƙe rassa.
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 70)
Idan muka duba ƙafofin ƙarshe na wannan baiti
na sama, za mu tarar kowace ƙafa ta ƙare da doguwar gaɓa mai ɗauke da alamar lamba
huɗu a samanta (4),
wannan yake nuna mana cewar illar Ƙaɗa’i ta afka wa ƙafar. Ga wani misali
a ƙasa:
ɓ ɓ - ɓ - / ɓ ɓ
- ɓ
- / ɓ ɓ
- -4
Ka zamo maje/ gaba kar a bar/ ka a baya,
ɓ ɓ - ɓ - /-3 - - 4/ -3 - -4
A wajen hidim/tawa har/shen Hausa.
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 103)
A wannan baiti na
sama a ɗango na farko da na
biyu, za a ga illar Ƙaɗa’in dai ta ƙara sauka, da ta
sauka a ƙafar ƙarshe ta ɗango na farko, sai ta
mayar da ƙafar haka (ɓ ɓ - -4)
maimakon haka(ɓ ɓ
- ɓ
-). Amma a ɗngo na biyu ƙafar ƙarshe sakamakon
zihafin Ilmari da illar Ƙaɗa’i ne suka taru suka
afka wa ƙafar, sai ta koma haka (-3 - -4)
a madadin haka ((ɓ ɓ
- ɓ
-). Ga wani misali kuma a nan ƙasa kaɗan:
-3 - ɓ - /ɓ ɓ - ɓ - / -3 - -4
Mui taƙama /da abinmu, shi/
ne daidai,
-3 - ɓ - / ɓ ɓ
- ɓ - / -3 - -4
Kar mui sake/ wasu can su mo/re Hausa.
(Tashɗirin Waƙar HMBH bt. 130)
Idan muka lura da ƙafar ƙarshe na ɗangon farko da na
biyu na wannan baiti na sama, za mu ga ƙafafuwan biyu sun
zama haka (-3 - -4), maimakon haka(ɓ ɓ
- ɓ
-). To a nan ma zihafin Ilmari ne ya fara afka wa ƙafar, sai kuma Illar Ƙaɗa’i ta zo ta yi
aikinta. A taƙaice dai, idan muka dubi waƙar da kyau, za mu ga
tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta babu baitin da illar Ƙaɗa’i ba ta afka wa ƙafar ƙarshensa ba, wannan
kuma ba abin mamaki ba ne, domin daman haka ɗabi’ar illa take.
3.0
Kammalawa
Kamar yadda aka yi
bayani a baya, Tashɗiri yunƙuri ne na yin ƙari a rubutacciyar waƙar Hausa, wadda mutum
biyu suka tsara, wato nau’in Tarbi’i da Tahamisi. Sai dai shi Tashɗiri da waƙa ‘yar tagwai kawai
ake yin sa, wadda a tsarinsa baiti ɗaya zai koma baiti biyu, bayan an yi masa
Tashɗirin. Wannan bincike
ya gano waƙar Tashɗirin Hausa mai ban Haushi, an gina ta ne a kan karin
‘Kamil’. Karin Kamil yana daga cikin karuruwan da ake kira maimaitau, domin
kuwa ana maimaita ƙafa ɗaya domin a samar da shi. A wannan kari ana riɓanya ƙafa ta takwas domin
samar da karin. Misali: 8+8+8 ( ɓ ɓ – ɓ - / ɓ ɓ – ɓ - / ɓ ɓ – ɓ –), Mutafaa’ilun/Mutafaa’ilun/Mutafaa’ilun. Sai dai an sami
shigar zihafai guda biyu, wato, Ilmari da Waƙasi. Sai kuma Illar
Kaɗa’i, wadda ta biyo
dukka ƙafafuwan ƙarshe na waƙar.
Manazarta
Bello, A. da Sheshe, I.N. (2013). Arulin Hausa a Sauƙaƙe. SMGraphics Publishers.
Dala, A.S. (2018). Arulin Hausa a waƙe. Century Research and Publishing.
Dunfawa, A.A (2003). Ma’aunin waƙa. Garkuwa
Publishers.
Galadanci, M.K.M (1975). The poetic marriage between Arabic and Hausa, Harsunan Nijeriya, 5 .1-16.
Muhammad,
S.S (2019). Matakan nazarin rubutacciyar
waƙar Hausa. Ahmadu Bello University press limited
Sa’id, B. (2016). Rubutacciyar waƙar Hausa ma’auninta da
amsa-amonta da ire-irenta. Bayero University press.
Zulyadaini, B.
(2003). Dialect miɗture in the twentieth
century Hausa Poetry. [PhD Thesis], Department of Language and linguistics,
UNIMAID.
Zulyadaini, B. (2017). Lacca da aka yi a aji, Umar Suleiman College
of Education Gashu’a.
[1] “Wannan kalma Balarabiyar kalma
ce, an samo ta daga shaɗara,
wato tsaga ko daddaga wani abu guda ɗaya ya koma biyu.” In ji, Farfesa Aliyu Muhammad Bunza.
[2] Bayani daga Farfesa Sarki Ibrahim,
Sashen Koyar Da Larabci, Jami’ar Bayero, a cikin Bello Sa’id (2016:44).
[4]
An sami shigar zihafin Ilmari, matsala ce ta zihafi wacce take faruwa a
kan gajerun gaɓoɓi masu zaman kansu daga farko, idan
matsalar ta zo takan haɗe
waɗannan gaɓoɓi biyu na farkon su zama doguwar gaɓa guda ɗaya.
[5]
Illar Kaɗa’I ta
shiga. Wanna illa ce ta ragi wadda take aukuwa a kan doguwar gaɓar da ke bisa turke, idan illar ta
auku takan mayar da doguwar gaɓar
ta zama gajera daga nan kuma sai ta haɗe
wannan gajerar gaɓar
da gajeriyar gaɓar da
take kan turke su zama daguwar gaɓa
guda ɗaya.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.