Ticker

6/recent/ticker-posts

Kididdigar Salo Da Sarrafa Harshe A Wasu Wakokin Dakta Aliyu Usman Tilde

Citation: Ibrahim BABA, Bappah BABANGIDA & Bashir KAWU (2021). Ƙididdigar Salo Da Sarrafa Harshe A Wasu Waƙoƙin Dakta Aliyu Usman Tilde. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 9, Issue 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

ƘIDIDDIGAR SALO DA SARRAFA HARSHE A WASU WAƘOƘIN DAKTA ALIYU USMAN TILDE

Ibrahim BABA, Bappah BABANGIDA & Bashir KAWU

Tsakure

Salo da sarrafa harshe suna daga cikin abubuwan da ake nazarta a rubutattun waƙoƙin Hausa, a nazarin, akan yi ƙoƙarin fito da muhimman abubuwan da suka shafi waɗannan abubuwa na salo da kuma sarrafa harshe. Ƙididdiga kuwa hanya ce da ake bi wajen nazartar wasu abubuwa a waƙoƙin Hausa, sawa’un waƙoƙin rubutattu ne ko kuwa na baka ne. Aikin ya gudana bayan karanta waƙoƙin da tsinkaye zuwa ga wasu ayyuka makamantansa da masu binciken suka iya samu na ilimi daga wasu ayyuka masu kamanceceniya da wannan aikin. Wannan nazari an ɗora shi bisa kan ra’in da Abba da Zulyadaini (2000) da kuma Ɗangambo (2007) suka ɗora ayyukansu. A wannan binciken, an yi ƙoƙarin ƙididdigar salo da sarrafa harshe a wasu rubutattun waƙoƙi guda biyar daga cikin littafin Waƙoƙin Arulin Hausa na Dakta Aliyu Usman Tilde. Wannan nazari ya yi ƙoƙarin fito da abubuwan da suka shafi salo da sarrafa harshee ta hanyar amfani da alƙaluman ƙididdiga, sannan tare da yin bayanin abubuwan da aka zaƙulo na salo da sarrafa harshen cikin kyakkyawar sura da fassara wasu kalmomin da aka aro daga wasu harsuna.

1.0 Gabatarwa

Rubutacciyar waƙɗaya ce daga cikin rukunan adabin Hausa da ake ƙoƙarin nazari da zaƙulo wasu muhimman abubuwa da suka shafi ɓangarorin ilimi daban-daban. Ta wannan nazarin, ake gano abubuwan da suka shafi jigo, da salo, da sarrafa harshe, da al’ada, da addini, da sauran dukkanin abubuwan da ilimi zai iya ganowa kuma ya adana a matsayin wani muhimmin abu da zai yi amfani a fagen ilimi. Wannan nazarin, ya yi ƙoƙarin bin rubutattun waƙoƙi na Hausa domin zaƙulo abubuwan da suka shafi salo da sarrafa harshe a wasu waƙoƙin littafin Waƙoƙin Arulin Hausa na Dakta Aliyu Usman Tilde, inda aikin ya yi amfani da salon ƙididdiga.

Ɗangambo (2007, sh. 38) ya bayyana salo da cewa, wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci. Wannan yana nufin yin amfani da wata kalma, lafazi, yanayi, hanya ko tunanin a maimakon wani.

Akwai dabaru da masana suka bayyana wajen fitar da salo, waɗannan dabaru kuwa su ne: Kamantawa (ta daidaito, ta fifiko, ta ƙasƙanci), Siffantawa, waskiya, ƙarangiya, jerin sarƙe, jaddadar ƙarfafawa, kambamar zulaƙe, jinsintarwa (mutuntawa, dabbantawa, abuntarwa, alamtawa), kalmomin fannu, baubawan burmi, jinkirtar faɗar sakamako.

Shi kuwa sarrafa harshe, an bayyana shi da cewa, “Hanya ce ta amfani da harshe a cikin waƙa. Wannan hanya ta ƙunshi irin yadda marubuci ke zaɓar kalmomi da jimloli da kuma irin yadda yake amfani da su wajen isar da saƙonsa ga jama’a.

A nazarin sarrafa harshe, akan yi la’akari da karin magana, aron kalmomi, amfani da tsofaffin kalmomi, zaɓen kalmomi, ƙirar kalma a cikin jimla, adon magana, kirari, zuga, zambo, habaici, gugar zana, shaguɓe, baƙar magana, ba’a, zagi, tatsuniya, almara, tashe, abincin Hausawa, tasirin addini, tufafin Hausawa, sana’o’in Hausawa da sauransu.

CNHN (2006) ya bayyana ma’anar ƙididdiga da cewa “Yin ƙididdiga ko ƙwakkwafe abu”. Wato lissafa yawan abu ko abubuwa domin sanin adadinsu.

Ita dai ƙididdiga ana yin ta ne ta hanyar lissafi. Ana ƙididdige yawan abu ko abubuwa da ake bincike a kansu. Idan za a ƙididdiga, ana tsara jadawali na musamman domin aiwatar da ita. Duk alamar da aka gano, sai a sa alama ɗaya a cikin wannan jadawali da haka har a gama. Idan an gama, sai a sake zana wani jadawali mai gida biyu. Gida na farko yana ɗauke da sunan abun da ake ƙididdaga a kansa. Yayin da na biyu kuma yake ɗauke da yawan abubuwan da aka gano.

Dangane da wannan bincike kuwa, an yi amfani da kalmar ‘Ƙidddiga’ ne a matsayin alƙaluman ƙididdiga na yawan dabarun salo da sarrafa harshe da wannan fasihin mawaƙi Dakta Aliyu Usman Tilde ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa wajen isar da saƙonsa ga jama’a. Wato an ƙididdige yawan kowace dabara da ya yi amfani da ita, sannan aka saka sakamakon a cikin jadawali mai gida biyu.

2.1 Ra’in Bincike

Ra’i a bincike abu ne da yake samar da kyakkyawan tsari da fahimtar da mai karatu inda binciken ya dosa. Wannan ta sanya aka ɗora wannan aiki a ra’in da Abba da Zulyadaini (2000) da kuma Ɗangambo (2007) suka yi amfani da shi a nazarin waƙoƙin Hausa. Koda yake Abba da Zulyadaini (2007) sun fi mayar da hankali ne a waƙoƙin baka, amma hanyar da suka kawo ana iya amfani da ita a baka da kuma rubutacciya.

2.2 Hanyoyin Zaɓen Waƙoƙi

An yi wannan aiki ne ta hanyar karance-karance, da bibiyar wasu ayyuka makamantan wannan, sannan aka nazarci waƙoƙin da aka yi nazarinsu. Wannan aiki, an yi ƙoƙarin bibiyar waƙoƙi guda biyar cikin waƙoƙin littafin ‘Waƙoƙin Aruli’, inda aka zaɓi waƙoƙi guda biyar kacal wajen nazartar salo da sarrafa harshe. Waƙoƙin da aka zaɓa kuwa su ne: Waƙar Ilmi, da Waƙar Fure; Saniyata, da Waƙar Yas’alunaka, da Waƙar Kamila, da kuma Waƙar Nasiha ga Buhari.

3.0 Ma’anar Rubutacciyar Waƙa

Masana sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anar waƙa; imma dai ta baka ce ko kuma rubutacciya. Sai dai a nan, mun taƙaita wajen kawo ma’anar rubutacciyar waƙa kawai. Yahaya (1976, sh. 1) ya ce“Waƙa magana ce ta fasaha a cure wuri ɗaya a cikin tsari na musamman”. Shi kuwa Umar (1980, sh. 3) cewa ya yi: “Waƙa tana zuwa ne a sigar gunduwoyin zantuka waɗanda ake kira baitoci ko ɗiyoyi kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman”. Ɗangambo (2007, sh. 6) kuma ya ce: “Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”. A nasa ta’arifin Yahya (1997, sh. 2-3) cewa ya yi: “Waƙa maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani saƙo da ke ƙunshe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru, kuma zaunannu”.

 Ta la’akari da waɗannan ma’anoni, za mu iya kallon waƙa da cewa, waƙa tsararriyar magana ce da ake yin ta cikin hikima da zaɓin kalmomi, ba kara zube ba, domin isar da saƙo ko wata manufa ga al’umma.

3.0 Salo da Sarrafa Harshe a Waƙoƙin Dakta Aliyu Usman Tilde

Kamar yadda ya gabata, salo hanya ce da ake gane dabaru ko hikimar da mawaƙi ya bi domin isar da saƙo. Salo wani abu ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci. Wannan yana nufin yin amfani da wata kalma, lafazi da sauransu, maimakon wani.

Shi kuwa sarrafa harshe hanya ce ta amfani da harshe a cikin waƙa, wato yadda aka nuna gwanintar harshe ta wajen tsarma karin magana, baƙar magana, aron kalmomi da harshe, ginin jimla da sauransu. Don haka, an yi ƙoƙarin gano salon Dakta Aliyu ya yi amfani da shi; salon kuwa na gaba ɗaya, waɗanda suka haɗa da: kwatancin kamantawa da siffantawa da jinsintawa da kuma yadda ya sarrafa aron kalmomin wasu harsuna da karin harshen da ya yi amfani da shi.

3.1 Salo A Waƙoƙin Dakta Aliyu Usman Tilde

A nan, an bibiyi salon da Dakta Tilde ya yi amfani da shi wajen rubuta waɗannan waƙoƙi. An yi wannan aiki kuwa ta hanyar ware rassa na salo da kuma fito da misalan abin da ake so a nuna a kowane babin da buƙatar hakan ta taso.

3.1.1 Kwatantawa

 Ana kwatanta ko auna abubuwa biyu ko fiye, domin a fitar ko a gane dangantakar da ke tsakaninsu. Kwatantawa ta kasu kashi uku, akwai kamantawa da siffantawa da kuma jinsintawa.

3.1.1.1 Kamantawa

Wannan hanya tana kamanta abu biyu ko fiye ta hanyar amfani da wasu kalmomi irin su: ‘kamar’ ko ‘tamkar’ ko ‘awa’ ko ‘ya’ ko ‘kaɗai’ ko ‘ya zarce’ ko ‘ɗara’ ko ‘wuce’ ko ‘fi’ ko ‘gota’ ko ‘tsere’ ko ‘gaza’ ko ‘kasa’ da sauransu. Dabarar kamantawa ta rabu kashi uku, kamancen daidaito da kamancen fifiko da kuma kamancen ƙasƙantawa.

3.1.1.1.1 Kamancen Daidaito

A nan mawaƙi zai kamanta wasu abubuwa biyu ko fiye, yana nuna ɗayan daidai yake da wani, ko waɗansu abubuwa daidai suke da waɗansu. Wannan kamanci na iya zama don aibatarwa ko don rage darajar abin da ake yin kamanci a kansa. Wannan dabara ta fito a waƙar Ilmi da Fure da Kamila da Nasiha ga Buhari da kuma Bulalar Gaskiya. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN KAMANCEN DAIDAITO

1

ILMI

01

2

FURE, SANIYATA

02

3

KAMILA

03

4

YAS’ALUNAKA

02

5

NASIHA GA BUHARI

01

Misali na 1: A waƙar ‘Yas’alunaka’, inda yake cewa:

 A kan na haɗu ka zan mutumin amana,

 Tana da isa kamar maƙata iyawa.

A wannan baiti an daidaita amana da maƙata. Ma’ana amana a wajen sana’a na kai sunan mutum ko kamfani nesa, ya kuma jawo masa alheri daga nesa kamar yadda maƙata ke jawo reshe da ‘ya’yan itatuwa daga sama.

A wakar ‘Nasiha ga Buhari’, an kawo wannan kamancen daidaito a baiti na 16 kamar haka:

 Ka zam tamkar Umar wancan na farko,

 Ka zauna kai ta kukan jarrabawa.

A wannan baiti an shawarci Buhari ya yi ƙoƙari ya zama tamkar Sayyadina Umar wajen yin adalci da kuma yin kukan zuci.

3.1.1.1.2 Kamancen Fifiko

A kamance na fifiko akwai kalmomi da ake amfani da su wajen nuna fifikon wani abu ko wasu abubuwa a kan wani ko wasu. Kalmomin mizanin sun haɗa da: ‘zarce’ ko ‘wuce’ ko ‘ɗara’ ko ‘fi’ ko ‘gota’ ko ‘tsere’ da sauransu.

A irin wannan kamanci, mawaƙi yakan nuna wani abu ko wasu abubuwa da ya kawo sun fi wani ko wasu daraja ko muhimmanci da dai sauransu.

A waƙoƙin Dakta Aliyu Usman Tilde da aka yi nazari, an lura cewa ya yi amfani da wannan dabara a waƙar Fure da Kamila da kuma Nasiha ga Buhari. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN KAMANCEN FIFIKO

1

FURE, SANIYATA

05

2

KAMILA

01

3

NASIHA GA BUHARI

01

Misali na 2: A waƙar Fure, inda yake cewa:

 Nan wurin ne zan tsaya don bayani,

 Ga uwar Bonaji ce, White Fulani,

 Dole ne in ko yi baye ta ba ni,

 Karsanar nono yawa tai da launi,

 Haihuwa har ma ta zarce uwarta.

A wannan baiti an yi kamancen fifiko tsakanin wannan saniya (Fure) da uwarta. An kawo fifikon cewa saboda yawan haihuwar da Fure take yi a kai a kai, har ma ta zarce uwarta ‘ya’ya.

Wani misali kuma na kamance na fifiko shi ne a waƙar Kamila, inda yake cewa:

 Daga ya aje mana ‘yan kuɗi,

 Mu ce ne ba ai ba kamar shiya.

A wannan baiti an kawo kamancen fifiko. An nuna cewa, mutane idan an ba su ‘yan kuɗi kaɗan, sai ka ji suna cewa, ai wannan mutum babu ya shi a cikin al’umma. Wato an nuna mai ba da kuɗi ya fi sauran jama’a.

3.1.1.1.3 Kamancen Ƙasƙanci

A kamancen ƙasƙanci mawaƙi kan ƙasƙantar da ko rushe ko rage darajar wani abu ko wasu abubuwa a kan abin da yake son ya kamanta su da shi. Ana amfani da kalmomin mizani irin su ‘gaza’ ko ‘kasa’ ko kalmomin korewa ‘bai’ ko ‘babu’ ko ‘ba’ da sauransu.

Dakta Aliyu Tilde ya yi amfani da wannan kamance na ƙasƙanci a waƙar Ilmi.Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN KAMANCEN ƘASƘANCI

1

ILMI

 03

Misali na 3: Dubi baiti na ashirin da biyar na waƙar, inda mawaƙin yake cewa:

 Da kuɗi da mota har da dangi su na baya,

Gida har da mata duk ba za sui kamar ilmu.

Da farko dai an ci karo da kalmar korewa ‘ba’, wadda ita ta rage wa duk wani mai daraja ko matsayi daraja, idan aka kwatanta shi da ilmi. Wannan kalma ta ‘ba’ ita ta ɗaukaka ilmi, ta hanyar fitar da shi daban a kan sauran abubuwa. Don haka, an ƙasƙantar da kuɗi da mota da gida da mata da dangi a kan ilmi.

A wakar ta Ilmi kuma duk dai a baiti na (28), inda mawaƙin yake cewa:

 Idan za su kwan yunwa tana cin cikin hanji,

 Ku san ko kaɗan ba ta kamar sui rashin ilmu.

A wannan baiti har ila yau, an nuna cewa, zafin rashin ilmi ya fi kwana da yunwa ciwo. Ma’ana an ƙasƙantar da kwana da yunwa a kan rashin ilmi.

3.1.1.2 Siffantawa

Siffantawa kwatance ne na kai tsaye tsakanin wani ko wasu, domin a nan za a ɗau wani abu a ce shi ne kaza. Ita siffantawa ta kasu kashi biyu. Akwai gajeriyar siffantawa da doguwar siffantawa.

3.1.1.2.1 Siffantawa Gajeriya

A wannan rukuni akan fito da darajar abu ne kai tsaye ba tare da wani dogon bayani ba. Wato akan yi amfani da wasu kalmomi kamar haka: iri-iri, kaza-kaza, akwai kaza, baƙi, fari da sauransu. Akwai irin wannan hikima a waƙar Ilmi da kuma Kamila. Ga jadawalin kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN GAJERIYAR SIFFANTAWA

1

ILMI

02

2

KAMILA

02

Misali na 4: A wakar Ilmi, inda yake cewa:

 Ku san ilmi bai komai idan ba hali mai kyau,

 Hali aƙ ƙasa, kai ne ruwa ke zuba: Ilmi.

A wannan baiti an siffanta ilmi da cewa shi ne ruwa.

Haka nan akwai irin wannan dabara kuma du dai a waƙar Ilmi, inda yake cewa:

 Mu ilmi na dina har da duniya ba haddin,

 Ado ne abin ƙauna ga kowa ka ɗau ilmu.

A nan ma an siffanta ilmi da cewa shi ne ado.

3.1.1.2.2 Doguwar Siffantawa

Ita doguwar siffantawa wata dabara ce da mawaƙa kan yi don bayani wajen fitar da siffar abin da suke so, su bayyana wa masu saurarao a cikin waƙoƙinsu. Dabara ce da manazarci zai fahimci abin da mawaƙi yake yi masa bayani tamkar yana ganin abin a gabansa (a idon zuci) ko kuma hoton abin a zahiri. Akwai irin wannan dabara a waƙar: Ilmi da Fure da Dola da Munajati. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN DOGUWAR SIFFANTAWA

1

ILMI

01

2

FURE

02

Misali na 5: A waƙar Fure, inda yake cewa:

 Ga Fure nan ta yi ‘ya mai jikinta,

 ‘Yar gajera! Ta yi launin uwarta,

 Ta yi hantsa tim da nono gare ta,

 Za a tatsa ai mayawa wajen ta,

 Ba tsayo, kyautarsa Sarkin halinta.’

A nan Dakta Tilde ya zayyana siffar saniyarsa, sai mutum ya ga tamkar yana ganin ta ne a gabansa.

Misali na shida: Haka nan a baiti na (9) a cikin wannan waƙar, ya ƙara kawo wata doguwar siffantawa, inda yake cewa:

 Haihuwa ce har Fure ba daɗewa,

 Karsana ce ga jiki zan na shawa,

 Ta yi gwal launinta sai dai yabawa,

 Ta yi fata, har da gashin abawa,

 Ga jiki girma da sauri a gunta.

A nan za a ga cewa mawaƙin ya fito da siffar wannan saniya (Fure).

3.1.1.3 Jinsintarwa

Jinsintarwa dabara ce inda akan yi kwatance ta fuskar jinsi, wato a ɗauki halayyar wani jinsi a ba wa wani jinsi daban. Kalmar jinsi na nuna yanayin halitta ko wani abu daban. Akwai jinsintarwa ta mutum da dabba da wani abu daban. Ta la’akari da ma’anar kalmar ne wannan rukuni ya sami kashe-kashe.

3.1.1.3.1 Mutuntawa

A wannan kashi mawaƙi kan yi amfani da wannan dabara ce ta hanyar ɗaukar waɗansu halaye ko siffofi ko wasu abubuwa masu kama da haka na bil-Adama, sannan sai a lanƙaya su ga wani wanda ba mutum ba. Misalin wannan hikima ta mutuntawa, akwaita a waƙar Yas’alunaka da Nasiha ga Buhari da kuma Fure Saniyata. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN MUTUNTAWA

1

YAS’ALUNAKA

02

2

NASIHA GA BUHARI

02

3

FURE,SANIYATA

01

Misali na 7: Mutuntawa a nan, shi ne kamar yadda Dakta Aliyu yake cewa a waƙar Nasiha ga Buhari:

 Ga zahinci ka ce tir ba abota,

 Ka korai kulla yaumin ba ragawa.

 

 Idan ya zo ta hanyar ɗan gida ne,

 Ka ce mar ka ƙiya ba ka kulawa.

Idan aka duba waɗannan baitoci za a ga cewa lalle mawaƙin ya yi amfani da hikima ta mutuntarwa. A nan ya mutuntar da ‘zalinci’, yadda ya nuna cewa yana magana.

Misali na takwas: Haka nan, a waƙar Yas’alunaka, ga inda mawaƙin yake cewa:

 Ka san ko a kul ka aikata ko ɗayansu,

 Tsiya a guje tana tafe ba jimawa.

A nan, ya mutuntar da tsiya, inda ya ce tana gudu wadda a zahirin gaskiya ba haka abin yake ba.

3.1.1.3.2 Dabbantarwa

Wannan wata dabara ce da mawaƙi ke mayar da mutum ko wani abu zuwa dabba. A irin wannan dabara akan kamanta bil-Adam da wasu halaye ko siffofi irin na dabbobi.

3.1.2 Kambamar Zulaƙe

 Kambamar zulaƙe dabara ce ta jawo hankali da mawaƙi kan yi amfani da ita. A wannan hanya mawaƙan kan nuna aukuwar wani abu a cikin waƙoƙinsu wanda a zahiri idan aka duba abin da suka faɗɗin sai a ga cewa a haƙiƙa, ba zai faru ba. An sami wannan dabara a wuri ɗaya tak da a misali na gaba.

Misali na 9: A waƙar Fure, inda yake cewa:

 Saniyata, ba ta barka: Yawita,

 In yi nono; in yi nama rabauta,

 Kyan jininta; har na yaɗa maƙwabta,

 Har na nesa, duk su zo don biɗarta,

 In ko ba su taimako, godiyata.

A nan Dakta Aliyu ya nuna cewa, saboda kyan jinin saniyarsa har na haska maƙwabta, kuma ma mutumin da yake nesa ma, zai iya hango ta! Don haka, idan aka duba za a ga cewa abu ne wanda ba zai taba faruwa ba in ba a waƙa ba.

3.2 Sarrafa Harshe

Wannan wata hanya ce ta zaƙulo yanayin harshe da aka rera waƙa da shi. A wannan ɓangare, za a duba abubuwa da suka haɗa da:

3.2.1 Aron Kalmomi

A wannan wuri manazarci zai duba waƙar da ke gabansa, domin tantance shin waƙar an yi amfani da Hausa tsagwaronta ne ko a’a ko kuma an yo aron wasu kalmomi daga wani harshe, kasancewar mawaƙa wasu lokuta sukan aro kalmomi daga Larabci, Turanci, Fulatanci, Barbanci da sauransu.

A bisa nazarin waƙoƙi guda goma na Dakta Aliyu Tilda da aka yi, za aiya cewa aron kalmomi daga wasu harsuna musamman Larabci gonarsa ce. Ya aro ɗimbin kalmomin Larabci, ya aro wasu daga Ingilishi, kaɗan kuma daga Fulatanci, sai dai kuma yakan fassara waɗannan kalmomi shi da kansa.

3.2.1.1 Kalmomin Larabci

Kamar yadda aka faɗa a baya cewa Dakta ya yi aron kalmomi masu yawa daga harshen Larabci. To, hakan ta faru ne saboda tarin ilmin addini da yake da shi. An yi amfani da wannan dabara a cikin kowace waƙa. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN KALMOMIN LARABCI

1

ILMI

23

2

FURE, SANIYATA

23

3

NASIHA GA BUHARI

08

4

YAS’ALUNAKA

28

5

KAMILA

07

Misali na goma: A waƙar Ilmi, baiti na 29 da 33, inda yake cewa:

 Fa ya Rabbi na roƙe ka Sarkinmu mai ilmu,

 Ka nunan Arewata da yara masu ilmu.

 Amana cikin zuciya da ƙauli kaza aiki,

 Ka ƙaro ƙwarewa duk muhimmai ga mai ilmu.

Kalmomin Larabci su ne :

Fa ya Rabbi - To ya Ubangiji

Ƙauli - Magana

3.2.1.2 Kalmomin Ingilishi

Mawaƙin ya yi aron kalmomi daga harshen Ingilishi a wurare kaɗan cikin waƙar Ilmi da Fure da kuma Nasiha ga Buhari. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN KALMOMIN INGILISHI

1

ILMI

01

2

FURE, SANIYATA

05

3

NASIHA GA BUHARI

03

Misali na goma sha ɗaya: Haka nan a waƙar Nasiha ga Buhari, inda yake cewa :

 Mashawarci, minister ko asistan,

 Idan ya bi su ce mar :ban iyawa.

Kalmomin Ingilishi su ne :

Minister - Minista

Assistant - Mataimaki na musamman

Misali na goma sha biyu: A waƙar Fure, nan ma ya yi aron kalmomin Ingilishi kamar yadda yake cewa:

 Nan wurin ne zan tsaya don bayani,

 Ga uwar Bunaji ce : ‘White Fulani’,

 Dole ne in ko yi baye ta ba ni,

 Karsanar nono yawa tai da launi,

 Haihuwa har ma ta zarce uwarta.

Kalmar Ingilishi ita ce :

White Fulani - Shanu farare

3.2.1.3 Kalmomin Fulatanci

Har ila yau, Dakta ya yi aron kalmomi daga harshen Fulatanci. Wannan ba sabon abu ba ne ga mawaƙin saboda ya fito ne daga ƙabilar Fulani kamar yadda aka ambata a baya cikin tarihinsa. Akwai irin wannan aro a waƙar Ilmi da Fure. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN KALMOMIN FULATANCI

1

ILMI

02

2

FURE

10

Misali na goma sha uku: A waƙar Ilmi, inda yake cewa:

 Mi tuubi karambani ku yafe ni,

 Ina ma a ce da na yi himma a kan ilmu.

 Jahala garen wallah da ƙwalwa marar komai,

 Fa ya Rabbi yafe min mauni wala ilmu.

Kalmomin Fulatanci su ne:

Mi tuubi - Na tuba

Min mauni wala ilmu - Na gima ba ilmi

Misali na goma sha huɗu: Haka nan a waƙar Fure, nan ma akwai aron kalmomi daga Fulatanci kamar yadda yake cewa:

 Can Ɓokos ne, Milkway an sayo shi,

 Kai! Ɓaleri, yai jiki don da ƙoshi,

 Ya tsaya cak, duk sifa ba kamar shi,

 Shekaru kau, shekara tak gare shi,

 Sai ka ce an yai bakwai ba kumaita.

 Nai rubutun sha na bayar lalura,

 Basmala nai, Fatiha har Tabara,

 Nai Ƙurayshi, sai salati na ƙara,

 War Fure am! Yardu bindu, ishara,

 De’itin, Jooman a jaabo da simta.’

Kalmomin Fulatanci su ne:

Ɓaleri - Baƙin bijimi

War Fure am! Yardu bindi - Zo Fureta! Shanye rubutu.

De’itin - Kwantar da hankalinta

Jooman a jaabo da samba - Allah karɓi addu’a, nono ya ɗigo.

3.2.2 Karin Harshe

 Hausa na da kare-karen harshe da suka haɗa da: Kananci, Sakkwatanci, Katsinanci, Zazzaganci, Bausanci, Guddiranci da Dauranci. A nan ana buƙatar manazarcin waƙa ya tantance karin harshen da mawaƙi ya yi amfani da shi cikin waƙarsa. In ma wani karin harshe ya jefa yayin da yake rera waƙarsa, to duk mai nazarin waƙa zai fayyace. Dakta Aliyu Tilde dai Babaushe ne, amma saboda zamansa da ya yi a Sakkwato, hakan ya yi tasiri a cikin waƙoƙinsa. Akwai karin harshen Sakkwatanci a cikin waƙar Fure da Kamil da Nasiha ga Buhari. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN KARIN HARSHEN SAKKWATANCI

1

FURE, SANIYATA

06

2

KAMIL

04

3

NASIHA GA BUHARI

03

4

YAS’ALUNAKA

04

Misali na 15: A waƙarsa ta Fure, inda yake cewa:

 Ka gane ni , na yi kiwo da tsara,

 Yau da girma, na yi garke da yara,

 Dukkaninmu, za mu miƙa mu gyara,

 Shan ruwansu, kwanciyarsu da shara,

 Za mu shubka can a gona hakinta.

 In buƙatar kiwata ne yawaita,

 Sai ku kiwo zan Fulani ƙasata,

 In ko nono ko ko nama buƙata,

 Sai ku inganta da baye ga mata,

 Sai ku samo san Gudale wadata.’

Kalmomin Sakkwatanci su ne kamar haka:

Haki - ciyawa

Zan - Kamar

Shubka - Shuka

Misali na 16: Wannan misali ya zo waƙar Kamila, inda yake cewa:

 Daga ya aje mana ‘yan kuɗi,

 Mu ce ne ba ai baya kamar shiya.

Kalmar Sakkwatanci ita ce:

Shiya - Shi

Misali na 17: Haka nan mawaƙin ya yi amfani da karin harshen Kananci a wuri ɗaya cikin waƙar Kamila, inda yake cewa:

 Bara ma ya zam kuma takara,

 Da ƙwafa mu zam masa dariya.

Kalmar Kananci ita ce:

Bara ma - Balle ma.

3.2.3 Tasirin Al’adu

Kasancewar waƙa wani ɓangare ne na adabin gargajiya, adabi kuma tamkar hoton rayuwar Bahaushe yake baki ɗaya, shi ya sa da wuya mawaƙi ya rera waƙa ba tare da an sami tasirin wani ɓangare na al’adun Bahaushe ba a cikinta. Ga mai nazarin waƙa, to ya zama masa lalle ya yi la’akari da irin al’adu da mawaƙi ya zayyana, tare da fito da su filla-filla. Waɗannan ire-iren al’adu sun haɗa da:

3.2.4 Adon Magana

Wannan wata hikima ce da mawaƙa ke amfani da ita domin ƙara wa waƙarsu zaƙi da armashi. A wasu`lokuta adon magana kan zo da siga irin ta karin magana, amma bai kai karin magana nauyi ba. Dakta Aliyu Tilde ya yi amfani da adon magana a cikin waƙar Ilmi da Fatiha da Kamil. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN ADON MAGANA

1

ILMI

01

2

KAMIL

03

3.2.5 Kirari

Kirari wata dabara ce da mawaƙa suke amfani da ita cikin waƙokinsu su yi wa wani kirari. Wannan mawaki ya yi amfani da wannan dabara a wuri ɗaya tak.

Misali na goma sha takwas: A wakarsa ta Fure, saniyata’, inda yake cewa:

 Ga misali gun Fure ‘yar amana,

 Gun jininta, ‘yar Gudale-da Buna,

 Can uwarta, Buna ce in ka auna,

 Ga ɗiyar Buna-maso-Frisiana,

 Za a nono mai yawa du agunta.

3.2.6 Zagi

A wasu lokuta mawaƙan Hausa kan fito su yi zagi a cikin waƙoƙinsu. Irin wannan zagi yakan sha bamban da habaici ko zambo ko shaguɓe. Wannan mawaƙi ya yi amfani da wannan dabara a cikin waƙarsa ta Kamil. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN ZAGI

1

KAMIL

02

Misali na goma sha tara: A waƙar Kamila, inda yake cewa :

 Akasin hakan mu yi tsinuwa,

 Daga nan mu ce masa ɗan tsiya.

 Da ƙashin tsiya a gare shi ai,

 Haka nan muke ta ashariya.

3.2.7 Tasirin Addini

Kamar yadda aka sani addinin Bahaushe shi ne Musulunci. Mawaƙa kan yi amfani da wannan dama wajen saƙala addini a cikin waƙoƙinsu. A wasu lokuta mawaƙa sukan fito da yadda Musulunci yake da tasiri a cikin waƙoƙinsu ta hanyar ambaton Ubangiji da godiya gare Shi. Misali, Dakta Aliyu Usman Tilde ma ya yi amfani da wannan dama a cikin waƙoƙin, domin a ƙarshen kowace waƙarsa yakan godewa Allah da ya ba shi ikon yin waƙar.

3.2.8 Abincin Hausawa

A wasu lokuta mawaƙa kan zayyana wasu daga cikin ire-iren abincin Hausawa a cikin waƙoƙinsu. Wajibi ne mai nazarin waƙa ya fito da ire-iren waɗannan nau’o’i na abinci kamar yadda mawaƙin ya ambata. Dakta Aliyu Tilde ya yi amfani dawannan dabara a cikin waƙarsa ta Fure. Ga jadawalin yawansu kamar haka:

LAMBA

WAƘA

YAWAN AMBATON ABINCIN HAUSAWA

1

FURE

01

4.0 Kammalawa

Idan aka natsu, za a ga lalle wannan nazari ya yi shawagi cikin kogin rubutattun waƙoƙin Dakta Aliyu Usman Tilde, inda aka fara da bayyana ma’anar rubutacciyar waƙa, Sannan aka shiga batu a kan salo, sarrafa harshe da kuma ƙididdiga. Nazarin, ya yi ƙoƙarin fito da wasu abubuwan da suka shafi salo da sarrafa waƙa a cikin waƙoƙin Marubucin, inda aka taƙaita aiki a waƙoƙi biyar kacal da suke cikin littafinsa na Waƙoƙin Aruli. A nazarin, an yi ƙididdigar waɗannan abubuwa, wato salo da sarrfa harshe, tare da amfani da alƙaluman lissafi na ƙididdiga.

A wannan nazari, an gano yadda marubucin ya yi amfani da ɓangarori na harsunan da yake iya amfani da su wajen tsattsarma kalmomin a cikin wasu waƙoƙinsa. Sannan an gano yadda ya fito da wasu abinci na Hausawa a ɓangaren al’ada. Sannnan an ga tasirin addinin Musulunci a waƙoƙinsa, kamar yadda aka ga kirari da kuma zagi, duk da kasancewar sun ƙaranta a waƙoƙinsa sakamakon tasirin addinin Musulunci. Ta fuskar salo kuwa, an ga abubuwa da dama da aka yi ƙididdigarsu. Wannan nazari ya ƙarƙare da wannan taƙaitattun bayanan kammalawa da abin da binciken ya gano.

Manazarta

Abba da Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan waƙar baka ta Hausa. Kaduna: Gaskiya

CNHN. (2006). Ƙamusun Hausa na jami’ar Bayero. ABU Press.

Corporation.

Umar, M. B. (1980). Nazarin waƙoƙin Hausa. Hausa Publication Centre.

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar gadon feɗe waƙa. Amana Publishers.

Yahaya, I. Y. da Muhammad, S. (1976). Darussa a kan adamin Hausa. institute of Education, Ahmadu Bello University.

Yahya, A. B. (1997). Jigon nazarin waƙar baka. Fisba Media Serɓice.

 Rataye

Jadawalin yawan ƙididdigar salo da sarrafa harshe na waƙoƙi biyar na Dakta Aliyu Usman Tilde da muka yi nazari a cikinsu.

LAMBA

SUNAN WAƘA

 YAWAN DABARUN

FITAR DA SALO

YAWAN SARRAFA

HARSHE

YAWAN TASIRUN

AL’ADU

1

IMLI

 07

 33

 01

2

FURE

 08

 50

 03

 

NASIHA GA BUHARI

 04

 09

 01

4

YAS’ALUKA

 04

 29

 01

5

KAMILA

 08

 08

 03

 Yobe Journal


Post a Comment

0 Comments