Ticker

6/recent/ticker-posts

Saye A Matsayin Mahadin Wasu Magungunan Hausawa Na Gargajiya

Citation: Dr. Nura LAWAL & Hadiza Balarabe ADAMU (2021). Saye A Matsayin Mahaɗin Wasu Magungunan Hausawa Na GargajiyaYobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 9, Issue 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

SAYE A MATSAYIN MAHAƊIN WASU MAGUNGUNAN HAUSAWA NA GARGAJIYA

Na

Dr. Nura LAWAL

Hadiza Balarabe ADAMU

1.0 Gabatarwa

Al’ummar Hausawa al’umma ce wadda take da hanyoyi da matakai na gane cututtuka na sarari da zuci da kuma suke samar da magunguna domin samun waraka ko sauƙin raɗaɗinsu. Haka kuma, ire-ren waɗannan magunguna suna da mahaɗai domin samun biyan buƙata daga waɗannan magungunan nasu. Hakan tasa saye yana ɗaya daga cikin ire-iren waɗannan mahaɗan magunguna domin samun biyan buƙata. Waɗanda suka yarda kuma suka aminta da su. Binciken masana da manazarta al’adun Hausawa, kamar su Bunza (1990 da 2006 da 2011) da Adamu (1998) da Sallau (2010 da 2013) da Tukur (1988) da Gobir (2012 da 2013) da Gulbi (2013) da Salim (1978) da Yahaya (2012 da 2013) duk sun yi nazari dangane da magani da cuta da waraka da kuma wasu mahaɗan maganin, da kuma saye, amma, babu wanda ya nazarci saye a matsayin mahaɗin wasu magungunan Hausawa na gargajiya. Hakan ta bayar da damar gudanar da wannan bincike.

 Manufar wannan takarda ita ce yin sharhi dangane saye a matsayin mahaɗi wasu magungunan Hausawa na gargajiya. Daga cikin ƙananan batutuwan da wannan takarda ta yi magana a kansu akwai saye da mahaɗin magani a wajen Bahaushe da sayen a wasu sana’o’in Hausawa na gargajiya. Sannan kuma aka fito da matsayin saye na mahaɗin magna daga wasu sana’o’in Hausawa na gargajiya kamar; sana’ar noma da ta wanzanci da ta ɗori da ta su da ta fawa da ta farauta.

2.0 Saye da Mahaɗin Magani A wajen Bahaushe

Al’ummar Hausawa, mutane ne masu hikimomi wajen cuɗanya da mu’amalla a tsakaninsu da kuma a tsakaninsu da wasu al’ummomi, da kuma ta fuskar aiwatar da wasu sana’o’insu na gargajiya, musamman ta fuskar matanonin maganganunsa da suke tafiya bisa jagorancin al’adu. Bahaushe ya samar da hanyoyi mabambanta, wajen samar da magunguna na cututtuka daban-daban domin samar da ingantacce al’umma mai ƙoshin lafiya. Haka ta sa kowane ɓangare na al’adun Hausawa aka yi ƙoƙarin gina hikima don kyautata tarbiyyar al’umma da kuma tsarin zamantakewarsu ta yau da kullum. Wani lokaci a wajen samar da magani ko mahaɗinsa akan yi wasu al’adu kamar camfi ko wani imani domin samun biyan buƙata. Ire-iren waɗannan al’adu suka ba wa saye damar shiga cikin ire-ren waɗannan mahaɗan magungunan Hausawa na gargajiya. Al’ummar Hausawa sun rungumi wannan al’ada ta hanyar aiwatar da ita a cikin wasu ayyuka na masu sana’o’i Hausawa gargagiya, musamman na samar da magunguna.

Salim, (1978:92) ya bayyana saye na nufin ƙin faɗar wani abu ko wani jinsi ko adadi hali ko yanayi da inkiyarsa ta asali. A maimakon haka, sai a yi nuni ko ishara ko alami a kansa ta waɗansu kalmomi ko wasu jimloli waɗanda al’adar al’umma ta aminta da su da za su iya saya ko lanyace ma’anoninsu domin tabbatar wani ɓangare na al’ada.

Wani lokaci al’ada kan yi tasiri a kan yadda za a yi amfani da harshe, da kuma yadda al’adar kan sa Bahaushe ƙin yi amfani da wata kalma, a maimakon haka sai ya ƙirƙiro wata kalmar ya danganta ma’anarta da waccan wadda ya ƙi faɗar. Ke nan kalmar saye na nufin ƙin kiran abu da sunansa, ta hanyar sayawa sai a yi amfani da wata ko wasu kalmomi da suke da kusan ma’ana ɗaya da shi, amma kuma aka amince da su a madadin waccan ɗin (Idris, 2014:52). Ke nan, a iya cewa, saye na nuna cewa Bahaushe mutum ne mai tunani da hangen nesa dangane da tsare al’adunsa da kuma kyautata lafiyar al’umma, ta fuskar wasu magungunan Hausawa na gargajiya.

Magani wata hanya ce ta warkar da ko kwantar da ko rage wata cuta ta ciki ko ta waje ko wadda aka samu ta haɗari. Ko kuma neman kariya ga cuta ko abokan hamayya ko neman ɗaukaka ta daraja ko ta buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-sihirce na ban al’ajabi (Bunza, 1990:25). Shi kuma, Sallau (2010:101) ya bayyana magani shi ne Ƙoƙarin kawar da cuta kowace iri daga jikin mai fama da ita, ko kwantar da ita, ko kuma neman kariya daga kamuwa da cuta, ko abokan hamayya ko maƙiya, ko kuma neman gwada bajinta da ƙwazo da ɗaukaka da daraja a idon mutane ta hanyar nuna tsatsube-tsatsube da sihirce-sihirce masu ban tsoro da mamaki da al’ajabi. Haka zalika, Gulbi (2013:746) ya nuna cewa magani shi ne duk wata hanya da za a yi amfani da ita domin riga-kafin cuta ko rage raɗaɗinta ko ma a kawar da ita gaba ɗaya ko warware ta, ta kimiyar zamani ko a gargajiyance, watau hanyar tsafi da tsibbace-tsibbacen al’umma.

3.0 Saye a Wasu Sana’oin Hausawa na Gargajiya

Bunza (2006:117) ya bayyana cewa “wayewar al’umma da bunƙasarta ya dogara ga irin tsarin tattalin arzikinta da yadda take kyautata shi, Hausawa suna girmama sana’a sosai har ya kai babin cewa, duk wanda ba ya da sana’ar yi ba a ɗauke shi mutum mai kishin kansa ba”.

Haka kuma, sarakuna ko shugabanin ko wasu masu aiwatar da wasu sana’o’i na Hausawa na gargajiya, suna bayar da magunganan wasu cututtuka da suka shafi sana’o’in nasu da kuma gudanar da wasu al’adu na kare sana’a da kuma martabar gado da kuma neman kariya tare da nuna wata buwaya ko yin wata wobuwa ko nuna gwaninta. A bisa waɗannan dalilai masu irin waɗannnan sana’o’i kan nemi hulɗa da Iskoki ko hanyar surkulle ko tsafi. Misali, kamar yadda namoma ke yin wobuwar hatsi da kuma mahauta da suke yin ta nama da masunta da suke yi wobuwa ta hanyar ‘yanruwa da sauransu. Wannan shi ya haifar da wuya a samu wata daɗaɗɗiya sana’a a ƙasar Hausa da ba su gaji Iskoki ko wasu tsatsube-tsatsube ko tsafi domin kare martabar sana’ar da kuma gidansu ba. Kodayake a yau, wannan al’ada ta samu koma-baya saboda tasirin addinin Musulunci. Amma duk da haka, a tattare da waɗannan magunguna ko kare martabar sana’a da gida akan samu al’adar saye a bisa dalili da camfi ko tsoro ko girmamawa ga waɗannan al’adu.

A al’adar Hausawa akwai wasu itatuwa da tsirrai da sassan jikin dabbobi da ma’adanai da wasu masu sana’o’in gargajiya sukan sakaya sunayensu, musamman inda za su yi amfani da su a matsayin mahaɗin magani (Lawal, 2019:185). Haka kuma, wannan na faruwa a dalili na camfin Bahaushe wanda ya yi imani da shi. Hikimar a nan kuma ita ce idan har za a yi amfani da wani nau’i na itatuwa ko tsirai ko ma’adani a matsayin mahaɗin magani to, ba za a faɗi sunansa na asali ko na yanka ba sai dai a sakaya sunansa. Domin da zarar an faɗi sunansa tsirara to maganin ba zai yi ba ko da an haɗa shi yadda aka umarta. Daga cikin ire-iren waɗannan sana’o’i akwai:

3.1 Saye a Sana’ar Noma

 Noma shi ne tonon ƙasa a fitar da amfaninta ta hanyar zafe ta da zankaɗe ta da yin shuke-shuke a bayanta. Ta nan ne ake samun tsirrai na ci da na tsotsa da na yin tufafi da sauransu (Alhassam da wasu, 1988:42). Hausawa na yi wa noma kirari “Noma na duƙe tsoho ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar”. Wannan kirari yana bayyana sana’ar noma daɗaɗɗiya ce a wannan duniya ba wai ga Hausawa kaɗai ba.

Manoma su ma suna yin magunguna, musamman na neman biyan buƙata tare da kare martabar sana’arsu da kuma gado da kuma bayar da wasu magungunan ga saura jama’a. wannan al’ada ta samu ne dalili neman waraka da biyan buƙata. Ke nan wannan buƙata tanada dangantaka da cuta da magani da kuma waraka.

A bisa wannan dalili ne suke aiwatar da wannan al’ada ta saye.Wasu daga cikin ire-iren mahaɗan magungunan da suke yin sayensu akwai:

3.1.1 Icen Gawo

Gawo ana saya shi da Gawa goma, inda za a haɗa maganin maƙiyi, wato maganin kariya daga maƙiya da mahassada, ma’ana duk wanda ya nufe shi da wani mugun abu to, a yi gawa goma gidansa ko a gidansu. Sannan kuma, ana haɗawa da ƙiraran sassabe, amma sai a kira shi da sassaben kawai.

3.1.2 Gwadar Daji

Har wa yau, idan manoma za su haɗa maganin sanda, ana haɗawa ne da Gwandar daji, to amma, suna sakaya ta da Tagida Tadawa, saboda a bisa imaninsu na camfi da har aka faɗi sunan mahaɗin iri waɗannan magunguna to, ba zai yi ba. Ma’ana da dawa take, amma, a gida za a yi amfani da samu biyan buƙata.

3.1.3 Icen Tarauniya

Ana mahaɗin maganin tsarin gida da icen Tarauniya, amma a bisa camfi suna sakaya ta da Ka tsaremu gida Ka tsaremu daji. A bisa tunanin manoma, idan aka haɗa wannna magani, to, mutum zai samu kari da tsaro daga wani abin cutarwa ko wane iri ne a gida da kuma daji, musamman a bisa imani na camfi. Haka kuma, ana haɗa maganin hawan jini ana haɗa shi da icen Tarauniya, amma a nan ana sakaya shi da Kantakara.

3.1.4 Icen Zowu

Idan manoma za su haɗa maganin Miyagu suna amfani da icen Zowu, amma suna sakaya shi da Bukki, saboda al’adar camfi.

3.1.5 Maganin Farfaɗiya

Idan za su haɗa maganin farfaɗiya, manoma suna amfani da icen Sassami, amma suna sakaya shi ne da Sarkin itatuwa. Sassami na yi masa saye da sarkin itattuwa ne ta lura da yadda aka ɗauke shi a matsayi mahaɗi magunguna da yawa.

3.1.6 Maganin farin jini

Maganin farin jini ana haɗa shi da icen Rimi, amma suna sakaya shi da Ɗan’asali. An samar da wannan saye na Ɗan’asali, musamman ta lura da yana sigar rimi, tare da imanin cewa idan aka yi hakan buƙata za tan biya.

3.1.7 Maganin Kunama

Har wa yau, manoma suna maganin kunama da turare, amma a bisa al’adar camfi sai an sakaya sunan sannan maganin zai yi a bisa wannan dalili ne suke sakaya turare da Ruwan Ƙamshi. Ana sakaya saye da ruwan ƙamshi ta la’akari da yana yanayi na ruwa kuma yana da ƙamshi, da an yi hakan kuma sai a samu biyan buƙata.

3.1.8 Maganin Susa

Haka kuma, ana amfani da icen Tsada a wajen haɗa maganin susa ko bulala (borin jini) amma sai su sakaya ta da Tsaya.

3.1.9 Maganin Tsini

Manoma, mutane ne masu amfani da kayan aikace-aikace da suka dangaci tsini, wannan ne ya ba manoma damar samar da maganin tsini, wanda suke haɗawa da ciyawa ko tsiron Dayi, to amma sai an sakaya sunansa sannan maganin zai yi a bisa wannan ne suke yin sayensa da Na raƙumi. Wannan saye da aka yi wa Dayi da bai rasa nasaba da yadda raƙumi yake cin Dayi, wato abinci raƙumi ne.

 3.1.10 Maganin Maciji

 A yayin haɗa maganin maciji ana amfani da Sayan Kaba, amma suna kiransa da Matuƙiya. Wato idan aka yi amfani da ita za ta sa mutum cikin ya tuƙa ya amayar da dafin macijin, ta lura da wannan yanayi sai suka saye ta da matuƙiya.

3.1.11 Kuka Mahaɗin Magani

A bisa al’adar manoma wajen bayar da magani sukan yi sayen wasu itatuwa ko tsirrai, idan za su haɗa magani, musamman a dalili na camfi ko kuma masu amfani da Iskoki. Misali, kuka akan sakaya sunata na asali da uwar hanya masu amfani da kuka a matsayin mahaɗin magani, musamman ‘yanbori da sauran masu hulɗa da aljanu wajen harkar samar da magani. Dalilin wannan sayen shi ne lura da yadda manyan aljanu, musamman mata suka fi ta ruwa a kan kuka. Hakan ta sa a duk lokacin da za a ba da umarnin a ɗebo wani abu daga jikin kuka domin a haɗa magani to, ba za a faɗin sunan kuka ba sai dai a ce uwar hanya. Idan har aka yi karambanin faɗar sunan kuka kai-tsaye to, ko da an haɗa magani ba zai yi ba.

3.1.12 Rama Mahaɗin Magani

Akan yi amafani da rama wajen haɗa magunguna daban-daban, kuma, idan za a yi amfani da rama a matsayin mahaɗin magani akan sakaya sunanta domin samun biyan buƙata. Saboda camfin da masu bayar da magani suke da shi na cewar idan har aka faɗi sunan rama tsirara to, maganin ba zai yi ba. Misali, idan za a haɗa maganin karya tambaya ko sihiri ko jifa ko surkulle akan sayaka sunan rama da Siyaye. Haka kuma, idan za a haɗa magani na cutar da wani ko na mugun abu to akan sakaya sunan rama da Ƙeƙasheshe. Saboda, duk lokacin da mutum zai yi magani da ya shafi mugun aiki, to ba zai irin wannan magani ba sai zuciyarsa ta ƙeƙashe.

3.1.13 Tufafiya Mahaɗin Magani

Tumfafiya akan sakaya ta da ‘Yanmatan dare ko Maiƙorai. Manoma sun lura da yanayin ‘ya’yan tumfafiya sun yi kama da ƙwarya sai dai su ƙanana ne a kan ƙwarya. Har wa yau, da ake sakaya sunan tumfafiya da ‘yanmatan dare, wannan ya samu ne a dalilin imani da Bahaushe ya yi na cewar itaciyar tumfafiya takan rikiɗa da daddare ta kuma yanyi ko siffa ta mutum, musamman a sura ta mata.

3.1.14 Tsamiya Mahaɗin Magani

Har ila yau, tsamiya akan sakaya ta da Mai tsami ko Mai ƙwanƙwamai, abin lura a nan shi ne, Bahaushe ya yi la’akari da yanayi tsamiya na tsami ya sakaya ta da maitsami. Sannan kuma, Bahaushe tun asali yana da imanin cewa tsamiya wuri ko matattara ce ta iskoki, wato aljanu, sai ya yi sayen tsamiya da Mai ƙwanƙwamai, musamman idan za a haɗa maganin samu ko na kariya.

Haka kuma, manoma akan sakaya sunaye wasu itatuwa domin samar da magunguna a al’ada ta camfi. Misali; Gawo ana sakaya shi da Gawa musamman idan za a magani kariyar jiki, ma’ana duk wanda ya nufe ka wani mugun abu samu ko jifa ko to, a yi gawa a gidansa. Haka kuma, akan sakaya sunan saiwar farar ƙaya da Duddushe, idan za a yi laƙanin dusashe ko dakushe ɗaukakar wani, musamman maƙiyi. Icen marke ana sakaya shi da Maraka, musamman idan za a yi wa mutum asirin barin gari, wato kurciya akwai kuma bagaruwa da ake sakaya ta da Ta-majema, ita kumaCeɗiya idan za a maganin shawara da wasu magunguna na sirri suna sakaya ta da Ta-tsakar gida.

Har wa yau, Manoma suna amfani da wasu daga cikin aljanu, amma yawanci Manoman da ke amfani da aljanu, sun fi amfani da Farir aljana, wato Baba, wanda kuma sun yi imani shi ne Uban aljanu. Sannan kuma, duk masu amfani da wannan aljani ba su kirarsa da Baba, musamman a lokaci da za a yi aiki da shi sai dai su sakaya shi da Dogo. Akwai kuma, aljani Duna, wanda suke ɓoye sunansa da Ɗanɓaleri, sai kuma, Kure da suke yi wa saye da Bakurari da kuma, aljana Inna da suke ɓoye sunanta da Dadu. Manoma masu amfani da waɗannan aljanu sun yi imanin cewa duk lokacin da suke da wata buƙata daga waɗannan aljanu, to dole sai an ɓoye sunayensu, saboda girmamawa da kuma tsarin al’adunsu na noma.

Manoma suna aiwatar da wannan al’ada ne a yayi gudanar da ayyukansu na samar da mgani ga al’umma a tsawon rayuwarsu. Haka kuma, wasu daga cikin manoma, musamman waɗanda suka tasirantu da ilimin addinin Musulunci da kuma na zamani sukan sauka daga bisa doron wannan al’ada.

3.2 Saye a Sana’ar Wanzanci

Sana’ar wanzanci tana nufin amfani da askar aski domin yin aski da gyaran fuska da yin kaciya da kuma amfani da kalaba da ƙoshiya don belun-wuya. Sana’ar wanzanci ba ta tsaya a nan ba don kuwa ana amfani da ‘yar tsaga don yin ƙaho da cire angurya a gaban mata da yin tsagar gado da ta kwalliya da ta magani. A sana’ar wanzanci dai, ana yin hujen kunne da yanke yatsar cindo (shiddaniya) da yanke linzama a cikin bakin jarirai da wasu ayyuka da dama. Haka kuma, masu yin sana’ar wanzanci na bayar da magungunan gargajiya ga waɗanda suke buƙata.

Wanzamai suna aiwatar da wannan al’adar saye ne a bisa dalilin biyan buƙata ta magani da kuma shahara. Da kuma dalili na raya al’adun sana’arsu tare da kare martabar gado. Sannan kuma, akwai dalilin dangantakar cuta da magani da kuma waraka. A bisa waɗannan dalilai ne wanzamai suka samar da wannan al’ada ta saye. Misalin ire-iren sayen da wanzamai ke yi a wajen gudanar da sana’arsu. A yayin haɗa bikin wanzamai inda kowa wane wanzami yake nuna gwanintarsa, misali bikinsu na al’ada, waɗanda suke cikin fili da jarirai suna amfani da hakin Gogamasu da BushiyaTo, saboda camfi da kuma tsoro ko gudun kar surkulle ko rufa idon ya ƙi yi to, ba a faɗar sunayensu tsirara sai an saya shi hakin gogamasun ana saye da bushiya ita Bushiya ana saya ta da JariraiSaboda samun biyan buƙata a bisa tunaninsu da imanin da tsatsube-tsatsubensu, wato, idan an yi wannan saye, to da zaran an zo yin wannan al’adar bushiyar ce za ta zama jariran, amma idan wajen samo su ba a sakaya sunayensu ba to, sun yi imanin cewa abun ba zai yi ba.

Haka kuma, suna sakaya icen Gamji da Matattarar tsuntsaye, idan za a ɗebo shi ana yi masa kirari da “Assalamu Gamji, wanda bai san ka ba shi yake ce maka Gamji Ni da na san ka Matattarar Tsuntsaye kake”. Shi kuma icen Gawo ana sakaya shi da Ba-gawa, ana faɗar haka ne domin duk wanda ya neme ka da wani mugun nufi to shi zai zama gawa ba kai ba wato ba kai ba zama gawa a dailin hakan, musamman yadda ya yi wani tsihiri ko tsafi da makamantansu domin ya ga bayanka. shi ma, idan za a ɗebo shi ana yi masa kirari da “Assalamu Gawo, wanda bai san ka ba shi yake ce maka Gawo Ni da na san ka Ba-gawa kake”Waɗannan itatuwa wanzamai suna maganin mayu da kuma maganin kuskurar baki, wato duk wanda suka yi wa baki zai kama shi. Sannan kuma, wanzamai suna sakayawa sunan Haɓo, musamman waɗanda suke yin maganin haɓo ta hanyar addu’a suna kira shi da Durum. Haka kuma, Guna suna ɓoye sunanta da Guna-guna, musamman idan za su ba da magani ƙanƙancewa zakarin yaro. Amma wajen ɗebo ta ana yi mata kirari da “Assalamu alaikum, Guna wanda bai san ki ba shi yake ce maki Guna Ni ko da na san ki Guna-guna kike”.

 Wanzamai na gudanar da wannan al’ada ne a yayi gudanar da ayyukansu na samar da magani da kuma bukukuwansu na al’ada a tsawon rayuwarsu. Haka kuma, wasu daga cikin wanzamai, musamman waɗanda suka tasirantu da ilimin addinin Musulunci da kuma na zamani sukan sauka daga bisa doron wannan al’ada.

3.3 Saye a Sana’ar Ɗori

Sana’ar ɗori na daga cikin sana’o’in gargajiya na Hausa da suka shahara a jiya wajen kula da lafiyar al’ummar ƙasar Hausa da ma maƙwabta, don kuwa a wancan zamani, idan ƙashin mutum ya kare ko ya goce ko kuwa ya sami targaɗe a wata mahaɗar ƙashinsa idan aka kira masu yin ɗori za su ɗora shi ko su gyara wurin da raunin yake ya kuma warke cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ba tare da fuskantar wata matsala ba.

 Maɗora suna gudanar da wannan al’adar saye ne a bisa dalilin neman biyan buƙata ta magani da kuma shahara. Da kuma dalili na kare martabar gado. Sannan kuma, akwai dalili na dangantakar cuta da magani da kuma waraka. Haka kuma, Maɗora suna da nasu camfe-camfe, musamman wajen samo ko ɗebo mahaɗin maganin da suke amfani da su wajen maganin waraka, ko haɗa wasu abubuwa na tsatsube-tsatsubensu. Daga ciki irin ice da tsirran da suke amfani da akwai:

Ɗinya suna sakaya ta da Nonu, sannan kuma, Raiɗorai shi kuma, suna sakaya shi da Tafasar Masar, wato wasu suna ganin kamar asalinsa da Masar ne ko kuma, Masar ma akwai shi. Ana kuma sayensa da Lafiya Dubu, wato lura da yadda ake haɗa magunguna da shi masu yawan gaske.

Har ila yau, Dayi maɗora suna sakaya shi da Ƙayar Raƙuma, saboda yadda raƙumi ya mayar da dayi yana da yanayi na ƙaya sannan kuma, abincin raƙumi ne. hakan ta sa aka yi amfani da wannan yanayi aka saye shi da ƙaryar raƙumi. Sannan kuma, icen darni suna yin sayensa ne da Bazana.wato ya bayan zana ko darni ake amfani da shi, ko kuma, sun yin imani idan suka haɗa wani magani da shi mutum ko yana da layar zana, to, idan zo wajen su ba za ta yi aiki ba.

Haka kuma, Yakuwa ana sakayenta da Sure, sannan kuma Zarangade ana ɓoye sunansa da Rukuɓu. Har ila yau, akwai icen Ƙawari da suke yi wa saye da Rama sama. Zurman sunan ɓoye sunansa da Ledar Ƙadangare. Shi kuma, tsiron da ake kira da Hannu suna sakaya shi da Naruwan zafi, saboda da shi ne ake gasar wurin da aka gyara na karaya ko gucewa ko targaɗe ko tsagewar ƙashi. Igiya kuma, ana sayenta da Azargagi, musammaidan za a yi gyara ta hanyar amfani da aljanu. Haka kuma, Katsinka suna yi masa saye da Ƙimi. Maɗora kuma, suna sakaya sunan abubuwa na hayaƙi, musamman idan ana amfani da aljanu wa aikin. Misali, Kajiji da Ƙaro suna sakaya su da Jinnu. Haka kuma, idan za su haɗa magani da runhu suna sakaya sunansa da Ganyan-mata. Sai kuma tumfafiya da suke ɓoye sunanta da Mutum. Yawancin waɗannan abubuwa maɗora sun yi amfani ya yanayinsu ko amfaninsu suke saye su da shi domin samun biyan buƙata ta magani da sauran tsatsube-tsatsubensu na yau da kullum.

 Maɗora na yin wannan al’ada ne a yayi gudanar da ayyukansu na samar da magani a tsawon rayuwarsu. Haka kuma, wasu daga cikin maɗora, musamman waɗanda suka tasirantu da ilimin addinin Musulunci da kuma na zamani sukan sauka daga bisa doron wannan al’ada.

3.5 Saye a Sana’ar Su

Su sana’a ce da ake shiga ruwa hannu-biyu ko da taru ko da koma ko da mamari ko ma da fatsa, don a kama kifi don ci ko don a sayar, masu wannan sana’ar ana kiransu da Masunta. Saboda muhimmancin Masunta a ƙasar Hausa har sarakuna ake naɗawa da ake kira da Sarkin ruwa.

 Masunta suna aiwatar da wannan al’adar saye ne a bisa dalilin neman biyan buƙata ta magani da kuma shahara. Da kuma dalili na raya al’adun sana’arsu tare da kare martabar gado. Sannan kuma, akwai dalili na dangantakar cuta da magani da kuma waraka.

Masunta kan ɓoye, wasu sunayen mahaɗan magunguna da suke bayarwa daga tsirrai da itatuwa da wasu hilittu na cikin ruwa da na kan tudu. Suna yin hakan ne domin girmamawa da kuma camfi, bisa tsarin al’adunsu, domin kauce wa wata matsala tare da neman biyan buƙata. Masunta suna yin saye na camfi domin neman biyan buƙata da kuma kare martabar gado da sana’a. Misali, icen Ɓaure, ana saka sunansa Jan ice, idan za a yi maganin sanyi da shi. Ita kuma, Kaɗanya, ana sakaya ta da Kaɗa, idan za a maganin hawan jini. Idan za a maganin sammu, masunta suna amfani da Tsamiya, amma ana ɓoye sunanta da Baƙin ice. Haka kuma, Jema, ana maganin sanyi da ita, amma idan za a yi amfani da jema akan sakaya sunanta da Icen kan iyaka. Sannan kuma, masunta ana ba sa kiran sunan Gawa kan-tsaye, musamman a cikin ruwa, saboda kauce wa tsoratar da abokanin aikinsu da kuma waɗanda suke a cikin ruwa. Bisa wannan dalili ne suka sakaya sunan Gawa da Mari ko Gungume.

Har ila yau, masunta suna sakaya sunan Kainuwa da ta-kan-ruwa da kuma, Bado na-kan-rauwa, musamman idan za a yi maganin sanyi da kuma maganin ɓacewa. Icen Gamji ana sakaya shi da jan ice, idan za a yi maganin, buwaya, ana yi sama wannan saye ta lura da yanayi jikinsa, musaman idan aka sara ko aka fasa shi, wato ja ne. a wannan dalili sai ake saye shi da jan ice domin samun biyan buƙata da faranta wa iskoki da ke jikinsa ko tattare da shi a bisa tunanin masunta da imaninsu. Ita kuma, Tsintsiyar Kogi ana sakaya ta da A bar shara, musamman idan za yi maganin ƙarfin gaban maza.Ta samu wannan saye ta lura da yanayin amfanin tsitsiya ta shara. Itaciyar Kaɗanyar Kogi ana sakaya ta da jan ice, idan za a yi maganin sanyi da na kariya. Haka kuma, Lemun kogi ana sakaya shi da sha ko maganin sha, ana farar haka ne saboda yawan amfani da shi a wajen haɗa magunguna. Sassaƙen Ɗinya suna sakaya shi da shayi, waɗannan abubuwa ana yi masu saye, saboda ana maganin sammu ko sihiri da su, kuma idan ana son a samubiyan buƙata, to dole sai an sakaya sunayensu. Haka kuma masunta kan saka sunaye waɗanda itace, musamman idan za a yi maganin sanyi ko maganin sammu ko maganin kare da shahara, waɗannan itatuwa sun haɗa da; zuwo ana sakaya shi da Zare da ƙawari da suke sakayawa da jan ice da kuma ƙirya da suke sakayawa da Baƙin ice ko namijin Ice. Ƙirya ta samu wannan saye ta lura da yanayi, wato ice ne mai wuyar sarfawa. 

Har wa yau, Masunta na sakaya icen Baushe da Abin harbi, da kuma, Tawatsa da suke sakayawa da a bar wuta, sai kuma, Tsada da lemon tsami, sannan kuma, icen Ciwo suna yin sayensa da mai sunan rauni, haka ma icen Kukkuki suna sakaya shi da kuɗi, akwai ko kuma, Tafasa Bakin Kogi ana sakaya shi da Aga, da kuma, Judar Ƙasa da suke sakayawa da yuyu-da-ƙasar maganin sanyin jiki, da kuma maganin mayu da laƙanin dabo. Haka kuma, Runhu ana sakaya shi da Dalbejiyar daji, idan za a yi maganin ciwon ƙuda da ciwon zuciya da shi. Idan kuma, Masunta na yin Su, suka ci karo da Ƙaidaji ko Sarƙarƙiya suna sakaya su da reza, domin sanar da ‘yan’uwansu su kauce masu. Icen Gauɗai da Maɗaci da Ƙirya na cikin ruwa suna sakaya su da Tuf, idan za a yi maganin sanyin ƙashi da Sirri da amfani da su domin yin dabo ko siddabaru da kuma sauran magani na kariyar sana’arsu.

Haka kuma, Masunta ba su faɗar sunan Kada tsirara sai dai suna ɓoye su kira shi da Ƙadangare, kuma duk maganin da za a haɗa da Kada ko wani sashen jikinsa sai dai a ce a samo abin Ƙadangare. Sannan kuma, suna sakaya sunayen ‘Yanruwa; da Uwa misali, Uwar Wudil a Wudil da kuma Maikilago ko Marmara, ko kuma a ɓoye da Baba ko Iya ko yaya. Haka kuma, masunta suna da farin aljani mai suna Abdullahi wanda suke ɓoye sunansa da Alzara. Haka kuma, suna sakaya sunan Dorina da Saniyar ruwa ko jirgi ko fasa jirgi ko Mai-almakashi. Mesa kuma, suna sakaya ta da Bula ko Shimfiɗa ko Maikumbura, ana yi masu wannan saye ne, musamman idan za a haɗa maganin na dabu ko siddabaru ko wobuwa, musamman a kan abin da ake son yi da ya danganci ruwa da abubuwan da ke ciki. Haka kuma, yawancin Masunta ba sa cin naman Mesa, saboda wasu sirrika nasu.

 Masunta na gudanar da wannan al’ada ne a yayin gudanar da ayyukansu na samar da magani da kuma bukukuwansu na al’ada a tsawon rayuwarsu. Haka kuma, wasu daga cikin wanzamai, musamman waɗanda suka tasirantu da ilmin addinin Musulunci da kuma na zamani sukan sauka daga bisa doron wannan al’ada.

4.0 Kammalawa

A wannan takarda an yi tsokaci ne dangane da saye a matsayin mahaɗin magani a wasu sana’o’in Hauswa na gargajiya. Ta haka ne aka yi bayani dangane da saye a matsayin mahaɗin magani a sana’ar noma da ta wanzanci da ta ɗori da ta fawa da ta farauta da ta su. Haka kuma, an fahimci saye yana da matuƙar tasiri wajen samun biyan buƙatu na magani daga cututtuka na sarari da kuma na zuciya da kuma kariya da buwaya da kare martabar sana’a da kuma ta gado, musamman ga wasu masu gudanar wasu sana’o’in Hausawa na gargajiya. An kuma, lura cewa, wannan al’ada ta saye a wasu sana’o’in Hausawa gargajiya tana taimakawa wajen adana wasu al’adun Hausawa. A wannan takarda an gano, cewa akwai dangantaka a tsakanin sayen da cuta sarari da ta zuci da kuma waraka, musamman, ta fuskar magungunan Hausawa na gargajiya. Har wa yau, ana gano cewar, fahimtar sayen a wajen haɗa wasu magungunan Hausawa na gargajiya yana da alaƙa da samun waraka daga cututtuka da kuma samu biyan buƙata daga masu bayar da magungunan da kuma masu amfani da su. Hakazalika, saye a wasu sana’o’in Hausawa na gargajiya na ɗaya daga cikin taskokin adana wasu matanonin zantukan Hausawa da suke taskace al’adunsu da kuma hikimominsu.

Manazarta

Adamu, M.T. (1998). Asalin magungunan Hausawa da ire-irensu. Sarki Kura Publishers Limited.

Alhassan, H. da Musa, U.I. da Zarruƙ, R.M. (1988). Zaman Hausawa. Islamic Publications Bureau.

Brown, P. & Leɓinson, S. (1987). Politeness: Some uniɓersals in language usage. Cambridge: University Press.

Bunza, A.M. (1990). Hayaƙi fid da na kogo: Nazarin siddabaru da sihirin Hausawa. [Kundin Digiri na Biyu]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Bunza, A.M. (2006). Gadon feɗal’ada. Tiwal Publishers Nigerian Limited.

Bunza, A.M. (2011). Magana da iskoki ta bakin dokinsu. In Yalwa, L.Ɗ.da Bichi, A.Y. da Sani, S. (Editoci). Studies in Hausa Language, Literature and Culture. The Siɗth Hausa International Conference. 449-473.

Fermandez, E.C. (2006). The language of death: Euphemism and conceptual metaphorization in ɓictorian obituaries.SKY Journal of Linguistics. Vol 19.

Gobir, Y.A. (2012). Tasirin iskoki ga cutuka da magungunan Hausawa. [Kundin Digiri na uku]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Sokoto: Jami’ar Usumanu Ɗanfodiyo.

Gobir, Y. A. (2013). Najasa a mahaɗin maganin iska. Harsunan Nijeriya Volume ƊƊIII, Special Edition.

Guo, Ƙ. (2010). Cultural Difference in Chinese and English euphemisms. Cross-Cultural Communication Vol.6 (4). 135-141. htt://citeseerɗ.ist.psu.edu

Gulbi, A.S. (2013). Hanyoyin tsafe-tsafe domin magani a al’ummar Hausawa. Cikin Yalwa da Wasu (Editoci). Taron Ƙara wa Juna Ilimi na Ƙasa kan Harshe da Adabi da Al’adun Hausa na Farko. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano. Zaria:Ahmadu Bello University Press.

Idris, H.A. (2014). Tasirin harshen Inglishi a kan al’adar saye a Hausar ‘yan boko. Harshe 8, Journal of African Languages.

Lawal, N. (2019). Nazarin sayen a tunanin Bahaushe jiya da yau. [Kundin Digiri na Uku]. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Salim, B.A. (1978). Saye a Hausa. Harsunann Nijeriya Ɓiii.

Sallau, B.A. (2010). Wanzanci da muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa. M.A. Najiu Professioinal Printers.

Sallau, B.A. (2013). Wanzanci da sauye-sauyen zamani. Ahmadu Bello University Press.

Tukur, A. (1988). Nazari a kan cututtukan da suka shafi fatar jiki da magungunansu a Bahaushiyar al’ada. [Kundin Digiri na Ɗaya]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Yahaya, N. (2012). Euphemism expressions for death in Hausa language. In Amfani, A.H. da Alhassan, B.S.Y. da Malumfashi, A.I. da Tsoho, M.Y. da Amin, M.L. da Abdullahi, B. (Editoci). In champion of Hausa cikin Hausa a festchrift in honour of Ɗalhatu Muhammad.

Yahaya, N. (2013). Sayen suna a ƙasar Hausa : Jiya da yau taɓarɓarewar al’adun Hausawa. Zaria: Ahmadu Bello University Presss.

 Yobe Journal

Post a Comment

0 Comments