Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwaya Da Warwarar Jigon Wakar ‘Tabban Hakikan’ Ta Shehu Usmanu Danfodiyo

Citation: Dr. Ɗahiru ABDULƘADIR (2018). Ƙwaya Da Warwarar Jigon Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ Ta Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 6. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

ƘWAYA DA WARWARAR JIGON: WAƘAR ‘TABBAN HAƘIƘAN’ TA SHEHU USMANU ƊANFODIYO

Dr. Ɗahiru ABDULƘADIR

1.0 Gabatarwa

Waƙa wani sarrafaffen harshe ne mai tsari da dokoki na musamman da al’ummar Hausa take amfani da ita cikin hikima da basira ta yi wa kanta maganganu kan inganta rayuwarta. Ta haka ne waƙa ta zama kafa ce ta isar da saƙonni daban-daban da suka shafi yi da hani zuwa ga al’ummar Hausawa. A wannan takarda za a yi sharhin waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ wadda Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya rubuta a tsari na rubutacciyar waƙa wadda ake zaɓo kalmomi a daidaita sua tsara su cikin azanci bisa baiti-baiti tare da amsa-amo ta hanyar amfani da dabarun jawo hankalin mai sauraro don cim ma manufa.

1.1 Marubucin Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’

Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ne ya tsara wannan waƙa mai suna ‘Tabban Haƙiƙan’ kuma ana zaton ya yi wannan waƙa ne a Sifawa a cikin shekara ta 1809 yayin da ake gudanar da jihadi. Shehu Usmanu ya tsara waƙar cikin harshen Larabci, sannan ’yarsa Nana Asma’u ta fassara ta zuwa harshen Hausa. Daga bisani kuma ɗansa Malam Isan Kware, autan Shehu ya yi mata tahmisi a shekara ta 1832 (1247H.).

2.0 Taƙaitaccen Sharhin Jigon Waƙar

Waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ cike take cunkus da gargaɗi da tsoratarwa a kan wasu halaye da mutane suke yi a wannan lokaci. Gundarin jigo na wannan waƙa ta ‘tabban haƙiƙan’ shi ne neman mutane su daina ayyuka na assha, su tuba su dawo kan ayyukan salihai domin Allah ya yafe musu, su sami tsira a lahira.

2.1 Ƙwayar Jigo

Ƙwayar jigon wannan waƙa ta bayyana a baitit na 3 kamar haka:

3. Kui nazar ’yan’ uwa ku samu ku duba,

Don nasiha ku zam faɗi don muhibba,

Mui ta bin godabe mu tsere azaba,

Duk ku saurari za ni waƙa ku tuba,

Don ku samu ku tsira tabban haƙiƙan.

A nan Shehu Usmanu ya yi gargaɗi wa ’yan’uwa su dinga yin nasiha da faɗakarwa kan a dinga bin hanya madaidaiciya ta yadda za a iya kuɓuta daga fushin Allah da kuma azaba tasa. Mawallafin ya daɗa bayyana ƙwayar jigon waƙar na gargaɗi yana cewa:

4. Ko mutum ya zamo mutum mai muƙami,

Ko sarauta gare shi ko ko adimi,

Ko ganiyyi marowaci ko karimi,

Wanda bai girgiza ma Sarkin Musulmi,

Shi ka mutuwa ga jahalu tabban haƙiƙan.

5. Don ibadakka mai yawa wadda kay yi,

Ka zamo salihi na Allah waliyi,

Ko sani ag gare ka tari jaliyyi,

Wanda duk yaƙ ƙi bin hukunci da yay yi,

Ba shi hujja ga gobe tabban haƙiƙan.

Cikin waɗannan baitoci guda biyu Shehu Usmanu ya ja hankalin al’umma kan su girmama duk wanda Allah ya danƙa riƙon jama’a a hannunsa, musamman Sarakunan Musulunci. Kuma a karɓi hukunci da suka yi ba don halinsu ba, sai dai domin yin hakan bin umarni ne na Allahu, tabaraka wa ta’ala

Shi kuma Shugaban ana so ne ya kyautata wa jama’arsa don su amince masa ko ya sami tsira. Ga misali:

6. In fa ka zam Imamu to yo karimci,

Nai foron ka ya da hanyab bahilci,

Don ka samu ga ’yan’adam duka aminci,

Wanda yaz zamu Imamu yay yo adalci,

Shi da inwa ga gobe tabban haƙiƙan.

7. In daɗa ka zamo Imamun mutane,

To tsare alhakinsu balle ubanne,

Ka ji kyauta daɗa fa don kar ka ƙone,

Wanda yaz zam Imamu don cin mutane,

Shi wuta kan ci gobe tabban haƙiƙan.

11. Masu iko su ba da himma su kyauta,

Kun jiya masu ji daɗa kada ku ɓata,

Ba da tsanini garin biɗowab bukata,

Masu matsuwat talakka ko don sarauta,

Su ka matsuwa ga gobe tabban haƙiƙan.

2.2 Warwarar Jigon Waƙar ‘Tabban Haƙiƙa’

Tun a tashin farko a wannan waƙa, Shehu Usmanu ya yi kira ga shugabanni su zamo masu adalci, kuma yin haka a al’amuran iko da shi ne a wurin Allah za a iya samun rahamarsa. Amma dukkan shugabancin da aka gudanar bisa musguna wa mabiya, to, fa sakamakonsa azabar Allah.

Waƙar nan kuma ta ƙara fito mana da wata mummunar hanya da wasu kan bi domin su zama shugabanni. Ga abin da Shehu Usmanu yake faɗi:

8. Wanda duk yab biɗo ga rainai sarauta,

Don shi sam dukiya shi samo bijinta

Don shi kurɗa daɗa cikin masu cuta,

Masu aza dukiya garin ban sarauta,

Babu shakka su ƙuna tabban haƙiƙan.

A baitin nan da ya gabata an yi nuni na illar da ke tattare da neman shugabanci domin burin tara dukiya. Masu irin wannan ɗabi’a kuwa za su auka cikin ƙunar wuta.

Sannan Shehu Usmanu ya ci gaba da faɗakar da mu kan amsa kiran mai shara’a wanda abu ne na ibada. Ga abin da waɗannan baitoci suke nunawa.

16. In fa Alƙali yai kira zo ka karɓa,

Ƙin zuwa cana Jalla shi anka saɓa,

Kama hanya zuwa garai kar ka raɓa,

Wanda Alƙali yak kira yaƙ ƙi karɓa,

Shi wuta kan kiraya tabban haƙiƙan.

18. In fa Alƙali can cikin nashi hukumi,

Yaƙ ƙi bin godabe ku san ya yi zulmi,

Gobe can Lahira ana sa shi ƙuƙumi,

In fa Alƙali kul fa ya sake hukumi,

Kafira na da amdu tabban haƙiƙan.

Amsa kiran mai hukumci wato Alƙali a kowane matsayi wajibi ne. An kira mutum ne kuwa a matsayin wanda ake tuhuma ko mai ba da shaida. Irin wannan hukunci ba wai sai a ɗakunan da aka gina domin shari’a kawai ba, har da kwamitoci da a kan naɗa a makarantu da ma’aikatu don bin kadin waɗanda aka zalunta. Duk wanda ya ƙi amsa kiran mai shara’a to a gaskiya ba makawa zai shiga wuta.

Hakazalika duk mai hukunci da ya bi son ransa yayin gudanar da wani hukunci to azabar Allah na nan tana jiran sa. Tafarki madaidaici don yanke hukunci shi ne bin abin da Allah ya ce a yi ko a bari.

Har ila yau akwai nuni a kan tsare alƙawari da sanin matsayin ɗan’uwa mumini. Ga misali a waɗannan baitoci.

21. Wanda yak ka kwance alƙawari ya yi zambo,

Dud da mai rena mumini sai shi tuba,

Ya yi saɓo ina kamatai ku duba,

Mai fa bautad da ɗa shi shawo azaba,

Shi ka bautar wuta fa tabban haƙiƙan.

22. Masu cin kura kasuwa duk akwai su,

Wansu keri su kai su samo bukinsu

Wansu na nan ina faɗa ma kamassu,

Masu cin dukiya ta baital wasunsu,

Su wuta kan ci gobe tabban haƙiƙan.

Baitocin nan sun tabbatar da ƙin cika alƙawari laifi ne mai girma, haka maɗaukar ɗan’uwa mumini a bakin baza. Maganin wannan shi ne a tuba a gyara. Sannan ƙarin kuɗi cikin sha’anin kasuwanci laifi ne mai girma, haka kuma ƙarya ko cin dukiyar baitil-mali duka laifuka ne, azaba na nan jiran mai aikata su idan bai tuba ya daina ba.

Shehu Usmanu ya kalli daraja da matsayin mata sai bai bar su a gefe ba. Dangane da abubuwan da suka shafi mata Shehu Usmanu yana cewa:

38. Wansu can gobe za suna har lahira,

An ƙuƙumce su sun ƙi tun nan su gyara,

Su ka sha gobe can bugu har su ƙara,

Dud da matan da ke fita ba lalura,

Ba su tsira ga gobe tabban haƙiƙan.

39. Dud da kau mai matse adimi ga bashi,

Dud da kau mace wadda tat tar da kishi,

An yi foronta babu kyawo ta bar shi,

Hakana mace mai fa kwarcen kiyoshi,

Gobe ana zallata ta tabban haƙiƙan.

Dubi kuma wani gargaɗi da Shehu Usman ya yi a baitocin da suka gabata kan fitar mace daga gidan mijinta babu dalili da ya zama tilas, laifi ne babba, wanda zai kai ta ga shiga wutar sa’ira. Ashe ke nan gaskiyar masu azanci da sukan ce, darajar mace ɗakinta. Mawallafin wannan waƙa ƙarara ya nuna kishi ba shi da amfani don haka a guji yin sa, saɓanin haka kuwa za a iya saduwa da azabar Allah a ranar lahira.

Kuma Shehu Usmanu ya yi wani nuni a kan da illar da ke tattare da ƙwace da zalunci da kuma ɓoye ganima ta yaƙi kamar dai yadda yake ambatawa a baitocin da suke tafe kamar haka:                              

26. Lokacin nan na cin gari ba da zulmu,

Babu kyawo haƙiƙatan nan gare mu,

Wansu na nan suna ta yi nai cikinmu,

Masu ƙwace ma wanda yaf fara kamu,

Su wuta kan fa ƙwace tabban haƙiƙan.

27. Ba da ɓoyon fa dukiya babu shakki,

Ai ta yaƙi a kai ta duk inda Sarki,

Wansu na nan haƙiƙan masu tarki,

Masu hana airabo da khumsi ga yaƙi,

Su wuta ar rabon su tabban haƙiƙan.

28. Can ga yaƙi idan fa an sami sa’a,

Anka sam bai walau na nan nan a bai’a,

Wansu nan ba su bin tafarkin shari’a,

Masu zafi su faɗa bai ba bara’a,

Su ka faɗa wuta fa tabban haƙiƙan.

Waɗannan baitoci sun fito da illar fin ƙarfi, musamman a ƙwace abin da ɗan’uwa ya samu lokacin yaƙi. Haka nan ba ya bisa ƙa’ida mayaƙa kowa yai gamon kansa da duk dukiyar da ya samo lokacin yaƙi. Ballantana kuma mata waɗanda ake kamawa a ganimar yaƙi sai wasu su mayar da su nasu har su dinga faɗa musu ba su yi bara’a ba. Akwai tsayayyen tafarki na raba ganimar yaƙi bisa shari’a.

A waƙar, har wa yau, Shehu Usmanu ya taɓo al’amarin zama da iyali sannan da haƙƙin maƙwabtaka, yana faɗin:

36. Wanda bai tuba kun ji haƙƙan shi ƙuna,

Kun jiya wa’azu na ku zam yin fa sauna,

Kada ku ɓoye ma kowanne ko zuru na,

Hakana wanda yaƙ ƙi daidaita kwana,

Gobe ana karkace shi tabban haƙiƙan.

Wajibi ne ga duk mijin mata biyu ko abin da ya fi haka ya daidaita kwana a tsakaninsu. Duk wanda bai yi haka ba, ya yi zalunci, kuma ko shakka babu zai ɗanɗana azabar Allah. A baiti na gaba ya yi maganar sata kamar haka:

37. Wansu himmarsu ba su ci sai ga ƙwace,

Wansu ko na jirin a ɓoye su sace,

Wansu sata sukai suna nana ƙwace,

Masu ɗamre miji su ƙulla da kwarce,

Su akan ɗamre gobe tabban haƙiƙan.

Mujaddadi Shehu Usmanu ya nuna mana a cikin al’umma akwai waɗanda ke rawar ƙafa domin yin sata. Ba sa wani kazarkazar sai sun laluba sun ɗauke kayan wani da ya adana. Haka nan akan sami mata da kan sa mazansu cikin wani hali na cutarwa. Duka yin hakan ba shi da kyau. In an ƙi bari, to da ma Hausawa na cewa, ‘abin da aka shuka, shi ake gurba’.

Akwai kira na neman ilimi da Shehu Usmanu ya yi a cikin ƙarfafawa kuma ya tabbatar da shi ne ginshiƙin ci gaban rayuwa. Ga wani baiti da ya faɗa a kan haka:

31. Kui karatu zumai ku san tar da ilmi,

Shi ka ba ɗan’adam shi zam mai muƙami,

Kada ka zamna cikin waɗanda bas u san ta komi,

Masu ƙwace cikin ƙasaisan Musulunci,

Gobe za su zo wuta fa tabban haƙiƙan.

Wajibi mutum ya kasance yana neman ilimi kowane lokaci, ko kuma ya zama kusa da masani, amma kada ya yi nesa da su. Yin haka shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma. Shehu Usmanu kuma yana nanata kira a wurare daban-daban cikin waƙar kan abubuwan da yake zayyanawa a matsayin gargaɗi ga jama’a. Ya kuma ƙara jan hankali na mutane da a tubadomin Allah. Idan har an yi hakan, to za a sadu da rahamar Ubangiji, kamar dai yadda ya gabata cikin baiti na 46:

46. ’Yan’uwa na cika daɗa kun ji haƙƙan,

Don ku karɓa cikin zukatanku haƙƙan,

Gaskiya na faɗi ga nau kun ji haƙƙan,

Ya jama’a ku tuba don wanda haƙƙan,

Yay yi tuba shi tsiri tabban haƙiƙan.

3.0 Kammalawa

Kamar yadda bayanai suka gabata, awannan takarda an yi nazari ne na gundarin jigo na waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ ta Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, sannan aka kuma yi bayani na warwarar ƙananan saƙonnin da waƙar ta yi magana a kansu. Waƙar ta yi gargaɗi ne da nuni cikin faɗakarwa a kan dukkan dangogi na rayuwar mutum, Musulmi. Waƙar ta kawo yadda za a yi shugabanci da yanayin biya da zaman aure da na maƙwabtaka da illar zalunci. A waƙar, har wa yau, an nemi al’umma ta himmatu ga yin ilimi da sauran abubuwan da suka wajaba Musulmi ya nema.

An lura wannan waƙa cike take da baƙin kalmomi, musamman daga harshen Larabci da kuma ambaton nassoshin Alƙur’anida na hadisai. Haka kuma waƙa ce wadda ta farfaɗi tsagwaron hukunce-hukunce na shari’a na yi da bari da kuma sakamakon da za a samu idan an yi da abin da za a cim masa na azaba idan ba a yi ba.

Hakazalika, an fahimci idan aka yi aiki da darussan da wannan waƙa take koyarwa za a yi rayuwa mai sauƙi, ba tare da shiga cikin wata tsangwama ba. Sannan kuma za a sami albarkatun rayuwa ta kowane gefe na hidimomi na zamantakewar al’umma. Allah ya sa mu dace, mu yi gam-da-katar da sa’adar rayuwa,

MANAZARTA

Auta, A. L. (2017). Faɗakarwa a rubutattun waƙoƙin Hausa. Kano: Bayero        University Press.

Gusau, S.M. (2015). Mazhabobin ra’i da tarke a adabi da al’adu na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Junaidu, I, & ’Yar’aduwa, T.M. (2007). Harshe da adabin Hausa a kammale: don manyan makarantun sakandare. Ibadan: Spectrum Books Limited.

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar gadon feɗe waƙa (sabon tsari). Kano: K.D.G. Publishers.

Ɗangambo,A. (2008). Rabe-raben adabin Hausa (sabon tsari). Zaria: Amana Publishers Limited.

Mukhtar, Isa (2005). Bayanin rubutattun waƙoƙin Hausa. Abuja: Countryside Publishers Limited.

Sa’id, B. (2016). Rubutacciyar waƙar Hausa: ma’auninta da amsa-amonta da ire-irenta. Kano: Bayero University Press.

Yahya, A.B. (1997). Jigon nazarin waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Yobe Journal Volume 6, 2018

Post a Comment

0 Comments