Ticker

6/recent/ticker-posts

Rikici a Masallacinmu Ya Ki Ci, Ya Ki Cinyewa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, rikici a masallacinmu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa: Yau a sauke wannan limamin, gobe a kawo wani, jibi shi ma a cire shi. Sannan gata a soke wannan kwamiti, citta a naɗa sabo, bayan kwana biyu shi ma a kawar da shi, a sake naɗa sabo! Wai meye mafita ne a irin wannan halin?

RIKICI A MASALLACINMU YA ƘI CI, YA ƘI CINYEWA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Kafin mu ji mafita a cikin wannan ya kamata mu gano tushen matsalar: A mafi yawan lokuta kwamitoci suna taimakawa wurin haifar da matsalolin da ke ruguza shugabanci da kyakkyawan jagoranci a masallatai.

Galibi ’yan kwamiti a masallatan Ahlus-Sunnah ba malamai ko ɗaliban ilimi ba ne, waɗansu ma ba Ahlus-Sunnah ba ne. Sun zama ’yan kwamiti ne kawai lura da irin matsayin su na alhazan birni ko manyan ’yan kasuwa ko tsofaffin ma’aikatan gwamnati. Ana tsammanin su masu kishin addini ne domin halartan sallolin jam’i, ko zama a wurin darussan da suke yi a masallacin wani lokaci.

Daga cikin abubuwan da sukan haifar da matsaloli a masallatan Ahlus-Sunnah a fahimtata akwai:

1. Wurin zaɓen limamin masallacin ba safai akan kula da ɗauko masanin Alƙur’ani da Sunnah a gaskiya ba. Galibi akan fi damuwa da wanda ake so ne, kamar ɗan dangi ko wanda zai yi biyayya ga ’yan kwamiti, wanda kuma kwamitin zai iya juya shi!

2. Akan bi wasu matakan da ba muhimmai ba a Shari’a a wurin tantance limaman! A kan kayar da wanda aka so domin wani abin da ba shikenan ba, kamar wanda ya kasa bayyana kansa sosai da Larabci, ko ya kasa isowa wurin tantancewar da wuri, ko ya kasa iya amsa wata tambaya ta Nahawu, ko kuma wanda ya kasa iya warware wata mas’ala ta Fiƙhu kamar a Babin Gado!!

3. Abubuwan da ake karantar da jama’a a masallaci sau tari ba sa yin daɗi ga shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya da su kansu ’yan kwamitin ma a wani lokaci. Don haka akan yi ƙoƙarin neman mai karatun ya sassauta, in ba haka ba kuma a ɗauki matakan tuɓe shi tare da limamin da ke goya masa baya.

4. Karatu mai rai da ake yi a masallatan Ahlus-Sunnah ba ya yiwuwa ya bi ra’ayin kowa, sai dai kowa ya bi shi. Ƙoƙarin neman matsakaiciyar hanyar bi a nan shi ke janyo a fara takun-saƙa a tsakanin mai karatun da mabiyansa a gefe ɗaya, da kuma ’yan kwamiti ko da liman ma a ɗaya gefen.

5. Yawancin manya a masallaci ba su samun halartan darussa akai-akai, don haka duk lokacin da aka so sanya wani abin da aka karanta a aiki sai su ƙi yarda, suna masu kafa hujja da cewa ba su san wannan abin ba! Har kuma wani lokaci su riƙa zargin mai karatun da zuwa da baƙin littaffan da ba a san su ba!!

6. Yawancin malamai ko ɗaliban ilimi masu karantarwa a masallatan Ahlus-Sunnah matasa ne masu zafin-kai da ɗimin ƙirji, kuma masu shaawar bin Sunnah sak! Saɓanin yawanci tsofaffi da dattawa masu neman a lallaɓa. Wannan shi ke kai matasan ga zargin manya da neman yi wa nassi karan-tsaye!

7. Akan samu zargi da gulma da ƙulla makirci da cin-dunduniyar juna a tsakanin malamai domin neman kuɗi ko gindin-zama ko matsayi da sauransu. Wannan kan janyo sa-in-sa a tsakanin manya, wanda hakan kan kai ga mummunan rikici, wani lokaci ma har da zubar da jini!

8. Rashin wata ƙwaƙƙwarar sanaa da liman ko malami ke dogara a kanta kan janyo su riƙa kallon ɗan abin sadaka da ake tarawa a masallaci. Daga baya idan sun samu matsala da wani ɗan kwamiti sai a fara zargin cin kuɗi tare da ƙoƙarin tuɓe liman ko malami ko ’yan kwamitin da suka mara musu!

9. Bambancin ra’ayin siyasa ko dai wani abu makamancin haka a tsakanin ’yan kwamiti, wanda kuma kan gangara har zuwa ga malamai da limamin masallacin, kan haifar da mummunar matsala, wani lokaci ma har ga sauran masu sallah a cikin masallacin.

10. A waɗansu lokuta rikicin masallacin Ahlus-Sunnah kan yi ƙamari har ya kai ga zuwa ofishin yan sanda ko fadojin sarakuna, waɗanda yawancinsu ke kallon malamai da limaman irin waɗannan masallatan a matsayin tsageru ’yan ta-da-zaune-tsaye. Shiyasa galibi zuwa wurinsu ba ya samar da mafita ta-dindindin.

MAFITA:

Domin samun mafita daga irin waɗannan matsalolin a fahimtata sai a ɗauki waɗannan matakan, in shaa’al Laah:

1.A cire son zuciya ko ra’ayi a wurin zaɓen limamin masallaci. A bi abin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce kawai:

« يَؤُمُّ الْقَوْمَ أَقْرَؤُهُمْ لِكِتَابِ اللَّهِ ، فَإِنْ كَانُوا فِى الْقِرَاءَةِ سَوَاءً فَأَعْلَمُهُمْ بِالسُّنَّةِ ، فَإِنْ كَانُوا فِى السُّنَّةِ سَوَاءً فَأَقْدَمُهُمْ هِجْرَةً ، فَإِنْ كَانُوا فِى الْهِجْرَةِ سَوَاءً فَأَقْدَمُهُمْ سِلْمًا »

Wanda zai yi wa mutane limanci shi ne wanda ya fi su karatun Alƙur’ani. Idan kuma sun zama daidai a karatun, sai wanda ya fi su sanin Sunnah. Idan kuma sun zama daidai a Sunnah, sai wanda ya riga su yin hijira. Idan kuma sun yi daidai a wurin hijira, sai wanda ya riga musulunta ko wanda ya fi girma a shekaru. (Sahih Muslim: 673)

2.A bi matakan adalci wurin bincike da gano zurfin hardar Alƙur’ani na ’yan takara. A saurari kyawun karatun kowannensu ko akasinsa a kan ƙaidojin Tajweed, da kuma yadda siffar tsarki da sallarsa ta yi kusa ko nesa da ta Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Sai kuma a binciki wani abu na ilimin Fiƙhun sallah daga kowannensu.

3. Limamin da aka zaɓe shi shugaba a cikin al’amarin sallah a amince kuma ya zama shi ne shugaba a cikin dukkan al’amuran da suka shafi shugabanci da gudanar da masallacin. Bai kamata a ɗora kwamiti ko wani daga ’yan kwamiti a sama da liman ba.

4. Sauran ’yan kwamiti su zama kamar ma taimaka ko mashawarta ne kawai ga Liman. Amma ba waɗanda suke da ƙarfin zama su tsige shi ba, domin kawai ya yi wani abin da ya kauce wa wata ƙaidar da wai suka shimfiɗa kafin a naɗa shi, wataƙila ma ba da saninsa ba!

5. Liman da ’yan kwamiti su zama suna da son gudanar masallacin a kan Sunnah, kuma ya zama kowannensu yana da sana’ar da take riƙe shi da iyalinsa, wadda kuma ba za ta hana shi sauke nauyin da ke kansa ba.

Domin samun kyakkyawan sakamako, ana iya sanya wa limami ko malami hanun-jari a cikin wata harkar kasuwanci ta halal domin kare mutuncinsa daga roƙo ko bara ko sa-ido a kan kuɗaɗen masallaci.

6. Liman ya zaɓo ladani ko ladanai da malaman da ya amince da su da sauran ma’aikata domin su taimaka masa wurin gudanar da harkokin masallaci, kamar sallah da karantarwa a cikin masallaci. Ana iya taimaka musu da ɗan kuɗin sanya mai a cikin abin hawa lokaci-bayan-lokaci.

7. Liman da mashawartansa su zama masu yin aiki da duk wata aya ko wani hadisin da masu karatu suka janyo, musamman waɗanda suka shafi masallacin da jagorancinsa da gudanar da shi. Wannan shi zai samar musu da alkhairi da albarka da haɗin-kai a cikin masallacinsu, in shaa’al Laah.

8. Ana iya ɗaukar matakan tuɓe liman ne kawai idan ya samu larurar da ta wajabta haka, kamar in ya haukace ko ya samu rashin lafiyar da ya hana shi iya gudanar da aikinsa na limanci ko karantarwa, ko kuma idan aka tabbatar ya aikata wani mummunan aikin fasiƙanci da ya wajabta hakan. Amma a yi shi a cikin mutuntawa da girmamawa, ba tare da shahartawa a cikin jamaa ba.

9. Liman da mashawartansa su tsara yadda za su riƙa tara taimako da gudunmawa daga masu hali daga cikin masallata ko ɗaliban da ake yi musu karatu ko darussa a masallaci. Daga baya a yi amfani da abin da aka tara wurin gyara masallacin da masallata da ɗalibai masu halartan masallacin.

10. Liman ya tabbatar ana yi wa jama’ar masallaci bayanin irin kuɗaɗen da ake tarawa da yadda ake kashe su dalla-dalla, domin kowa ya san inda kuɗaɗen da ake bayarwa suke tafiya. Babu laifi a ɓoye sunaye da abin da kowane ma’aikaci ke ɗauka, amma a adana bayanansa a ɓoye a cikin rajista.

Ina ganin bakin haka ya isa, in shaa’al Laah.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments