Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwatancin Salo A Littattafan Wasan Marafa Da Kishi Ko Bata

Citation: Muhammad ADAMU & Ibrahim Muhammed OGAH (2021). Kwatancin Salo A Littattafan Wasan Marafa Da Kishi Ko Ɓata. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 9, Issue 1. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

KWATANCIN SALO A LITTATTAFAN WASAN MARAFA DA KISHI KO ƁATA

Na

Muhammad ADAMU

Ibrahim Muhammed OGAH

1.0 Gabatarwa

Salo wani babban batu ne da masana suke tattaunawa a kai mai daɗaɗɗen tarihi da ya bazu a kan adabi wanda ake nazarinsa cikin harka ta ilmi. Salo kamar yadda Ɗangambo (2007) ya ce, “Salo harshen wani mutum ne; salo ya shafi saɓa ko kauce wa ƙa’ida; salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci, da sauransu”. Wannan aiki zai mai da hankali ne a kan rubutaccen wasan kwaikwayo na littafin Wasan Marafa da Abubakar Tinau ya rubuta da littafin wasan kwaikwayo na Kishi ko Ɓata na Zara’u Ibrahim Waya. Cikin takardar an kwatanta salon da suka yi amfani da shi a cikin wasan, domin wasanni ne masu armashi da faɗakarwa kan yanayin rayuwa a cikin al’umma, musamman Hausawa, domin littattafan sun karkata ne kan rayuwar Hausawa, ta ɓangaren sunayensu da kuma ɗabi’unsu. Za a fito da ma’anonin salo da wasan kwaikwayo, sannan a biyo baya da salasalan da ke cikin wasannin biyu.

Cikin wannan aikin, an bi wasu hanyoyi wajen ganin an samu bayanai da za su taimaka kan gina aikin.

Da farko an karanci littattafan nan biyu (Wasan Marafa da Kishi ko Ɓata) don a fito da salon da ke cikin wasanni. An yi haka kuma an samu wasu salasalan a cikin wasannin biyu. Haka kuma an yi karance-karance na littattafan wasan kwaikwayo daga masana daban-daban na cikin gida da wajen Nijeriya, domin duba yadda ake nazarin wasan kwaikwayo, musamman ma salo. Sannan an ƙara da duba kundayen bincike da muƙalu da aka rubuta na manazarta daban-daban a ɓangaren wasan kwaikwayo. An ɗora aikin ne a kan aikin da ’Yar’aduwa (2008) ya yi.

1.1 Wasan Kwaikwayo

Wasan kwaikwayo ya taɓo dukkan harkokin rayuwar ɗan’Adam ta yau da kullum, domin yana bayyana wa mai kallo ko sauraro ko karatu hanyoyin rayuwar jama’a ta fuskar sana’o’insu da yanayin zamansu da al’adunsu.

Wasan kwaikwayo kamar yadda aka sani kalmomi ne guda biyu da aka yi amfani da su wajen gina kalmar, wato wasa da kwaikwayo. Wasa na nufin wani abu wanda yake ba da gaske ba, ko wani aiki ne na motsa jiki don nishaɗantarwa, ko a yi abu don ilmantarwa ko faɗakarwa cikin raha da nishaɗi. Kwaikwayo kuwa na nufin a yi wani abu da wani ya yi, wato koyi. Idan aka haɗa kalmomin nan biyu wasa da kwaikwayo, shi ne koyi da wani abu cikin raha ko nishaɗi, wato a kwaikwayi wata ɗabi’a ta rayuwa domin a nuna wani darasi.

Saboda haka, masana da dama na adabin Hausa da suka yi nazari a kan wasan kwaikwayo sun sha tattaunawa dangane da ma’anar wasan kwaikwayo a cikin littattafansu da kuma takardu da suka gabatar a tarukan ƙara wa juna ilmi. Kamar su: Ɗangambo (1984/2008) da ’Yar’aduwa (2007/2008) da Yahaya da wasu (1992) da Umar (1987) da sauransu suka bayyana.

Ɗangambo (1984/2008) ya kawo ma’anar wasan kwaikwayo dalla-dalla domin fahimtar ma’anar sosai kamar haka:

Wasa na nufin:

i.   Wani abu wanda ba da gaske ake yi ba.

ii.   Wani abu wanda ba da yaƙini ba.

iii.   Abun da ba a ɗauke shi da muhimmanci ko da zafi ba.

iv.   Raha, nishaɗi, tsokana.

v.   Motsa gaɓoɓin jiki don samun walwala.

Kwaikwayo na nufin:

i.   Koyi da wani abu.

ii.   Yin abin da ka ga wani ya yi (koyi).

Saboda haka, Ɗangambo (2008, sh. 25) ya ce, “Wasan kwaikwayo kamar yadda sunan ya nuna, wasa ne da ake gina shi kan kwaikwayon wani labari, ko wata matsala ta rayuwa da ake son nusarwa ga jama’a. Akan aiwatar da labarin, matsalar da sauransu cikin siffar ‘yaƙini’ wato zahiri”.

Umar (1987, sh. 38) yana cewa, “Wasan kwaikwayo kamance ne na wasu halaye ko yanayin rayuwa da akan shirya yinsa akasari cikin raha. Wannan kamance na iya zama na wasu zayyanannun halaye, wato abubuwa da aka san sun faru a rayuwa ta haƙiƙa, misali, yaƙi ko wani abin da ya gudana a tarihi.

Yahaya da wasu (1992, sh. 2) sun ce, “Wasan kwaikwayo kamance ne na halaye ko yanayin rayuwa da mutane masu hikima suke shirya gudanar da shi don jama’a su gani da idonsu, su samu nishaɗi da jin daɗi. Ana shirya shi ne yadda za a kamanta rayuwa ta gaske ta hanyar fito da al’adun mutanen da ƙudurin sadar da wani saƙo gare su”. Ya sake ba da ma’anar wasan kwaikwayo da cewa, “Karantarwa ce ga jama’a a kan muhimman abubuwan rayuwarsu ta yau da kullum domin su fahimce su, su kuma rungume su, su yi amfani da su domin kyautata rayuwarsu. Da kuma yin nuni ga munanan abubuwan rayuwa, domin su fahimce su, kuma su ƙyamace su, su guje musu da yadda rayuwarsu za ta yi daɗi da armashi. An aiwatar da shi ta hanyar annashuwa da nishaɗantarwa”.

’Yar’aduwa (2008, sh. 2) ya ƙara da cewa, “Wasan kwaikwayo hanya ce ta baje kolin halayen jama’a da yanayin rayuwarsu ta cikin nishaɗi da raha domin su gani, su kuma zaɓi nagari su yi amfani da su sannan su yi watsi da munana domin rayuwarsu ta yi kyau su samu kwanciyar hankali”.

Daga ƙarshe idan aka lura, ma’anar wasan kwaikwayo daga masana daban-daban, suna nuna cewa, nuna wasu halaye masu kyau da munana da ke koyar da darasi ga jama’a wajen ganin yadda ya kamata su gudanar da rayuwasu ta zahiri. Wasa ne da ba zahiri ba, sai dai domin a fito da yanayin rayuwa a fili ga mai sauraro ko kallo ko kuma karantawa. Saboda haka, wasan kwaikwayo abu ne mai muhimmanci ga rayuwar jama’a kowace iri.

1.2 Salo

Kalmar salo kalma ce da aka saba jin sunanta a fannin nazarin adabi da ma harshe a Hausa. An fara amfani ko sanin kalmar ce sanadiyar shigowar Turawa ƙasar Hausa a kan nuna abubuwa da suka danganci Hausawa a tatsuniyoyinsu, da dai sauransu a ɓangaren adabi. Saboda haka, salo ya zama gaggarumin batu ne a nazarin Hausa, wanda yake nuni da yadda ake nazarin waƙa da ƙagaggun labarai da wasan kwaikwayo, ganin irin tsarin da aka bi wajen tsara waɗannan nau’o’in adabin Hausa.

Wannan ya sa masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan kalmar salo, domin kowanne cikinsu ya kalli kalmar ce dangane da yadda ya fahimce ta. Game da ma’anar salo, ga yadda wasu masana da aka duba suka ba da nasu bahasi kamar haka:

Gusau (2003, sh. 10) cewa ya yi, “Salo wata hanya ce da ake bi a nuna gwaninta a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa da zaɓar abubuwan da suka dace da abin da yake son bayyanawa”. Gusau (2003, sh. 10) ya sake cewa, “Salo wata dabara ce wadda ake amfani da ita wajen ƙawata furuci ko rubutu wato da ake yi wa harshen da ake amfani da shi ado ko kwalliya da nufin a isar da saƙo cikin furucin da rubutun”.

Ɗangambo (2007, sh. 37) yana cewa salo shi ne, “Bisa jimla, muna iya cewa salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo”.

Mukhtar (2004, sh. 2) ya duba salo ta fuskoki da dama kamar haka;

a.   Salo harshen wani mutum ne.

b.   Salo wani tsari ne a cikin rubutu.

c.   Salo zaɓi ne a cikin rubutu.

d.   Salo shi ne yake bayyana ma’ana.

e.   Salo shi ne saɓƙa’ida.

f.   Tsarin amfani da harshe ne na marubutan zamani da ake ciki.

Idan aka bi yadda waɗannan masana suka ba da ma’anar salo, za a ga bayani suke a kan yadda ake isar da saƙo ta amfani da wasu dabarun jawo hankalin mai sauraro ko kuma mai karatu da kallo. Wato dabara ko hanya ce da akan sa hankali ya karkato har ya fahimci abin da ake nufi. Saboda haka, salo yana tasiri matuƙa wajen rubutu a ɓangaren adabin Hausa musamman wasan kwaikwayo.

1.3 Salo a Littattafan Wasan Marafa da Kishi Ko Ɓata

Kamar yadda masana suka ba da, salo sun kasa shi kashi biyu, akwai maganganun hikima da sarrafa harshe. Idan aka ce maganganun hikima, wato sun danganci kalmomi irin su salon magana, karin magana, habaici, zambo, kirari, take da sauransu. Sannan a ɓangaren sarrafa harshe ya danganci amfani da harshe wajen isar da saƙo kamar su zaɓar kalmomi, ginin jimla, baƙin kalmomi, da sauransu, domin samun sauƙin fahimta. Haɗa kuma da adon harshe su ne; siffantawa, dabbantarwa, kamantawa, mutantarwa da dai sauransu. ’Yar’aduwa (2007/2008)

1.3.1 Karin Magana

Wannan wasu ’yan guntayen maganganu ne waɗanda idan aka faɗe su suna ɗauke da bayani ko ma’ana mai tsawo. Ko kuma a ce, shi ne wata ’yar ƙaramar jimla wadda ma’anar kalmomin da suke cikinta ba ta dace da ma’anar maƙasudin karin maganar ba. Ana kuma a iya cewa, karin magana wasu gajerun jimloli ne wanda ba kasafai ma’anar kalmomin ta zahiri kan nuna abin da suke nufi ba. Wannan yana nufin a karin magana akan sakaya ma’anar abin da ake nufi (Ɗanhausa, 2012).

Saboda haka, cikin waɗannan littatttafan wasan kwaikwayon biyu an fito da karin magana kamar yadda marubutan suka sako su domin jawo hankalin masu karatu. Ga misalansa daga ciki kamar haka;

A littafin Wasan Marafa ga abin da ya fito:

Kumatu: Kada mu zama haihuwar guzuma, ɗa kwance uwa kwance. (shafi 4)

Kumatu: Ai na Allah ba ya ƙarewa. (shafi 5)

Sai kuma littafin Kishi ko Ɓata, ta fito da karin magana kamar haka:

Aminu: To ka yi sauri in ba haka ba, a yi maka sakiyar da ba ruwa. (shafi 10)

Aminu: Shi ke nan, faɗuwa ta zo daidai da zama. (shafi 10)

Hajara: Ai ina ga ta yi na’am da shi amma gwanda a tambaye ta, waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. (shafi 13)

’Yarƙarama: Faɗuwa ta zo daidai da zama. Ai ko wannan lokaci shi ne daidai lokacin zuwa. Tun da yanzu ba ta daɗe ba kin san an ce, da zafi-zafi akan bugi ƙarfe. (shafi 18)

Hajiya Furaira: Allah ya raba nagari da muguKomai ya yi zafi maganinsa Allah. (shafi 41)

Hajiya Furaira: Hausawa na cewa; mai haƙuri shi kan dafa dutse ya sha romansa. (shafi 53)

Hajara: Allah mun gode maka, ‘Hausawa na cewa, na ɗaka bai san ana rana ba’. (shafi 57)

Kamar yadda bayanai suka gabata, waɗannan su ne karin maganganu da aka suke cikin littattafan biyu. Sun yi amfani da su wajen ƙawata wasan domin nishaɗantarwa ga masu karatu.

1.3.2 Adon Magana

Adon magana ma na ɗaya daga cikin dabarun da marubuta ke amfani da shi a cikin labari ko wasan kwaikwayo. Domin magana ce da ake yinta cikin hikima ɗauke da ma’ana mai tsawo.

Kamar yadda aka bayyana wannan dabara ce ta amfani da wasu kalmomi domin ƙawata zance. Wato lafazi ne na hikima wanda yake ɗauke da ma’ana ta ɓoye ba kamar sauran kalmomi ba. Ba za ka san ma’anar a zahiri ba, sai ka nemi ka sani ko kuma ka sani. Za a iya cewa kalmomi ne da ake yi wa ado da abubuwan al’ada na zahiri ta yadda idan aka yi amfani da su, sai waɗanda suka san al’adar ne za su gane ko fahimci abin da ake nufi (Umar, 1987).

Adon magana kan zama kalmomi ne da suke cuɗanya da juna ya haɗu ya zama suna da suna ko siffa da suna. Adon magana akasari ba sa wuce kalmomi biyu zuwa huɗu, da sukan yi amfani da ita wajen ƙarawa saƙonsu zaƙi da armashi. Laccar digiri na ɗaya LLH 262 (2002).

Waɗannan marubuta sun yi amfani da wannan hikima ta adon magana domin ƙarawa saƙonsu armashi ga mai karatu a cikin littattafan nasu. Ga abin da suke cewa kamar haka:

A littafin Wasan Marafa marubucin ya kawo wannan hikima inda ya ce,

Wajen Shela: Gidansu kuma kamar a kwanta ƙasa ba tabarma, don tsafta. (shafi 26)

Citumu: Baba, ai ya kamata mu kore wa maƙwabcin nan namu zomo.

  (shafi 28)

Sai kuma a littafin Kishi ko Bata, marubuciyar ta fito da adon magana kamar haka:

Aminu: Goro, yau mutumin ya na ga bakinka har ƙeya ne. (shafi 15)

Kulu: Lallai ba ki san kishi ba. Idan kika kuskura kika ba ta wuri, to wallahi kashinki ya bushe. (shafi 17)

’Yar Ƙarama: Ki bi a sannu kin ga abin da ya kamata mu yi shi ne ki zo in raka ki wajen wani Malami aikinsa yankan wuƙa ne don a yi miki magani. (shafi 18)

Malam tsirgwai: Kun zo inda za a share muku hawaye. (shafi 18)

Tsigai: Kuma da alama cikinta ya fara tsufa. Ni kam na lashi takobi sai dai a haife shi a wani wuri ko a baƙonci lahira. Shafi 49)

Tsigai: To, ni wai me yake faruwa! Ba komi sai na ga bayanta! (shafi 50)

Tsigai: (Tana ta sharholiyarta ba ta san an ga Tarasulu ba). Ai ni ina cikin gaɗa da farin ciki! (shafi 61)

Ɗanladi: (Ya shiga, ya kalli yaron sai ya ga kamar an tsaga kara da shi.

Adon magana ya yi tasiri a cikin wasannin nan biyu, domin marubutan sun ƙawata ciki sosai da shi. Inda aka fito da su sukan sa a yi tunani wajen sanin ma’anar da suke ɗauke da ita, kamar yadda aka ga abin da ma’anar adon magana yake nufi.

1.3.3 Kirari

Kirari ma ba a bar shi a baya ba wajen fitar da dabarun salo a cikin wasan kwaikwayo kamar yadda masana suka bayyana. Kirari abu ne mai kambama ko zuga mutum wajen aikata wani abu, wani lokaci mai kyau, wani lokacin kuwa mummuna.

Kirari dangane da sunansa, a iya cewa, wasu zantuka ne na tsumarwa wanda mutum yakan yi wa kansa ko wani. Ko kuma kirari tsararriyar magana ce da ake yi da murya mai ƙarfi cikin hikima musamman don a kambama ko koɗa wani mutum, ko kushe wani ko wasu, ko wata dabba ko wani gari ko wasu masu wata sana’a. Haka kuma a iya cewa, wata tsararriyar magana ce wadda akan yi da baki domin kambama ko kururuta wata halitta ko wani abu, da zai iya kasancewa za a iya yi wa wani kuma zai iya yi wa kansa. Wato kalamai ne na kumbura kan mutum, domin wasa shi ake yi (Gusau, 2002).

Kirari abu ne da akan iya yi wa abubuwa masu rai da waɗanda ba su da rai, kamar yadda ma’anarsa ya nuna. Wannan ya sa ana amfani da shi wajen nishaɗantarwa a cikin littattafan labari da wasan kwaikwayo da waƙa ganin an jawo hankalin mai sauraro ko karatu ko kallo. Cikin waɗannan wasannin biyun, marubutan sun sako wannan dabara ta jawo hankalin mutane, a ga sun nishaɗantu da abin da aka rubuta. An fito da wamnan batu a cikin littattafan kamar haka:

A littafin Wasan Marafa, marubucin ya yi amfani da kirari, inda ya nuna hakan a wurare irin su:

Boka: (Ya buga tambarinsa). A sha da magani ga ɗan-mai-ganye! A sha magani ga jikan Ladi! Maganin ƙwarai sai gado! Sai ni goga jikan Ladi! (shafi 5)

Boka: Yanzu-yanzun nan sai in warkar da kai. Ni ne ɗan-mai-ganye, jikan Ladi! (shafi 6)

Boka: Ha, wani ya ɗauki kurkunu ya faɗi. Sai ni jikan Ladi! A sha da magani a yi wanka da magani na jikan Ladi! (shafi 8)

Yabani: Sai ni gatan baba da inna!

Maroƙa: Marafa ɗan bahago! Marafa amanar likta! Na dubagari na malamin makaranta! Fartanya ta ba ka gaskiya, ka ba ta. Kada ka sake da duniya, ɗan Muhamman da Muhamman jikan Muhamman da Abubukar da Ibrahim! Na Fatse, gatan Kumatu, Magajin Citumu! Rago duniya ta bashe shi, bai daɗa komai ba! Ka sa mana riga da wando da taguwa da hula da rawani da takalma. Ka haushe mu bisa doki ɗan dubu na ƙawa! Abar shi, ka yi mai gida ka huta! (shafi 29)

Sannan a wasan Kishi ko Bata, a ɗaya ɓangaren, ita ma marubuciyar ta kawo kirari littafin nata kamar haka:

Matar Iro: A’a ai tsofaffi sai goro fari ɗan goma. (shafi 6)

1.3.4 Zagi

Zagi shi ma wani nau’i ne na maganganun azanci, wanda ake aiwatar da shi a fili ba kamar habaici da zambo ba. Wato akan yi ma mai shi ne kai tsaye ba a fakaice ba, domin za a ji kalmomin da aka yi amfani da su ba sa ɓoye komai da wanda aka yi wa zagin.

Kamar yadda sunansa ya nuna, zagi wata dabara ce ta amfani da wasu kalmomi wajen ƙasƙanta mutum, domin nuna gazawa kan wani abu ko ɓata wa wani rai ya sa ya aikata hakan. Laccar digiri na ɗaya LLH 262 (2002).

Akan yi amfani da zagi a zaman dabara ta fitar da salo a cikin littattafan labari da wasan kwaikwayo.

A nan ma marubutan waɗannan littattafai, sun yi amfani da wannan dabara ta fitar da salo na zagi. Alal misali,

A littafin Wasan Marafa, Malam Tunau ya yi amfani da zagi kamar haka:

Marafa: Aikin banza! Tashi ka ba mutane wuri, mutumin banza! Mutumin wofi, maƙaryaci. Tafi ka ba ni wuri! Maƙaryatan banza, ku shiga gari kuna cin kuɗin mutane a kan banza. Ashe ma ba shi da maganin kome, yana ta ƙarairayi. (shafi 7)

Wani Mutumin Gari: Kai, wane irin mahaukacin tsoho ne wannan? Tafi ka ba mu wuri! (shafi 8)

Sai kuma a littafin Kishi ko Ɓata, inda ita ma marubuciyar ta yi amfani da zagi a wajen gina salon labarin wasan nata, kamar haka:

Kulu: Bar ni da wancan tunkiyar ai sai na yi maganinta kin san na riga na shiga gaban maigidan sai yadda na yi da shi. (shafi 31)

Matar Manomi: Ni fa ban yarda ka ɗauko min karuwa ka kawo min gida ba. Ai sai ta fita ta ba ni wuri. (shafi 32)

To, waɗannan ma su ne zagin da aka fito da su daga cikin littattafan nan na Wasan Marafa da Kishi ko Ɓata, kamar yadda aka gani.

1.3.5 Baƙar Magana

Masana adabi sun ba da ma’anar baƙar magana da cewa, “Baƙar magana wata magana ce ta ɓacin rai da mutum yakan faɗa a lokacin da wani ya gaya masa magana da ta sosa masa rai, don ya rama, kuma ya nuna cewa ransa ya ɓaci da wannan maganar da aka gaya masa (Galadanci da wasu, 1990).

Baƙar magana wato zance ce wadda take sosa zuciya. Tana sa ɓacin rai da mutum zai nuna damuwarsa kan wannan maganar da aka faɗa masa. Wanda shi ma ya mayar da martani ganin bai ji daɗin abin da aka gaya masa ba. Baƙar magana an kasa ta zuwa na ɓacin zuciya da wanda ake yi cikin raha.

Saboda haka, a dangane da baƙar magana masana sun bayyana ta daga cikin dabarun fitar da salo a cikin littattafan wasan kwaikwayo da na ƙagaggun labarai. Marubutan littatattafan da aka ɗauko domin wannan aiki, sun nuna baƙar magana a cikin wasan kwaikwayo da suka rubuta. Misali,

A littafin Wasan Marafa, marubucin ya yi amfani da baƙar magana a cikin labarin don ganin ya gina salon labarin wasan da ya rubuta. Ga abin da ya kawo kamar haka:

Boka: A’a tsaya tsoho, ai ba ni na sa maka kurkunu ba. Bari in tsince kayana da ka watsar. (shafi 7)

Marafa: A’aha, yau Allah ya gwada mini tsageran yaro, wofi. Yanzu tsofai-tsofai da ni, don ba ni na haife ka ba, za ka ce mini mahaukaci? Ka ga lalataccen yaro! (shafi 8)

  Idan muka duba littafin Kishi ko Ɓata a ɗaya hannun, za a ga cewa ita ma marubuciyar ta yi amfani da baƙar magana a wajen gina salon labarin wasan nata. Misali,

Kulu: Yauwa, amma na ga alama ba ki da hankali, yanzu duk irin shirin da muka yi shi ne za ki sakar wa yarinyar nan fuska har Bebi ma take yi wa wanka! (shafi 17)

’Yar Ƙarama: Lallai! Wankan Bebi ai wannan kinibibi ne da munafinci. So take ta shiga jikinki sai ta ƙwace miki ’ya’ya sannan ta kore ki. (shafi 17)

  Waɗannan misalai da aka fito da su, su ne dangane da baƙar magana da aka tsamo daga cikin littattafan da aka yi nazarinsu.

1.4 Sarrafa Harshe

Idan aka yi maganar sarrafa harshe, dole ne a waiwaici ababan da marubuta waɗannan littattafai suka wanzar ciki kan harshe. Salon sarrafa harshe, shi ne hanyoyin da marubuci ya bi wajen sadar da saƙonsa ta yin amfani da harshe. Abin da ake nufi a nan shi ne, sarrafa harshe ko a ce salon sarrafa harshe, yana nuna gwanintar wanda ya yi amfani da shi harshen ko a ce walwalar harshen yadda yake kasancewa wajen ganin ya ƙayatar a cikin rubutun da aka yi.

A wannan fage, marubuta na iya yin amfani da harshe mai sauƙi wajen rubutunsa yadda kowane mai karatu zai iya fahimta cikin sauƙi. Domin shi harshe yana bunƙasa, sannan wajen rubutu ana amfani da shi matuƙa ganin irin rawar da yake takawa a ɓangaren ƙawata wani saƙon da ake son isarwa. Wannan na iya kasancewa ta zaɓan kalmomi masu sauƙin gamsarwa da gina jimloli masu sauƙi waɗanda za su fito da ma’ana cikin sauƙi (Gusau, 2003).

Saboda haka, harshe na fito da ɓangaren salo da masana suka yi ittifaƙi da cewa ana samun abubuwa kamar yadda suka zo cikin wannan sakin layi da ke sama da wannan. Bugu da ƙari, akwai ma irin su: Aron kalmomi da tsarin jimla da tsofaffin kalmomi da karin harshe da ƙirar kalma da dangantakar kalmomi da sababbin kalmomi da sauransu. Ganin haka, za a dubi yadda salon sarrafa harshe da akwai cikin littattafan nan da aka zaɓo don wannan aiki.

1.4.1 Zaɓen Kalmomi

A wannan fage ana magana ne a kan irin kalmomi da aka yi amfani da su domin kyautata fahimtar mai karatu. Saboda haka, waɗannan marubuta sun yi amfani da kalmomi masu sauƙin fahimta a cikin rubutunsu. Wannan ya sa littattafan nasu da akwai sauƙin karantawa da kuma fahimta. Sannan sun tsara kalmomi wasanni a cikin jimloli masu sauƙi, ƙananan jimloli marasa wahalar ganewa cikin ƙa’idojin rubutu mai sauƙi. Jimlolin da suka yi amfani da su miƙaƙƙu ne babu sarƙaƙiya ciki. Misali,

A cikin littafin Wasan Marafa, Abubakar Tunau ya tsara jimlolin wasan cikin hanya mai sauƙin karantawa. Alal misali:

Kumatu: Marafa? Halan ba za ku tafi gona ba yau? Ga shi har hantsi ya taka? (shafi 1)

Marafa: Kun sani dai wannan tafiya ba na son ta. Sai don ta zama min tilas, sai in tafi haka nan. Ina gorana da sandana, miƙo mini suna nan. Shi ke nan, sai Allah ya dawo da ni lafiya. (shafi 1)

Haka nan cikin littafin Kishi ko Ɓata, Zahra’u Ibrahim Waya ta sarrafa kalmomin da babu wahalar karantawa, ta ba wa kowane ɗan wasa abin da zai ce cikin sauƙi. Misali,

Alhaji Mahmud: Barka kadai! To, karɓi wannan, (Ya ɗauko kuɗi ya miƙa mata). Maza je ki direba na jiran ki ya kai ki. A kula kuma a mai da hankali ga karatu ban da wasa. (shafi 1)

Kulu: Habawa! Yanzu na san kin ɗauki hanya. Kin san ni da na auri wannan mijin kafin in ɗauko ki daga ƙauye, uwargidata maɗinkiya ce kowa garin nan ya san ta saboda iya ɗinki. Amma da na sakar mata wani ciwon hannu sai da aka yi sallah babba da ƙarama ƙwandala ba ta karɓa ba. To, tun da kin fuskanci inda ya kamata, bari ni in koma gida. (shafi 21)

Idan aka lura za mu ga cewa irin kalmomin da suka zaɓo domin gina jimlolinsu suna dacewa da kuma dangantaka da abin da saƙon ke ƙoƙarin isarwa. Waɗannan misalan sun ba da haske kan yadda marubutan suka baje kolinsu wajen amfani da kalmomin da suka dace na gina jimlolin wasan da suka rubuta.

1.4.2 Baƙin Kalmomi

Baƙin kalmomi ko kuma a ce kalmomin aro, su ne kalmomi waɗanda ba na harshen da ake magana da shi ba. Domin harshen Hausa ya samu shigar wasu harsuna a cikinsa kai tsaye ko kuma a fakaice. Harshen Larabci da na Ingilishi suna daga cikin harsuna manya da suka yi kaka-gida a cikin harshen Hausa saboda hulɗoɗi da ma’amaloli daban-daban da suka wanzu a tsakani. Bayan waɗannan akwai wasu cikin harsunan gida da suka shiga harshen Hausa da jimawa. Irin waɗanann harsunan sun haɗa da Fulatanci da Barbarci da Yarbanci da Igbo da Azbinanci da Nufanci da sauransu.

A cikin waɗannan wasannin nan biyu, marubutan sun yi amfani da irin kalmomin nan da ba na harshen Hausa ba. Da yake wannan hulɗa ta kasance tsakanin Hausawa da sauran harsunan, yana da wahala a ce an yi rubutu ba a sa su ciki ba. Waɗannan kalmomi suna ƙara ƙayatar da rubutunsu ɗin ne, domin yin haka yana ba da salon rubutun wane da wane. Cikin littattafan, ga abin da aka tsamo na baƙin kalmomi kamar haka.

A cikin littafin Wasan Marafa, marubucin ya yi amfani da kalmomin Larabci da Ingilishi tuƙuru wajen sadarwa da ya kasance tsakanin ’yan wasa. Waɗannaan kalmomi su ne kamar haka:

Larabci

Ingilishi

Maraba

Caji ofis, Spectacles

Alhamdulillah

Yes sa, Dispenser

Allah

Look, Samitary

Salamu alaikum

Kam, Inspector

Subhana

Guinea warm, Dresser

Alaikum salam

Safer, Fandaje

Bismillah

Stethescope, Now, Patient

Sannan a littafi Kishi ko Ɓata, marubuciyar ita ma ta yi amfani da irin waɗannan kalmomi. Abin lura a nata littafin, littafin wasan kwaikwayo ne da ba ta jima da rubuta shi ba, saboda zamani ya yi tasiri a ciki. A nata wasan kalmomin harshen Larabci da Ingilishi da akwai ciki, kamar yadda ta kawo kamar haka:

Larabci

Ingilishi

Assalamu alaikum

Hedimistare

Wa alaikas salam

Sakandare

Allah

Firamare

Marhabin

Homework

Alhadulillah

Test

Addu’a

Firinsifal, Pref

Innalillahi

Falo, Ingilishi

Subhanallahi

Off, Lamba

Saboda haka, masana sun yi magana da cewa, harshen Larabci da na Ingilishi su ne manyan harsuna da suka fi yin tasiri a cikin harshen Hausa. Wannan ya sa idan aka lura da abubuwan da aka fito da su cikin waɗannan littattafai, sun tabbatar da cewa harsunan sun yi fice a harshen Hausa. Marubutan nan ba su fita daga marubutan da suke sa irin waɗannan kalmomi a rubutunsu ba, ganin yadda dukkansu biyu suka yi amfani da waɗannan harsunan wajen ƙawata wasannin da suka yi.

1.4.3 Tsarin Jimla

Masana adabin Hausa sun nuna cewa, a cikin rubutu akan bi wasu dokoki na ganin an tsara wannan rubutu domin bayar da ma’ana cikakkiya. A kowane irin tsarin rubutu, dokokin nahawu suna da fa’ida ganin yadda mai karatu zai fahimci abu, kuma ya ɗora tunaninsa a kai, inda ganin domin an bi ƙa’ida ta ginin jimla ta amfani da suna, da wakilin suna da sauransu da kuma a fito da lokuta daidai yadda ya kamata.

Tsarin jimla ko ginin jimla kamar yadda masana suka ba da, ya shafi yadda marubuta suke tsara jimlolin a cikin rubutunsu. Wanda akan samu jimloli masu tsayi ko dogaye, da kuma gajerun jimloli ko guntaye, wani lokaci a samu jimla matsakaiciya. Haka kuma ana samun wasu nau’o’i na jimloli daban-daban da suka haɗa da jimlar suna ko jimlar aikatau ko jimlar korewa ko jimla mai sauƙi ko jimla mai tsauri ko jimla mai harshen damo da sauransu. (Gusau, 2003)

Saboda haka, cikin wasannin nan da marubuta suka rubuta, sun yi amfani da jimloli dogaye da ma gajeru. Sai dai, sun fi amfani da dogayen jimloli masu ɗauke da kalmomi da yawa, amma jimloli ne masu sauƙi ba tsauri ko kuma sarƙaƙƙiya. Sannan jimloli ne masu ɗauke da yankin suna da aikatau kamar yadda ya kamata jimlar ta kasancewa. Misali,

A cikin littafin Wasan Marafa, ga dai yadda marubucin ya tsara jimlolinsa, cikin tari mai sauƙi da saurin fahimta da daɗin karantawa. Ga wasu jimlolin kamar haka:

Kumatu: haka nan dai za ka lallaɓa ka tafi. Ai na Allah ba ya ƙarewa ba za ka bar mu, mu duka mu mutu ba. ka ga tsumman zanina nan sai ka laga, ga sauran ƙasari nan cikin gora, ka yi guzuri da shi in ya ƙare ka sai da tsumman, ka sai abinci, ko ma ka yi bara. (shafi 5)

Diresa: (Ya ɗauko kayan aiki) Bari in wanke maka kwantar da ranka, tsoho. Nan ba wurin jin tsoro ba ne. yanzo zan sa maka magani mai kyau, mai amfani, in ɗaure maka da bandeji, nan da nan za ka warke wannan mungun ciwo. Ai lalle ka yi dabara da ka yi hanzari ka zo nan asibiti wurin taimakon jama’a. amma kuma kada ka sake barin ciwo ya kusa cin ƙarfinka haka, ka ji? (Yana magana, yana wanke masa ƙurajen kurkunu). To, yanzu sai ka dakata in je in gaya wa malamin na ƙare wanke maka, wataƙila likita ya gaya masa wata magana wadda yake son a shaida maka. (shafi 17)

Sannan a littafin Kishi ko Ɓata ma, ita marubuciyar mafi yawancin jimlolin da ta yi amfani da su dogaye ne. ga abin da Zahra’u ta kawo na waɗannaan jimloli kamar haka:

Hedimastare: (Shugabar makaranta ta tara yara ’yan aji shida ciki har da Tarasulu don ta bayyana musu cewa za su rubuta jarabawar shiga sakandare. Ta yi wa ɗaliban faɗa da su yi ƙwazo don ganin sun ci gaba da makaranta ta gaba. Ta nuna muhimmancin ilmi ƙwarai da gaske don ta ƙarfafa wa ɗaliban guiwa kuma su zage dantse wajen himmar cin jarrabawa). Na tara ku ’yan aji shida don in gaya muku kun kusa fara jarrabawa ta zuwa sakandare. Ina so ku mayar da hankali sosai a karatunku. Ku dage ku sami sakamako mai kyau. (shafi 2).

Kulu: Yauwa, amma na ga alama ba ki da hankali. Yanzu duk irin shirin da muka yi shi ne za ki sakar wa yarinyar nan fuska har Bebi ma take yi wa wanka! Lallai ba ki san kishi ba. Idan kika kuskura kika ba ta wuri, to wallahi kashinki ya bushe. Ki tuna jikar sarki ce kuma gwaggwanta tana auran yayansa, ke ce bare. To, ki yi maza-maza ki san abin da kike ciki. To ni zan tafi shawara ra rage taki, ke za ki zama bora. Sai an jima. (shafi 17)

Waɗannan su ne wasu misalai daga cikin dogayen jimloli da marubutan littattafan Wasan Marafa da Kishi ko Ɓata suka yi amfani da su cikin littattafan nasu.

Kamar yadda a baya aka ce mafi yawanci sun yi amfani da jimloli dogaye, haka ma akwai wanda ba a raba su da amfani da gajerun jimloli ba. Domin a littattafan wasan kwaikwayo, akwai masu amfani da gajerun jimloli mafi yawanci. Saboda haka, marubutan nan sun sako gajerun jimloli a cikin littafin wasan kwaikwayo da suka rubuta. Alal misali,

Abubakar Tinau a cikin littafinsa na wasan Marafa akwai wurin da ya ba wa ’yan wasa suka faɗi gajerun jimloli. Misali,

Marafa: To, madalla. Ai kuwa ina so. (shafi 1)

Citumu: Haka dai ya fi kyau baba. Je ka, ko Allah ya ba ka sa’a. (shafi 3)

Marafa: Ni dai na tuba, malam. (shafi 17)

Yabani: Baba, har da ni? (shafi 21)

Ita ma Zahra’u Ibrahim Waya ta yi amfani da gajerun jimloli a wasu wurare, waɗannan jimloli shi ne kaɗan kamar yadda na ambata a baya. Ga wasu daga cikinsu kamar haka:

Alhaji Mahmud: Tarasulu an shirya zuwa makaranta ne? (shafi 1)

Tsigai: (Ta yi kwana bakwai tana yi wa Tarasulu girki) Barka ka dai, amma wane ƙoƙari ai yi wa kai ne. (shafi 16)

Tarasulu: A huta lafiya. (shafi 16)

Matar Iro: To malam, Allah ya sa mu game. (shafi 51)

Haka waɗannan su ma wasu ne daga cikin jimloli gajeru da aka yi amfani da su a cikin littattafan nan biyu, na Wasan Marafa da Kishi ko Ɓata. Saboda haka, marubutan nan sun yi amfani da sarrafa harshe domin sun gina wasan nasu ya yi armashi. Salon sarrafa harshe, salo ne wanda marubuta kan duba yadda za su fito da salo mai kyau wanda zai samu karɓuwa a cikin rubuce-rubucensu, kamar yadda muka gani a baya na zaɓar kalmomi da baƙin kalmomi da tsarin jimloli da sauransu da ba a rasa ba, domin ƙawata labarin da ke cikin wasan da suka rubuta.

1.5 Kammalawa

Waɗannan littattafai na Wasan Marafa da Kishi ko Ɓata, sun shigo da salo mai armashi na rubutu da kuma tsarin da yake da kyau wanda ya ginu a kan saƙon gargaɗi. Littattafan sun ƙayatar matuƙa gaya, haka kuma marubutan sun yi amfani da tsarin rubutu mai kyau, na bin ƙa’idojin rubutu, da kuma sa karsashi a jikin mai karatu ta ƙara masa ƙaimi da himma ganin yadda wasan zai ƙare.

Saboda haka, idan aka lura da waɗannan littattafai biyu, kwatanci da aka yi ya nuna cewa, wasan kwaikwayo yakan tafi kan kusan salo iri ɗaya. Domin littafin Wasan Marafa abubuwan da aka fito da su ɓangaren salo, ba su nesanta daga na littafin Kishi ko Ɓata ba, ganin kowannensu ya zo ne da jigon gargaɗi ko faɗakarwa kan wasu halaye da ba su dace ba.

Sannan an kawo dukkan salasalai da ake ganin littattafan ke ɗauke da su, kamar dabarun jawo hankalin makaranci na maganganun azanci irin su; karin magana, adon magana, kirari, zagi da sauransu. Baya ga waɗannan, akwai sarrafa harshe na amfani da tsarin nahawu da ya haɗa da; tsarin jimla da zaɓen kalmomi da baƙin kalmomi da sauransu.

  Saboda haka, wannan bincike ya gano cewa, maganganun azanci suna yin tasiri wajen ƙarfafa gwiwar marubuta kan rubuce-rubucen da suke yi kan adabi musamman ma wasan kwaikwayo da aka yi nazarinsa. Domin hakan ya nuna a cikin waɗannan wasannin da aka yi nazarinsu (Wasan Marafa da Kishi Ko Ɓata), ganin sun ƙawata littattafan sosai da sosai suka yi armashi. Fito da su ya taimaka wajen nuna yadda makaranta za su samu annushuwa ko yin wasan a zahiri kan dandamali idan za a kwaikwaya. Haka ma yake kasancewa da sarrafa harshe, wato yana nuna tsarin kalmomi da jimloli da makamantansu wajen sauƙaƙa karatu da fahimtar littattafan cikin sauƙi.

Manazarta

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-raben adabin Hausa da muhimmancinsa ga rayuwar  Hausawa. Triumph Publishing Company.

Ɗangambo, A. (2008). Rabe-raben adabin Hausa (Sabon Tsari). K.d.g Publishers.

Ɗanhausa, A. M. (2012). Hausa mai dubun hikima. Century Research and Publishing Company.

Galadanci, M. K. M., Yahaya. I. Y., Ɗangambo, A., Garba, M. M., Salim, B. A. da Ibrahim, S. M. (1990). Hausa don ƙananan makarantun sakandare 1. Longman Nigeria.

Galadanci, M. K. M. Yahaya. I. Y., Ɗangambo, A., Garba, M. M., Salim, B. A. da Ibrahim, S. M. (1992). Hausa don ƙananan makarantun sakandare 3. Longman Nigeria.

Gusau, S. M. (2002), Salihu Jankiɗi sarkin taushe. Baraka Press and Publisher.

Gusau, S. M. (2003). Jagoran nazarin waƙar baka. Benchmark Publishers.

Muhammad, U. A. (1989). Kwatanta jigon rubutaccen wasan kwaikwayo da wanda ba rubutacce ba. [Kundin Digiri na farko], Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Mukhtar, I. (2010). Introduction to stylistic theories, practice and criticisms. Usman Al-Amin Publishers.

Shu’aibu, M. (2013). Tasirin mazahabobin adabi kan tarken adabin Hausa. [Kundin Digiri na Uku], Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Umar, M. B. (1987). Dangantakar adabin baka da al’adun gargajiya. Triumph Publishing Company

Ɗiaomeng, S. (2013). Rubutaccen wasan kwaikwayo a rukunin adabin Hausa: Haɓakarsa da muhimmancinsa. Gidan Dabino Publishers.

Yahya, A. B. (2001) Salo asirin waƙa. Fisbas Media Serɓices.

Yahaya, I. Y. Zariya, M. S., Gusau, S. M. da ‘Yar’aduwa, T. M. (1992). Darussan Hausa don manyan makarantun sakandare 3. University Press.

’Yar’aduwa, T. M. (2007). Wasan kwaikwayo na Hausa nau’o’insa da sigoginsa. Usman Al-Amin Publishing Company.

’Yar’aduwa, T. M. (2008). Nazarin rubutaccen wasan kwaikwayo: Jagoran nazarin wasu littattafan wasan kwaikwayo. Usman Al-Amin Publishing Company.

Yobe Journal

Post a Comment

0 Comments