Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallah a Gida

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Limamin masallacin da yake zuwa sallah ba ya natsuwa a cikin sallar, shi kuma gidansa yana da nisa daga masallacin, kuma yana fama da matsalar ƙafa. To wai ko waɗannan matsalolin sun isa hujja a kan ya riƙa yin sallah a gida?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah:

A gaskiya saboda Allaah! Ba su isa ba, saboda dalilai kamar haka:

1. Sallah a cikin jama’a wajiba ce a kan kowane musulmi namiji baligi mai lafiya, wanda kuma ya ji kiran sallar. Wannan ita ce mazhabar Hanaabilah kuma ita ce daidai, in shaa’al Laah. Saɓanin Hanafiyyah da Maalikiyyah da suke ganin ita Sunnah ce mu’akkadah kawai, ko kuma Shaafi’iyyah da suke ganin ita farali ce ta kifaayah kaɗai, ko kuma Zaahiriyyah da suka zaƙe har suka ɗauke ta a matsayin sharaɗi ga ingancin sallar!

2. Sallar Tsoro da Allaah ya wajabta wa musulmin da suka fita jihadi domin kare addini cewa su yi ta a cikin jama’a, duk kuwa da tsananin da suke ciki:

وَإِذَا كُنتَ فِيهِمْ فَأَقَمْتَ لَهُمُ الصَّلَاةَ فَلْتَقُمْ طَائِفَةٌ مِّنْهُم مَّعَكَ وَلْيَأْخُذُوا أَسْلِحَتَهُمْ فَإِذَا سَجَدُوا فَلْيَكُونُوا مِن وَرَائِكُمْ وَلْتَأْتِ طَائِفَةٌ أُخْرَىٰ لَمْ يُصَلُّوا فَلْيُصَلُّوا مَعَكَ وَلْيَأْخُذُوا حِذْرَهُمْ وَأَسْلِحَتَهُمْ وَدَّ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْ تَغْفُلُونَ عَنْ أَسْلِحَتِكُمْ وَأَمْتِعَتِكُمْ فَيَمِيلُونَ عَلَيْكُم مَّيْلَةً وَاحِدَةً وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إِن كَانَ بِكُمْ أَذًى مِّن مَّطَرٍ أَوْ كُنتُم مَّرْضَىٰ أَن تَضَعُوا أَسْلِحَتَكُمْ وَخُذُوا حِذْرَكُمْ إِنَّ اللَّهَ أَعَدَّ لِلْكَافِرِينَ عَذَابًا مُّهِينًا

Kuma idan ka kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su ta tsaya tare da kai, kuma sai su riƙe makamansu. Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga bayanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tare da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makamansu. Waɗanda suka kafirta sun yi gũrin da dai kuna shagala daga makamanku da kayanku domin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma babu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, ko kuwa kun kasance masu jinya ga ku ajiye makamanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Ya yi tattali, ga kafirai, azaba mai walakantarwa. (Surah An-Nisaa: 102).

Wannan shi ne babban dalili a kan wajibcin jam’in a kan duk wanda yake zaune a cikin gari lafiya lau. Sannan idan da sallar jam’in Sunnah ce kawai da bai farlanta wa mujahidai da suke cikin halin firgici da rashin natsuwa ba. Kuma in da farilla ta kifaya ce kaɗai da bai wajabta ta a kan jama’a ta biyu a cikin sallar tsoron ba.

3. Hadisin makahon da ya nemi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya sama masa sassaucin yin sallah a gida. (Sahih Muslim: 653).

Idan dai har makaho mara ɗan-jagora zai rasa samun sassaucin yin sallah a gida daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), to ina kuma ga mai matsala a ƙafa kawai a irin waɗannan zamunnan na ƙarshen zamani?!

4. Babu ranar da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya taɓa zama bai yi sallah a cikin jama’a ba, har a lokacin rashin lafiyarsa na ajali! (Sahih Al-Bukhaariy: 687).

Shiyasa manyan malamai daga cikin Sahabbai irinsu Ibn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) yake cewa:

مَنْ سَرَّهُ أَنْ يَلْقَى اللَّهَ غَدًا مُسْلِمًا فَلْيُحَافِظْ عَلَى هَؤُلاَءِ الصَّلَوَاتِ حَيْثُ يُنَادَى بِهِنَّ فَإِنَّ اللَّهَ شَرَعَ لِنَبِيِّكُمْ -صلى الله عليه وسلم- سُنَنَ الْهُدَى وَإِنَّهُنَّ مِنْ سُنَنِ الْهُدَى وَلَوْ أَنَّكُمْ صَلَّيْتُمْ فِى بُيُوتِكُمْ كَمَا يُصَلِّى هَذَا الْمُتَخَلِّفُ فِى بَيْتِهِ لَتَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ وَلَوْ تَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ لَضَلَلْتُمْ وَمَا مِنْ رَجُلٍ يَتَطَهَّرُ فَيُحْسِنُ الطُّهُورَ ثُمَّ يَعْمِدُ إِلَى مَسْجِدٍ مِنْ هَذِهِ الْمَسَاجِدِ إِلاَّ كَتَبَ اللَّهُ لَهُ بِكُلِّ خَطْوَةٍ يَخْطُوهَا حَسَنَةً وَيَرْفَعُهُ بِهَا دَرَجَةً وَيَحُطُّ عَنْهُ بِهَا سَيِّئَةً وَلَقَدْ رَأَيْتُنَا وَمَا يَتَخَلَّفُ عَنْهَا إِلاَّ مُنَافِقٌ مَعْلُومُ النِّفَاقِ وَلَقَدْ كَانَ الرَّجُلُ يُؤْتَى بِهِ يُهَادَى بَيْنَ الرَّجُلَيْنِ حَتَّى يُقَامَ فِى الصَّفِّ.

Duk wanda yake sha’awar ya haɗu da Allaah gobe a halin yana musulmi, to ya kiyaye a kan waɗannan sallolin a duk inda aka yi kiran sallarsu. Domin Allaah Ta’aala ya shar’anta wa Annabinku (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) Sunnonin Shiriya, kuma su ɗin suna daga cikin Sunnonin Shiriya. To idan da kun tsaya yin sallah a cikin gidajenku kamar yadda wannan da yake ƙin zuwa jamin yake yin sallar a cikin gidansa, to da kuwa kun bar Sunnar Annabinku. Idan kuma da kun bar Sunnar Annabinku, to da kuwa kun ɓace. Babu wanda zai yi tsarki, kuma ya kyautata tsarkin sannan ya taka da nufin zuwa ɗaya daga cikin waɗannan masallatan, face Allaah ya rubuta masa lada da kowace takawa da yake yi, ya ɗaga masa daraja da ita, kuma ya kankare masasa laifi da ita. Haƙiƙa! Na gan mu (a zamanin Sahabbai), babu mai ƙin zuwa sallar jami sai dai munafukin da kowa ya san munafuncinsa. Kuma haƙiƙa! Ya kasance ana rungumo mutum (mara lafiya) a tsakanin mazaje biyu, har sai an tsayar da shi a cikin sahu. (Sahih Muslim: 654).

A cikin riwaya sahihiya da ke cikin Sunan Abi-Daawud: 550, ya ce:

وَلَوْ تَرَكْتُمْ سُنَّةَ نَبِيِّكُمْ -صلى الله عليه وسلم- لَكَفَرْتُمْ

Idan kuma da kun bar Sunnar Annabinku (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) to da kuwa kun kafirce!

Wannan kuwa shi ya fi tsananin wurin razanarwa.

5. Rashin natsuwar liman shi ta shafa, saboda hadisin Abu-Hurairah wanda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa a cikinsa cewa:

« يُصَلُّونَ لَكُمْ ، فَإِنْ أَصَابُوا فَلَكُمْ ، وَإِنْ أَخْطَئُوا فَلَكُمْ وَعَلَيْهِمْ »

Limamai suna yi muku sallah, to idan suka dace da daidai kun haye. Idan kuwa suka kuskure wa daidai, to kun haye su kuma sun nutse. (Sahih Al-Bukhaariy: 694).

A ƙarshe dai abubuwan da malamai suka ambaci cewa yana iya hana mutum zuwa jamin sallah a masallaci sun haɗa da:

• Rashin jin kiran Sallah saboda nisan inda ya ke daga masallaci.

• Idan ladan ya ce: ‘Ku yi sallah a gida’, saboda sanyi ko ruwan sama.

• Larura mai tsanani, kamar ta rashin lafiya ko rashin kyawun hanya domin ruwa.

• Samuwar abincin da yake sha’awarsa.

• Matsuwa ta buƙatar kewayawa. (Mausuuatul Fiƙhiyyah: 2/217-220).

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments