Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudummawar Adabin Baka Wajen Bunkasar Shirye-Shiryen Gidan Rediyo: Nazarin Kwalliyar Magana A Cikin Shirin Inda Ranka Na Gidan Rediyon Freedom Fm 99.5 Kano

Citation: Dr. Abdullahi ASIRU (2018). Gudummawar Adabin Baka Wajen Bunƙasar Shirye-Shiryen Gidan Rediyo: Nazarin Kwalliyar Magana A Cikin Shirin “Inda Ranka Na Gidan Rediyon Freedom Fm 99.5 KanoYobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 6. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

GUDUMMAWAR ADABIN BAKA WAJEN BUNƘASAR SHIRYE-SHIRYEN GIDAN REDIYO: NAZARIN KWALLIYAR MAGANA A CIKIN SHIRIN “INDA RANKA NA GIDAN REDIYON FREEDOM FM 99.5 KANO

Dr. Abdullahi ASIRU

ABSTRACT

This paper examines the Rhetorics in “Inda Ranka” Programme of Freedom Radio 99.5 FM Kano. The paper focuses on the presenter’s usage of Hausa Rhetorics in conducting the programme. The Rhetorics employed in the programme includes: sarcasm, egocentrism incites, lampoon, praising, as well as exaggerations. The use of these Rhetoric serve as the main reason that makes the programme famous among the teaming listeners of the ‘Inda Ranka’ programme. Hence it also makes the media house the most popular in Kano and beyond.

1.0 Gabatarwa

Wannan takarda ta yi tsokaci ne a kan irin rawar da shirin “inda Ranka” na gidan rediyon (Fredom 99.5FM Kano) yake takawa. Wannan shiri ya ƙara wa gidan rediyon samun farin jini da karɓuwa ga jama’a a sakamakon yin amfani da kwalliyar magana. Wannan takarda ta bibiyi wasu daga cikin ire-iren waɗannan shirye-shirye domin fayyacewa.

Ire-iren kwalliyar maganar da aka duba sun haɗar da habaici da yabo da zuga da kirari da shaguɓe da zambo da koɗa kai da kambamawa.

1.1 Taƙaitaccen Tarihin Gidan Rediyo (Freedom 99.5 FM Kano)

Freedom muryar jama’a (Ɓoice of the people) wanda ya fara gudanar da ayyukansa na shirye-shirye a watan Disamba, 2003 da isassun kayan aiki na zamani da ƙwararrun ma’aikata. Ya kasance gidan rediyo mai zaman kansa na farko a jihar Kano da ke Arewacin Nijeriya da ya fara gudanar da shirye-shirye masu gamsarwa ga jama’a.

Gidan Rediyon (Freedom) ya fara gudanar da shirye-shirye da tasha ɗaya a Kano, sannan ya ƙara buɗe wata tashar a garin Dutse da ke Jihar Jigawa a shekarar (2007). Haka sun sake samun lasisin kafa wasu tashoshin har guda huɗu, wato na Sakkwato da Maiduguri da Dala FM Kano. Sannan an buɗe tashar Kaduna a shekarar 2012.

A cikin jajircewa da ƙwarewa wajen samun ingattattun labarai masu madogara, al’amuran yau da kullum da ƙirƙirarrun shirye-shirye masu ƙayatarwa ga jama’a. Haka sun ƙware wajen dabarun ilimantarwa ga ɗimbin masu sauraro. Lallai a yau gidan Rediyon Freedom ya kasance mafi shuhura a faɗin wuraren da ake sauraronsa.

Wannan tasha ta Rediyon Freedom tana da mahanga kamar haka, wato ta kasance wata kafa wacce ‘yan ƙasa za su samu damar faɗar ra’ayoyinsu, tare da bayyana tunaninsu da abin da zai kare daraja da ƙimarsu. Haka kuma manufar tashar Freedom ita ce ta kasance kafar yaɗa labarai mai zaman kanta da ciyar da haɗin kan ƙasa gaba, ta hanyar bawa marasa dama, samun damar ta hanyar shiriye-shiryenmu, masu ilimantarwa da ƙayatarwa ta hanyar da ta dace da manufa da kulawa da rashin tsoro da bin dokokin da tsarin mulkin ƙasa ya tanadar wa kafafen ya ɗa labarai, da sauran dokokin da suke taimaka wa wajen gudanar da ayyukan kafafen yaɗa labarai a Nijeriya, da kuma kai wa matuƙa wajen ciyar da aikin jarida gaba a faɗin wuraren da ake saurarunmu.

Tashar ta Rediyon Freedom tana da alamar tsuntsu, wato Aku. Aku dai wani fitacen tsuntsu ne wanda ya samo asali a Afrika da Asiya kuma sananne ne wajen haddacewa da maimata muryoyin da ya ji kuma wanda aka yabawa wajen shirya idanu da wayewa.

Freedom Rediyo sun zaɓi aku a matsayinn alamarsu, domin jaddada manufar ba da sahihin labarai, abubuwan da suke aukuwa da ke ara’ayoyin jama’a. Fitattun idanun da ke jikin aku suna nuni ne da hikima da balaga wajen yadda suke gudanar da shirye-shiryensu.

1.1.1 Tarihin Samuwar Shirin “Inda Ranka”

Shirin “Inda Ranka” yana ɗaya daga cikin shirye-shiryen Rediyon Freedom wanda miliyoyin al’ummar duniya suke sauraro. Jama'a da dama, suna nuna gamsuwa da sha’awar shirin. Kuma har ila yau shi ne shiri mafi karɓuwa da ya riƙe kambunsa, ta hanyar binciken aikin jarida da ilimantarwa tare da nishaɗantarwa. Kuma wannan shiri an fara shi ne tun farkon buɗe wannan gidan rediyon a shekarar (2003).

Jerin sunayen masu gabatar da shirin “Inda Ranka”:

i. Nasir Salisu Zango

ii. Ado Sa’idu Warawa

iii. Yusuf Ali Abdallah

iv. Yusuf Nadabo Isma’il

v. Ibrahim Abdullahi S/Ɗinki

vi. Abdullahi Isa

vii. Abubakar Tijjani Rabi’u

viii. Aminu Abdu Bakanoma

ix. Asma’u Mohd Sani

x. Shamsu Da’u Aliyu

1.2 Ma’anar Adabin Baka

Ɗangambo (2008) ya ce “Wannan kalmar adabi, kamar yadda aka sani, an aro ta ne daga Larabci ma’anrta ta aslai a Larabci ita ce “halin ɗa’a, fasaha, ƙwarewa”. To amma a harshen Hausa har ma a Larabci, wannan kalma tana nufin abubuwa da suka shafi al’ada da rayuwa da fasaha na al’umma, wani lokaci da kuma nazarinsu.

A taƙiace muna iya cewa adabi shi ne madubin ko hoton rayuwa ta al’umma wannan ya ƙunshi yadda al’adunsu ɗabi’unsu hashensu, halayyarsu, da abincinsu, tufafinsu, makwancinsu, hulɗarsu, tunaninsu da ra’ayoyinsu da sauran abubuwa da suka shafi dabarun zaman duniya don ci gaba da rayuwa”.

Zarruƙ da wasu (1987, sh. 12) sun bayyana kalmar adabi da cewa “Adabi dai kalmar Larabci ce mai bayyana fannin ilimi da fasahar rayuwar al’umma. Wato a nan za mu iya ganin cewa wannan matsayi na adabi ya yi kama da azancin Hausawa”.

1.2.1 Rassan Adabin Baka a Fannin Ilimi

Ɗangambo (1984, sh. 12) “ya kasa adabin Hausa zuwa gida biyu wato adabin gargajiya da adabin zamani.

Adabin gargajiya kamar yadda sunan ya nuna adabi ne da Hausawa suka gada daga kaka da kakanni. Kuma akan kira shi da adabin baka ko adabin ka. Saboda asalinsa ba a rubuce yake ba.

Adabin zamani kuwa shi ne kamar yadda sunan ya nuna , adabi ne da zamani ya kawo. Wannan adabin akan kira shi da rubutaccen adabi. Kuma ya rabu gida uku wato:

1) Rubutattun waƙoƙi

2) Rubutun zube

3) Rubutaccen wasan kwiakwayo.

Su ma Zarruƙ da wasu (1987, sh. 13) “sun bayana rabe-raben adabi kamar haka: “kowane ɗan’adam akwai irin baiwar da Allah ya yi masa a kan kowace harka ta rayuwa; na farko dai akwai waɗanda suke da baiwar iya shirya labari. Don haka zube wani ɓangare ne na rubutaccen adabi. Na biyu kuma shi ne baiwar iya waƙa. Na uku kuma shi ne rubutaccen wasan kwaikwayo”.

Saboda haka daga cikin rassan adabin baka da masana suke nazarta sun haɗa da:

i. Tatsuniya

ii. Labari

iii. Hikaya

iv. Tarihihi

v. Tarihi

vi. Waƙoƙi

a. Waƙoƙin baka

b. Waƙoƙin cikin tatsuniya

c. Waƙoƙin daka

d. Waƙoƙin reno

e. Waƙoƙinn bikin aure

vii. Karin magana

viii. Ba’a

ix. Zambo

x. Habaici

xi. Shaguɓe

xii. Kirari

xiii. da sauransu

 

 

1.3 Yanayin Aiwatar da Adabin Baka Cikin Shirin “Inda Ranka”

Ire-iren kwalliyar maganar da ake amfani da su a cikin wannan shirin domin jawo hankalin mai sauraro, sun haɗa da: habaici da yabo da zuga da zambo da koɗa-kai da shaguɓe da kirari da kambamawa.

1.3.1 Habaici

Haƙiƙa masana adabin baka sun bayana ma’anoni masu tarin yawa a kan habaici. Misali:

Ɗangambo (1984, sh. 42) ya ce, “Habaici, magana ce mai ɓoyayyiyar manufa, idan ba mutum ya san kan zancen ba, ba kasafai ake gane wanda akai habaicin dominsa ba”.

Shi kuma magaji (1980) ya ce “Habaici shi ne yi da mutum a ɓoye. A kan faɗi wasu kamannu ko kuma hali na mutum yadda daga ji za a fahimci ko da wa ake yi”.

Gusau (1979, sh. 80) ya ce “Habaici wasu maganganu ne da ake faɗa a fakaice don ɓata wa wani mutum rai ba tare da bayyana mutumin da ake nufin ɓata wa ƙuƙuru ba”.

Sau tari masu gabatar da shirin “Inda Ranka” suna sarrafa “habaici” ta sigogi da dama domin su jawo hankalin masu sauraro da ƙawata magangnaun da suka furta a cikinn shirin misali:

i) Shirin Ranar (26/08/2015)

“Mai rabon ganin baɗi dai ko ana dakawa a turmi sai ya gani”

“Wani jariri da ake zaton ɗan gaba da alfatiha ne da aka haifa ta ɓarauniyar hanya, kuma aka jefa shi a rijiya kuma dai an tsamo shi daga rijiyar garau da shi”.

A nan habaici shi ne: “mai rabon ganin baɗi ko ana dakawa a turmi sai ya gani

ii) Shirin Ranar (26/08/2016)

Kafin tafiyar ta yi nisa kuma tauraronsa ya fara dusashewa, Shugaban Hukumar Kula da Zirga – Zirgar Ababan Hawa (Kano Road Traffic Agency “KAROTA”) na Jihar Kano Mustapha Hamza Buhari Bakwana ya a jiye muƙaminsa. Giwa ta sha ƙasa, kafin tauraronsa ya fara dusashewa.

A nan Habaiciin shi ne:

a) Giwa ta sha ƙasa

b) Taurarunsa ya fara dusashewa

iii) Shirin rannar (28/08/2015)

Shugaban ya yi rantsuwar cewa: ƙalan sharri aka yi masa domin ɗaura masa jakar tsaba, aka yi domin bai wa kaji damar su bi shi.

Habaici shi ne:

a) An ɗaura masa jakar tsaba

iv) Shirin Ranar (28/08/2015)

Ɗankuka dai shi ne ke jawo wa uwatar jifa, yin wannan naushin da shugaban ya yi ne ya zamo masa hanyar yin adabo da mukaminsa.

A nan habaicin shi ne:

a) Ɗankuka shi ne ke jawo wa uwatar jifa.

v) Shirin ranar (28/08/2015)

Abin da ya ci Doma ba ya barin Awai, su ma dukkan daraktocin Hukumar Kula da Zirga – Zirgar Ababan Hawa (Kano Road Traffic Agency “KAROTA”) an sauya musu wajen aiki a wani yanayi na garambawul.

A nan habaicin shi ne:

a) Abin da ya ci Doma baya barin Awai

vi) Shirin Ranar (27-06-2017)

Gwamna ya umarci ‘yansiyasa dake da sha’awar zama a gwamnati cewa ko dai su zama masu haƙuri da jama’a ko kuma dai ungulu ta koma gidanta na tsamiya.

A nan habaici shi ne:

a) Ungulu ta koma gidanta na tsamiya.

vii) Shirin Ranar (08/12/2016)

Kotu ta ce su dakata, amma sun yi shakulatun ɓangaro da umarninta.

A nan habaicin shi ne:

“Shakulaton ɓangaro”

viii) Shirin Ranar (08/12/16)

Ganin buzu a masallaci ya isa tunkiya ta yi wa kanta ƙiyamullaili.

A yau ne dai kotu ta bayar da belin kwamishinan ƙasa da tsare-tsare na jihar Kano Malam Ibrahim B.B. Faruk.

A nan habaici shi ne:

Ganin buzu a maslalaci ya isa tunkiya ta yi wa kanta ƙiyamullaili.

ix) Shirin ranar (06/07/17)

Idan ajali ya yi kira, ko babu ciwo sai an amsa kira”. Wani Ɗankarota ya koma ga mahalicci bayan ya sha maganin gargajiya na basir.

A nan habaicin shi ne:

Idan ajali ya yi kira ko babu ciwo sai an amsa kiran.

x) Shirin Ranar (06/07/2017)

Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya tak aka ce wai ita ce ta mai kaya”. Wani matashi da ke yin sojan gona cewar wai shi danjarida ne har ma yake barazanar zai tona asiri ko a bashi kuɗi, ya shiga hannu?

A nan habaicin shi ne:

Rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya.

xi) Shirin Ranar (05/07/2015)

Sabo da yi, wai gawa da gatsine. Wani matashi ya gwada halinsa na sabo da yi, wai gawa da gatsine, saboda ya sibare wayar salula ta wani Ɗansanda da yake bincikensa a chaji ofis.

A nan habaici shi ne:

Sabo da yi gawa da gatsine”

xii) Shirin ranar (10/07/2017)

“Fatara mai tayar da tsohon bashi”. Tsofaffin kansilolin da aka sauke, sun tayar da bore, suna cewa a ba su fanshansu a huta.

A nan habaici shi ne:

Fatara mai tayar da tsohon bashi

xiii) Shirin Ranar (10/07/17)

“Hantsi dai ya dubi ludayi”. Tsofaffinn kansilolin sun nuna takaicin ƙin biyansu haƙƙoƙinsu, ga kuma yanzu hantsi ya dubi ludayi.

A nan habaici shi ne:

“hantsi ya dubi ludayi”

xiv) Shirin Ranar (04/07/17)

Karatun ta nutsu. Rundanar ‘yansandan Jihar Kano ta ƙara faɗaɗa hannunta na yin afuwa ga duk ɗandabar da ya yi karatun ta nutsu.

A nan habaici shi ne:

“Karatun ta nutsu” wato a daina aikin masha’a

xv) Shirin Ranar (04/07/2017)

Da walakin goro a miya. Ba wai haka kawai kamfanonin da aka zaɓa, su yi jigilar alhazai suke tsawwala farashin kujerun aikin hajjin ba, domin su ma sai sun bayar da toshiyar baki, nan da can.

A nan habaici shi ne:

“Da walakin goro a miya”

xvi) Shirin Ranar (05/01/2017)

Shan Koko dai ɗaukar rai. To amma wasu na ganin cewar wannan doka tamkar cin fuska ne ga masu riƙe da sarautun gargjaiya da kuma ƙoƙarin daƙile al’ada.

A nan habaici shi ne:

“Shan koko ɗaukar rai”

Wannan habaicin an yi wa Gwamnatin Kano ne saboda sanya dokar yi wa masu sarautun gargajiya ritaya.

1.3.2 Kirari

Manyan masana sun bayana kirari daidai fahimtarsu. Mislai “Zarruƙ da wasu (1987:50) sun bayyana kirari da cewa “shi kirari haka yake waƙa-waƙa magana,-magana. Sai dai ba waƙa ba saboda ba rangwaɗar da murya, shi kuma ba magana ba kara-zube ba saboda kama iya jin wani kari a cikinsa. Zarruk da Alhassan (1982, sh. 1) sun bayyana kirari da cewa “wani nau’i ne na fasahar shirya taƙaitacccen kwatance, wanda ya ƙunshi bayanin abubuwa ko halaye ko al’amura”.

Shi kuma Muhammad (2003, sh. 26) ya ce “kirari wata sarrafaffiyar magana ce wadda akan yi da baki dama kambama ko kururuta wata halitta ko wani abu, kuma kirari mutum zai iya yi wa kamsa ko ayi masa”.

Ɗanhausa (2012, sh. 13) ya ce “kirari wasu lafuzza ne da akan yi na hikima da nuna balagar kwarewar harshen mai magana domin mutum ya koda wani abu idan har buƙatar haka ta taso ko mutum ya koɗa kansa kamar yadda masu hikima kan ce “ɗanmagori” koɗa kanka da kanka”.

Kaɗan daga cikin ire-iren kirarin da suke amfani da su wajen yin kwalliyar da ƙawata shirye-sharyensu su ne:

i) Sirin Ranar (05/07/2017)

An yi amfani da kiraarin “yau take Laraba Tabawa ranar samu”.

“A kan yi irin wannan kirarin musamman ranar Laraba idan an zo gabatar da shirin misali “yau take Laraba Tabrawa ranar saamu”.

An yi amfani da kirarin ne domin nuna irin muhimmancin ranar ga al’umma wadda Bahaushe yake ƙaddarawa da idan an yi abu a ranar musamman na alheri to sai an ci nasara.

ii) Shirin Ranar (05/07/2017)

An yi amfani da kirarin “Bizi ba sata ba, sai dai idan mai abin ya gani ka ba shi abin sa.

An yi amfani da kirarin ne domin nuna yadda ƙwararrun ɓarayi ke yi wajen nuna ƙarfin hali da dakewar zuciya, idan an kama su da kayan sata.

iii) Shirin Ranar (30/08/2015) an yi amfani da kirari “zai zame maka jangwam”

“Ba ni da wasa wajen kawo rahoton da ka iya zame maka jangwam”.

A nan wani sojan gona ne ya ce wai shi ne Yusuf Ali Abdallah, ɗaya daga cikin masu kawo rahotonnin Gidan Rediyon (Freedom) ya shiga hannu.

iv) Shirin Ranar (05-09-2017)

An yi amfani da kirarin “wannan harka ce ta alwajudu”.

Kasancewar wannan harka ce ta alwajuuduu, sai ka ga alƙalai na bijirewa wannan umarnin da aka ba su.

A nan an nuna da cewa alƙalan na samun wani abu mai romo ne ya sanya ba sa bin umarnin da aka ba su.

1.3.3 Shaguɓe

A wajen ƙoƙarinn tayar da ma’anar shaguɓe an bibiyi mabambantan ra’ayoyin masana. Misali: Bargery (1993, sh. 922) ya bayyana shaguɓe da cewa “shi ne yi da mutum ko bayyana aibun mutum a gabansa, amma ba tare da kama suna ba, ko a ce shi ne jirwaye da kamar wanka”?

Shi kuma Ɗangambo (2012, sh. 20) ya bayyana shaguɓe da cewar: “shaguɓe wani hannunka mai sanda ne da akan yi wa jama’a tamkar gyara kayanka ne”.

i) Shirin Ranar (26/06/15)

An yi amfani da shaguɓen “Ɗan da aka haifa ta ɓarauninyar hanya”.

Wani jariri ne aka yar, da ake zaton an haifa ta ɓarauniyar hanya.

A nan an yi wannan shaguɓen ne domin nuna cewa dai wannan jariri ba ta hanyar sharia, wato hanyar aure aka haife shi ba, sai ta hanyar yin zina.

ii) Shirin Ranar (26/08/15)

An yi amfani da shaguɓen “abin fallasa da ya ta so ajiye muƙamin ba ya rasa nasaba da wani abin fallasa da ya ta so a Hukumar Kula da Zirga – Zirgar Ababan Hawa (Kano Road Traffic Agency “KAROTA”)”.

A nan an sakaya abin da ya faru a hukumar, amma an yi shaguɓen da sai wanda ya san kan wannan ne zai gane.

iii) Shirin Ranar (27/08/2017)

An yi amfani da shaguɓen “An yi masa karan tsaye”.

“Wannan matakan dai ya sanya (M.D) yana ganin cewar ai an yi masa karaan tsayee ne”.

A nan ana nuna an yi wa wannan (M.D) rashin kyautata wa.

iv) Shirin Ranar (30/08/2015)

“Wani mataashii ya yi basaja, yana cewar wai shi ɗanjarida ne”.

A nan an yi amfani da shaguɓen domin nuna irin aikin da wannan saurayin ya yi na sojan gona, yana ci da buguzum.

v) Shirin Ranar (06/07/2017)

An yi shaguɓen “Shiga su ga oga, su ga Madam”.

Shiga-su-ga-ogo-su-ga-madam

Su ga madam, su bayar da toshiyar baki nan da can, kafin samun amincewa, a ba su aikin jigilar alhazan.

An yi amfani da shaguɓen ne domin sakaya laifin da suke aikatawa, saboda hukuncin mai karɓɗaya ne da na mai bayarwa.

1.3.4 Zuga

A wajen yin bayanin zuga Ibrahim (2003, sh. 13) ya ce “makaɗa kan zuga sarakunan da suke yi wa waƙa su kai su inda Allah bai kai su ba. Har sukan ce Sarkinsu ya fi kowane sarki a ƙasashen Hausa. Ko kuma ma a cikin duniya duka”.

To shi ma mai gabatar da wannan shirin na “inda raka” yakan yi amfani da zuga domin cimma burinsa. Misali

i) Shirin Ranar (26/05/17). An yi amfnai da zugar “shi jiragensa ras suke”.

“Kamfanin Kabo ya ce jiragensa ras suke kuma an ba su damar ɗaukar alhazan bana”.

A nan an nuna cewa dai kamfanin ba shi da matsalar kayan aiki da ta ma’aikata. Kuma har ya sami amincewa daga gwamnati domin ya gudamar da aikin jigilar alhazai. A nan an zuga kamfanin zirga – zirgar jiragen kamfanin Kabo.

ii) Shirin Ranar (26/08/15). An yi amfani da zugar “halin shago”

Za a naɗa wa hukumar sabon shugaba, wanda ko ban faɗa ba, ba zai yi halin shago ba.

A nan ana nufin ba zai yi halin ‘yandambe ba, domin shahara da kwarewar shago a fagen damben gargajiya. An zuga sabon shugaban ne domin ana zaton ba zai yi halin na da ba.

iii) Shirin Ranar (26/08/2015). An sarrafa zugar “Ci gaba da gashi, tun da suya sai ran sallah”.

Muƙaddashin shugaban ƙasa ya tabbatar da cewa kai ne dai za ka ci gaba da gashin, tun da suya sai ran sallah. Wato Ibrahim Magu ne zai ci gaba da rikon Hukumar (EFCC) ya bayyana wannan ne a Kaduna lokacin buɗe sabon ofishin Hukumar.

iv) Shirin Ranar (26/08/2015). An sarrafa zugar “tayar da ƙayar baya”.

Kansilolin da suka sauka a watan jiya ne suka tayar da ƙayar baya. Wato suka fusata tare da nuna fushinsu a fili.

An nuna yaddda kansilolin suka fusata da nuna cewa lallai a biya musu buƙatunsu.

1.3.5 Yabo

A wajen ƙoƙarinn tayar da ma’anar yabo, Ibrahim (2003, sh. 9) ya ce “makaɗan sukan yabi sarakuna da iya mulki da riƙe addini, da rushe tsafi. Kuma sukan yabe su da jarumta.

Mai gabatar da wannan shirin na “Inda Ranka” ya ƙware wajen sarrafa yabo domin jawo, hankalin masu sauraron shirin. Misali:

i) Shirin Ranar (26/08/2017). An sarrafa yabon “abin nema ya samu”.

Al’amari mai kama da abin nema ya samu. Gwamna Ganduje ya yi na’am da wannan murabus da shugaban ya yi.

A nan, an nuna cewa daman gwamnati ta ƙosa da irin halinsa, kuma daman ko bai yi murabus ɗin ba, to ana gab da a yi masa.

ii) Shirin Ranar (30/08/2017). An sarrafa yabon “dirar mikiya”.

Hukumar tsaro ta farin kaya wato D.S.S. (D.S.S ma’ana Directorate of State Security Service) wato Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta yi wa wasu alƙalan kotun ƙoli biyu dirar miikiya a kwanakin baya.?

Note: i. wasu ba yabo ba ne

ii.a tantance yabo da adon magana a gani a fili.

1.3.6 Koɗa-kai

A wajen bayyana ma’anar koɗa-kai dai. Bargery (1993, sh. 917) ya ce: “koɗa-kai dai shi ne yabon kai”.

Haka shi ma Ibrahim (2003:19) ya ce “ a wajen koɗa kai ma makaɗan sarauta ba a bar su a baya ba. sau da yawa sukan wasa kansu da kansu a cikin waƙoƙinsu. Wani lokaci ma idan za su wasa kansu, sukan haɗa da na ubangidansu, su wasa tare.

To a cikinn wannan shiri ma na “Inda Ranka” mai gabatarwar yana yin amfani da irin wannan jigon. Misali:

i) Shirin Ranar (03/07/2017). An yi amfani da “koɗa-kai”.

Ɗanjarida kan fuskanci ƙalubale da samun kansa a halin tsaka mai wuya a lokacin gudanar da aikinsa.

A nan a nuna irin matsaloli da ‘yanjaridu kan gamu da su a lokacin aikinsu, amma sukan nuna juriya da sanin makamar aikin.

ii) Shirin Ranar (10/07/2017). An yi amfani da “Koɗa-kai”.

Salon yaƙin nan na shege ka fasa.

Salon yaƙin nan na shege ka fasan ya haifar da ɗa mai ido, domin har jama’ar gari sun gamsu da shi.

A nan an nuna cewa wannan salon yaƙin kwalliya ta biya kuɗin sabulu, domin irin nasarar da ake samu a wajen aiwatar da shi. Sannan da nuna babu sani balle sabo a lokacin da ake aiwatar da shi.

1.3.7 Kambamawa

Bargery (1993, sh. 544) ya bayyana wannan kalma da cewa: “kambamawa na nufinn haiba ko kwarjini ko girmama”.

Mai gabatar da shirin “Inda Ranka” yana amfani da wannan kambamawa domin jawo hankalin masu sauraron shirin, musamman domin ya zuzuta ko ya kwarzanta abu. Misali:

i) Shirin Ranar (26/08/2015). An yi amfani da “kambamawa” kamar haka:

Mutanen da iftilia’in bam ya ritsa da su, musamman ma harin bam ɗin babban masallacin Juma’a na Kano ne suka yi cincirindo a fadar Maimartaba Sarkin Kano, domin bayyana masa irin halin da suke ciki.

A nan kambamawar ita ce “iftila’i” da “cincirondo”. Ana nuna cewa babbar masifa ce ta same su. Haka kuma cincirindo yana nuna irin yawan al’ummar da ta taru a fadar.

ii) Shirin Ranar (26/08/2015). An yi amfani da kambamawa ta “har da wani ƙanƙanin yaro”

A cikinsu har da wani ƙanƙanin yaro, wanda ya

rasa idanuwansa duuka biyun da ƙafa ɗaya.

A nan an bayyana ƙanƙantar yaron ne tare da irin munin raunin da ya same shi.

iii) Shirin Ranar (24/12/2016). An yi amfani da ya yi facaka da binciken ƙwaƙwaf”.

Wani babban alƙali ya fuskanci tasgaro bayan da binciken ƙwaƙwaf ya gano cewar, a shekarar (2015) albashinsa Naira miliyan (24) ne kacal, amma cikin watanni (10) ya yi facaka da ta kai Naira miliyan (500).

A nan an yi amfani da kalmar maganar “facaka” domin nuna yadda ya kashe waɗannan zunzurutun kuɗaɗe sama da albashinsa. Sannan an yi amfani da binciken ƙwaƙwaf domin a nuna cewar lallai wannan binciken an yi ta gamsasshiyar hanya mai madogarar gaske.

iv) Shirin Ranar (12/12/17). An yi amfani da “ƙalubale” da halin “tsaka mai wuya”.

Sai dai dama ‘yanjarida kan fuskanci ƙalubalee da samun kansu a halin tsakaa mai wuya a wajen ɗauko rahootanni.

An yi amfani da wannan kambamawa ne domin a nuna yanayin da suke afkawa lokacin ɗauko rahotannin.

v) Shirin Ranar (05/01/2017). An yi amfani da ta kambamawar “dandazo wurin ya cika maƙil”

A hukumar yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa ta Jihar Kano dai daandazoo aka ganoo, kasancewar wurin yaa cika maaƙil da matasa”.

A nan an yi amfani da wannan ta “kambamawa” ne, domin a nuna cewar daandazon, ya nuna yawan al’umma. Haka maaƙil na nufin wurin dai ya cika babu masaka tsinke.

2.0 Kammalawa

Kamar yadda ya gabata, wannan takarda ta yi tsokaci ne a kan ire-iren kwalliyar maganar da mai gabatar da shirin “Inda Ranka” na gidan Rediyon Freedom 99.5FM Kano) yake amfani da su a wajen gabatar da wannan shirin. Haƙiƙa yin amfani da wannan kwallliyar maganganun yakau ƙawata shirin gaya. Kuma shirin yana daɗa samun farin jini da karɓuwa ga jama’ar da ke sauran gidan rediyon.

MANAZARTA

Bargery, G.P. (1993). A Hausa-English dictionary and English-Hausa ɓocabulary. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Gusau, S.M. (1979). Salihu jankiɗi da waƙoƙinnsa. Kano: Ƙungiyar Hausa, Jami’ar Bayero.

Ibrahim, S.M. (2003). Kowa ya sha kiɗa, abokin hira na 2. Lognman Nigeria Plc.

Muhammad, Y.M. (2003). Adabin Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-raben adabin Hausa da muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa Kano: Triumph Publishing Company.

Ɗangambo, A. (2008). Rabe-raben adabin Hausa (sabon tsari). Zaria: Amana Publishing Limited.

Ɗanhausa, A.M. (2012). Hausa maidubun hikima. Kano: Century Research and Publishers Company.

Zarrauƙ da wasu (1982). Sabuwar hanyar nazarinn Hausa don ƙananan makarantun sakandare littafi na I. Ibadan: Ibadan Uniɓerrsity Press.

Zaruƙ da Alhassan (1982). Kirarin duniya. Kano: Ganuwa Publishers 

 Yobe Journal Volume 6, 2018

Post a Comment

0 Comments