Sauyin Yanayi-
Alamominsa da Illolinsa da Tasirinsa a Ƙasar Hausa
Daga
Muhammad Abubakar Zabi
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Sa’adu Zungur University, Gaɗau
08136844199
muhammadabubakarzabi@gmail.com
Da
Musa Alhaji Abdulrahaman
Department of Languages and Linguistics
Yobe State University, Damaturu
abdulrahamanmusa1661@gmail.com
08036719021/08027277904
Tsakure
Wannan nazari ne kan matsalar sauyin yanayi da
yadda yake shafar rayuwar al'ummar Hausawa a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa
maso Gabas na ƙasar nan. Nazarin zai bayyana alamomin sauyin yanayi
kamar su; fari, ambaliyar ruwa da kwararowar hamada, da kuma tasirin su
ga ƙasar Hausa da al’ummarta, musamman harkar noma da
kiwo da samuwar ruwan sama da lafiya da kuma zaman
lafiya. Takardar ta kuma binciki matakan daidaitawa da ragewa da za a ɗauka ko kuma ya kamata
a ɗauka don fuskantar
wannan ƙalubale. Haka kuma, Don cimma manufar binciken,
takardar ta yi amfani da Ra'in Dangantakar Al'ada da Muhalli (Cultural
Ecology Theory) a matsayin gishikin bincike. Wannan ra'in ya taimaka wajen
fito da yadda sauyawar muhalli ke tilastawa al'ummar Hausawa sauya dabi'unsu na
gargajiya da hanyoyin rayuwarsu. Binciken ya gano cewa alamomin sauyin yanayi
kamar zafin rana mai tsanani, rashin tabbas na damina, da kwararowar hamada sun
bayyana a fili a yankin. Wadannan abubuwa sun haifar da illoli masu yawa da
suka hada da karancin abinci, rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, da
kuma yawaitar talauci. Haka zalika, takardar ta nuna cewa sauyin yanayi ya yi
tasiri wajen sauya al'adun Bahaushe, inda ya sanya dole aka sauya nau’ukan irin
shuka, aka rungumi gine-gine na zamani, kuma aka samu yawaitar cirani da hijira
zuwa birane domin neman abin yi. A karshe, takardar an gabatar da shawarwari ga
mahukunta da al'umma kan muhimmancin dasa bishiyoyi, samar da hanyoyin noma na
zamani, da kuma wayar da kan jama’a domin rage radadin wannan matsala.
1.0 Gabatarwa
Duniya tana fuskantar gagarumin sauyin yanayi, wanda
masana ke kira da "sauyin yanayi" (climate change).
Wannan batu ya zama ɗaya daga cikin
manyan ƙalubalen da bil'adama ke fuskanta a wannan ƙarni na ashiri da ɗaya 21, tare da illoli
masu tasiri kai tsaye ga rayuwar miliyoyin mutane, musamman a ƙasashe masu tasowa
wanda ƙasar Hausa ba ta tsira ba. Sauyin yanayi yana nufin
gagarumin sauyi a tsarin yanayin zamantakewar al’ummar duniya kuma har da ƙasar Hausa da
yankunanta, wanda zai iya bayyana a matsayin sauyin yanayin zafi da ruwan sama
da yanayin iska, ko sauran alamomin yanayi na tsawon lokaci (UNDP, 2021).
Dalilan faruwarsa kuwa sun haɗa da ayyukan ɗan Adam kamar ƙona ɓurɓushin mai (fossil fuels)
da sare itatuwa, da kuma dagolon masana'antu.
Yankin da Hausawa ke zaune, wanda ya mamaye manyan
sassan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas na Najeriya da kuma wasu sassan
Jamhuriyar Nijar da Kudancin Chadi, yana daga cikin yankunan da ke fuskantar
matsanancin tasirin sauyin yanayi. Wannan yanki, wanda yawancin al'ummarsa suka
dogara ga noma da kiwo don rayuwarsu, yana haddasa da matsaloli
kamar Fari mai tsanani da ambsaliyar ruwa ta
lokaci-lokaci da kuma kwararowar Hamada da ke ci gaba da ci
gaba. Waɗanna matsaloli suna
haifar da ƙarancin abinci da rashin wadatar ruwa da tabarɓarewar lafiya da
kuma ƙaura da rikice-rikice na zamantakewa.
1.1 Sauyin Yanayi
Don fahimtar sauyin yanayi, yana da muhimmanci a fara
bambanta tsakanin yanayi (weather) da gurbi
(climate). Yanayi na nufin yanayin sararin samaniya na ɗan gajeren lokaci, kamar
yadda yake a yanzu (misali, "yau yanayin zafi ne" ko "akwai
hadari"). Gurbi kuwa yana nufin matsakaicin yanayin sararin samaniya na
dogon lokaci a wani yanki, misali, "gurbi a arewacin Najeriya yana da zafi
da bushewa." Sauyin yanayi ke nan shi ne gagarumin sauyi
a wannan matsakaicin yanayin gurbi na tsawon lokaci, wanda zai iya kai wa
shekaru da dama.
Babban dalilin canjin yanayi na zamani shi ne ƙaruwar hayaki mai
gurbata iska, wato gasassu masu kama zafi (greenhouse gases), kamar su
carbon dioɗide (CO2) da methane
(CH4) da nitrous oɗide (N2O). (UNDP, 2021).
Waɗannan gasassu suna
fitowa ne daga ayyukan ɗan Adam, musamman:
·
ƙona burbushin mai (fossil fuels): Wato mai da gas da
gawayi don samar da wutar lantarki da sufuri da masana'antu.
·
Sare
itatuwa (deforestation): Itatuwa suna shan carbon dioɗide, don haka sare su yana
kara yawan carbon dioɗide a sararin samaniya.
·
Ayyukan
noma da kiwo: Misali,
takin zamani da dabbobi suna fitar da methane.
·
Masana'antu: Wasu masana'antu
suna fitar da gasassu masu gurɓata iska.
1.2 Tarihin Canjin Yanayi: Tun daga juyin juya halin
masana'antu (Industrial Reɓolution) a ƙarni na 18, yawan
gasassu masu kama zafi ya ƙaru sosai a sararin samaniya. Masana kimiyya sun fara
lura da hakan tun shekarun 1980s, da kuma rahotanni daga ƙungiyoyin duniya
kamar Intergoɓernmental Panel on
Climate Change (IPCC) sun tabbatar da cewa sauyin yanayi yana faruwa
kuma ayyukan ɗan Adam ne ke da alhakin
hakan (IPCC, 2023).
1.3 Alamomin Sauyin Yanayi
Akwai alamomi da dama da ke nuna cewa sauyin yanayi
yana faruwa a duniya da kuma a yankin ƙasar Hausawa:
·
Ƙaruwar Zafin Jiki da Gurare: Matsakaicin zafin
jiki na duniya yana ci gaba da hawa. A yankin Hausawa, ana ganin ƙaruwar tsananin lokutan
zafi da kuma gajartar lokacin sanyi.
·
Sauyin
Yanayin Damina da Rani: Ana samun sauyin yanayin damina, inda wasu
lokutan ruwan sama ke ƙasa ko kuma ya yi yawa har ya haifar da ambaliya.
Lokacin damina na iya gajarta ko kuma fara jinkiri.
·
Karuwar
Tsananin Fari: Fari
ya zama ruwan dare a yankuna da yawa, yana shafar noma da samar da ruwa.
·
Yawaitar
Ambaliyar Ruwa: Ko
da yake ana samun fari, amma kuma ana samun ruwan sama mai yawa a lokaci guda,
wanda ke haifar da ambaliya a yankunan da ba a saba gani ba.
·
Kwararowar
Hamada: Hamada
tana ci gaba da cin yankunan da ke da tsiro, musamman a jihohin arewa.
·
Sauye-sauye
a Yanayin Iska: Ana
lura da sauye-sauye a tsarin iska da kuma yawaitar guguwa ko iska mai ƙarfi a wasu
lokutan. (Saɓe the Children, 2023).
1.4 Manufar Bincike
Manufar wannan bincike ita ce, binciko alamomi da illoli da tasirin
sauyin yanayi a kan al'umma da muhallin Ƙasar Hausa. Don haka, muradun da za a cimma a ƙarƙashin manufar su ne:
1.4.1 Muradun Bincike
Waɗannan muradu ne da aka
keɓe waɗanda za a cimma su ta
hanyar nazari mai zurfi:
Muradi na 1: Tabbatar da Alamomi
·
1.4.1.1 Gano
yadda karuwar matsakaicin zafin rana da tsawaitawar lokacin
rani suka bayyana a cikin bayanai na kimiyya a cikin shekaru goma na ƙarshe a yankin Ƙasar Hausa
·
1.4.1.2 Tabbatar da
yadda rashin tabbas na ranakun fara Damina da ƙaruwar ambaliyar
ruwa suke shafar lokacin da manoma ke yi na shuka a shekara.
Muradi na 2: Nazarin Illoli da Haɗari
·
1.4.2.1 Nazarin alaƙar da ke
tsakanin kwararowar hamada (desertification) da kuma
tsanantar rikicin makiyaya da manoma a yankin, wanda hakan ke
nuna ƙarancin albarkatun ƙasa.
·
1.4.2.2 Bayyana
yadda raguwar amfanin gona da ke faruwa saboda sauyin yanayi ke
haifar da ƙarancin abinci da talauci na dindindin a cikin
al'ummar karkara ta Hausa.
Muradi na 3: Fahimtar Daidaitawar Al'adu
·
1.4.3.1 Binciko waɗanne hanyoyin noma
na zamani (misali: noman ban ruwa, shuka iri mai saurin nuna) ne Hausawa
suka runguma a matsayin hanyoyin daidaitawa don kiyaye tsarin
rayuwarsu.
·
1.4.3.2 Fito da
yadda cirani (migration), musamman na matasa, ya zama
babbar dabi'ar daidaitawa ta al'adu a cikin Ƙasar Hausa, kuma yadda
hakan ke shafar dangantaka a tsakanin iyali.
2.1 Ra'in Bincike
Wannan bincike yana dogara ne kacokan kan Ra'in
Dangantakar Al'ada da Muhalli (Cultural Ecology Theory).
2.1.1 Ra'in Dangantakar Al'ada da Muhalli (Cultural Ecology
Theory)
Wannan ra'i, wanda Julian Steward (1955) ya gabatar,
yana duba yadda al'adun wata al'umma ke daidaitawa da muhallin da suke ciki.
Ra'in ya mai da hankali kan:
1. Tsarin Rayuwa (Culture Core): Wannan shi ne ɓangaren al'ada wanda ke da alaƙa kai tsaye da rayuwar yau da kullum (misali:
yadda ake noma, yadda ake gine-gine, da tattalin arziki).
2. Daidaitawa (Adaptation): Yadda al'umma ke canza Tsarin Rayuwarsu
idan muhalli ya yi musu barazana.
2.2.2 Aiwatar da Ra'in a Ƙasar Hausa
A cikin Ƙasar Hausa, Tsarin Rayuwa yana dogara ne kan noman
damina. Saboda haka, illolin sauyin yanayi (fari da zafi) suna barazana kai
tsaye ga wannan tsari. Wannan takarda za ta yi amfani da ra'in ne wajen
binciko:
·
Amsar Bahaushe: Waɗanne
hanyoyin Daidaitawa ne Hausawa suka kirkira (misali: hijira
daga ƙauye zuwa
birni, ko kuma sauya sana'a daga noma zuwa kasuwanci) don kare Tsarin
Rayuwarsu daga matsalar sauyin yanayi?
3.0 Hanyoyin Gudanar da Bincike
3.1 Gabatarwa
Wannan babi yana bayanin dabarun bincike da aka yi amfani da su
wajen gudanar da wannan aiki. Ya kuma bayyana yadda aka gano tushen bayanan,
hanyoyin tattara su, da kuma yadda aka yi nazarin bayanan da aka samu domin
cimma maƙasudin
binciken da aka gindaya a Babi na Daya.
3.2 Tsarin Bincike
An yi amfani da Tsarin Bincike na Nazari da Bayyanawa
(Descriptiɓe Ƙualitatiɓe
Research Design). An zaɓi wannan tsari ne saboda burin aikin shi ne ya
yi nazari da ya fassara da kuma bayyana alaƙar da ke tsakanin sauyin yanayi da kuma dabi'u
na al'adu a Ƙasar
Hausa. Tsarin ya dace da amfani da Ra'in Dangantakar Al'ada da Muhalli
(Cultural Ecology Theory) wajen nazarin dabi'un mutane.
3.3 Wajen Bincike
Wajen Binciken shi ne Ƙasar Hausa, wanda ya haɗa da jihohin da suka fi dogara da noma kuma suke fuskantar
barazanar kwararowar hamada, kamar Kano da Katsina da Sokoto da Zamfara. Zaɓin wannan wuri ya dace ne saboda shi ne yankin da ya fi kusa da
yankin Sahel kuma illolin sauyin yanayi suna bayyana karara a can.
3.4 Tushen Bayanai
Domin gudanar da wannan bincike, an dogara ne kan tattara bayanai
daga tushe guda biyu:
3.4.1 Bayanan Taimako
Wannan shi ne tushe mafi muhimmanci ga wannan takarda. An tattara
bayanai daga rubuce-rubucen da aka riga aka yi a baya, waɗanda suka shafi sauyin yanayi da al'adu a Arewacin Najeriya.
·
Tushen Bayanai:
o Littattafan Ilimi: Littattafan da suka yi bayani kan Cultural Ecology da
kuma nazarin muhalli a Afirka (misali: littattafan Mortimore, 1989).
o Jaridun Ilimi (Peer-Reɓiewed
Journals): Makaloli
daga mujallu na duniya da na gida da suka tattauna Alamomi, Illoli, da Hanyoyin
Daidaitawa (Adaptation) a Najeriya (misali: makalolin Abaje et al.,
2014).
o Rahotanni (Official Reports): Rahotanni daga Hukumomin Gwamnati (FGN), da na
Majalisar Ɗinkin
Duniya (UN), da kuma na Hukumar Kula da Yanayi ta Duniya (IPCC).
3.5 Tasirin Sauyin Yanayi Dangane da Noma da Kuma
Abinci da Muhalli
Noma shi ne jigon tattalin arzikin al'ummar Hausawa,
inda sama da kashi 70% na al'umma ke dogara a kai kai tsaye ko a kaikaice.
Canjin yanayi yana haifar da babbar barazana ga wannan fanni, yana shafar samar
da abinci da rayuwar miliyoyin mutane.
Fari da Ambaliyar Ruwa
·
Fari: Yanayin fari mai
tsanani yana haifar da rashin isasshen ruwan sama, wanda ke shafar noman rani
da na damina. A yankuna kamar Misali: A wasu Yankunar Ƙasar Hausa Jigawa,
Kebbi, Kano da Sauransu da Arewa maso Gabas, kamar wasu sassan Jihar Yobe da
Borno,
an sha fama da fari da ya lalata amfanin gona, ya kuma kashe dabbobi, wanda
hakan ya haifar da yunwa da karancin abinci. Fari yana rage ingancin kasa,
wanda ke ƙara ɗaurewa manoma kai. (UNEP, 2021).
·
Ambaliyar
Ruwa: Duk
da matsalar fari, ana kuma samun ruwan sama mai yawa a lokaci guda, wanda ke
haifar da ambaliya mai tsanani. Ambaliyar ruwa tana lalata
gonaki da gidaje da ababen more rayuwa kamar tituna da gadoji. Misali, a
shekarun da Suka gabata shekarun da aka yi ambaliya a Najeriya, misali:
2012 da 2022 da 2024 an shafe dubban hekta na gonaki a jihohin Misali:
Jigawa da Kebbi da Bauchi da kuma Yobe, saboda ambaliyar ruwa, wanda
ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa. Wannan yana sanya manoma
cikin halin }a}a-ni-kayi, da rasa jari da kuma hanyar dogaro da
kai. (UNEP, 2021).
Kwararowar Hamada
Kwararowar hamada wata babbar matsala ce a yankin
Sahel, wanda ya haɗa da arewacin Najeriya
da Nijar. Wannan lamari ne na faɗaɗar hamada zuwa yankunan
da a da suke da tsirai da albarkar ƙasa, sakamakon canjin
yanayi da kuma ayyukan ɗan Adam kamar sare
itatuwa ba bisa }a'ida ba da kiwon dabbobi fiye da kima da kuma noma ba tare da
bin ka'ida ba. Jihohin kamar Borno, Yobe, Jigawa, Katsina, da Zamfara suna
fama da wannan matsala sosai (NPC, 2017). Kasa mai noma tana rasa gurbinta,
tana zama yashi, wanda ke sa noman ya yi wuya ko ma ba zai yiwu ba. Wannan yana
haifar da ƙaura daga yankunan karkara zuwa birane ko wasu yankuna
masu albarka, wanda ke haifar da cunkoso da ƙaruwar matsalolin
zamantakewa.
Rashin Wadatar Abinci (Food Scarcity and Insecurity)
Sakamakon fari da ambaliya da kwararowar Hamada da
samar da abinci a yankin ƙasar Hausa ya ragu matuƙa. Wannan yana haifar
da:
·
Karancin
Abinci: Akwai
karancin kayan abinci na gida, wanda ke sanya dogaro ga abinci daga waje.
·
Hawan
Farashin Abinci: Idan aka samu karancin abinci da farashin
kayayyaki na hauhawa, wanda ke shafar talakawa da matasa. Wannan yana sanya
rayuwa ta zama mai tsada da wahala.
·
Yunwa
da Gurɓacewar Abinci: ƙarancin abinci yana
haifar da yunwa, musamman a tsakanin yara ƙanana, wanda ke shafar
lafiyarsu da ci gabansu. A wasu lokuta ma, ana iya cin abincin da bai inganta
ba saboda tsananin yunwa. (Zabi, 2017)
4.0 Tasirin Sauyin Yanayi ga Ruwa da Lafiyar Al’umma
Ruwa da Lafiyar Jama'a
Samuwar ruwa mai tsafta yana da matuƙar muhimmanci ga lafiyar
jama'a da rayuwa gaba daya. Canjin yanayi yana shafar albarkatun ruwa a yankin
Hausawa ta hanyoyi da dama:
·
Ƙarancin Ruwa Mai Tsabta: Fari da raguwar ruwan sama suna
haifar da bushewar koguna da tabkuna da rijiyoyi. Misali, Tabkin Chadi ya
bushe matuƙa a cikin shekaru goma da suka gabata saboda canjin
yanayi da kuma amfani da ruwa fiye da kima, wanda hakan ya shafi miliyoyin
mutane da ke dogaro da shi don noma da kiwo da kamun kifi (UNEP, 2021). Wannan
yana tilasta mutane yin dogon tafiya don neman ruwa, wani lokacin ruwan ma ba
shi da tsafta.
·
Cututtuka
Masu Alaƙa da Ruwa Kan Bijirowa Al’umma: Samar da ruwan da
bai dace ba ko kuma ambaliyar ruwa na iya haifar da yawaitar cututtuka masu yaɗuwa. Cututtukan
kamar kwalara (cholera) da zazzabin cizon sauro
(malaria) da typhoid suna yawaita a lokacin damina da
kuma bayan ambaliya saboda gur~acewar ruwa da kuma yawaitar sauro. Yanayin zafi
kuma yana goyon bayan ya]uwar kwayoyin cuta da kwari masu ya]a cututtuka.
·
Tasirin
Zafi Mai Tsanani: Karuwar zafin jiki na iya haifar da matsalolin
ga lafiyar al’umma kamar su bugun zuciya (heatstroke), musamman ga
tsofaffi da yara ƙanana. Yana kuma shafar damar yin aiki a waje,
musamman ga manoma da ma'aikatan gine-gine. (IPCC, 2023).
5.0 Tasirin Sauyin Yanayi ga Tattalin Arziki da
Zamantakewar Jama’a
Tasirin canjin yanayi baya tsayawa ga noma da
ruwa kaɗai; yana kuma shafar wasu
fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'ummar.
Tattalin Arziki
·
Raguwar
GDP: Yankunan
da suka dogara da noma da kiwo suna ganin raguwar abin da suke samarwa. Saboda
lalacewar amfanin gona da dabbobi. Wannan yana shafar tattalin arzikin gida da
na jihohi da na ƙasa baki ɗaya (Gross Domestic Product - GDP).
·
Asarar
Dukiya: Fari
da ambaliyar ruwa suna haifar da asarar manyan dukiyoyi kamar gonaki da dabbobi
da gidaje da sauran kayan al'umma. Wannan yana sanya iyalai da yawa cikin
talauci mai yawa, yana jefa su cikin tsananin kuncin rayuwa.
·
Rashin
Aikin Yi: Lalacewar
noma da kiwo yana haifar da rashin aikin yi ga miliyoyin
mutane, musamman matasa. Wannan yana tura su zuwa birane don neman aiki, wanda
ke haifar da cunkoso da kuma ƙaruwar laifuffuka. Wasu
ma suna komawa ga ayyukan ta'addanci saboda rashin bege. (NPC, 2017).
·
Zamantakewa
da Gudun Hijira
·
Kaura
da Gudun Hijira: Tasirin canjin yanayi, musamman kwararowar
hamada da fari, yana tilasta al'ummomi yin ƙaura daga garuruwansu zuwa wurare masu
albarka. Manoma da makiyaya suna ƙaura daga arewa zuwa
tsakiyar Najeriya don neman abin dogaro da kai. Wannan yana haifar da cunkoso a
sabbin wuraren da suka koma. (Alhassan, 1982)
·
Rikicin
Manoma da Makiyaya: Gudun hijira da canjin yanayi sukan haifar
da ƙara ruruta wutar rikicin manoma da makiyaya.
Makiyaya da ke neman ciyawa da ruwa ga dabbobinsu suna shiga gonakin manoma,
wanda ke haifar da rikice-rikice da asarar rayuka da dukiyoyi. Wannan ya zama
babban matsalar tsaro a ƙasar Hausa da makwabtanta, musamman a jihohin Misali:
Kaduna, Benue, Plateau, Nasarawa (Armed Conflict Location & Eɓent Data Project -
ACLED, 2024).
·
Matsalar
Tsaro da Ta'addanci: Masana sun nuna cewa canjin yanayi na ɗaya daga cikin abubuwan
da ke rura wutar ta'addanci a yankin Sahel. Rashin wadata da
talauci da canjin yanayi ke haifarwa na iya sa matasa su zama masu sau}in shiga
}ungiyoyin 'yan ta'adda kamar Boko Haram da ISWAP, wa]anda ke ba su abinci da
kudi don su shiga sahunsu (UNDP, 2021).
6.0 Matakan Daidaitawa da Ragewa
Don fuskantar ƙalubalen canjin yanayi,
akwai bukatar a ɗauki matakan daidaitawa
(adaptation) da ragewa (mitigation).
Matakan Daidaitawa (Adaptation)
Waɗannan matakai ne da
ake ɗauka domin daidaita
rayuwa da illolin canjin yanayi da suka riga suka faru:
·
Noma
Mai Dorewa:
o Amfani da Irin Noma Mai Jure Fari: Manoma su koma
amfani da irin amfanin gona da aka inganta wanda zai iya jure yanayin fari da
kuma bukatar ruwa kaɗan.
o Fasahar Ban Ruwa: Karfafa tsarin ban
ruwa na zamani kamar irin su drip irrigation don amfani da ruwa yadda ya
kamata.
o Noman Zamani: Koyar da manoma sabbin hanyoyin noma
da za su taimaka musu wajen amfani da ƙasa yadda ya kamata da
rage yashewar ƙasa.
·
Tsarin
Gudanar da Ruwa (Water Management Systems):
o Gini da Gyaran Madatsun Ruwa: Samar da sabbin
madatsun ruwa da kuma gyara tsofaffin don tattara ruwan sama da kuma amfani da
shi a lokacin rani.
o Rijiyoyin Burtsatse: ƙara yawan rijiyoyin
burtsatse (boreholes) don samar da ruwan sha mai tsafta.
o Kare Koguna da Tabkuna: ɗaukar matakai don kare
albarkatun ruwa daga gurbatawa da bushewa.
·
Inganta
Tsarin Gargadi na Farko (Early Warning Systems): Samar da tsarin gargadi na farko don
sanar da al'umma game da fari ko ambaliya da ke tafe, don su iya daukar matakan
kariya.
·
Ƙarfafa Gine-gine Masu Ɗorewa: Ginin gidaje da
ababen more rayuwa da za su iya jure wa tsananin yanayi kamar ambaliya ko iska
mai karfi.
7.0 Matakan Ragewa (Mitigation)
Waɗannan matakai ne da
ake ɗauka don rage fitar da
gasassu masu kama zafi zuwa sararin samaniya:
·
Sake
Dasa Itatuwa (Afforestation/Reforestation): Samar da shirin dasa itatuwa mai
inganci a fa]in yankin ƙasar Hausawa don shawo kan kwararowar hamada da kuma
shan carbon dioɗide.
·
Amfani
da Makamashi Mai Sabuntawa (Renewable Energy): Faɗaɗa amfani da makamashi
mai sabuntawa kamar hasken rana (solar energy) da iska (wind energy) don rage
dogaro ga burbushin mai.
·
Wayar
da Kan Al'umma: Ilmantar
da al'umma kan illolin sare itatuwa, konewar daji, da kuma yadda za su iya kare
muhallinsu.
·
Tsarin
Sarrafa Sharar Gida: Inganta tsarin sarrafa sharar gida don rage
fitar da methane daga wuraren zubar da shara.
8.0 Matsayin Gwamnati da Ƙungiyoyi Masu Zaman
Kansu (NGOs) Kan Sauyin Yanayi
Gwamnatoci a matakai daban-daban (tarayya da jiha da
kuma ƙananan hukumomi) suna da muhimmiyar rawa wajen ]aukar
matakan daidaitawa da ragewa. Suna bukatar samar da manufofi da dokoki da kuma
ku]a]en da za su tallafa wa waɗannan ayyuka. ƙungiyoyi masu zaman
kansu na ƙasa da na duniya ma suna bayar da gudunmawa mai yawa
ta hanyar ayyukan wayar da kai, samar da taimako da kuma aiwatar da ayyukan
daidaitawa a matakin al'umma. Misali, Saɓe the Children da Mercy Corps suna
aiki a yankin Arewa maso Gabas wajen taimaka wa al'ummomin da canjin yanayi ya
shafa (Saɓe the Children, 2023).
8.1 Ƙalubale da Shawarwari
Duk da ƙoƙarin da ake yi,
akwai ƙalubale da dama wajen magance matsalar canjin yanayi
a ƙasar Hausa.
8.1.1 Ƙalubale
·
Rashin
Isassun Kuɗi da Fasahar zamani: ƙasashen masu tasowa,
ciki har da Najeriya da Nijar, suna fama da karancin kuɗi da kuma fasahohin zamani da ake buƙata don aiwatar da
ayyukan daidaitawa da ragewa.
·
Karancin
Wayar da Kai: Yawancin
al'umma, musamman a yankunan karkara, ba su da cikakkiyar masaniya kan illolin
canjin yanayi da kuma hanyoyin da za su kare kansu.
·
Matsalar
Tsaro: Rikicin
Boko Haram da sauran 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma
yana hana ayyukan ci gaba da shiga yankunan da abin ya shafa, wanda ke kawo
cikas ga aiwatar da shirye-shiryen magance canjin yanayi.
·
Rashin
Haɗin Kai: Akwai rashin haɗin kai tsakanin matakan
gwamnati daban-daban da kuma tsakanin sassan gwamnati, wanda ke rage ingancin
aiwatar da manufofi.
·
Karancin
Bincike da Kididdiga: Akwai karancin bincike na gida da kuma
takamaiman ƙididdiga kan tasirin canjin yanayi a wasu yankuna,
wanda ke sa tsara manufofi yake zama mai wahala.
8.1.2 Shawarwari
Don fuskantar waɗannan ƙalubale da kuma rage
illolin canjin yanayi a yankin Hausawa, ana ba da shawarwari masu zuwa:
1. Ƙara Saka Hannun Jari: Gwamnatoci su kara
saka hannun jari mai yawa a ayyukan daidaitawa da ragewa, kuma su nemi tallafi
daga kungiyoyin ƙasa da ƙasa.
2. Ƙarfafa Bincike da
Fasahar Zamani: A
tallafa wa bincike kan irin noman da ya dace da yanayin canjin yanayi da kuma
sabbin fasahohin sarrafa ruwa da makamashi mai sabuntawa.
3. Ƙara Wayar da Kan
Al'umma: A
samar da shirye-shiryen wayar da kai ta rediyo da talabijin da kuma gidajen
rediyo na al'umma don ilmantar da jama'a kan canjin yanayi. A yi amfani da
hanyoyin gargajiya na sadarwa.
4. Haɗin Gwiwa: A karfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci da al'ummomi da kungiyoyi
masu zaman kansu da kuma hukumomin }asa da }asa domin samun ingantacciyar amsa
ga matsalar.
5. Daidaita Tsaro: Inganta tsaro a
yankunan da abin ya shafa domin ba da damar aiwatar da ayyukan ci gaba da
taimako.
6. Manufofin Dogon Lokaci: A samar da
manufofin canjin yanayi na dogon lokaci waɗanda za su ɗore kuma ba za su canza ba duk lokacin da gwamnati ta
sauya.
7. Yana da muhimmanci ga gwamnatoci da al'ummomi da
kungiyoyi masu zaman kansu da kuma ƙasashen duniya su haɗa kai wajen tunkarar
wannan matsala. Dole ne a ɗauki mataki na gaggawa
da kuma na ɗorewa don kare
albarkatun ƙasa da inganta rayuwar al'umma, da kuma tabbatar da
makoma mai kyau ga al'ummar Hausawa masu zuwa. Fuskantar canjin yanayi ba wai
zaɓi ba ne, wajibi ne don
tsira da ci gaba
9.0 Kammalawa
Wannan takarda ta tabbatar da cewa Sauyin Yanayi ba labari bane,
a’a, gaskiya ce mai barazana ga rayuwar al’ummar Hausawa.
·
An gano cewa alamomin
sauyin yanayi kamar ƙaruwar
zafin rana da rashin tabbas na damina sun bayyana a fili a
yankin Sahel, kamar yadda rahotannin duniya suka tabbatar.
·
Illolin da suka biyo baya
sun haɗa da karancin abinci, talauci, da kuma
tsanantar rikicin manoma da makiyaya saboda matsin lamba
kan albarkatun ƙasa.
·
Binciken ya nuna cewa Ra'in
Dangantakar Al'ada da Muhalli (Cultural Ecology Theory) ya dace sosai.
An ga yadda barazanar yanayi ta tilastawa al'ummar Hausawa canza tsarin
rayuwarsu (Culture Core) ta hanyar yin Cirani da kuma sauya
hanyoyin noma a matsayin dabarun daidaitawa.
·
A takaice, ana iya cewa
al'adun Hausawa na ci gaba da daidaita kansu da sabon yanayin muhalli domin
dorewar rayuwa.
Manazarta
Abaje, I. B., Sawa, B. A., & Ati, O. F. (2014).
Climate ɓariability and change,
impacts and adaptation strategies in Dutsin-Ma Local Goɓernment Area of Katsina State, Nigeria. Journal
of Geography and Geology, 6(2), 103–112.
Alhassan, H. (1982) Zaman Hausawa 2.
Islamic Publication Bureau, Lagos.
Auta, A. L (2006) “Tattalin Arzikin Al’umma: Nazairin
Sana’o’i da Kasuwancin Hausawa” A cikin Algaita, Kano : Jami’ar Bayero
ACLED (Armed Conflict Location & Eɓent Data Project).
(2024). Real-time data on political ɓiolence and protests. Wurin da za a
nemo: https://acleddata.com/.
Funtuwa, S. A. (2006) “Ƙananan Sana’o’in Hausawa
Da Yadda Ake Aiwatar Da Su: Nazari Na Musamman a Kan Sana’ar Ƙwadago Da Ate, da Dako,
da Yankan Farce, da Gyartai”. Kundin Digiri Na Ɗaya. Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto.
FGN (Federal Goɓernment of Nigeria). (2020). National
adaptation plan framework. Federal Ministry of Enɓironment
Intergoɓernmental Panel on Climate Change (IPCC).
(2023). Synthesis Report of the Siɗth Assessment Report (AR6). Wurin da za a
nemo: https://www.ipcc.ch/report/ar6/syr/.
Mortimore, M. (1989). Adapting to drought:
Farmers, famines, and desertification in West Africa. Cambridge Uniɓersity Press.
Mortimore, M. (2010). Adapting to drought and the
challenge of deɓelopment. International
Deɓelopment Planning Reɓiew, 32(1),
1–19.
National Population Commission (NPC). (2017). Nigeria
Demographic and Health Surɓey 2018 (NDHS 2018). [Wurin da za a nemo: Ka duba
rahotannin NDHS daga hukumar NPC ta Najeriya, ko kuma daga USAID/DHS Program].
(Ana iya samun bayanai kan yanayin rayuwa da muhalli a ciki).
Saɓe the Children.
(2023). Rahotanni kan ayyukan agaji da ci gaba a Arewa maso Gabas,
Najeriya. [Wurin da za a nemo: https://www.saɓethechildren.org/.
United Nations Deɓelopment Programme (UNDP). (2021). Climate
Change and Conflict in the Sahel: A Reɓiew. Wurin da za a nemo: https://www.undp.org/.
United Nations Enɓironment Programme (UNEP). (2021). The
shrinking Lake Chad: A report by UNEP. Wurin da za a nemo: https://www.unep.org/.
Zabi, M. A (2014) Matsalolin Amfani Da Maganin Kwari A
Kayan Gona littafi Unpublished
Zabi, (2017). Tasirin Da Barazanar Zamani A Kan
Sana’ar Noma In the Beam: journal of Arts and Science. Vol 9 Umar Ali
Shinkafi Polytechnic, Sokoto
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.